Hausa novels

Gargadar So Chapter 81 By M Shakur

Turo mata baki Khaleel yayi ashagwabe yace “kinata kadamin ass a riga shine nadan taba fa” dasauri tashiga karban kanta ganin neman kasheta yakeyi da jin kunya Khaleel yahanata yana kallon kirjinta ta gaban rigan, dasauri Hawwa tace “wai bazaka saken naje nai salla ba”? Kaman zaiyi kuka yace “i want to kiss you kadan sai muje, rabon danai kissing naki since that day in that house dakina rashin lafiya fa” wani irin runtse idanu Hawwa tayi ta fizge kanta da sauri ta sauka daga gadon tai kofa maye harya manta yayi kissing nata wajen biki to ita bata manta da komiba, tace “kai salla kayi jam’i a mosque na la’asar naughty boy” tabude kofa tafice da sauri yabita da kallo yana murmushi tashi yayi baccin dayayi yamai dadi bathroom yashiga ya cire kanulan hannunshi yadauro alwala yafito ya sanya jallabiya yayi zuhur kaman ba Khaleel ba saiya tashi yawuce ya sanya farin jumper na farin material yafesa turare yafito yana kamshi sosai kai tsaye kawai yabude kofan dakin Hawwa yashiga daidai tana fitowa daga bayi daure da towel ko kadan ta manta bata saka key ba. “Wayyyooo!” Hawwa tafadi a tsorace takoma cikin bayin da sauri tana datse kofa shima Khaleel jiyayi kaman alwalanshi zai karye dasauri yajuya kawai yafita, sunada masallaci agidansu ta wajajen gateBabanshi na zaune cikin masallacin da an kira salla jira suke atada yaga Khaleel yashigo kara juyowa Excellency yayi cus he can count how many times yataba ganin Khaleel acikin masallacin nan kafin yamai magana aka tada duk suka tashi sukai sallan ana idarwa suka fito Excellency yace “kaci abincin da Maman ka ta aiko muku dashi”? Ranshi abace yace “I will not eat any food made by her Matana zatamin girki” murmushi kawai Excellency yayi yace “toh yajikin? Yaushe zamuje kayi all those tests da Dr ka yace kayi? Should we go tommoro”? Ahankali Khaleel yace “my wife will go with me Pops” baki Excellency yasaki yanda Khaleel ke my wife my wife komi dudda yanda he’s worried sosai azuciyanshi dan harya fara kiran manya manyan doctors na Khaleel a turkey kan ciwonshi but ance yafara test first agani but seeing this love made him happy yace “okay go with her” murmushi Khaleel yamai yace “bye Pops” yawuce side nashi Excellency yabishi da kallo Khaleel is changing for the first time yaga sense of being intentional from Khaleel, he’s very very intentional akan Hawwa, wow! Excellency yasake fada yana murmushi yana jinjina kai irin na manya.Sai bayan Hawwa tayi sallan la’asar tabude kofa ahankali tafito hannunta rikeda wayanta ta chanza kaya dan tabata da Khaleel yayi adaki ya yamutsata duk saida jikinta ya lalace, manya manyan flask daban daban tagani kan dinning hakan yasa tawuce wajen ta tsaya tafara bude warmers din daidai nan wayanta yahau ringing dasauri takalli screen din Ammi ne hakan yasa ta sauri tadauka tana zama kan kujeran tace “Ammi kina gate?” Dasauri Ammi tace “gate kuma Hawwa? Ana zaman lpy zanzo ni da ki ganni agidanki sai bayan kin haihu da yardan Allah” abu Hawwa taji yazo mata wuya wama yagayama Ammi zata yarda da Khaleel harma ayi zancen ciki ko haihuwa auren 1month ko 1week. “Hawwa!” Ammi ta katse mata tunani ahankali tace “Na’am” Ammi tace “Aminu zai kawo Miemie da Ramla su kawo miki wasu magunguna da Munawwarah tahada miki dan Allah dan Allah ina begging naki sabida nasan ko anan da kyar kikesha, Promise me zaki dinga sha kullum mace saida gyara Hawwa, promise me, murya chan kasa tace “uhm” Ammi tace “uhm mene” ahankali tace “zansha Ammi” Ammi tace “yauwa suna baki su juyo su dawo gida ban yarda kowa ya dameki ba kina amarci” dan turo baki Hawwa tayi tace “wani amarci”? Ammi dabata jita da kyau ba tace “mene”? Ahankali Hawwa tace “bakomi” Ammi tace “tom bari na barki saida safe” kaman Hawwa tawuce takoma gida takeji daidai tana cire wayan daga kunne Khaleel yana bude kofa yashigo dakin hada idanu sukayi dasauri ta dauke kai ya maida kofa yarufe yataho dinning din yana kallonta kaman yau ya fara ganinta dan kanta ba dankwali ga hannuwanta lalle hakama kafafunta dasauri