Novel Document

Fansar Fatalwa Complete Novel Download Pdf

Fansar Fatalwa Complete Novel By Shamsiyya 6

Description/Story:

Fansar Fatalwa! Complete Hausa Novel Document Written By Shamsiyya Manga

 

Description

GARIN GIWA

Ba wanda ya san abun da yake faruwa da Amrah ɗin a can gidan nasu, sai dai kafin wani lokaci wasu daga cikin tsirarun ƴan garin sun fara cin karo da videon inda kan kace kwabo har video ya fara yawo a cikin garin tunin rabin ƴan garin sun samu ganin wannan videon rashin kunyar na Amrah domin kuwa har waɗanda basu da waya ma sai da suka ga videon wannan nunawa wannan wannan nunawa wancan haka aka rinƙa fasin-fasin da videon inda magana ta shiga tashi a cikin garin irin ƙananan maganar nan,da yawa take suka shiga yin Allah wadai da wannan halin da Amrah ɗin ta ɗakko,inda wasu kuma suka shiga yin Allah ya ƙara daman ai shi Malam Kabiru laifin shine ba ya dage sai ƴar shi tayi karatu ba,to ai ga irin ta nan tun ba a je ko ina ba ta janyo mishi abun kunya. Wasu kuma cewa suka yi daman kwaɗayin abun duniya ne da kuma son duniya ya sanya shi har ya kai ƴar shi makaranta wata uwa duniya, cikin waɗanda suke waɗannan maganganun hadda manyan abokanan Malam Kabiru ɗin,waɗanda lokacin da suka samu labarin cewar Malam Kabiru zai tura ƴar shi karatu jami’a sun same shi sun bashi shawara akan kar ya kaita ɗin inda suka nuna mishi illar hakan amma sai baiyi amfani da shawarar ta su ba,abun da ba a fiye yi a garin ba shine a kai yarinya makarantar gaba da secondary, yawancin yara daga secondary school an musu aure.

Da yawa daga cikin masu maganar sun fi ganin laifin Malam Kabiru akan laifin Amrah domin kuwa cewa suke da ace bai kai Amrah ɗin makarantar ba da duk haka bata faru ba, sai dai bakin alƙalami ya riga da ya bushe ƙaddara ta riga fata!.

Haka dai kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa kan kace mai duk wani alkhairin Malam Kabiru ya disashe a idon mutane inda aka shiga jifan shi da munanan maganganu saɓanin da da duk wanda zai buɗi baki ya faɗi magana a kan Malam Kabiru ɗin to alkhairi ne zai biyo ba, daga shi har iyalan shi ba wanda yake da wani mummunan aibu a idon mutane, amma gashi yau an wayi gari mutane sun buɗawa idon su toka sun manta da waye Malam Kabiru a wajen mutanen garin dalilin abun kunyar da aka ci karo dashi na ƴar shi.

Malam Kabiru ne ya fito daga cikin rumfar ƙofar ɗakin nashi,sanye yake cikin babbar riga wanda kana gani shi ka san mutum ne mai cike da dattako da kamala.

Buta ya ɗauka a wajen randa inda ya nufi bayi domin kama ruwa kasancewar lokacin sallahr Azhar ya ƙarato.

Bayan ya fito daga bayin ne ya tarar da Gwaggo Sa’adatu tsaye a bakin rumfa tana jiran shi hannun ta riƙe da asuwaki, tana ganin fitowar tashi tayi saurin ƙarasawa ta karɓi butar hannun shi sannan ta kai mishi wajen alawla sai da ta miƙa mishi asuwakin ya fara yi domin kuwa hakan yana daga cikin al’adar shi in dai zai alawla to sai yayi asuwaki haka bayan ya kammalla ma.

Ɗan rusunawa Gwaggo Sa’adatu tayi ɗin kafin daga bisani tace.

“Malam dan Allah ko zan iya cewa wani abu?”.

Zama Malam Kabiru yayi akan dutsen da yake alawlar kafin ya dube ta yace.

“To Shikennan kiyi maganar ki Allah dai ya sa ba doguwar magana bace ba”.

“Malam yau ɗin ne naga kamar wani abu yana ɗan damun ka?, Allah dai yasa lafiya”.

Dogon numfashi Malam Kabiru ɗin ya ja sannan yace.

“Bakomai, amma idan na dawo daga massallaci zamu yi magana”.

Ya faɗa sannan ya cigaba da yin asuwakin.

Bayan ya kammalla asuwakin ne ya fara gabatar da alawlar cikin nutsuwa ya idar da alawlar sannan ya yi addu’ar bayan idar da alawla tare da ɗaga hannun sama yayi addu’a sannan ya tashi tare da duban Gwaggo Sa’adatu yace.

“To ni zan fita sai kuma Allah yayi dawowar mu”.

“To Shikennan Malam a dawo lafiya”.

Sa kai yayi tare da ficewa a cikin gidan sai dai mai yana fita ya ji massallacin da yake jan su Sallah har an fara ƙiran sallar, ko kaɗan malam Kabiru bai kawo komai a ranshi ba ya cigaba da nufar masallacin a tunanin shi yayi lattin fitowa ne shiyasa wani ya karɓi limancin duk kuwa da cewar wannan shine karo na farko da hakan ta taɓa faruwa.

Sai dai mai! Tun daga lokacin da ya fito daga cikin gidan nashi ya lura da cewar duk indai ya wuce majalisar mutane sai ya ga ana nuna shi ana ƴan maganganu ta ƙasa-ƙasa. Ƙarin wani abun mamakin ma shine duk inda ya wuce ya musu sallama sai ya ga ana ɗauke kai ana sunkuyar da kai ƙasa, saɓanin da da idan ya nufo majalisar mutane ma tun daga nesa za’a fara ɗaga mishi hannu ana gaisheshi cikin girmamawa.

Kan Malam Kabiru ne ya ɗaure ganin baƙon al’amarin da yake cin karo da shi ɗin,haka dai ya daure ya ƙarasa cikin massallacin amma zuciyar shi tana raya mishi wani abu yana shirin faruwa.

Wasu mutane ya gani tsaye daga gefen masallacin sun idar da alawla suna jiran a yi ƙiran shiga salla su shiga cikin massallacin.

Ɗaya daga cikin mutane aminin Malam Kabiru ne ƙut da ƙut tare suka taso, sannan kuma shine wanda ya ƙira salla a yau ɗin.

Da sallama ɗauke a bakin Malam Kabiru ɗin ya ƙarasa wajen mutanen sannan ya miƙa musu hannu yana cewa.

“Malam Ɗalha sannun ku dai, da alamu yau nayi lattin fitowa sallar nag……”.

 

File Name   Fansar Fatalwa… Hausa Novel Doc.
Title    Fansar Fatalwa
Author    Shamsiyya Manga
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Horrors Story
Published Date    09/06/2024
File Size    400Kb
Format Size    TXT
Phone No
Download Fansar Fatalwa Complete Novel Document By Shamsiyya Manga

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button