Halysaah Page 118 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 118
Bayan fitar Ajay da minti goma Khaleesat ta daure gashinta ta sauka daga saman gadon ta shiga bandaki, kallon set din tsadaddun oral hygiene products dinsa dake bandakin ta dinga yi, duk sai da tayi using mouthwash din da ta gani a wajen ta kuskure bakinta sannan tayi wanka da daya daga set din Body wash din da ta gani, bayan ta gama ta bude inda yake ajiye set of towels dinsa tana ta kallo kamar ta dauka kamar kuma kar ta dauka, can dai ta tura baki ta dau daya ta goge jikinta sannan ta shanya a bandakin, ta mayar da kayan baccinta ta dauro alwala ta fita daga bandakin, tana ta zaune gefen gado don babu hijab din da zata yi sallah bayan abinda kare yayi mata da hijab dinta jiya, bata ma ga hijab din a dakin ba, gaba daya incident din jiya ya dinga dawo mata lokaci daya jikinta yayi sanyi zuciyarta ya dinga bugawa, to me tayi ma karen nan ne haka da ya tsaneta baya son ganinta, hawaye taji ya kawo idonta ta fara gogewa a hankali, ganin lokaci na ta wucewa bata yi sallah ba ta dau duvet dinsa ta lulluba da shi saboda kayan baccin jikinta that is very light and translucent, ta nufi kofa tana leka parlon kamar munafuka, zaune ta samesa kan kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran hannunsa rike da Glass din soft drink ya lumshe idonsa, ta jingina da kofar Bedroom dinsa a hankali tace “Ina son zan yi sallah, ka dauko min wani hijab a can dakin pls” Sai a sannan ya bude idonsa jin muryarta amma bai kalli direction dinta ba, har yaji kamshin Body wash dinsa, wato wanka ma tayi masa a bandaki, after almost 30 seconds ya juya ya kalli inda take tsaye, marairaicewa tayi tana kallonsa, shi kam ya dinga kallon farin duvet dinsa da ta lullube da shi har yana jan kasa, can ya kalleta yace “Kee, wai uban me ya kawo ki gidan nan?” Ta turo baki taki cewa komai, ya ajiye Glass cup din hannunsa ya mike yace “Koma ciki ki dauko duk wani property dinki ki zo ki koma inda kika fito” Ta hade rai kamar zata yi kuka tace “Ni wallahi bana son apartment din, bazan iya zama a can ba ni kadai” Ajay ya mata wani kallo yace “Dole kuwa za ki zauna tunda dama can ke kadai kike zama, fito ki tafi” Kamar zata fashe da kuka ta juya ta koma dakin tana cewa “Ni wallahi babu inda zan je, bana son apartment din kuma, kawai ni kadai a katon gidan nan” Tana fadin haka ta tura kofar Bedroom din ta rufe, Ajay ya shafa kansa yana kallon kofar dakin, sai kuma ya koma ya zauna ya tallabi chin dinsa, after almost 10 mins sai gata ta sake lekowa daga cikin dakin ta marairaice tace “Don Allah ka dauko min wani Hijab a daki na, kaga har gari ya fara wayewa ban yi sallah ba fa” Ya wani kalleta yace “Ni zan dauko maki hijab saboda baki da hankali ko?” Tace “To ae saboda karen ne” Yace “Kin taɓa ganin karen a sama?” Shiru tayi tana kallonsa, zata fito ya wani hade rai yace “Idan baki koma kin ajiye min duvet ba zaki sha mamaki yanxu” ta tura baki ta juya ta koma dakin ta ajiye masa duvet dinsa da take lullube jikinta da shi saboda kayan baccinta, bandakinsa ta shiga tana kallon farin towel dinsa da ta shanya, can ta dauka ta fito, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta dora towel din a kirjinta tana tafiya kamar mara gaskiya ta fita parlor, da mamaki Ajay ya bi ta da kallo babu ko kiftawa ganin yanda ta maida