Halysaah Page 99 By Khaleesat Haydar
Washegari da safe yaran Mama Zubaida kanana suka shigo parlor da gudu suna sanar ma Nenne manyan motoci har hudu suna kofar gida wai a bude masu gate za su shigo, Nenne ta kalli su Aunty Murja da wata hamshakiyar makociyarsu na nan Tudun Yola dake zaune parlon, makociyar tasu me suna Hajiya Zaliha tace “To a bude masu gate din mana” Nenne dai sai zazzare ido take, can tace “Ina Parida?” Aunty Murja tace “Tana kitchen kamar” Da sauri Nenne ta mike ta nufi kitchen din ta samu Aunty Farida da Mama Shatu sun gama dama kunu a babban bokiti dan ko break fast ba ayi ba, Mama Zubaida da Sha’awa da wata makociyarsu na can Mariri kuma na backyard din kitchen din suna ta suyan kosai, Nenne na gwala ido ta tsaya kusa da Aunty Farida tayi kasa da murya tace “Ke Parida kin ji wai su Munzali suka shigo yanzu suke cewa ga can manyan motaci a waje suna jiran a bude masu get din gidan nan su shigo, su shigo su mana me? anya la fiya kuwa Parida? Ko aika su aka yi su kwashe mu?” Aunty Farida tayi shiru tana kallon Nenne da mamaki ita ma jin abinda take gaya mata, can tace “Bari inje in ga su waye tukunna Fita tayi daga kitchen din Nenne ta bi bayanta da sauri, sai da Aunty Farida ta dauko gyale sannan ta fita waje, nan ta tarar da Labibah ta shigo daga kafar gidan ita ma taje ganin matocin, Labibah tace “Wai kaya za su shigo da Nenne da duk ta gama tsurewa tace “Kayan me kuma? Labibah ta zauna Balcony tace “Oho” Aunty Farida dai ta nufi gate din gidan ta bude ta fita, gaisawa tayi da mutumin dake tsaye shi kadai jikin motar farko, don motoci ne hudu a jere kofar gidan kuma duk manyan motoci, mutumin na kallonta with calmness yace “Sunana Mukhtar, daga masarautan Bauchi muke, kaya ne za a sauke, ban san ko ba a sanar maku da zuwan mu ba Aunty Farida tace “Ачча, sannun ku da zuwa, bari a bude gidan Daga haka ta juya ta koma ciki, su Labibah ta sa su bude gate din bayan Nenne ta dubo makulli don duk makullan na wajenta dama, daya bayan daya duk motocin suka shiga compound din suka yi parking don akwai enough space, ita dai Aunty Farida na tsaye Nenne ma ta yafo tsadadden mayafinta ta fito ta tsaya tana kallon ikon Allah, Aunty Murja ma Nenne ta dauko mata hijab din Aunty Farida gogagge har kasa ta bata ta saka ita da wata er uwarsu, Hajiya Zaliha ma ta fito duk suna tsaye compound din gidan, Hajiya Shafa’atu ce ta sauko cikin shiga ta alfarma tare da wata da zata girme mata a shekaru, da fara’a fuskarta ta fara gaida su Nenne, Aunty Farida ta karasa har inda take ta gaisheta, Hajiya Shafa’atu ta amsa tayi mata side hug tace “Sai dai mun yi maku shigowar safe kuma babu notice, fatan mun same ku lafiya?” Aunty Farida tace “Alhamdulillah, Sannun ku da zuwa Har gaban Nenne Hajiya Shafa’atu taje ta kara gaisheta da ladabi, sannan ta kara gaida Hajiya Zaliha da ita ma ta sha gwala-gwalai, ita dai Hajiya Sumayya da suke tare da Hajiya Shafa’atu dama daga inda take tsaye tayi gaisuwanta bata karasa ba tana danna waya, tuni mazan dake ko wani mota suka sauko daga matocin suka fara sauke akwatunan cikin motocin, Nenne tace “To Bisimillan ku mu shiga ciki, Sannun ku da zuwa A haka duk suka karasa parlor suka zauna, a nan Hajiya Sha fa’atu ta gabatar masu da kanta da Hajiya Sumayya a matsayin kannen Mai martaba, Nenne ta kara masu maraba cikin mutuntawa, tuni su Mama Zubaida suka sauke kaskan kosai suka dawo parlor da Mama Shatu da Sha’awa don ganin me ke faruwa, Aunty Farida ta ma