Halysaah Page 4 By Khaleesat Haydar
✨✨ HALYSAAH ✨✨
By Khaleesat Haiydar✍🏻
4…..
Khaleesat ta zauna gefen gadon dakin Safiyyah duk jikinta a sanyaye, jawo wayarta tayi tana duba agogo taga karfe bakwai har da rabi, sam bata ji zata iya kwana gidan nan ba, tasan probably yanzu House mate dinta na gida, to ya ta iya? Hakan dai zata koma gidan tayi masa knocking, the thought of this made her weak, shigowar Safiyyah dakin yasa ta daga kai, Safiyyah ta rike haɓa tace “Kinsan kuwa shegiyar matar nan bata ajiye mana abinci ba, ai ko sai ga yaya Musty kamar an jefosa kuma night shift fa yake yi wallahi, kinga ko ba komai sai ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki yau, abincin da na lissafo masa ko rabinsa baza mu iya ci ba kuma kwalelenta sai dai in har shi yayi dubaran siyo mata nata daban, ban taɓa ganin me tsinannen hali kamar matar nan ba tirr, ni ai na zata in mutum zai taho wata kasar barin baƙin halinsa yake a gida, to ita dai da nata ta taho wallahi” Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace “Lallai kam, kinga ni kuma tafiya zan yi fa, da ma bai siyo abincin ba, yanzu Housemate dina ya kirani yace he is back home” Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallonta, can tace “Ban gane ba, yaushe kika samu number Housemate dinki har ya kira ki? Wallahi ban yarda ba kawai so kike ki tafi, bari ki ji in dai don Surayya ce nima fa zaman hakuri nake da ita a gidan nan Khaleesat, mugun halinta bai da part 2, gwara kawai kiyi zamanki in ma shekara zaki yi a nan babu yanda ta iya tunda ba gidan ubanta bane kuma warmly Ya Musty zai yi welcoming din ki” Khaleesat tace “Sophie ni fa tunda Housemate dina ya dawo bazan kwana a gidan nan ba, dama bani da kayan da zan canza sannan na ma manta na bar kaya a washing machine kin ga bani kadai bace a gidan, may be zai yi laundry shi ma” Safiyyah ta hade rai tace “A takaice me kike nufi kenan? Kina ji ina lissafa ma Ya Mustapha abinda zai siyo mana don walakanci ki ce ke zaki tafi? shima ai bazai ji dadi ba idan ya dawo da abincin yaga kin tafi kuma saboda ke ya fita ya siyo don in dan ta nice sai dai yunwan ya kasheni in bai ga dama ba” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Zan jira ya dawo, sai in tafi da abincin gida kawai” Safiyyah da har ranta ya ɓaci tayi mata banza ta tafi ta dau wayarta tana dannawa, Khaleesat dai bata sake cewa komai ba, komin fushin Safiyyah ita kam baza ta kwana gidan nan ba, after a while Ya Mustapha ya dawo gidan da abincin da ya siyo masu, Safiyyah ta mike ta nufi kofa bayan ya kirata a waya, Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita sannan tayi murmushi, Safiyyah ta karasa dinning table ta dau abincin da Cousin din nata ya ajiye masu ta koma daki, iya wanda zata ci ta cire ta bar ma Khaleesat duk abincin, Khaleesat tace “Ya zanyi da abincin nan me yawa Sophie?” Ba tare da Safiyyah ta kalleta ba tace “Wannan kuma ke kika sani” Khaleesat bata son jan maganar yayi tsayi kawai ta mike ta dau veil dinta da handbag sannan ta dau ledan abincin tace “Sai mun hadu gobe, thank you so much dear” Safiyyah tace “Kinyi order din ride ne?” Khaleesat tace “Sure” Mikewa Safiyyah tayi suka fito dakin a tare, dai dai fitowar Mustapha parlor shi ma, yana kallonsu da mamaki yace “Ya aka yi kuma?” Safiyyah ta langwabar da kai tace “Her Housemate is back, shine kawai zata tafi gida wai” Yace “Isn’t it late?” Safiyyah ta kyabe baki tace “Nima dai haka nace mata” Ya kalli Khaleesat da ta sunkuyar da kanta, yace “Kiyi hakuri ki bari gobe mana Khaleesah, yanzu ai dare yayi….” Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta dago kai cikin sanyin murya tace “Akwai abinda nake son zan yi ne idan na koma gida” Mustapha ya daga kafada yace “While, if you insist….” Ta gyada masa kai tace “Nagode” Safiyyah ta wani harare ta, Mustapha yace “Zan koma aiki ne dama, mu je sai inyi dropping din ki ko” Khaleesat bata yi expecting offer din nasa ba, ta ɗan kallesa tace “Na riga nayi order din Lyft ai….” Safiyyah ta mata wani kallo tace “Haka kuma you can cancel it ai ko….” Kasa cewa komai Khaleesat tayi, lkci daya ta zama uncomfortable, Mustapha dai kallonta kawai yake, after few seconds a hankali tace “Ohk” in response to Safiyyah, Kofa Mustapha ya nufa, Safiyyah tayi kasa da murya tana kallonta tace “Ke in zaki saki jiki ki saki jiki, a ko da yaushe sai kin nuna ke er…. Ya ma sunan wannan unguwan naku a kano?” Khaleesat ta dinga kallonta, can ta juya ta nufi kofa tana tafiya slowly, Safiyyah ta fara dariya kasa kasa tace “Good night girlfriend” Ko tankata Khaleesat bata yi ba. Yana zaune cikin motarsa yana jiranta har ta karaso, ta bude gaban motar ta shiga, sai kallon entrance din gidan take tana fatan kar matarsa ta fito ta gansu, ya tada motar suka bar garage din, sai a sannan ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tayi fastening seat belt dinta a ranta ta dau alwashin wannan shine zuwanta na karshe gidansu Safiyyah, bayan sun hau saman hanya taji yace “Where do u stay?” Idonta na kan titi ta gaya masa, yace “Co-living kike yi kenan?” Tace “Um” Yace “Menene yasa baki dawo ku zauna gidana tare da Safiyyah ba instead of living alone with a stranger?” Ko rufe baki bai yi ba tace “Ai yawanci ni kadai ce a gidan, my Housemate is not always around” Yace “Ok then” After almost a minute yace “Kema er kano ce?” Tace “Um” Yace “Wani anguwa?” Tayi shiru, sai kuma ta ɗan kallesa ta gefen ido taga kallonta yake at the same time yana tuki, ta sauke idonta kasa ta gaya masa, she is so uncomfortable with him, Yana gyada kai yace “Ohk, i am also from kano, Sharada to be precise” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, cikin minti 13 ya kawota gida, ya juya yana kallonta bayan yayi parking, daukar ledan abincin tayi tace “Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi” Wayarsa taga ya mika mata, ta daga kai ta kallesa, yace “Ki sa min digit dinki sai mu dinga gaisawa, in kina bukatar wani abu kuma feel free to ask me anytime” Khaleesat ta sauke idonta, ita da ta sani babu abinda zai kai ta gidansa yau, da kawai dawowarta tayi ta zauna bakin apartment dinta ta jira har sanda Housemate dinta ya ga daman dawowa ya bude mata kofa, muryarsa ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi ta daga kai da sauri ta kallesa, bata ma san me yace ba taga dae yana kallonta, da kyar tayi stretching hannu ta amshi wayar ta sa masa digit din nata, yayi dialing, ita dai kanta na kasa, wayarta dake cikin jaka ya fara vibrate, yace “Kiyi saving nawa digit din” Tace “Um” Yace “Good night, take care Khaleesah” Tayi karfin halin cewa “Nagode” Daga haka ta bude motar ta sauka, kallon window din kitchen na apartment dinta tayi ganin wuta a kunne, sannan taga mota a Garage, she felt relieved sanin cewar her Housemate is around, ta zaga zuwa gaban apartment din tana jin sanyi na shigarta sosai don sanyi ya fara shigowa kasar, knocking din kofar parlor tayi gently, sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji muryarsa yace “Who is there?” Ta kauda kai a takaice tace “Somebody” Yace “Somebody? I am not expecting somebody this late” Ta wani hade rai tace “Ni ka bude min kofa in shiga gida” Yace “Ke wa zan bude ma kofa?” Kin cewa komai tayi cause she is already provoke, yace “Ohk then, i am going back to my room after all i am not a door keeper” Tana jin haka a fusace tace “Don Allah ka bude min” Yace “Ke wa?” Tace “Ban gane ni wa ba?” Yace “Ohh, tsawa ma kike min?” Ta kara marairaicewa tace “Don Allah ka bude mana” Yace “To ai ni ban san wacece ba, baki da suna ne?” Shiru tayi tana kallon kofar kamar zata fashe da kuka, Yace “Ke zan fa yi tafiyata daki in baza ki fadi sunanki in san wa zan bude ma kofata ba cikin daren nan” Ta sauke idonta kasa, after a few seconds ta dake tace “Khaleesat” Yace “Halysaah…” Wani harara ta zabga ma kofar, Kamar yana counting harufan sunan yace “Ha.. lee…saah” A fusace kamar zata yi kuka tace “Sanyi fa nake ji ka ki bude min kofa, ko don ba kai bane tsaye cikin sanyin?” Bude kofar yayi yace “Baki san da sanyin ba kika je kika yi dare a titi?” Ko kallonsa bata yi ba ta kusa bangajesa ta shige parlon fuskarta a murtuke, yace “Wajen saurayinki kika tafi kenan kika yi dare, naga ma shi ya ajiye ki a mota, Allah sa ba me sa ki kukan nan bane dai” Direct dakinta ta nufa without even looking at him abinda ya fada na sinking zuwa cikin kanta, ya bi ta da kallo yace “Ok…. ga Door keeper dinki ya bude maki kofa ko? Tomorrow is another day, better look for ur lost key in ba so kike ki kwana a waje ba next time” Tuni ta bude kofar dakinta tayi shigewarta ta sa makulli tare da jan dogon tsaki. Da safe tunda Khaleesat ta tashi take zaune tana tunanin how today will be like, taje schl din ne ko ta hakura kawai tunda bata da makulli yanzu, zaro ido tayi bayan ta tuna lecture din da za su yi ranan, she just can’t miss that class don course din is a bit complicated, mikewa tayi ta shiga bandaki, wajen karfe tara ta fito parlor hoping house mate dinta bai fita ba, don jiya wajen karfe sha biyu da rabi na dare ta fito don saka abincin da bata iya ta ci ba a fridge ta gansa kwance a parlor yana bacci, har ta gama abinda zata yi a kitchen ta fito bai farka ba, tun zuwansa gidan ranan ne rana na biyu da taga ya kwana a gidan, babu kowa parlorn ta karasa kusa da tagan parlon tana leka Garage ko zata ga motarsa taga motar na nan alamar he is around, ajiyar zuciya ta sauke don da ya fita shkkn babu tafiyarta makaranta kenan, kitchen ta tafi ta hado shayi ta debi cookies ta dawo parlon, har ta gama breakfast bai fito parlor ba, sai kallon agogo take don goma ta kusa gashi bata son tayi latti, kuma ita dai bazata taɓa masa maganar ya bude mata kofa zata fita ba, goma saura minti goma ya fito parlorn, ita dai bata dago kanta ba tana ci gaba da danna wayarta, taji yace “Good Morning, Halysaah” Without looking at him tana ci gaba da danna wayarta kamar tana ma kanta magana tace “Ok” Ta gefen ido ta bi sa da kallo ganin ya nufi kofa ta mike ta bi bayansa, yana lura da ta biyosa sai ya fasa bude kofar, ya juya yana kallonta keeping a serious face yace “Me ya faru?” Ta kauda kai taki cewa komai, mayar da makullin yayi aljihunsa zai bar wajen ta wani kallesa tace “Ni dai ka bude min kofa zan tafi makaranta” Yana gyada kai yace “Ohhh, ohk kin boye makullinki ne don in zama door keeper dinki dama?” Taki kallonsa don bata ma san me zata ce masa ba, ganin da gaske barin wajen zai yi ta marairaice tace “Makaranta zan tafi