Halysaah Page 63 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 63…Khaleesat na isa kofar parlon ta bude a hankali tana kallon wanda ke tsaye bakin kofar, sauke idonta tayi ta koma gefe ta tsaya, babu yabo babu fallasa yana kallonta yace “Me yasa kika kira wayana kina kuka kamar ni na aike ki? Why didn’t you call Jay kiyi masa kukan sai ni?” Ta daga jajayen idanuwanta ta kallesa, ji tayi wasu hawayen sun cika idonta ta sunkuyar da kanta, after some seconds ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, da kyar tace “Ni dai in ka san sa kayi masa magana he should delete my pictures off his phone plss, Aunty Farida ma fa sai da ta turo min hoton, ni kuma wallahi ban san sa ba” Yace “Baki san sa ba kika tsaya gefensa kina washe hakora ku ka yi hoto?” Ta fashe masa da kuka ta juya da sauri ta bar wajen ta koma cikin parlor ta kwanta kan kujera tana rera kuka, tsabar mamaki da haushi yasa ya kasa cewa komai ya bi ta da kallo, ya tsani unnecessary kukan mace a rayuwarsa, ya kuma lura bata da aiki sai kukan banza tun da ya santa a haka ya santa da kuka, how is Jay coping interacting with her this way, shi ba shi da irin wannan patient din, parlon ya shiga ya kulle kofar, ya saka hannunsa a aljihun Jacket din jikinsa cause he is already cold kawai ɗan tsayuwar da yayi a waje, ya karasa har inda ta kwanta take kukan ya hade rai yace “Don’t you dare call my line again kina kuka, ni ban aikeki ki bi silly friend dinki zuwa party har ayi maku hoto da wani namiji ba, stop stressing me with ur troubles pls, i am not Jay” Ta dakatar da kukan da take ta wani kallesa ta hade rai tace “Ni ba party muka je ba, get together ne, ka dena cewa party” Wani kallo yayi mata, ta kauda kanta tana goge idonta, ya kalli Heater din parlon sai kuma ya tafi ya kunna, ta bi sa da kallo ganin ya nufi window din parlon ya bude drape din yana kallon snow dake sauka waje sosai, he was just imagining how he managed to get here in this snowstorm, mikewa tayi a hankali tayi wucewarta sama, ya juya ya bi ta da kallo. Wajen karfe takwas da rabi Khaleesat ta fito daga dakinta tana leka downstairs daga corridor din da take tsaye, taga yana zaune har sannan a parlon ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa a lumshe, ta zata ma ya tafi, after some minutes ta sauko downstairs tana kallonsa, har sannan bai bude idonsa ba, tana tafiya a hankali ta nufi window tana duba waje taga it’s still snowing outside, dawowa parlor tayi ta tafi kitchen, after a while ta fito da cup din tea biyu ta tafi har inda yake zaune ta tsaya tana kallonsa, a hankali tace “Ga shayi” Bude ido yayi, sai kuma ya gyara zama yace “Did i send you message?” Ta wani kallesa, sai kuma tace “To ai naga kamar sanyi kake ji tunda gashi ka kasa tafiya” Ya kalleta yace “Zan juye maki shayin a baki in baki matsa gabana ba, ba ke kika fito da ni cikin sanyin ba? Kin zata idan Jay yana nan zan saurare ki ne? Ai shine wahalalle dama” Tace “Ni ban fito da kai cikin sanyi ba, tunda ba cewa nayi ka zo ba ai, kawai kiranka nayi nace kace mutumin nan ya cire hotona a Instagram, amma ban ce ka zo ba” Kallonta ya dinga yi, at this point kamar he is lost of words, ta juya ta koma kitchen ta ajiye cup daya ta fito ta wuce sama tana rike da cup din nata shayin, still ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Khaleesat na gama shan tea din ta kwanta ta rufa da duvet ta lumshe ido tana addu’an Allah ya sa kar ta kara mafarkin da zai firgitata kamar daxu, kamar warce ta tuna abu ta bude idonta a hankali, ta jawo wayarta tana dubawa ko Housemate dinta