masa daki public room, ita kuwa taki yarda ta kallesa ta nufi kofar fita daga parlon da sauri gabanta na faduwa, a haka har ta fice daga parlon, tana isa corridor ta hango legend downstairs yana zarya a parlor, duk da bai ganta ba haka ta kwasa a dari da sittin kamar mahaukaciya ta koma part din Ajay tana shiga parlon ta nufesa da gudu ta zauna kusa da shi cikin gigicewa tace “Wallahi i saw it” Sai kuma ta fashe da kuka kamar er yarinya tana kallonsa, shi dai kallo daya yayi mata ya dauke kai don ba tare da towel din ta dawo parlon ba, ita kanta bata san ta gantalar da towel din a wajen gudu ba, ganin yaki kulata ta mike zata wuce dakinsa ya bi ta da kallo, within few seconds ya dauke idonsa ya maida wani direction daban after seeing what he wasn’t prepared to see, Sai da Khaleesat ta koma cikin dakinsa ta hango kanta ta madubi ta zaro ido with shock ganin babu towel a jikinta, ta tafi edge din gado ta zauna da sauri tana zumburo baki, after 10 mins ya bude kofar dakin ya jefa mata hijab din hannunsa without looking at her ya juya ya bar wajen…. Bayan ta idar da sallah ta gama azkar dinta sannan ta kalli wayarsa dake ajiye kan bedside drawer, mikewa tayi ta tafi ta dau wayar da sauri ta duba taga babu Password jiki ta koma kan darduma ta zauna ta bude wayar ta shiga call logs dinsa, kallon yanda yayi saving numberta ta dinga yi babu ko kiftawa, can ta wani tura baki ta fara scrolling taga uban miss calls din da tayi masa and it is not as if baya picking sauran calls dinsa, nata ne kawai baya picking, ta hade rai ta shiga WhatsApp dinsa, taga last messages da aka turo masa was from yesterday night alamar rabonsa da bude data tun jiya da daddare, tayi searching contact dinta sai gashi ya fito, ta shiga ciki, babu ko kiftawa ta dinga kallon screen din wayar ganin blocking dinta yayi ta WhatsApp din ashe, after some seconds ta kunna data dinsa messages dinsa duk suka shigo, wani number da taga anyi saving da Pinky ta bude message din da aka turo tun karfe biyun dare taga an rubuto “Good Morning Aristocrat, hope u slept well, jiya nayi bacci sanda ka kira, idan na dawo school zan kira direct call, have a nice day, bye” Khaleesat ta maimaita message din a zuciyarta yayi sau uku, ta kalli WhatsApp call da yayi ma number wajen karfe takwas na daren jiya, scrolling chat dinsu ta dinga yi tana karantawa, har sai da ta kai dai dai inda aka turo masa hotunan Birthday tana duba hoton taga Inteesar ce, ta dinga kallon hoton for almost a minute, sai kuma ta ci gaba da scrolling chat din nasu, bude kofar dakin aka yi tayi saurin cusa wayar cikin hijab dinta tayi keeping straight face tana kallon wani wajen daban, ko kallonta bai yi ba ya tafi zai dau wayarsa inda ya ajiye amma yaga babu wayar a nan, tana ganin haka tayi dubara ta cusa wayar a kirjinta don rigar baccin jikinta na da tight-fitting daga chest dinta, Yana ta tsaye for like 15 seconds yana kallon wajen da yasan ya ajiye wayarsa, can ya kalli other side din nan ma bai ga wayar ba, ita dai Khaleesat taki yarda ta kallesa fuskarta a daure, ya juya ya fita daga dakin zai duba parlor duk da shi dai yasan wayar a bedroom dinsa ya bar sa, amma ya gama duba parlon gaba daya bai ga wayar ba, har kasa sai da ya sauka yana duba wayar, can dai ya dau other phone dinsa yayi dialing number wayar, Khaleesat na jin vibration din