Daga Makamai

Alamomin da mutum zai gane akwai Aljani a jikinsa ko kuma an yi masa sihiri.

Alamomin da mutum zai gane akwai Aljani a jikinsa ko kuma an yi masa sihiri

*ALAMOMI GUDA TALATIN (25) DA SUKE NUNA CEWA MUTUM YA GAMU DA SHAFAR ALJANU.

🛑 Gargadi: ba kowanne ciwon bane za’a dorawa jinnu sai an bincika sosai.

1. Rashin son karatun Alƙur’ani ko sauraren shi.

2. Rashin son yin ibada ko a yita cikin ɓacin rai da kasala.

3. Yawan ciwon kai mai tsanani ko tsagin kai ko kuma jiri.

4. Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki ko ƙirji.

5. Yawan jin tafiyar wani abu a jiki kamar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a kai.

Karanta >>> Kalolin mata guda biyu da ya kamata duk wani namiji ya sani.

6. Yawan mafarke mafarke na ban tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma kiji wani abu mai nauyi ya danne ki ko ya shaƙe miki wuya.

7. Yawan jin tsoro ko faɗuwar gaba ko wani abu ya ringa yimiki gizo ko kuma kiji kamar ana kiran sunan ki.

8. Yawan jin sanyi ko zafi ko riƙewar ƙafa ko wani sashe na jiki.

9. Rashin iya bacci da daddare ko yawan jin motsin wani abu ko surutai ko kuma takun tafiya.

10. Rashin son yin kitso ko kuma a taɓa miki kai.

Karanta>>> Innalillahi wainailaihi rajiun 😭 Mahaifiyarta takama babanta yana zina da yar’sa

11. Yawan ɓacin rai ko jin haushin mutane ba tare da wani dalili ba.

12. Rashin son shiga cikin mutane ko yawan zargin su ko kuma yawa rigima da su.

13. Yawan kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba.

14. Yawan jin kamar ana yimiki raɗa a kunne ko a ringa raya miki a zuciya akan ki aikata wani lefin kamar kisan kai ko zina ko kuma sata.

15. Rashin son yin Aure ko korar samari ko kasa tsayar da guda ɗaya ƙwaƙƙwara.

Karanta>>> Ladubban Karbar Addu’a Guda 25 Daga Malam Aminu Daurawa

16. Ɗaukewar Sha’awa ko rashin jin daɗin saduwa da miji ko kuma tsanar shi da wulaƙan tashi ba tare da wani dalili ba.

17. Yawan kallon mudubi ko Sha’awar kallon tsiraici.

18. Yawan son kaɗe-kaɗe da raye-raye.

19. Yawan son dare ko cikin duhun ko yin shuru kamar bakya gurin.

20. Rikicewar Jinin Al’da ko na Nifasi.

Karanta>>> Addu’ar Neman Tsari Daga Sharrin Aljani Ko Wanne Iri Ne Da Izinin Allah

21. Rashin Haihuwa ko yawan ɓari ko Haihuwar ɗan babu rai ko kuma wasu matsaloli su biyo bayan Haihuwa kamar jijjiga.

22. Aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba, sai daga baya ki ringa nadama ko mamakin yadda akayi kika aikata.

23 Yankewar jiki a faɗi ƙasa ba a cikin hayyaci ba ko kurma ihu da rugawa a guje ba tare da kin san inda zaki ba.

24. Yawan wasiwasi ko mantuwa acikin dukkanin Al’amura musamman a lokacin ibada.

25. Taɓuwar ƙwaƙwalwa dadai saurausu. Idan kuma kanasan magani zakai mana magana Insha Allah muna dashi duk taurin kan Aljanu zakasami sauki wajan Allah.

 

Back to top button