Hausa novels

Gargadar So Chapter 36 By M Shakur

Chak Baban Yaseer ya tsaya sabida yanda Baba yahanashi, Baba na kallonsu yace “ba’a dukan mata barta da halinta kutafi kawai, Ni’ima karki damu babu ko biyar na mijinki a asibitin nan, kutafi Aliyu” kunya ne yakama Baban Yaseer kaman kasa ya tsage yashiga ciki, yajata da karfi yace “let’s go” tutturjewa take tana kallon Hawwa dake zaune abakin gadon gwanin ban tausayi tana goge hawaye dake zubomata da sun kasa daina zubowa, Ni’ima can’t even describe yanda takejin tsanan Hawwa kawai so take ta mutu atleast idan ta mutu zata huta, Baban Yaseer zai natsu, ina jitayi bazata iyaba a haukace ta fizge hannunta kaman mai ciwon hauka ta taho tace “Wlh wlh saina kasheki banga dalilin da mijina zaifi sonki akaina ba, yana kirana dakikiya sabida ke ba, he’s telling me kinfini komi” kawai Ni’ima tai kan Hawwa da sauri Ammi ta zauna tana kama Hawwa zuwa jikinta dake sheshekan kuka ahankali dabai fita irin hurtful cry dinnan dayake fita daga soul naka, azuciye Baba ya tare Hawwa da Ammi yakama karfenshi daya a hammata gamgam yazare daya yarike a hannu yadaga sama, daidai Baban Yaseer na kamata tana ihu da karfin gaske, Baba yace “Idan ban miki karatun Alam nashara da karfen nen ba ba sunana Baba ba, hauka kikeyi ne? Nace hauka kikeyi ne? Ni’ima kin haukace ne? Kinmanta kawarki dakuke zuwa wajena nabaku kwandala kwandala na siyan alawa? Ni’ima Hawwa fa dakike fushi dani idan na bata mata rai? Sabida miji Ni’ima kikema kawarki fatan mutuwa? Ina amintan? Ina kauna da soyayya ina? Ina zumunta? Duniyan nan duka duka guda nawa take? Dudda ina nemawa y’ata miji har ina bada sanarwa a masallaci mesa bantaba mata kwadayin mijinki ba? Kin taba tunanin maisa ban ma Aliyu tayin Hawwa ba? Sabida nasan ayanda y’ata ke sonki bazata taba so ta auri mijinki ba! Nima bazan taba kaunar ku lalata zumuntan ku ba! Ni’ima haukacewa kikeso kiyi ne? Kunfi shekaru ishirin kuna tare meyayi zafi haka? Auren Aliyun tayine menene haka? Bakida lafiya a kwakwalwanki ne”? Tana kallon Baba tana fizge fizge da Baban Yaseer tace “eh hauka nakeyi Baban Hawwa! Akan Aliyu zan iyafin hakama haukacewa, yarka ta kiyayi mijina kawai kagaya mata, ta kiyayeshi!” kallon Aliyu Baba yayi yace “Aliyu dudda bansan ko Ni’ima ko wacece wannan ba amman dauketa kubar wajen nan kar raina yabaci” daidai lokacin some Doctors da Nurses da security na shigowa dakin, senior consultant dinsu yace “what is going on here? This is hospital not arena, why are you all traumatizing my patients? Everyone outside” Fizge hannunta Ni’ima tayi kaman mahaukaciya tana kallonsu tace “sakan mini hannu” takalli likitocin tace “patient dinku tai kwantai batai aure ba, ubanta gabaki daya yagaji da ita har tallanta yake gida gida lungu lungu, shine yanzu suke kokarin a manna ma mijina ita” Dr yakalli Baban Yaseer dake faman riketa yace “Sir I know you are a Muslim and bazaka so nasa security maza su dauki matarka ba, nabaka 30secs idan baka dauketa kun fitaba zansa maza su fitar da ita this is hospital not wrestling arena, munada patients dayawa dakuke tayarma da hankali, we can sue her for this, please kindly take her out” Aliyu da kunyan dubiya yasa jikinshi ma yayi sanyi yakai hannu zai dauketa ta fizge tareda tureshi takalli Hawwa dake kallonta idanunta sunyi jajur sabida kuka tanuna kanta tace “mijina zakibi Hawwa? Mijina? Wlh wlh saidai ki mutu ko nida ke mu mutu tare daki auremin miji” tana maganan tai wajen gadon Dr yama security guys magana sukai kan Ni’ima suna tareta suka rirrike