rasa me zata kawo ma su Hajiya Sha fa’atu, kawai dai ta tafi ta dauko masu ruwa da lemo bayan ta ajiye tana kallon Hajiya Shafa’atu tace “A hado maku breakfast ne ranki shi dade?” Hajiya Shafa’atu tace “A’a wallahi mun yı breakfast, ruwan ma ya isa, mu da ba a ma san muna hanya ba, ai ba komai ruwan ya wadatar maa sha Allah Aunty Farida ta tafi dakin Umma tayi mata magana ta fito su gaisa, Sai da mazan nan suka shigo da tsadaddun akwati daddaya har ashirin da hudu parlon su Mama Zubaida da Mama Shatu na kirgawa a zuci, Hajiya Zaliha sai cewa take “Maa sha Allah” few bozes aka bude ana duba uban kayan ciki sama sama, Hajiya Zaliha ta ja Aunty Farida zuwa kitchen tana kallonta tace “Farida ko dai snacks din da nayi nace za a rarraba ma jama’a kawai a dauko a ba ma bakin nan don bai kamata a bar su haka ba duk da ba a san da zuwan su ba, amma gwara a fito kunya ka yaya kika ce Aunty Farida tace “lo Aunty hakan ma yayı, ni dama duk jikina yayi sanyi wallahi ban san me za a basu ba Hajiya Zaliha tace “Bari in kira Mai aikina kawai su kawo snack din dama har anyi packaging a foil an rufe, sai a biyo da shi ta kitchen kawai, akwai ruwan goran da yawa ne a gidan nan?” Aunty Farida tace “Pure water ne, na goran bai wuce pack biyu ba” Hajiya Zaliha tace “Toh bari in yi waya su kawo min, sannan kun san fa ana bada tukuici, shi kuma ya za ayi?” Aunty Farida tace “Toh, kamar ya kike ga za a bada Aunty?” Hajiya Zaliha tace “Wannan kaya haka Maa sha Allah kyau ace ko Miliyan daya ne a basu, amma kar a takura kai, ko dubu dari biyar ce sai a basu in zai ywu Aunty Farida tace “lah akwar cash dama na ciro sai ayi hatan Hajiya Zalsha tace “To ki koma parlon bari ingi waya yanzu Aunty Farida tace “Tah” Juyawa tayi ta koma Parlon don har taji sanyi wannan solution da new neighbor din tasu ta kawo, mata me kirki, Hajıya Zaliha tayi wayar da zata yi, tana ta tsaye kitchen har sai da mai aikinta da yan matan ta biyu suka taha da snacks din, meat pie, cup cake, samosa, Doughnuts, Spring rolls, duk haka aka yi packaging dinsu separately kuma ba laiți suna da Clan yawa, nan suka dire su a kitchen din, Mai aikin ta koma dauko pack din ruwa da lemo da tace su taho da, ko da Aunty Farida ta dawa kitchen din kasa cewa komai tayi don ita bata zata Small chaps din sun kai haka ba da Neighbor din tasu tay, gadiya ta fara yi mata, Hajiya Zaliha tace “Naga jiya an saya kaji, in da inda za a dibar masu shi ma a diba masu A Cooler me dan girma Aunty Farida ta dibar masu kajin ta cika shi dam, sannan suka fita da snack din parlor da Hajiya Zaliha don har suna shirin tafiya ne za su koma Bauchi wai a ranan, sosai Hajiya Shafa’atu ta nuna jin dadin snacks din da carton din ruwa da Lemo me dan dama da aka ajiye masu banda Hajiya Sumayya da ko uffan bata cewa a parlon, a haka aka kai masu packaged snack din da drinks da coolern nama zuwa mota, Nenne na kallon Hajiya Shafa’atu cikin nutsuwa tace “To Hajiya, da yake bamu san ya tsarin gidan naku yake ba, shi ne nace yanzu can Bauchin za aje yi mata Jere ko kuwa ya abun yake Hajiya Shafa’atu tace “A’a kaka, in ma jere ne idan ya bude gidansa na nan Kana sai a baku makulli a kai kayan nata can, ai yana da gidansa a nan, barin kayan a nan Kano zai fi sauki akan ace sai anje kai su Bauchi, balle yanzu dole masarauta za a kai ta, kun ga ai babu abinda za a bukata a can, in dai ba gidansa na Bauchin ba” Nenne tace “To Madallah, hakan ma ba laifi Hajiya” a haka su Hajiya Zaliha da Aunty