Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 37 Hausa Novel

Bata dade da kwanciya ba kuwa bacci ya dauketa saboda dama na jiya ba isarta yayi ba. Kamar a mafarki taji ana buga mata kofa, tayi firgigit ta bude ido. Ko ba a gaya mata ba ta san wannan bugun Habib ne don haka ta tashi zaune ta janyo wayarta ta duba lokaci; 8:25am. Ta janyo zanin goyon Hammad dake kusa ta rufe jikinta sanna tace ‘Shigo Habib.’Ya turo kofar ya shigo da sallama, tun kafin ta gama amsa sallamar tasa yace ‘Anti yau makara kika yi ne? Yanzu har past 8 fa kinga bamu tafi makaranta ba.’‘To me yasa baki tafi ba, ni ai na zata kun tafi tuni.’ Ya karasa ya zauna a bakin gadon da mamaki a fuskarsa yana cewa ‘Anti baki tashemu ba fa; nima bayan mun dawo daga masallaci da Abba har nayi wanka fa na dan kwanta don na san zaki tasheni shine bacci ya kwasheni. Su Afaf ma gasu can ko sallah ma basu yi ba sai yanzu na taso su har Hafsan.’Ta kama haba tana cewa ‘Ikon Allah. To ai ba nice da girki ba Habib, Antin ku ce. Itace zata tashi kowa ta shirya shi yasa ma ka ga ban fito ba.’Ya tabe baki yana zare ido ‘Tab, to ai kuwa daga ita har Abban babu wanda ya fito.’‘To Allah ya sa dai lafiya, kaje ka buga musu kofa. Ka murda kofar parlor din a bude take sai ka kwankwasa dakin kaji.’Ya mike ya fice daga dakin yayinda ita kuma ta zame ta gyara kwanciyarta da niyyar komawa bacci. …… A tsakiyar parlor din Habib yaci karo da Abban nashi yana fitowa da gaggawa, suka hadu a tsakiya suka yi cirkocirko. Abban nasu yace ‘Kai Habib meye haka? Na cewa Anti ku taso ni idan kun shirya me yasa baku taso ni ba? Kai ko uniform ma baka saka ba.’Yace ‘Abba ai makara muka yi, Anti Najan bata tashemu mun shirya ba.”Kafin ya bashi amsa sauran yaran suka shigo kowa da kayan bacci, ya kallesu sannan ya mayar da hankalinsa kan Habib din yana cewa ‘Wace Anti Naja kuma, ko dai Anti Khadeeja?’‘To ai itama Antin bacci takeyi yanzu naje tashinta tace min ba itace da girki ba Anti Naja ce zata shirya mu.’Mamaki ya kama shi; ya za ayi Khadeeja ta gayawa yaro wannan maganar? Wane irin wulakanci ne bayan itace ta saba shirya yaran kawai kuma yanzu sai tace Naja ce zata shiryasu?Ba tare da yace komai ba ya wuce yaran ya nufi dakin Khadeejan. Habib ya dubi ‘yanuwansa yace ‘Yau dai mun yi mising school, ni yunwa nake ji ma kuzo muje kasa bread yana can ko shayi sai mu hada.’Ya wuce suka bi shi suka sauka kasa.Kusan a fusace ya tura kofar, hangota da yayi a kwance tana bacci ya kara harzuka shi. Sautin bude kofar ne ya farkar da Hammad daga bacci. Ta tashi zaune tana mittsike ido sanna ta mika hannu ta daukeshi. Ta dubi Mustapha cikin halin ko in kula tace ‘Ohhh! Abba ka tayar min da yaro yanzu babu sauran bacci.’Ta daga shi yayi mika sannan ta saka masa nono yayinda Mustaphan yake cewa ‘Me ya faru naga baki tashi kin shirya yara ba bayan yau akwai makaranta, kuma fa ko da asuba sai da na ce miki idan sun shirya kice suyi min magana?’Tace ‘Oh! Ai basu zo sun ce min sun shirya ba na zata ma sun gaya maka kun wuce sai da Habib ya gaya min yanzu sannan na sani.’‘Ban gane ba, wai wace magana kike yi ne? to me yasa baki tashi kin shirya su ba?’‘Oh to ai wadda take da kwana itace da gida musamman ma da yake ni ina jego. Na zata da kai mata kwanan ka gaya mata abinda aka saba yi na running gidan.’Mamakin da yake fuskarsa ya karu ya hade da takaicin Khadeeja, yace ‘Ban gane wadda take da kwana itace take da gida ba Khadeeja. Ke kika saba shirya yaran nan kullum kuma kin san haka, shine yau saboda ganin ido zaki ce ita zata shiryasu? Idan kina jin haushina ai sai ki gaya min tunda ba dole nayi miki kika bar mata kwanan ba ko? Zaki fara wulakancin naki ko Khadeeja?’Tayi dariyar yake tace ‘Wallahi ni duk ban gane ba. Ai ni a yanda na sani duk matar da take da kwana da girki itace take duk wata harka ta kula da gida, nima idan na karbi girki sai na hada gaba daya nayi.’‘Khadeeja, bana son wulakanci. Yaran nan a hannunki suke kuma da ke suka saba, ya za ayi tana zuwa ki dora mata kula dasu ita da yau zata koma aiki.’