ya biyo kiranta bata sani ba, amma sai taga bai biyo kiran ba, har ta ajiye wayar sai kuma ta sake dauka a hankali ta kunna data dinta tayi login WhatsApp, tun call din da yayi mata da safe bata daga ba bai kara mata magana ta WhatsApp din ba, and he uploaded a status not long ago, sauke idonta tayi ta kashe datan ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta, nan da nan mood dinta ya canza, duk yanda ta so tayi bacci kasawa tayi, sai juye juye take har kusan karfe sha dayan dare, mikewa zaune tayi daga karshe ta cire duvet din jikinta ta dau Jacket dinta ta saka sannan ta bude kofar parlon a hankali ta fita, tsaye tayi a corridor din sama tana kallon Ajay dake kwance kan 3 seater idonsa a lumshe don wutan parlon a kunne yake, ta fi minti biyu tsaye tana kallonsa, sai kuma ta juya ta koma dakinta ta dau one out of the new duvet Jay got for her, ta cire farin duvet din daga pack dinsa sannan ta fito daga dakinta ta sauka downstairs, tana tafiya a hankali ta isa har inda yake kwance, gida biyu ta linke soft duvet din ta rufa masa a jiki, ba wai hannunta ya taɓa sa bane but she could feel he is running temperature, tana rufa masa Duvet din ya cire daga jikinsa ya wurgar ba tare da ya bude ido ba yace “Gerrout Jay….” Sai kuma ya fara kokarin juyawa a kan kujeran sai ga shi a kasan carpet ya fadi timm, rufe bakinta tayi da sauri, ita kanta bata san meyasa dariya ya taho mata ba don da har jikinta yayi sanyi after noticing that he is running temperature, amma wannan reaction din nasa yayi mugun bata dariya, cikin magagi yake cewa “Bana son haka Jawwad, why are you stressing me, gerrout pls, i think i caught a cold, can you help increase the room heater before getting out” Sai kuma ya bude ido a hankali yana dafe kansa da yayi masa nauyi cause bai ji Jawwad na responding ba, ita dai kallonsa kawai take da mamaki, he look so shock ganinta, ya fara bin parlon da kallo, sai kuma ya kalleta ya hade rai yace “Kee, fita ki ban waje” Bata san sanda tayi dariya ba tace “Ai to bani na fadar da kai kasa ba, ni kawai bargo na kawo maka, and you heavily fell down on the Carpet” Ya kara daure fuska yace “Get out of my sight, am i a joke to you?” Ta wani juya kai, sai kuma ta nufi stairs tana waigansa har ta haura sama ta shiga dakinta, sai a sannan ta fara dariya tana mamaki shi kuma haka yake, har bayan minti talatin Khaleesat bata yi bacci ba tana dai zaune dakinta, after a while ta mike a hankali ta kara fita daga dakin nata tana leka downstairs, bata gansa kwance a parlon ba, hakan yasa ta fara saukowa downstairs, ta kalli duvet din da ya ajiye saman kujera da makullin gidan, sai kuma ta kalli bakin kofa ta karasa can ta murda kofar taji a kulle, window ta tafi tana leka Garage taga babu motarsa, ta dawo parlon ta dau makullin gidan tana kallo taga ya cire guda daya a ciki, she felt somehow ganin bashi da lafiya kuma still ya bar gidan a haka gashi snow din raguwa kawai yayi, ta fi minti biyu a tsaye after a while ta dau duvet din zata koma sama taji vibration din wayarsa, dube dube ta fara yi amma bata ga wayar kan kujera ba, daga karshe sai karkashin kujeran taga wayar, kilan sanda ya fadi daga kan kujeran shi ne wayar ya shige karkashin kujeran, screen din wayar ta dinga kallo ganin Jay ne ke kiransa, tayi silencing wayar ta wuce sama tana rike da wayar da duvet, sau uku Jay na kiran wayar, ita dai ta ajiye wayar gaban madubi tayi kwanciyarta. Washegari ta idar da sallan asuba bayan ta gama azkar dinta zata kwanta wayar Ajay ya fara vibrate gaban madubinta, ta dinga kallon wayar sai kuma ta