Farida da Nenne da ma sauran mutanen parlon suka masu rakiya har zuwa gun motocin su ana masu Allah ya kiyaye hanya, bayan sun bar gidan Nenne ta kalli Hajiya Zaliha tace Lallai kin fidda mu kunya Zaliha, da sai dai a kulla masu koko da kosai a leda, sai da nace ma Parida ayi su cin cin da alkaki da dublan tace ta bada ayi a duniya yau za a kawo wai yanzu haka ake yi an dena ba kai wahala, to har yanzu ban ga idon cin cin ba balle Alkaki, da ya za mu yi da kunya yau ni Dije, lallai kin rufa mana asiri wallahi, Allah Ubangiji ya maki albarka ya raya maki zuria, mu ina muka san haka ake yi banda ke Hajiya Zaliha dai murmushi kawai tayi tace “Haba dai, babu komai Nenne” nan suka fara duba kayan lefen Khaleesat a tsanake a parlon, Hajiya Zaliha taga duk kayan babu na banza, kaya ne masu suna kaya ga uban yawa, har da tsadaddun Alkyabba biyar da lapaya babu adadi, Nenne har da hawaye ta ma rasa abinda zata ce don farin ciki da murna, da ta tuna irin yanda Abdul ya auri Khaleesat a gantale ko akwati daya basu gani ba a sunan lefe sai ta rushe da kuka, su Mama Shatu suka hau bata hakuri, ita dai Aunty Farida duk jikinta yayi sanyi sosai ko don saboda yanda aka daura aure babu nutsuwa ita kam bata yi expecting za a kawo wani lefe ba, tafi tunanin may be a bar mata a dakinta a can masarautar, a karamin kit Hajiya Zaliha taga dala dubu biyar, tana kallon su Aunty Farida tace “Wannan duk yanda aka yi kudin dinki ne suka saka” Nenne tace “Amma naga ba irin kudinmu bane ai ko kuskure aka yi” Hajiya Zaliha tayi dariya tace “In kika ji nawa ne wannan idan aka canza ai sai kin kama baki Nenne” Nenne ta saci kallon su Mama Zubaida sai kuma tace “Toh yi shiru Zaliha, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka, kema Allah ya kawo ma yan matan ki mazaje na gari” Hajiya Zaliha na murmushi tace “Ameen Nenne” Nenne ta gyara zama tace “Kin san daga inda kayan nan suka fito?” Hajiya Zaliha tace “A’a” a hankali Nenne tace “Masarautar garin Bauchi” Da mamaki Hajiya Zaliha tace “Kai haba Nenne?” Nenne tace “Kwarai kuwa, dan sarki ne mijin nata” Hajiya Zaliha tace “Ikon Allah” Mamaki ba kadan ba Hajiya Zaliha tayi, daga baya kuma taga meye ma abun mamaki a dai yanda Khaleesat take wanda ya fi dan sarki ma zai iya fitowa yace yana sonta don haka ba abun mamaki bane, ita kanta tana admiring komai na Khaleesat, tun da Hajiya Zaliha ta ji gidan da za a kai Khaleesat ta kebance da Aunty Farida tace “Farida ina ga gaskiya baza a fara taba masu duk abinda suka saka a lefe ba, probably idan aka kai ta Bauchin in suna da wani event da za ayi a can sai tayi using na lefen, in ma da event din definitely an ajiye mata kayan da zata yi using, amma dai daga nan gwara a canza kudin nan da suka sako a shiga kasuwa a siyo mata duk abinda zata yi amfani da shi na kece raini in za a kai ta, hakan ma kamar an kara kankaro mata mutunci ne, hatta Alkyabba baza a taba na lefen ba tunda ga kudi gwara a siya kawai, amma dai ban san yanda ku kuka tsara ba gaskiya, ina magana ne bayan na duba gidan da za a kai ta Kinsan irin wannan babban gida ba dai kananun zance ba, gwara su ga bata taba komai a kayansu ba hakan zai fi armashi” Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace “Wannan gaskiya ne Aunty, sai a je kasuwan kawai, nima nayi wannan tunanin wallahi, duk da akwai lapaya uku da na siyo mata da takalma da jaka, sannan akwal kayan dinkin ta da aka kawo jiya, amma gwara a karo mata wasu masu tsadan” Hajiya Zaliha