fa” Ya juyo yace “Be a good girl and beg politely first…..” Shiru tayi tana bin sa da kallo har ya koma cikin parlor ya zauna kan kujera, Ta dake da kyar tace “Please ka bude min. i am going to school” Yace “Ban ji ba” Takaici yasa ta dauke kai taji ranta ya kara ɓaci, ganin lokacinta kawai take ɓatawa ta sake juyowa trying to be calm tace “Plss ka bude min kofa i am going to school” Ɗan murmushi yayi ya mike ya dawo bakin kofar ya ciro makullin a aljihunsa yace “Never knew u can be this Obedient” Ita dai bata kallesa ba, ya bude kofar yace “In kika sake yin dare baza ki shigo gidan nan ba sai dai ki kwana bakin ƙofa ko kuma a Garage…” Bata tankasa ba ta fice daga parlon with annoyance almost brushing his shoulders, ya bude baki yana bin ta da kallon mamaki yace “Ohh, is this ur thank you??” Tuni har ta kusa titi abun ta, ta ja tsaki feeling so fed up with him. Bayan Khaleesat sun fito daga aji Safiyyah tace “Kinsan me Khalee?” Khaleesat ta juya ta kalleta, Safiyyah tayi dariya har da kyakyatawa tace “Wai Ya Musty ke tambayata ko kina da saurayi” Sai da gaban Khaleesat ya fadi, Safiyya bata fasa dariyar da take ba tace “Wallahi kuwa, he chatted me up yesternight wajen karfe sha biyu, bari ma in nuna maki ki ga, ni ko nace masa baki da kowa wallahi” Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace “Ban gane bani da kowa ba Sophie?” Safiyyah tace “To kina da shi ne? To in kallon saurayinki kike ma Abdul to ni wallahi kallon ɗan daba nake masa, ni dai nace ma Ya Musty bakya kula kowa saboda karatu don haka baki da saurayi, kema kin dai san da Ya Musty na da mugun hali da tuni na fesa maki ni da bakina baya shiru, ai ko don wannan er banzar matar tasa zan so ya kara aure, kuma ace kawata ya aura huhuhu za a ga rashin nasiha da jahilci wajena” Khaleesat ta mike tana gyara Veil din jikinta tace “Zan tafi gida sai gobe” Safiyyah ta tsuke fuska tace “Ban gane zaki tafi gida ba daga na kawo maki maganar arziki” Khaleesat tace “Wallahi da na sani babu abinda zai sa in bi ki gida jiya Safiyyah, haba fisabilillah, put ur self in the wife’s shoe in kece aka ma haka zaki ji dadi?” Safiyyah tace “Godforbid, her shoes will never size me sef kafin in sa kafata ciki Khaleesat, ai ni bani da mugun hali kamar ta, kina ga fa ko tsayawa ta amsa gaisuwarki bata yi ba ta wani ƙara waya a kunne ta wuce daki ita er iska, sannan bari kiji jiya iya cikina ta ajiye abinci a kitchen bayan nace mata nan zaki kwana kuma ta sani, ni dai wallahi in kika ce baki son yayana nice kawai baki so, Ya Musty bai da wani aibu wallahi, ga arziki ga Ilimi ga kyau, baza ma ki ce ya taɓa auren wata er iska ba wai ita Surayya, ɗan saurayi da shi” Khaleesat tace “In matarsa kike son tura ma haushi ai kema zaki iya aurensa tunda he is ur cousin brother kuma da aure tsakanin ku” Daga haka Khaleesat ta bar wajen tayi wucewarta, Safiyyah tace “Oho dai wallahi ce masa zan yi kin amince sai dai ki mutu, haka kawai kin makala ma kanki ɗan daba kina kiransa da wanda zaki aura, ki auresa ki ci uwar me da shi, wannan har duka sai ya dinga nakada maki babu me kwatarki in ku ka yi aure” Khaleesat na isa gida taga babu motar Housemate dinta a parking space, jingina tayi jikin entrance din apartment din nasu, gashi ta gaji sosai ga yunwar da take ji, babu wanda ta saba da shi a Neighborhood din balle ta shiga gidansa, balle su turawa basu yarda da hakan ba ma, ta kusa twenty minute a tsaye sai ga motarsa ta hango, sunkuyar da kanta tayi har yayi parking ya karaso