Na mammy kabeer
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 49/50
_______________Tashi Adeeb yayi cikin nutsuwa, da takunsa irin na jaruman maza ,ya nufi ɗakin da fattu ke ciki.
Fattu na zaune abakin gado, tayi shiru kamar mai tunanin wani abu,Adeeb ya turo ƙofar da sallama ɗauke abakinsa,saidai idan ba ka kasa kunne ba ,to bazakaji me yake faɗi ba.
Dago Kai fattu tayi jin muryar Adeeb datayi,baki buɗe take kallon Adeeb ,tunda take arayuwarta,zata iya cewa bata taɓa ganin mutum mai kyau irin na Adeeb ba .”masha Allah”fattu ta faɗa tana mai mikewa tsaye fuskarta ɗauke da murmushi,ta ƙure Adeeb da ido kamar yau ta taɓa ganinsa.
Ƙarasowa Adeeb yayi cikin ɗakin,shima idonsa na kanta ,dan haka kawai yaga tayi masa kyau shima .
Ɗan harararta yayi kafin yace ” Please karki cinyeni da kallo mana”ya faɗa yana ɗan wani gwabe fuska cikin shagwabar da baisan yayi ba.
Da sauri fattu ta sanya hannu tare da rufe fuskarta tana ɗan dariya ,dan kunya taji da yadda yayi salon maganar tasa.
“Hamma kayi kyau sosai ,kai mai kyaune” fattu ta faɗa kanta a ƙasa tana ɗan mirza hannunta.
Wani irin sanyi ne yake ratsa zuciyar Adeeb, sosai yaji daɗin maganar fattu ,dan haka cikin wani irin shauƙi ya mika hannunsa tare da dago habarta .kallon juna suke ido cikin ido,murmushi Adeeb yayi kafin yace “kin tabbata nayi kyau a idonki?wankana yayi miki kyau?” Ya faɗa yana mai kallon lips ɗin fattu ,wanda yake ji kamar ya cinyesu.
Lumshe ido fattu tayi tare da jinjina kai tace ” Hamma bantaɓa ganin mutum mai kyan ka ba,kuma Ni kullum ma kyau kakemin” ta faɗa tana ɗan riƙe lips ɗin ta na ƙasa da haƙoranta.
Wani irin abu Adeeb yaji yana masa yawo ajikinsa,sosai yake jin yana son rungumar fattu ajikinsa ,duk lokacin da yake tare da ita yakan tsinci kansa cikin wani irin shauƙin son kasancewa da ita .
Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskarta yace ” to me zaki bani matsayin kyautar dazan fita gurin taro da ita?” Ya faɗa idanunsa akan lips ɗin ta.
Shiru fattu tayi tana ɗan rarraba ido,to ita me take dashi ma ?dazata ba Hamma?
“Hamma Ni bani da komai fa ,bansan me zan baka ba.
Karanta Littafin>>> Tsintsacciya Hausa Novel Document
Kallonta yake baya ko ƙiftawa ,ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin ” shikenan tunda ba abinda zaki bani,zan tafi,amma karki fito ko ina kinji?ki kwanta kiyi barci da zaran mun tashi daga gurin taro zanzo in ganki “Adeeb ya faɗa yana mai kallon fuskarta.
Jinjina kai fattu tayi tana mai kallon Adeeb ɗin,sai taji bataji daɗi ba ,ace ya tambaye ta wani abu ita kuma bata bashi ba,kuma duk abinda take dashi ma ai shine ya siya mata,to mezata bashi?fattu ta faɗa cikin zuciyarta ,fuskarta ɗauke da yanayin damuwa.
Ahankali Adeeb ya fara takawa zuwa bakin ƙofar fita daga ɗakin haka kawai yake jinsa wani iri, sam baya don rabuwa da fattu yau ɗin nan.ganin yana neman fita yasa Fattu ta tako da sauri tare da rungumeshi ta baya.
Dammm!dammmmm!!dammmm!!!gaban Adeeb ya bada wani sauti na bugawa.
Cikin hanzari ya runtse idanunsa,dan yadda yaji fattun ajikinsa ,abin yazo masa cikin bazata.