tace “Amma sai kin yi shawara da Nenne da mahaifiyarta, wannan abu dai abu ne sau daya in a life time, so gwara ayi mata abinda ya kamata duba da inda za a kai ta ma” Aunty Farida tace “Toh ba damuwa bari in masu magana Aunty Ajay ya kira Jay for the countless time but he still can’t reach him, shi damuwarsa kawai yasan inda yake so they can talk, he needs to speak to him badly, shi dai yasan bai san ta yaya ba but probably they might arrive at a solution together idan suka hadu duk da bai ma san wani irin solution din ba at this point, gaba daya kansa a kulle yake tun jiya yake nazarin yanda zai billo ma al’amarin amma ya kasa arriving at any solution, duk tunanin da yayi sae yaga ba mafita bane cause he might end up disappointing his father, ko baccin kirki bai samu yayi daren jiya ba, har yanxu kuma kamar mafarki yake ganin al’amarin, ya kasa gane ta yaya Mai martaba ya iya switching comfortably without even considering the consequences after, a iya rayuwarsa bai taba zama confuse and lost kamar haka ba, bai ma san ko Jay zai yarda he knows nothing about the sudden switch ba, he don’t even know if he will believe him, ba a good 5 minutes Jay bai fado masa a rai ba and he is just restless, in his wildest dream he never saw this coming, bude kofar parlonsa aka yi ya daga kai da sauri, Mami ta shigo parlon kana ganinta kasan tana cikin tashin hankali matuka, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kai, ta karasa har tsakiyar parlon cikin rawan murya tace “Amma ka bani mamaki Junaid, wallahi ka ban mamaki, ban yi tunanin zaka yi ma Jawwad haka ba, baka duba irin son da yake maka ba da irin goya maka bayan da yake yi in every situation ko da kai ne baka da gaskiya, baya taba sauraron wanda zai karanto masa laifin ka har ni kuma, a kan ka Jawwad sai ya rufe ido ya gaya min babu dadi, duk abinda zan ma Jawwad bazai daga ido ya kalleni ba amma inyi kuskuren fadan wani aibu a kanka ranan sae abinda ya manta ne bazai gaya min ba cikin fushi, ya dauke ka tamkar wanda ku ka fito ciki daya, ya dauki son duniya ya daura maka and he is always ready to protect you at anytime amma wai kai zaka ci amanarsa ka auri warce kasan yake bala’in so kawai don nace ba yanxu zai aureta ba sai nan da warni Lokaci…. Kuka ta fashe da shi sosai tace “Daga kai har Sarki kun nuna mana iyakarmu da ni da Jawwad a gidan nan, wallahi da da zuciya daya kake zaune da Jawwad ko sarki ne yace zai aura maka yarinyar nan baza ka amince ba duk yanda zai yi da kai kuwa, instead fighting zaka yi har sai kaga Jawwad ya samu, amma saboda baka tare da Jawwad da zuciya daya you are just using him shi ne zaka yi masa irin wannan sakayya ka auri budurwarsa, don Allah ka gaya min meye ribar ka Junaid?” Ajay dal different direction yake kallo amma duk yana sauraronta, Infact mamaki ma ya sa yayi stiff kawai a inda yake zaune jin kalaman Mami, cikin kuka Mami tace “Magana nake maka kake kallon wani waje daban, ka gaya min me da na yayi maka da kake son ganin downfalt dinsa haka? Is it a crime don ya nuna yana yin ka, kuma yana goyon bayan ka?” Ajay ya kalleta kamar bazai ce komai ba, can dai yace “I new nothing about this marriage, ban san komai a kai ba, ke kika ce ma Mai martaba ya maida auren kaina which he did, ni ban san komai a kai ba, bai kuma yi shawara da ni ba” A fusace Mami tace “Baka san komai a kai ba amma auren ke kanka har yanxu kuma ga ka zaune comfortable as if nothing? In baka san komai a kai ba al birkice