wayar a kirjinta don ma it’s very low amma bata fito da wayar ba, bayan minti goma sai gashi ya dawo dakin yana mata wani kallo yace “Bani wayata kar in sa ki kuka yanxun nan” Tayi kamar bata san da ita yake ba don ko kallon inda yake tsaye taki yi, bude kofar dakin yayi sosai yana kallon parlor ya ɗaga murya yace “Hey Legend” Wani uban tsalle ta doka sai ga ta kusa da shi tana zaro ido a tsorace tace “Don girman Allah kayi hakuri, wallahi zan baka” Ya daure fuska yace “Bani” Sai ga Legend ya shigo parlon da gudu wai har yaji kiran da yayi masa, Khaleesat ta kurma ihu ta makale gefen Ajay tana rirrikesa cikin rawan jiki tace “Don girman Allah kace ya tafi wallahi zan baka, send it away plsss” Ajay ya tura kofar dakin slightly, ya juya yana kallonta yace “Where is it?” Ɗaga hijab dinta tayi da sauri tana zaro ido zata ciro wayar ya dinga kallon kirjin nata, tana ganin haka ta hade rai ta sake hijab din ta juya masa baya taki ciro wayar, bata ankara ba sai ji tayi ya fara fixge hijab din ta bayanta, ta rike da sauri tana zaro ido taki bari ya cire tana cewa “Nooo, don Allah ka tsaya zan baka wallahi” Kokuwa ta fara yi da shi taki yarda ya cire mata hijab din ganin da gaske cirewa zai yi, Legend ya ɗan leko dakin saboda noise din da yake ji, Khaleesat na ganinsa da karfi tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Ajay ya ɗagata sama da hannu daya ya tafi yayi dumbing dinta kan gado ta kwanta tana jawo duvet dinsa da sauri zata rufa da shi, kwace duvet din yayi sannan ya fixge hijab din gaba daya daga jikinta yana kallon chest dinta da ta cusa wayarsa, dama tana ganin Legend a bakin kofa ko yunkurin hanasa cire hijab din bata sake yi ba sai ma jawosa da take yi cikin tsoro tana son ya boye ta tana cewa “Plss send it away, shigowa zai yi, don Allah ka koresa” tsit tayi ganin ya fado kanta kawai daga jawosa, ta kasa kwakkwaran motsi don ji tayi kamar duk weight dinsa ya sakar mata, nan ta fara turasa da kyar tana zaro ido don ko magana ta kasa, amma kamar tana tura Rock don ko gezau, da wata irin muryar da bata san sa da shi ba yana kallonta directly in the eyes yace “Me kika yi da wayata?” Tana numfashi da kyar tace “Wallahi ba komai, ka duba ka gani” kawai ji tayi ya zura hannunsa ta kasan rigar jikinta a hankali, ta zaro ido cikin gigicewa bata san sanda ta kankamesa ba don sai taji kamar an hadata da naked electric wire cikin rawan murya tace “Na shiga uku, ba ta nan yake ba wallahi yaya, ka tsaya in ciro da kaina plss” ashe all this while ba duk weight dinsa ya sakar mata ba don tana kankamesa yayi collapsing gaba daya a kanta, hakan kuma bai hanasa kutsa hannunsa dake cikin rigarta har zuwa saman kirjinta ba, she couldn’t even react any more tsabar wani irin shock da taji a ko wani gaɓa na jikinta jin hannunsa a plain chest dinta yana fondling dinsa gently, tuni salon numfashinsa ya canza taji lips dinsa na bin wuyanta yana sauke wani ajiyar zuciya, bakinta; na rawa ta hade laps dinta tace “Plsss i want to use the restroom, ga wayarka na cire maka wallahi, i want to pee plsss” abubuwa da yawa suka yi mugun tsorata Khaleesat a wannan lokacin don ko Abdul bata ji masa irin wannan tsoron ba, cikin rikicewa take ta ce masa zata je tayi fitsari duk tunaninta baya jin ta ne, cikin wata muryar da bata san sa da shi ba me kama da rada taji yace “Yi a nan”