“Hamma kayi haƙuri wllh bani da abinda zan baka ,amma indai na tara kuɗina zan siya maka cin-cin burodi,nima baffa ke siyomin idan yaje gari, ka fadi abinda kake so nayi maka yanzun” ta faɗa tana mai gyara kanta dake kwance tsakiyar bayan Adeeb.
Cikin dauriya da jarumta Adeeb ya sanya hannunsa ya jawo fattu zuwa gabansa.bude idanunsa yayi dasuka fara rinewa sai wani lumshewa da budewa yake .
Ido ya ƙura mata na wani lokaci,kafin ya matso da fuskarsa zuwa gareta,ta yadda numfashinsa ke sauka akan Tata fuskar.
“Kin amince Ni na ɗauki Abinda nake ganin yayi amatsayin kyauta ta ” Adeeb ya faɗa cikin voice ɗinsa mai kama da yana mata raɗa.
Da sauri fattu ta gyada kanta ,dan yadda yayi maganar saiya sata jin wani iri atare da ita.
Karanta Littafin>>> Matar Hariji Page 51-60 Hot Romantic Hausa Novel
Lips ɗinta Adeeb ya kalla cike da tsantsar son jinsu cikin bakinsa.bai jira komai ba ya ɗora nasa lips ɗin nata.
Gaba ɗayansu sun shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ,cikin salo da narkar da zuciyar mace Adeeb ke kissing fattu ,yayi da ita kuma take jin abin da yake mata har cikin ranta.idonsu alumshe yake sun lula wata duniyar ,dan tuni Adeeb ya mance da batun taro ,ya sami lips ɗin fattu kamar ya sami lollipop.
Bugun da akeyiwa ƙofar ne yasa Adeeb saurin dawowa cikin hayyacinsa,ahankali ya zare lips ɗin sa daga bakin fattu yana kallonta .har lokacin idanunta alumshe suke ,sai sauke numfashi take cikin sauri,jikinta yana bari.
Bakin gado Adeeb ya zaunar da ita,tare da shafa gefen fuskarta yace ” wannan ma ya isheni nishaɗi har agama taron ,antee sururi Hulwa” Adeeb ya faɗa yana mai juyawa ya bar ɗakin.
Saƙare fattu ta zauna abakin gadon kamar wata butumbutumi,haƙiƙa tana jin Hamma har cikin ranta,wani irin shauƙi takeji game dashi,sannan ko kaɗan bata jin damuwa idan tana tare dashi,lallai Hammanta shine farin cikinta,ga shi aduk lokacin da Hamman nata ke sha mata baki tanajin wani irin nishaɗi sosai,ko me yasa ma yake sha mata bakin oho?
Murmushi tayi tare da shafa lips ɗin ta ,tanaji kamar har yanzu hamman na shan lips ɗin nata.
Taro yayi taro ta ko ina ka ƙalla jama’ane Malik a haɗaɗden dakin taron dake cikin masarautar,abie na zaune kan wata kyakykyawar kujera ta zinare, yayinda Adeeb ke gefensa shima zaune kan wata kujera mai shegen kyau da ɗaukar hankali.
Gaba ɗaya yan gidansu Adeeb suna zaune kan kujeru masu kyau,sai baki sarakuna da matayensu,kowa kagani yayi ado na kece raini,
Yan mata sai kaiwa Adeeb hari suke da idanuwansu da jikinsu, amma ba wacce ta ishe shi kallo acikinsu.
Anata jawabai da taya abie murnar dawowar ɗansa bayan tsawon lokaci da aka dauka ana nemansa.
Ammi na zaune ita da tawagarta,yayinda gimbiya suhaimat ke kusa da ita ,sai sauran baƙinta, hakama amma na zaune tare da Tata tawagar cikin ado mai kyau.wata matace zaune agefenta tana ɗan kallon ammi,kafin ta juyo da kallonta ga amma tace ” Dole saikinyi da gaske kafin ki gama da matar can,makircin ta yayi yawa,ina tsoron kaidinta”
Kallon ammi itama amma keyi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace ” karki damu Maryam,ninasan ta inda zan bullowa al’amarin nan,akwai Abinda ke ɗauremin kai sosai,game da gimbiya suhaimat,
ina don gano asalin gaskiyar abin kafin nayiwa ammi kwaf ɗaya,amma zanyi bincike sosai akan lamarin.
