Hausa novels

Gargadar So Chapter 79 By M Shakur

Tafito tana ganin ana wucewa da Khaleel clinic na gidan tawuce side nata ahankali tabude kofa ta shiga tawuce sama dakinta kasama chanza kayan tayi daya jike saitaji gabaki daya ta damu she’s not happy at all, so Khaleel yayi ciwo tun yana 8yrs old he had cancer har zuwa age 14? Could this be the reason iyayen suka batashi haka? Suka kasa bashi tarbiya? İs that the reason suke sonshi haka na fitina? İs that the reason sukeda asibiti agidansu sabida ciwon Khaleel? Could this be the reason Khaleel yazama likita? Is that the reason Mamanshi ke everything to make him happy bataso abatamai rai saidai afaran ta mai rai? Wani kalan cancer yakeda shi? Babanshi yace lokacin yafara ciwon da yawan suma is the cancer back yanzu wannan daya sume yana cikin magana? Nooooo tafadi da sauri, She knows batason Khaleel ko kadan but she felt so bad dataji yayi rashin lafiya, from age 8 to 13/14 that’s long time, sai kawai tadinga addu’a Allah yasa ba ciwon ne yadawo ba, tadamu sosai iya damuwa sai kawai ta tashi tafada bayi tacire kayan tayi wanka tafito tasaka wasu kaya tasa na bacc tasakai hijabi tafara salloli wlh kawai tadingama Khaleel addu’a, har zuwa 3 Hawwa bata runtsa ba, addu’a takemai har akai sallan asuba tayi itama sai ta sauko falo tazo jikin window tabude tana kallon tsakar gidan babu kowa banda securities nasu da bindigogi saita zauna akan kujera tai shiruuu chan takara tashi ta leka tsakar gidan but shiru haka tasake komawa ta zauna around 6 ta tashi tasake lekawa ta windowKhaleel ta hango yana tahowa side din sanye da kayan jiya ga kanula a hannunsa, dagudun gaske Hawwa tasaki labulen tayi kofa tabude da sauri tana kallon Khaleel chak Khaleel ya tsaya ganin Hawwa tabude kofa tana kallonshi damuwa sosai akan idanunta, wlh kallo daya yamata yasan babu one single sleep a idanunta, sai kallonshi take cikeda damuwa amman ta tsaya chak bata cemai komiba kuma batazo ba shikuma wlh she must show him care, da gangan yawani kama kanshi yace “ashhhhhhhh” sai kawai yayi baya kaman zai fadi dawani irin sauri Hawwa ta taho wajen ko silipas babu akafanshi tawani tareshi cikin murya mai bala’in dadi cikeda kulawa tace “Khaleeel” saukar da kanshi Khaleel yayi awuyanta ahankali yace “jiri take me inside” dasauri tashiga tafiya dashi hannunshi yakai yarike waist nata gam itama tarikeshi da kyau suka wuce ciki daidai su Mom da Excellency nafitowa daga clinic Excellency yace “look at wacce kika tsana! Look at them, jibi yanda ta fito ta tari danki jibi yanda yayi kaman ba shine yafito da kafansa ba”.Daki Hawwa tashiga dashi akan dogon kujera ta zaunar dashi ya zauna taje ta rufo musu kofa tazo wajen sai kawai yaga Hawwa tayi kneeling agabanshi tana kallonshi cikeda damuwa tace “me zakaci na dafa maka? Are you hungry”? Wani dadi ne yakashe Khaleel, kaman mai shirin suma yace “I want to drink kunu and kosai! But I wanna brush nai wanka da salla can you help me to my room”? Dasauri tace “yes” tashi tayi ta dagashi yatashi ahankali zatai stairs dashi yace “I can’t muje lift” lift din taje dashi suka shiga tana rike da shi sai kallon fuskanta yake sukakai sama tashiga kallon dakunan batasan wannene nashi ba wani room yamata pointing hakan yasa tayi wajen dashi tabude kofan suka shiga dakin yahadu zaunar dashi tayi abakin gado tace “bari nasakaka toothpaste a brush” bathroom nashi ta shiga yabita da kallo da gangan yashiga cire kaya harda wando yabar boxer kadai toothpaste tasamai tafito daga bayin ganinshi zaune ba kaya ga kayanshi akasa saida gabanta yafadi tadai daure bata wani kalleshi ba tace “muje” hannunshi takama yataso ahankali sukai bathroom din tace “zaka iya wanka a tsaye?” Ahankali yace “cikamin bathtub bazanyi a shower ba I can’t stand for too long” gyadamai kai tayi tawuce wajen bathtub shikuma yashigayin brush yana kallonta ta mirror cika ruwan tayı tana sa hannunta karyamai zafi da yawa takalli abubuwan wanka tasa komi yafara kunfa da kamshi tadawo daidai yana rinsing bakinshi da mouthwash ta tsaya gefenshi tana kallon fuskanshi tace “kagama”? Gyadamata kai yayi ahankali hannunta takai takamashi wani yirrrr Khaleel yaji sabida hannun da lema leman ruwa but yadaure bai nunamata ba suna kaiwa wajen bathtub din ba kunya yawani sauke boxer nashi kasa da mugun sauri Hawwa ta juya but still tana rike dashi, cire boxer yayi tass ya wurgan da boxer akasa sannan yashiga ruwan yace “you can turn around” Juyowa tayi tadan kalleshi shima shegen kallonta yake tace “bari nafito maka da kaya kagama call me” gyadamata kai yayi tajuya tafita yabita da kallo tana fita yawaniyi dancing cikin ruwan yana fancakali da kumfa yace “yessssss!” Walk in closet nashi Hawwa ta shiga tabi ko’ina da kallo kaman wani shugaban kasa tama tasa mezata ciromai sannin zaiyi salla yasa tadauko jallabiya da boxer da cream da turare guda daya ta ijiye agadon takıma tadauko short dawata yar t-shirt ta ijiye ta shimfida dadduma tadauki kayan daya zubar dasu anan kasa taga wani laundry basket a closet nashi taje tasa daidai tafito taji muryanshi kasa kasa yace “Moon” dan dakatawa Hawwa tayi takalli kofan bayin murya chan ciki yace “Moon, Wife” baki tabude kaman zata amsa saita tuna batai accepting nashi as miji ba ahankali tabude kofan bayin a tsaye taganshi tsirara cikin bathtub din dasauri tajuya tace “subhanallahi” murmushi yamata yace “give me towel from the hanger” dasauri takalli hanger wajen kofa tana mamakin yanda baya kunyanta tadauki sabon white towel dake wajen ta warware takare fuskanta tana tahowa, dariya kaman zai kashe Khaleel but yarike dariyan har gaban shi tazo tabashi ta juyamai baya dasauri, daura towel din yayi a waist jinshi Hawwa tayi abayanta dasauri tajuyo sai kawai ya rungumeta tsam tsam batare dayayi magana ba duk ruwan jikinshi ya manne mata a hijabi zuwa cikin jikinta wani yammm taji tama kasa magana saikuma adan hankali ataushashe cikeda kulawa da damuwa tace “meke maka ciwo yanzu?” Khaleel jiyayi kaman ya kurma ihun dadi ganin yanda Hawwa tadamu dashi, abin nema yasamu yawani kashe murya kaman wanda zai mutu yanzu yanzu yace “ko’ina kemin ciwoooo” yayi maganan ashageabe, gently Hawwa tadaura hannayenta abayanshi tai patting ahankali Hawwa tace “sorry ko” gyadamata kai yayi murya kadan like a baby, calmly tace “muje kasa kaya kai salla” gyadamata kai yayi yadago daga jikinta tarikeshi suka wuce daki zaunar dashi tayi kan gadon tanabin yanda gashin kansa ke fitar da ruwa saita juya takoma bayi karamin towel tadauko tazo gabanshi tadanyi jimmm tana kallonshi kaman mai lissafi but ganin baida karfi and baida lpy sosai kawai saita daura towel din a kanshi tana sharemai gently sabida kar kanshi yayi ciwo, Khaleel yadago kanshi yana kallonta kin kallonshi tayi ta goggogemai fuska da bayan wuya sai kawai ta tsugunna agaban gado dudda gabanta na faduwa ta daure towel din zuwa kirjinshi ta goge ruwan, sannan tama hannu da kafafu zuwa knee ta ijiye towel din a gefe, tadauki cream nashi tana budewa mamaki yagama kashe Khaleel da ace an gayamai Hawwa zata iya kula dashi haka he can swear karyane bazata iyaba, so Hawwa is tHis caring,zuba man tayi a hannu ta malka tadan kalleshi bakinta har rawa yake tace “uhnnn na….na shafamaka?”Gyadamata kai yayi yadan lumshe ido sabida ta shafamai comfortable, shafamai tayi a fuska gemunshi taushi sosai kaman tana shirya yaro, rawa hannunta yafara dazata shafamai a kirji but ta daure ta shafamai gaban Khaleel yafara tashi sabida hannunta dake shafamai jiki that is very soft amman ya harde kafa da sauri, a hannu ta shafamai zuwa kafa saitadauki jallabiyan ta samai aka tace “bani hannunka” bata yayi tasakamai, boxer ta kalla sai kawai tadauki turare ta fesamai takwashi kayan shafan tace “ka karasa ina zuwa” tawuce closet nashi tamaida abubuwa tana fitowa taga yasa boxer ya yarda towel din akasa, daukan towel din tayi takai bayi tafito tace “tashi kai salla” tashi yayi ganin haka tafice daga dakin tawuce dakinta wayanta ta dauka tafito tana sauka kasa tai dialing number Ammi ta shiga kitchen ringing daya Ammi ta dauka tace “oyoyo Amaryana” adan kunyace tace “ina kwana Ammi na” Ammi tace “kun tashi lpy ya mai gidan naki” murya Chan kasa tace “fine” sai cha tace “Ammi inada gero ahhhmm” ta idan shiru tace “wai kunu zaisha” murmushi Ammi tayi tace “da kyau yar albarka haka nakeso ki dinga dafa abincin mijinki da kanki eh akwai gero Daddo duk ta kawo miki kayan hatsi harda alkama Umma ina kukasa kayan hatsi Hawwa na neman gero” daga wajen Hawwa taji Umma na cewa ta duba store duk suna wajen, Ammi tace “ance kiduba store” gyadama Ammi kai tayi tashiga store nata wlh Baba da kowa ma sunyi kokari buhu buhu tagani haka tashiga budewa tana mamaki ina zatakai all this abubuwa taga gero ta debo da wake shima tafito ta jika tana neman blender nan taga bucymix.

Back to top button