Hawwa tamike tsaye zata wuce yasha gabanta yace “dawa kikai waya?” Dan kallonshi tayi suna hada ido tadauke kai tace “Ina ruwanka”? Hannunshi kawai yasa ya karbi wayanta tawani yi kanshi kaman yaro zata daka Khaleel yace “kin manta bani da lafiya ko” chak Hawwa ta tsaya tana kallonshi saikuma ta dauke kai call log nata yagani ganin Ammi ne sai kawai yakira Ammi back ta dauka tace “Hawwa” dasauri Khaleel yace “Mom nine shine nima baki kirani ba Matana kadai kika kira kinfi sonta ko”? Kunya Ammi taji yakamata Hawwa tasaki baki tana kallon Khaleel, Ammi tace “assha ai Ibrahim itama bawai nakira naji yataka bane kira nayi na sanar da ita na aiko su Ramla sukawo mata sako suna bata su juyo gida Aminu zai kawosu sabida tafada abarsu su shigo, ya kake ya Hawwa? Hope babu wani abu bata bata maka rai?” Hannun Hawwa kawai yaja yawuce kujera da ita ya zauna yana janta zuwa jikinshi zata fizge yahanata yasa wayan a speaker yace “Ammi me kikace banji ba”? Ammi tace “cewa nayi ya kuke Ya Hawwa dafatan bata batamaka rai babu wani abu”? Kallon Hawwa yayi da gangan yace “in fada”? Zaro idanu Hawwa tayi irin me haka Khaleel, itakuma Ammi dataji abinda yace dasauri tace “fada Khaleel metayi fadamin na cicimata”? Cikeda iskanci yadagama Hawwa gira daya yace “Ammi tace tadena karki damu takaramin zan kira na fada miki” Ammi tace “dan Allah Khaleel kome tamaka ka sanar dani zan gyaramata zama nine daidai da Hawwa, bari na barku to saida safen ku, Allah muku albarka, Allah baku zaman lpy, Allah ya dafa maka Khaleel yabaku yara masu albarka, ina Noor banji muryanta ba” Murmushi yayi yaji dadin addu’an Ammi sosai yace “yau sunday fun day nata ne taje outing” Ammi tace “tom shikenan sai anjiman ku” katse wayan yayi yadan kalli Hawwa datamai mugun kallo yamata murmushi kadan yaciro wayanshi yakai kunne yace “I will be having guest any moment Salman, a shigo dasu” ya katse wayan ya kalli Hawwa data dauke kai tace “ar…..e you not eating”? Shiru Khaleel yayi yana kallonta so ta damu tasan baici abinci ba, warmers na dinning ya kalla ahankali yace “I don’t want food from Mom! Kununa yarage?” Dan kallonshi Hawwa tayi saita dauke kai dasauri tace “Mesa za kasha kunu?” Murya chan kasa yace “I don’t want to make you work, our chef will start work gobe she’s coming from lagos” shifa Khaleel baisan wahala ba, yarone daya taso cikin hutu baisan cewa mata suppose cook ba not wasu chef, cus baiga Momy shi na girkiba, batare da Hawwa ta kalleshi ba tace “akwai abinda kakeso kaci?” Gyadamata kai yayi yace “uhm” ahankali still taki kallonshi tace “mene kakeson kaci?”Dagowa yayi yasa kanshi akan kafadanta dasauri ta kalleshi murmushi yamata yace “I want pasta da chicken” dan tureshi Hawwa tayi ta tashi dasauri tai kitchen tace “I don’t want any chef karma ka kawomin wata” yabita da kallo baitaba sanın she’s this caring ba wlh, jiyayi daga tashinta falon yadaina mai dadi sai kawai yatashi yabita kitchen din Hawwa na tara ruwa a pot yashigo yace “I want to help” wani shegen kallo Hawwa tamai irin see this one saita dauke kai tace “wat can you do?” Dasauri yace “everything” yana zama kan stool na gaban island na kitchen din, wajen maggi taje tadauko tasa a plate tazo tace “peel them” daukan maggi yayi yana kallo yana juyawa yace “wat is this?” Murmushi kadan Hawwa tamai bata amsashi ba tai banza dashi, tashiga wanke nama tana yankawa shikuma yana chan yana karance karancen all rubutun jikin maggi batare dayama fara budewa ba cus yanaso yasan menene abun tukunna, chan Hawwa tace “Khaleel” dasauri yadago kanshi yace “yes my baby” hade fuska tayi tajuyo dasauri yace “sorry i mean yes my Yar Sanda” ahankali ta juya, calmly tace “you were so rude to your Mom” dasauri yace “she was so rude to my wife” tsayar da abinda takeyi Hawwa tayi tace “iyaye can get angry with yara” dasauri yace “I’m the only one that is allowed to get angry with you!” This time juyowa tayi ya kalleshi if Khaleel is this protective over matayensa mesa ya sassakesu toh? Maisa yayi use and dump dasu? Maisa baya dadewa dasu?.

Back to top button