‘Amma dai ba dasu na zo ba a nan na samesu ko? Kuma idan ban manta ba nima daga zuwana aka hada ni da su, kamar ma ita an daga mata kafa. Hidimarsu ta makaranta ma wadda ta riga ta saba yi tun ma kafin ta auri ubansu balle yanzu da ta aureka, ai inaga wannan ma karamin abune.’Ya gama kulewa har wani huci yake, ya cije lebe sannan yace ‘Khadeeja bana son wulakancinki fa, yanzu me kike nufi da yaran nan?’‘Alkhairi nake nufi da kowa, kawai dai duk wadda take da kwana ta hada duk har gidan da yaran ta kula da su. Shikenan.’Har ya juya zai fita ya juyo ya nuna ta da yatsa yana cewa ‘Yanzu shikenan kintura mata yara har tsawon sati hudu?’Ta dago ta kalleshi cikin halin ko in kula tana cewa ‘Na tura mata mijin ma?’‘Mtsewww!’ ya ja dogon tsaki ya fice ya maka mata kofar.Tayi ‘yar dariya ta cigaba da wasa da Hammad.……..Har ya koma dakin tana kwance tana baccinta domin office din da zata ta riga tace sai wajen sha daya zata tafi saboda an canza mata branch sakamakon aurensu da Mustapha; ta san tunda yau zata fara reporting tana da damar makara. A hankali ya bude kofar ya shiga saboda kada ya tasheta daga bacci, ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yana shafa fuskar, gaba daya kansa ya kulle. Yayi zaton yaran nan tunda suna wajen Khadeeja shikenan a wajenta zasu cigaba da zamansu ko da ya kara aure. Gaba daya ma shi bai taba zama sun yi maganar yara da Naja ba, kawai dai yana sakata hidimarsu idan ta kama kuma yana nuna mata cewa yana so su sami kulawar da yake jin sun rasa daga wajenta. Baya jin zata bashi matsala saboda yanda yaga tana kulawa da su tun ma kafin ta aureshi balle yanzu da zata yi da hujja.Ya juya ya dan tabata. Ta bude ido ta kalleshi tayi murmushi sannan tayi mika. Tace ‘Honey har ka dawo?’Ya dan kawar da kai sanna yace ‘Daga ina?’‘Umm! Na zata ‘yan makaranta ka kai.’‘No, ban kaisu ba sun riga sun makara sosai sai gobe.’‘Ok, Allah ya kaimu.’Ta zuro kafafunta kasan gadon ta kwanta a kafadarsa tana cewa ‘Bari naje na yi wanka sai na fito na hada mana breakfast. Ina jin ma kawai sai na shirya ka bani lift.’Yace ‘Ai kuwa sai kiyi sauri don ga yara can ma ke suke jira ki zo ki bamu abincin gaba daya.’Ta daga kafadarsa ta dan kalli fuskarsa da mamaki ‘Antin bata nan ne?’Ya kawar da kai daga kallon da ta kafeshi da shi, yace ‘Tana nan. To ai kin ga kece da kwana don haka kece zaki dinga yin baimcin duka gida kina kula da yara, in ya so idan ta karbi kwana sai ta cigaba. Duk wadda take da kwana itace da gida.’Ta sake leka fuskarsa da mamaki a kan fuskarta tace ‘Ban gane ba, ai ni ban karbi girki ba, kwana ne kace ka tambayeta ta bamu har tayi arba’in. kuma yara ai na zata tunda a wajenta suke sai suyi zamansu duk abinda ya kama ai zan saka hannu.’‘A’a, wadda take da kwana itace zata dinga hadawa tayi komai kawai. Kiyi sauri kiyi wankan ki zo ki bamu abinci.’Shiru tayi kawai tana binshi da kallo. Jimawa kadan ya kalleta suka hada ido, ya gyara zama ya kama hannuwanta duka biyun ya rike sanna yace ‘Kin ga wannan fa ba wani abun damuwa bane, ai dama kin san duk inda ake da mace sama da daya ai dama duk wata hidima rabawa ake yi. Idan yanzu kika ki yin wani abu ai sai ki janyo kwanan amarcin ya kare tunda kin ga dole ne na koma kan tsarin kwana bibbiyu don tabbatarwa an yi adalci ko?’Ta sunkuyar da kai tana kallon kasa don gaskiya ita bata zata haka ba; ba wai ba zata kular masa da yara ba amma dai ta sa rai zasu yi zamansu a wajen uwarsu itace zata dinga hidimarsu ta kullum in ya so ita duk wanda yazo inda take a cikinsu zata yi masa duk wani abu da ya kama.Ta dago ta kalleshi tace ‘To yanzu kenan duk wadda take da kwana itace zata dinga tashi tana yiwa yara komai?’Ya daga mata kai alamar e.‘To idan zani aiki fa.’Ya kama habarta ya dago fuskarta, suka hada ido yayi mata murmushi sannan yace ‘Ki bari wannan a hankali zamu ga yanda za ayi.’Ta dan ja baya zata tashi, ya rike fukarta ya sake tsareta da ido har saida tayi murmushi, ya sumabi lebenta sannan ya mike yana cewa ‘Muna kasa muna jiranki ni da yara.’‘Ok.’ Ta amsa sannan ta shige bandaki.Ya tashi yafito daga dakin.

Back to top button