Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 32 Hausa Novel

Ta fice ba tare da ta saurari amsarshi ba.Tana fitowa daga dakin ustaphan ta tarar da Anti Binta a parlor tana ta jijjiga Hammad, tun kafin ta karasa wajensu tace ‘Yunwa yake ji, zo ki bashi ya sha.’Ta karbeshi ta shige dakinta Anti Binta tana biye da ita. Haka ta daure ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro har ta gama bashi nono suna hira da Anti Binta. Sai da ya sha ya koshi sannan ta mikawa Anti Binta shi tana cewa ‘Gashi Anti Binta, bandaki nake son shiga.’Ta karbeshi ta mike tana cewa ‘To muna can dakin yara muna hira da mutuniyata.’Ta fice ta ja mata kofa sannan ta mike ta shige bandakin don ta san idan dai tana cikin dakin nan wani sai ya zo nemanta, idan kuma ta rufe da mukulli za ayi ta fama tambaya. Tana shiga bandakin ta turo kofar ta jingina a jikin kofar, take hawayen da take rikewa suka kwace kamar an kunna famfo. Ta hada tafukan hannayenta ta rufe fuskarta tana jijjiga kai, saboda tsabar takurar da zuciyarta tayi har wani daci take ji a bakinta. Yaushe Mustapha ya raina ta haka? Wannan ma ya fi karfin raina ya koma wulakanci. To me yasa yayi mata haka? Daman can baya sonta ne ko kuwa son da yake mata ne ya kare? Bata taba tunanin zata auri miji ta zauna ita kadai ba amma dai ta dauka idan ka auri mutum zai cigaba da girmamaka yana ganin mutuncinka har karshen tarayyarku. A halin yanzu ta rasa wanne zatayi; murna ta haihu itama ta sami yaro ko kuwa jaje zata yiwa kanta tunda ko babu komai wannan yaron da ta haifa zai karawa alakarta da Mustapha tsawon rai. Bata san tsawon lokacin da zata iya dauka tana jure wulakanci irin wannan da Mustapha yake mata ba, amma dai ta san tabbas ba zata iya jurewa har abada ba. Gashi shi ba dukanta yake ko zagi ba, wani irin wulakanci ne yake mata yana nuna cewa komai normal ne, kuma a mafi yawancin lokuta ma idan tayi magana sai a dinga nuna mata haka maza suke. Domin kowa ce mata kawai yake idan dai namiji ne bata ga komai ba. Ta barwa Allah al’amarinta kuma zata jira su tare ta ga yanda yanayin zaman zai kama; amma tabbas idan aka cigaba a haka bata jin zata iya zama da Mustapha.zuwa yanzu kuma duk wasu alamu sun nuna mata cewa ba zai taba yi mata adalci ba ita da Naja, kamar ma dai yanzu ne yayi aure na soyayya wanda yake sa ran zai more rayuwarsa a ciki; tunda ta gama yi musu wahala ta raini yaransa lokacin da suke tsananin bukatar uwa. Yanzu sun girma sun zama mutane don haka sai ya aure wadda yake so ta zo su more rayuwarsu ita kuma a mayar da ita samiyar ware.A hankali ta zame a jikin kofar ta zauna ta sake fashewa da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta bawa kanta hakuri ta wanko fuskarta ta fito daga bandakin.……..Duk yanda take cikin damuwa da zarar Mustapha yana waje to sai ta shiga walwalarta da yara, yayinda shi kuma duk wasu shirye-shiryensa na tarbar amarya ne. har ta kai baya iya boye murnarsa; shi da yara kullum hirarsu ta Anti Naja ce. Musamman Afaf wadda zuwa yanzu kusan gaisuwa ce kawai take hadata da Khadeeja.Lafiya suka tare a sabon gida kuma kamar yanda ta zabi dakin sama haka ya hakura ya bata dakin saman; duk da daga baya yayi nadamar hakan. Domin da ace ya san ta riga ta san da maganat aurensa to da tabbas zai gaya mata amarya zai saka a sama. Sai dai a lokacin tunaninsa bata san da maganar auren ba kuma boye mata yake son ya cigaba da yi.Tsaf ta gyara dakinta da parlor, dakin su Afaf kuwa tunda taga ra’ayoyinta suna cin karo na da Afaf kuma tana nema tayi mata rashin kunya sai ta hakura. Sosai dakinta yayi kyau, ta tsara musu komai nasu ita da Hammad, don Baffanta ma da Mommy sai da suka kara mata kudi tayi sayayya.Sati yana zagayowa kuma aka shiga hidimar bikinsa.Babu yanda bata yi da Mustapha ba a kan ita bata so ayi mata taro amma ya ki amincewa; domin yace Hajia tace dangi basu san sabon gida ba don haka zasu zo su karbi amarya sannan suga gida.