karasa can tana duba screen din taga Jay ne still ke kiransa, ta juya ta koma saman gado tayi kwanciyarta, wajen karfe tara na safe ta gama shiri zata tafi school, tana tsaye gaban mirror din dakin tana kokarin daure gashinta sai ga Jay ya sake kiran wayar Ajay, ta dinga kallon wayar babu ko kiftawa sai kuma ta daga wayar ta sa handsfree bata ce komai ba, daga daya bangaren Jay yace “Why were you not picking ur calls Bruh, hope baka fita jiya ba cause naji anyi snow sosai, how are you doing?” Khaleesat dake sauraronsa ta sauke idonta tace “Good morning, he forgot his phone” Shiru Jay yayi daga daya bangaren for almost 10 seconds, can yace “Halysaah…” Tace “Good morning” Yace “Morning, where did he forget his phone?” Tace “In my apartment” Shiru Jay yayi bai ce komai ba, after some seconds a hankali yace “Ohk then” Daga haka ya katse wayar, Khaleesat ta dinga kallon screen din, sai kuma ta ajiye wayar tana kallonsa, sai bayan kusan minti daya ta iya ci gaba da gyara gashinta. Bayan Khaleesat ta gama abinda take ta saka wayar Ajay a jakarta zata tafi school da shi incase yaje zai amsa a department dinta, bata nuna ma Safiyyah komai ba da suka hadu a school duk da har sannan she is still very much angry at her, Safiyyah na kallonta tace “Yanxu dai sai hankalin ki ya kwanta don naje na duba na ga Aymaan ya cire hoton naku a account dinsa, ko wa yayi masa magana oho, ni kuma gashi bai min reply din WhatsApp message dina har yanzu ba” Khaleesat tace “Toh in ba dai he is irresponsible ba ta yaya zai dau hotona bai san ni ba yayi posting a account dinsa? Bai ma dau matarsa da muhimmanci ba in dai haka ne, who does that?” Safiyyah tace “Atoh, nima dai haka naji aka ce yana da mata amma ban sani ba ban kuma tabbatar ba” Khaleesat ta kalleta baki bude, Safiyyah tace “Wallahi kuwa, haka naji ana cewa, kuma wai yana da ciwon zuciya, ni dai bai min kama da me ciwon zuciya ba kuma ban ma yarda da wnn labari ba, kinsan yan mata na jin haushinsa saboda sai wanda ya ga dama yake kulawa shi yasa aka masa wannan sharrin, amma ki kalli mutum lafiyayye kamar sa a wani ce ciwon zuciya, gashi da son zuwa club” Khaleesat ta ma rasa abinda zata ce ma Safiyyah, kawai ta kauda kai don lamarin Sophie ya fara bata tsoro, the way she is saying it kamar bakinta da bakinsa suka yi magana ya gaya mata yana da ciwon zuciya kuma yana da mata, Safiyyah tace “Ni dai tashi mu je mu ci abinci yunwa nake ji, kilan ma haushin an sa shi ya cire hoton ne ya sa yayi banza da ni ta WhatsApp kuma na kirasa yaki picking, dama an masa shaidan girman kai and he is way too pompous of himself, bazai wuce Housemate dinki ya san sa ba shine yayi masa magana ya sauke hoton, dama ni fa sam gayen bai min ba ga wani jijji da kai da yake wai shi ɗan gidan Deputy sai kace ɗan vice president, deputy governors da ba a ma san da zamansu ba a Nigeria, gani yake yafi kowa a haka fa, kina kallon idonsa kinsan bazai rasa shan drugs ba” Khaleesat tace “Amma dai yanxu idan Abdul yaga hoton nan me kike tunani Safiyyah?” Safiyyah ta mike tace “Waye kuma Abdul? Pls mu je mu ga abinda za mu siya mu ci yunwa nake ji wallahi” Har Khaleesat ta bar school ranan bata ga Ajay ya zo amsar wayarsa ba, hakan kuma yasa taji a ranta he is sick. Mamaki abun ya ba Khaleesat ganin har ta dawo school Housemate dinta bai kirata ba ko kuma yayi mata magana ta WhatsApp, wayar Ajay ma bai sake kira ba, sai dad dinsa da ta ga ya kira wayar har sau biyu, da daddare taji zuciyarta ya kasa daurewa kawai tayi ma Housemate din nata magana via WhatsApp, ta gaishesa sannan ta tambayesa ya