kofar entrance din, gefe ta koma without looking at him, tun kan ya karaso kofar apartment din ya sa hannu a aljihunsa yaji babu makullin, ya ɗan bude ido still yana laluba duk aljihunsa, sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, juyawa yayi ya koma motarsa ta bi sa da ido, ya gama dube dubensa a motar bai ga makullin ba, ai tana ganin yanda yake dube dube tasan kilan ya yar da makullin, shikenan ta shiga uku, she is soo tired, har wani jiri take ji a tsayen da take, dawowa yayi yana kallonta yace “Look Halysaah, i think i left the key at where i am coming from” Ita dai bata ce komai ba kuma bata bari ta hada ido da shi ba, yace “Ko zaki shiga apartment din Neighbor dinmu kafin in dawo” Sunkuyar da kanta tayi still keeping mute, yace “Or ain’t you familiar with them?” A takaice tace “Eh” Yace “Ok i will be back as soon as possible” Juyawa yayi ya koma gun motarsa ta bi sa da wani kallo…. Khaleesat na ta tsaye har bayan wani minti sha biyar sai gashi ya dawo, yana kallonta yace “Allah ya taimake ki na gani” Wani kallo tayi masa wato ita Allah ya taimaka ma, yana bude kofar tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta ba tare da ta juya ba, sai da ta kwanta na kusan minti sha biyar sannan ta mike a hankali ta shiga bandakinta, bayan Khaleesat tayi wanka tayi sallah tana zaune kan darduma taji yayi knocking kofar dakinta, kallon kofar take bata ce komai ba kuma bata amsa ba balle ta tashi, taji yace “Halysaah” Bluntly tace “Me ya faru?” Jin ya murda kofar dakin ta zaro ido ta mike tsaye da sauri tace “What?” Tuni ta isa gun kofar ta bude tana masa kallon tuhuma, ledan hannunsa ya ajiye mata yace “I got you food, naga kin yi laushi” Ta kalli ledan, ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya koma parlor, sauke idonta tayi, bayan few seconds ta duka ta dau ledan ta juya ta koma dakin. Khaleesat ta bude abincin da ya kawo mata ta fara ci kenan wayarta ya fara vibrate, mikewa tayi ta bude handbag dinta ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ke kiran ta, zaunawa tayi gefen gado tana kallon screen din wayar har sannan gabanta na bugawa, kafin kiran ya katse tayi karfin halin dagawa ta sa handsfree sannan tayi sallama cikin sanyin murya, maimakon ya amsa sai ji tayi yace “Wato all this While ni kike jira in kiraki ko Khaleesat?” Ta sauke idonta a hankali tace “To ai cewa kayi duk sanda kake son magana da ni zaka kirani amma kar in sake in kira ka” Yace “Don nace kar ki kirani sai ki ki kiran nawa? Me yasa baki reason ne?” A sanyaye tace “Kayi hakuri” Yace “In ban hakura ba ya zan yi da ke? Ai saboda baki damu da ni bane yasa kika zama comfortable without calling me all this while, ko da bazan daga ba ai kamata yayi ki kira” Cikin sanyin murya tace “Kayi hakuri” Yace “Yaushe za ku fara jarabawa?” Tace “Probably nan da 6 to 7 weeks” Yace “I can’t wait har zuwa nan da sati bakwai ban gan ki ba Khaleesat, idan na samu lokaci zan shigo anytime from now in sha Allah” Shiru Khaleesat tayi as if trying to process what he just said, yace “Hello” Da sauri ta kifta ido tace “Na’am ina ji” Yace “Me yasa kika yi shiru? Ko baki son in zo ne?” Tayi yake tace “Aa ban yi shiru ba network ne, ban ji me kace ba” Yace “Ohk, nace you should expect me any moment from now” A hankali tace “Toh Allah ya kai mu” Yace “Ameen, me kike yi yanzu?” Tace “Abinci nake ci” Yace “Ohk switch to video call” A hankali tace “Toh” Mayafinta ta jawo sannan tayi yanda yace mata.
07087865788 for more info✍🏻