mata hannuwa Ni’ima tafara ihu na boo mutum tace “jama’a azo aga husband snatcher, wacce bakin halinta yasa for almost 30yrs babu wanda ya aureta, ubanta ma yagaji da ita neman kai yake da ita, infact yar iska ce, amfani take da kanta da daddare sannan take iya bacci, nitake kira ina bata maganin rage sha’awa kullu yaumin, aure takeso idanu rufe, da ace tanada mashinshini da tuni tabi maza sabida yanda takeda bakin jaraba, Hawwa harija ce duk dare saitai kukan neman namiji” wani irin nishi Hawwa tafara jin yanda Ni’ima ke tona mata asiri da karya da gaskiya zuciyanta yafara bugawa da karfi security sukai waje da Ni’ima, Ammi na ihu ganin yanda Hawwa keyi “Dr something is wrong with Hawwa na Innalillahi” akai kan Hawwa ana sa Baba da Ammi su fita waje.A reception Ni’ima tacigaba da ihu mutane na taruwa patients na fitowa daga daki suna lekowa aga meke faruwa, kaman ba ita ake jaba tana nuna Baba da Ammi dasuka fito suna kallonta tace “wazai taimakama tsohon nan ya auri yarsa datai kwantai ba miji? Bai bama yarsa tarbiya ba sabida ciyar dashi datake yasa maza ke tsoron aurenta, itace komi nashi babu abinda yake tsinanawa sai gulman yan anguwansu, kunsan yarsa har gayu takeci tasa janbaki kowani zai ganta yace yanaso amman shiru babu machinchini” “get this mad woman out of this hospital!” Sukaji muryan Khaleel dayasa kowa yajuyo har Ni’ima da Baban Yaseer daidai Khaleelna saukowa daga staircase, tundazu yana asibitin nan but yana office dinshi asama, karasowa yayi yana tafiya daidai kaman sarki ya tsaya daidai gaban Baban Yaseer dake kallonsa batare daya kalle kowa na wajenba sai Baban Yaseer din yace “take this mad woman and this photo husband of hers out of my hospital and duk randa nakara ganin any of them in my hospital I will fire tundaga gate workers to workers na reception din nan!” Yayi tsawan da saida wajen ya dauka, kawai Baban Yaseer yaga exra security na zuwa aka rikemai hannaye both side kaman baraw idanunshi cikin na Khaleel dake kallonshi irin kallon sworn enemies dinnan kawai aka jashi har sukakai wajen kofa kallon Khaleel Baban Yaseer yake sannan aka fitar dashi da matar tasa….Suna fita Baba kawai yaji jiri na dibansa yayi baya zai fadi dawani irin sauri Khaleel yazo wajen yatareshi ahankali yace “Baba!” Kallonsa Baba yayi ahankali, ganin hawaye na tsatsowa a idanun Baba yasa da sauri yakama hannun Baba yasa akan kafadanshi ya karbi crutches nasa daya yamikama Salman sannan yawuce da Baba yana dinginshi zuwa wani office dake wajen Ammi tabisu da kallo tana mamakin waye mutumin nan?.Zaunar da Baba Khaleel yayi kan gadon dakin Salman yashigo yabashi crutches din ya karba ya ijiye yawuce yafita sannan yadawo wajen Baba stethoscope dake office din yadauka ya makala a kunne sannan yadauki abun auna BP yazo wajen gadon yadan kalli Baba in very cute and dan shagwaba voice yace “Baba don’t pay attention to whatever she says” yashiga auna BP Baba duk Baba yana kallonshi, chan ya saurari pulse nashi da heartbeat sannan ya ciccire komi yace “jininka yahau kadan a little sleep da magani will help zansa akawo ma” yajuya zai fita ahankali Baba yace “Ibrahima!”Juyowa Khaleel yayi ahankali babu wanda yataba kiran sunanshi ahaka sai Baba, tsayawa Khaleel yayi gaban gadon gently Baba yace “kaima likita ne”? Ahankali Khaleel ya gyadamai kai yace “eh” gyadamai kai Baba yayi saikuma ahankali yakai hannayenshi dake rawa rawa yakama duka hannayen Khaleel yarike Khaleel ya kalli yanda yarikemai hannu yayi shiru, baki Baba yabude ahankali zaiyi magana saiya fashe