……..Tun dare ta sanar da shi cewa idan gari ya waye zata bi ‘yan makaranta taje gida wajen Mommy, kuma ba tare da wani musu ba ya amsa.Bayan ya kai ‘yan makaranta ya dawo suka zauna tare a parlor din sama suna cin abinci yayinda Hammad yake hannun Rashida. Shiru suke cin abincin babu wanda yake magana, kamar ma dai basa cikin walwala.Ya ajiye cokalin dake hannunsa yace ‘Kin ce babu wani abu da kuke bukata saboda taryar baki ko?’Ba tare da ta daina cin abncinta ba tace ‘Eh. Ni kam mai ai don dai ka hana ne da sai nayi tafiyata wajen Mommy idan aka kawota aka tafi sai na dawo da daddare ko ma da safe.’‘No, don Allah ki bar wannan maganar. Ai ya kamata dai ace a samu a karbi bakin nan cikin mutunci.’‘Um.’Suka cigaba da cin abincinsu, jimawa kadan yace ‘Hajia ma tace a nan zasu zo suyi biki ranar lahadin, in ya so sai su tsaya su karbi amarya sannan su tafi.’Ta kalleshi suka hada ido sannan ta kawar da kanta, wani malolo ya zo ya toare mata makogoro; su Hajia zasuyi biki a nan? Saboda suna murna za ayi mata kishiya ko me? Ta dauki kofin shayinia mai zafi ta kurba da fatan zafin shayin zai tafiyar mata da abinda ya tokare mata makogoro amma hakan bai samu ba. Ta kalleshi a jigace tace ‘Ka ga shikenan sai na tafi gidan Mommy ko? Tunda ka ga masu karbar amarya zasu zo.’Ya dan zaro ido yana cewa ‘Haba dai! Hakan kuma ai bai yi tsari ba, kina matar gida kuma azo biki gidan ba kya nan. Ko ba haka ba ma kin san Hajia zata ga kamar kin rainata ne shi yasa zaki tafi ki barsu su kadai suyi bikin. Please kiyi hakuri kawai saboda kada abun ya zama wata fitna kuma. Kin ji?’Ta daga kai tana cewa ‘Uh.’‘Yauwa, please kiyi hakuri a gama taron nan ba tare da wata matsala ba.’Tayi gajeran murmushi tace ‘In sha Allah.’Ya ture kwanon bayan ya kurbe dan ragowar shayinsa sannan yace ‘Zan saka miki kudi a account dinki saboda na san zaki iya bukatar wani abun ko don baki. Akwai ruwa da lemo wanda zan kawo, abincin kuma dama tunda kika ce ba zaki yi a nan ba na bayar da kudin don haka su Hajia zasu taho da shi.’‘Ok.’‘Idan kuma da bukata zaki iya yin wani abincin a nan ko da kadan ne.’‘Ok, babu damuwa.’Ya mike ya shige dakin domin ya karasa shiryawa. Nan take itama ta ture kwanon indomie din ta mike ta haye sama. Kuka take son tayi ko zata ji sanyi a ranta, amma bata so ta bata lokaci musamman da yake yana jiranta kuma tare zasu fita.Haka tayi sauri ta shirya suka sauko tare, ta karbi Hammad a wajen Anti Binta suka fice suka bar Anti Binta Hafsu wadda kanwar Rashida ce aka kawo mata bayan an yi auren Rashidan tun kafin ta haifi Hammad.Haka suka zauna a mota babu wanda yake magana da dan uwansa; ya riga ya kula da yanda take nema ta tayar masa da fitna a wajen bikin nan amma ba zai barta ba. Sosai ya ji dadi da Hajia tace zasu zo nan suyi biki don baya so ta bayar da matsala idan an kawo amarya, amma ya san tunda Hajia tana nan babu wata matsala da zata basu. Haka yaje ya ajiyeta a gidansu sannan ya wuce.………Tana shiga gidan ta sami Ahmad a parlor yana shan shayi; nan da nan ya mike ya karbi Hammad daga hannunta.‘Ina Mommy?’ ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar da yake mata.‘Tana dakin Baffa.’Ba tare da ta bashi amsa ba ta bar masa Hammad ta wuce ta nufi dakin.A zaune ta hango Mommy a kan dadduma ta mike kafa da waya a hannunta, ta jefar da mayafinta ta karasa gaba daya ta fada jikin Mommy ta rushe da kuka.‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Khadeeja me ya faru? Ina Hammad din?’ Mommy ta tambaya cikin tashin hankali.Da kyar ta bude baki tace ‘Yana hannun Ahmad.’Ita kanta saida taji ajiyar zuciyar da Mommy din tayi, sanna ta cigaba ‘To me ya faru kike wannan kukan haka? Ko Mustaphan sakinki yayi ne?’

Back to top button