ma Sarki zaka yi kace baka son auren baza ka iya cin amanar dan uwan ka ba, idan yaga ka daga hankalin ka ai zai nemi mafita, kuma ta nan ne zai san yayi babban kuskure abinda yayi, da nace ya maida auren kanka idan har ya dau Jawwad matsayin da sai yayi hakan? Wallahi duk abinda ya samu da na bazan taba yafe maku kai da Sarki ba, i will never forgive you two kuma sai na fito na sanar ma duniya duk abinda ake ciki babu abinda zan boye dama an dade ana ruwa kasa na shanyewa a gidan nan, an dade ana nuna mana iyakarmu ni da Jawwad, an kuma ci amanar Marigayi Yusufa, an ci amanar sa, da shi ne bazai taba yin haka ba, an ci amanar dan sa, in har wani abu ya samu Jawwad zan fito in sanar ma duniya komai wallahi” Cikin kuka sosal ta kare maganar, shi dai Ajay kallonta kawai yake don bai ma san me zal reba, Lace Dania sat da na ce ma jawwad shi ke son katsakani da Allah amma ba kai ba, kawai kana, using dinsa ne, shi kansa za gane hakari yanxu, tunda gashi ka ci amanarsa, in har ka cika dan halak samun Sarki zaka yi duk yanda zai yi yayi a warware auren nan da ya daura da kai, amma sain ka cika dan halak” Tana kai wa nan ta fice daga parlon Ajay ya bi ta da kailo, bai taba ganin mutum that is so perfect in manipulation kamar wannan matar ba, cikin few minutes ta juya lamarin ta dawo ita ce victim din, jinginar da kansa da yayi masa nauyi yayi ya lumshe idonsa, he wish zai iya da ya sake samun Mai martaba amma bazai so ya bata masa rai ba, don bata masa rai da aka yi tun farko shi ya ja har yayi wannan abun da yayi…. Tun da Nenne ta samu labarin Yau Lahadi za a kai Khaleesat Bauchi ta fara lissafin wa enda za su je kai amarya yanda baza ail kunya ba tunda ba garitalallen gida za a kal ta ba, Sha’awa har da kukanta da Nenne tace banda ita a yan kal amarya, Nerine ta gama lissato duk wa enda za su Bauchi ciki har da Baaba Gaje, Aunty Farida, Aunty Murja, Hajiya Zaliha da babban er ta, Uwar kishiyar Aunty, Murja, sai wata a manri wanda mijinta ke da kudi Hajiye Salaha, da kvar Menne ta lissafo Mama Shatu a cikinsu wal shima ann kar Maram All va kullacet………su raka yayarsu gidan auren ta, sai kuma Lamisah, sal da Aunty Farida tayi da gaske da Nenne sanrian Nenne ta yarda ta sa kawar umma wato: Mama Savame a yan kal amarya, daga karshe Nenne ta sa wata Cousin sister ginta ita ma dattijuwa kamar Baaba Gaje, duk sal da Nenne ta jaddada masu gidan Sarauta za aje kai Khaleesat su ruta mata asiri kar su bar abun fade a can, Aunty Farida tayi mamakin da Nenne bata ce zata je ba, bayan Nenne ta gama zayyano duk yan kal amarya sal kuma tace “In kuma a jirgi za aje kai amaryan to lallai sal an gaftare wasu mutane a wannan lissafin da aka yi kar ayi mana kallon yan iska” Throughout Jiya da shekaranjiya Khaleesat bata shiga darnuwar da take ciki ba yau da taji za a kai ta Bauchi, dama zuwa yanxu daga Jay din har Ajay babu wanda take kira a waya tunda bata samun su, duk wani……gayu tun daga jiya zuwa yau, ko dakin da take mutum ya shiga ba abinda zai ji yana tashi sal azababben kamshin jikinta, ga wani glowing da take, gashin kanta ma ya sha gyara na musamman dama gashi bakikirin, duk wanda ya kalleta sai ya sake kalionta, haka yarinyar Hajiya Zaliha ta zauna dakin tana ta kallonta kamar ta samu TV, komal na Khaleesat burgeta yake, turarurruka ba na wasa ba Hajiya Zaliha ta kai Aunty Farida suka siya ma Khaleesat har da turarumukan wuta tunda ga kudi enough, Banda Hajiya Zalihar abubuwa da yawa Khaleesat da…