da kuka irin na manya dinnan, Khaleel yayi shiru yana kallonshi sai kawai yaji he’s feeling bad, like really bad, he can’t remember the last time he felt this bad for anyone in his life, cikin murya mai raunin gaske dan maganganun Ni’ima sun taba Baba dudda bai nunaba yace “yau Ni’ima ta goranta mini, ta zageni, ta zagi y’ata duka agabana” cikeda damuwa Baba ya tsagaita kukan saiya kalli Khaleel yace “Ibrahima zuciyata batamin dadi ko kadan banmasan mesa nake gayama ba amman har cikin jinina nake jinka wlh, Allah ya dauramin kaunarka kaman danda na haifa” Baba yaja hanci yace “banda komi ko ada chan kaji nake gasawa da sauransu Hawwa tana around shekara 6-7-8 haka mukai hatsari mahaifiyarta tarasu nikuma nadawo haka saida aka guntulemin kafa daya, da kyar da wayyo Allah nasata tagama sakandire Allah yamata baiwan iya dinki kwandala nawa babu akaratunta na jami’a ita tasa kanta hartai masters tace zata fara aikin yan sanda, Hawwa ke kula damu da kannenta komi na gidana Hawwa ne, wata kila inda bata daurama kanta dawainiyan mu ba ta takura kanta harta fara aikin yan sanda ba da hala by now tayi aure nima inada laifi” ya goge hawaye yace “babu mai neman y’ata babu maison ya aureta an tsani Hawwa na, bansan yanda zanyi ba, hawan jini yakama Hawwa sabida tunani da damuwan mesa batai aure, kanninta hudu mata duk sunyi aure hadda yara, yaran unguwa dasuka taso tareda Hawwa wasu yaransu hudu biyar ma, dudda bata nunawa dan tanada jarumta da taurin zuciya amman damuwa yamata yawa, narasa yanda zanyi babu maison auren Hawwa na wayyooo Allah na kaico na amma y’ata gorin aure” Baba kawai yacigaba da kuka da zuciya daya, shi kadai yasan kalan damuwan dake zuciyansa, Khaleel yakai kusan 2min kallon Baba yake chan kaman mai koyan magana yace “inaso na auri Hawwa Baba!” Dawani irin sauri Baba yadago kanshi yakalli Khaleel danjin zancen yayi kaman saukan aradu, bakinshi har rawa yake yace “Ibrahima kace zaka auri Hawwa?” Gyadamai kai Khaleel yayi ashagwabe, bayan hannu Baba yakai ya goge fuskansa tass da sauri yana kallon Khaleel din yasake maimaitawa. “Ibrahima kace zaka auri Hawwa”? Gyadamai kai Khaleel yayi yace “eh” Dasauri Baba yace “kasanta ne”? Gyadama Baba kai yayi sounding like sangartaccen yaro din nan yace “inada Baby her name is Noor antaba kidnapping nata shine Dady na yakira wajen aikinsu ita ta tayamu nemo Noor lokacin nafara ganinta kenan” sosai Baba ke kallon Khaleel da yanda yaron ke magana kana ganinsa kasan dan gayu ne irin yaran masu kudin nan, yan gata he’s so adorable, washe baki Baba yayi yay kosasshiyar murmushi saikuma ya dakatar da murmushin yace “Maza da dama sunsha zuwa suce sunason Hawwa dazaran nace su turo magabatansu shikenan bazaka kara ganinsu ba, bazan takura maka ba Allah yasani zuciyata ta natsu dakai idanhar da gaske kake kanason Hawwa kaje kazo da iyayenka zuwa layinmu da magriba, kome yasamu ka kawo zan baka auren Hawwa, idan yaso bayan ta warke sai ayi maganan tarewa da sauransu kaji, layinmu yana nan kayin gwadabe babu wanda baisan Baba gurgu ba kuzo ina jiranku” ahankali Khaleel na kallonshi yace “okay Baba” the way yake sounding whenever he talks kaman Baby yasa baba yace “shekarunka nawa Ibrahima?” Ahankali yace “32yrs” murmushi sosai Baba yamai sai kawai yakai hannunshi ya shafa kanshi zuwa gefen fuskanshi yace “Allah maka albarka yarona” murmushi Khaleel yayi kadan saikuma kawai yahau gadon yazauna kusada Baba kaman dan yaro yadaura kanshi kan kafadan Baba, shi kawai yanason Baba without any reason.

Back to top button