“Shikenan zan ci gaba da baki goyon baya ,Abdul lokacin da kike buƙatar taimakona ƙofa abude take” cewar matar.
Godiya amma tayi mata cikin murmushi,
Nan dai suka ci gaba da tattauna akan yadda zasu ga bayan ammi.
Rashad na hango zaune cikin wani kaya masu kyau irin na sarauta,fuskarsa ɗauke da murmushi,ya kafe Adeeb da ido baya ko kiftawa.wayarsace tayi ƙara dan haka ya ɗauka tare da karawa akunnensa, har lokacin idonsa na kan Adeeb,wanda shima hankalinsa yayo kan Rashad ɗin,kallonsa yake cike da tsana, tun lokacin da ya zaune yake kallon Rashad ɗin yana kula da duk wani motsinsa.
Dan kwata-kwata zuciyarsa bata yarda da Rashad ɗin ba,gani yake kamar akwai wani makircin da yake ƙullawa.
Dan haka ya sa tareeƙ ya kula da Rashad sosai.
Karanta Littafin>>> Yaro Ne Page 11-20 Hausa Novel
“Ya kamata fa kaje ka aiwatar da abinda zakayi, kafin lokaci ya ƙure ” ammi ta faɗa tana ɗan kallon gefen da Rashad ke zaune,waya kange akunnenta,da alam ita ta kira Rashad ɗin.
Wata dariya Rashad yayi kafin yace ” ammina ta kaina ,ina sane da lokaci,yanzu zan tashi domin cike burina, yau saina hana Adeeb barci da irin aika -aikar da zanyi masa” Rashad ya faɗa idanunsa ƙur akan Adeeb, wanda ya Dan rangwafo kusa da mai martaba ,da alama suna magana ne.
Kashe wayar ammi tayi tare da sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi,kafin ta kalli gimbiya suhaimat tace ” Ni kuwa suhaimat ina wannan sarƙar taku ta ahali, bana gajiya da kallonta ko kaɗan ,naga banganta atare da ke ba” ammi ta faɗa tana mai kallon gimbiya suhaimat.
Murmushi matar tayi kafin tace ” har abada bazan taɓa rabuwa da wannan sarƙar ba,dan kuwa itace shaidar dazata sadani da ƴata, Aduk inda take,ina ji ajikina mun kusa haduwa da juna kuma nayi alƙawarin saina ɗauki fansar rabani da ita da akayi na tsawon shekaru,akan koma waye keda hannu cikin al’amarin ” ta faɗa idanunta cike da kwallah.kafin ta ɗan daga mayafin jikinta ,saiga sarƙar ta bayyana ,ƙurawa sarƙar idanu ammi tayi,tabbas wannan irin sarƙar wuyan yarinyar can ce ,hakan na nufin fattu itace ɗiyar suhaimat da suka rasa shekarun baya?innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.banga ta zama ba. Cewar ammi cikin zuciyarta.
Da sauri ta miƙe tana mai faɗin “suhaimat ina zuwa “bata jira amsar taba tayi gaba.
Rashad ma ganin ammi ta mike yayi saurin bin bayanta dan zuwa ga fattu,yau kam za’ayi ta ta ƙare.
Zulaihat dake zaune cikin ƙawayenta tana ta zuba izza da iyawa ,ganin su duka biyun sunyi waje hakan yasa itama ta mike cikin sauri ta rufa musu baya, dan kuwa tare zasu aikata mugun nufin nasu akan fattu, tana son ganin komai ya wakana akan idonta ,
Download>>> Kufan Wuta Hausa Novel By Safiya Huguma
Ko ina zasu kuma oho?
Muje zuwa masu karatu,
Manage please har yanzu muna cike da alhini.
Na gode sosai da addu’ar ku garemu,waɗanda suka kirani,da waɗanda sukayi min ta waya.
🙏🙏
Anty mammy ce
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.