jikin cousin dinsa, after almost 15 minutes yayi mata reply da Alhamdulillah, daga nan kuma bai sake cewa komai ba, she was taken aback, haka nan ta ajiye wayarta kawai ta kwanta tana jin wani iri a zuciyarta. Bayan kwana biyu Khaleesat da Safiyyah suna zaune a wajen department dinsu, Khaleesat na yi mata explaining wani course dinsu da tace bata gane ba, Murya can kasa taji Safiyyah na cewa “Ji gantalallen Aymaan din can, he is coming toward us, kar ki dago kanki” Khaleesat bata dago kai ba, ta ci gaba da bayanin da take ma Safiyyah, har ya iso inda suke zaune, calmly yace “Good evening Safiyyah and Khaleesat” Safiyyah ta washe baki tace “Hi Aymaan, how are you doing ya kwana biyu?” Yace “Lafiya lau, ya karatu?” Safiyyah na washe hakora tace “Alhamdulillah, tun ranan bamu sake haduwa ba sai yau” Yana kallon Khaleesat yace “Good evening Khaleesat” Ba tare da Khaleesat ta kallesa ba fuskarta babu fara’a tace “Ohk” Ya kalli Safiyyah yace “Naga kamar kawar taki a fusace take” Safiyyah tayi dariya da iyakarsa fuskarta tace “Ai bata ji dadin abinda kayi mata bane, duk da na fahimtar da ita ba da wata manufa kayi hakan ba, kuma ta fahimta, ita tsoronta ma kar matarka ta ga hoton” Yana kallon Safiyyah yace “Ke kika min auren?” Safiyyah tayi dariya tace “To ai kaga za a sa maku ido kuma shi yasa ta damu” Yace “Ohk in nasan haka ne ai da bazan sauke hoton ba, don wani guy that is full of himself i think saurayinta ne ya sameni yayi min magana about it, yasan ni, na sansa a kasar nan amma ba mu taɓa ma juna magana ba, had i know ban cire hoton ba in ga abinda zai yi” Safiyyah ta kwantar da murya tace “Kaga Aymaan Khaleesat fa matar aure ce babu wani boye boye….” Aymaan yayi wani murmushi without letting Safiyyah to go further yace “Ban yarda ba, shi wanda ya min magana in cire hoton zan nuna masa ba aurenta yayi ba ai….” Khaleesat ta daga kai fuska daure tace “Pls delete my pictures off your phone Mr man, don ban san ka ba, ban hada komai da kai ba ban kuma ga dalilin da yasa zaka yi posting dina ba, no sane person will do such, plss take my pictures off ur phone matar aure ce ni” Tana kai wa nan ta tura ma Safiyyah Laptop dinta ta mike ta figi handbag dinta ta bar wajen ko waigawa bata yi ba, Aymaan ya bi ta da kallo yana ɗan murmushi, Safiyyah tayi tagumi don har ta gaji da ce ma Khaleesat ta koyi siyasa da iya zaman duniya, da faram faram ya kamata ta samu ta rabu lafiya da Aymaan amma ga abinda tayi, Aymaan ya gyada kai yace “We shall see then” Safiyyah ta kallesa tace “Kasan tana da aljanu ne fa Aymaan kuma abun har ya taɓa brain dinta, da sauki ma basu tashi a nan ba, don wallahi duka take kuma in ta fara famfala gudu da kyar ake kamota, shi sa kullum zaka ganta babu fara’a ni kadai nake iya zama da ita wallahi, wanda kuma yasa ka cire hoton ba saurayinta bane believe me…” Aymaan yayi wani murmushi yace “Nima su gareni, kin ga dai dai kenan” Daga haka ya juya ya bar wajen, Safiyyah ta kara rafka wani tagumi. Khaleesat na isa gida wajen karfe biyar zata bude kofa taji kofar a bude, ta kalli parking space taga babu mota a nan, tura kofar tayi a hankali ta shiga parlon, zaune ta gansa ya kunna TV yana kallon kwallo, ko juyowa bai yi ba har ta karasa cikin parlon tana kallonsa, ya mike without looking at her yace “Bani wayata” Tace “Ya jikin?” Sai a sannan ya kalleta yace “Nace maki bani da lafiya ne?” Tace “A’a kawai na gane idan baka da lafiya surutu that is not comprehensible kake yi a bacci…..” Tana murmushi ta kare maganar tana kallonsa.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
