Fentin Zina Page 37 Hausa Novel
37*–Kara kwantar da kanshi yayi a kafafunta gami da sauke kakkarfan ajiyan zuciya yace ammy ina neman alfarmar dan girman Allah duk bukatar da kika ji na ambata ki dubeshi ta fuskar fahimta da adalci a gareni kuma ki sassauta mun.Ammar kenan! Ina so ka san cewa ni uwace mai yiwa kanta adalci balle kuma dan da na haifa kuma nike matukar so da kauna fiye da komai da kowa da yake rayuwa cikin wannan duniyar, koma mecece bukatar taka idan bai saba wa shari’ahr musulumci ba zan duba yiwuwa da kuma dacewar abun sai in yanke hukunci a kai.Wata sabuwar fargaba ce ta ziyar ce shi har yake jin inama da bai fara kawo mata zancen ba kuma babu halin yaki sanar da ita yanzu sai ta nemi jin ba’asi hakanan ya yanke shawarar bari yayi shahadar fada mata kawai.Ammy wannan patient din naki ta rannan mai suna fateema! Da sauri ta katse shi tana cewa eh meya faru da ita?.Ammy oooo babu abunda ya same ta Kuma ba akanta ma zanyi maganar ba akan ‘yar uwar tane.Sarai Dr. Amina ta fahimci inda ya dosa amma sai ta kyale shi don ya ci gaba da magana bata son katse shi.Jin bata yi magana ba sai ya cigaba da cewa Ammy ki gafarceni idan na fadi ba daidai ba amma zahirin gaskiya tun ganin farko dana mata zuciyata ta kamu da matsanancin soyayyarta a tsakanin kwanakin nayi iyakar kokarina domin na yakice tunanin ta daga kwakwalwa ta amma hakan ya gagare ni shiyasa dazu na yanke shawarar zuwa gidan su daman na bincika address din gidan su a cikin file din su toh naje na gabatar mata da abunda yake cikin zuciyata amma batayi na’am dani ba hasalima tace kada na kara kusantar inda take, a halin yanzu bansan ya zanyi ba a matukar dame nake. Ya karasa fada da muryar dake nuni da zallar sarewar shi.Ajiyan zuciya Dr. Amina tayi bayan ta gama sauraren bayanan shi domin kalaman shi na karshe daya ce ta kore shi ta kuma ce dashi kada ya kara kusantar inda take sai hakan ya faranta ranta har ya sanyata sakin karamin murmushi mara sauti ta cigaba da shafa kansa cikin son kwantar masa da hankali tace.Kayi hakuri! Ko wani bawa da ka gani akwai irin kalu balen sa da kuma nau’in jarabtarsa don haka wannan ba komai bane a wajen ubangijin mu, fatana dai kawai .Allah ya bamu ikon cin ko wace iriyar jarabawa ya jarabce mu da ita, sannan maganar Ameena ina so ka cireta a ranka domin bazan taba yin farin ciki ace dana yana aurenta ba, ba domin bata cancanta ba a’a sai domin wannan fentin zinar da baya goguwa har karshen rayuwa, koba komai ka samawa ‘ya’yanka kamilar uwa mai nagarta da kyawawan suffofi yana da kyau da muhimmanci kuma nasan wannan yarinyar bata rasa ba, sai dai ina so ka sani cewar ta rasa abu daya tak da zai iya sa koma waye ya gujewa neman auren ta shine TURBA hakika ni uwace da nike fifita bukatar dana sama da tawa bukatar, sannan ni uwace mai sadaukarwa ga danta akan dukkanin abunda ya zo mun dashi sai dai wannan karon kazo da al’amari mai girman gaske da bazai sanya zukatan mu a farin ciki ba don haka ne ma zan baka hakuri a karon farko dana gaza wajen biya maka bukata da muradin ka.Bai san tayaya ba sai ji yayi hawaye masu dumi suna sauka a saman fuskar shi ba tare da ya shirya wa hakan ba cikin hanzari ya goge su tun kamin ammy ta gani sai dai ya makara don tuni taji saukar su a saman kafafunta sai tayi tamkar bata ga komai ba.Cikin sanyin murya yace ammy zan shiga ciki in dan kwanta.Kallon mamaki ta mishi lokacin daya dago kai suka hada ido ganin yadda idanun sa suka rine sukayi ja sosai tace amma kana ganin magriba ta kawo jiki wani kwanciya zakayi a yanzu kai kuwa? Kamata yayi ka bari idan kayi sallahr isha sai ka kwanta bayan kaci abinci ko?.Lumshe ido yayi yana kokarin mikewa yace zazzabi nake ji sosai sannan ya mike.Subhanallahi ammy tace cikin rudewa kamin tayi wani yunkuri Ammar daya gama mikewa yaji kanshi yayi duhu daganan bai kuma sanin inda yake ba ya sulale ya fadi a kasa ya suma.Tashin hakalin da ammy ta shiga Allah ne kadai ya sani da gudu cikin kidima ta fita ta kira baba mai gadi suka dawo tare suka hada hannu da direban su sukayi waje dashi suka saka shi a mota suka nufi asibitin ammy dashi.Ammy kuwa cikin zuciyarta rudani ne pal a ciki tana kuma mamakin yadda soyayyar bazata tayiwa ammar dinta mummunan kamu, yaron da ko kallon ‘yan mata na second biyu baya yi, gefe daya na zuciyarta na fada mata ta ajiye jiji da kanta ta kuma zubda makamanta domin ta ceci ran yaron ta idan yaso cikin ruwan sanyi zata aiwatar da wani shiri ta yadda da kanshi zai nemi yarabu da yarinyar, jinjina kanta tayi bayan ta gama tunanin tana kuma kara karfafa kanta kan shawarar data yanke tsakaninta da zuciyarta. A haka har suka isa asibitin already daman tun kafin su taso Dr. Amina tayi musu waya hakan yasa suna isa akayi emergency dashi aka shiga bashi taimakon gaggawa, dukda kwarancewa irin na Dr. Amina amma a yau akan gudan jininta saidai ta zama ‘yar kallo domin tayi matukar kaduwa.Dr.fahad shine likitan daya jagoranci treating din ammar don haka yana fitowa ya kai kallon shi wurin Dr. Amina yace sannu dr. Juyowa tayi ta kalle shi tare da tashi da sauri tana tambayar ya yake ya farka kuwa is he safe? Duk ta hade masa tambayoyin ba tare da ta bashi damar amsa koda guda daya ba a ciki.Dr. Kinsan aikin mu yadda yake muje office mu zauna in miki bayani. Bata ce komai ba tabi bayan shi har zuwa office din suka zauna Dr. Fahad ya dauki tabaran idon shi dake ajiye a gefe ya makala a idon sannan ya maida kallon shi kan Dr. Amina wacce take shugabar shi yace Dr ke likitace saboda haka babu bukatar in miki boye boye Ammar zuciyar shi yana dab da bugawa sakamakon firgici ko tsoron ya rasa wani abu kamar dai yadda kika sani sauran bayani dai ba sai na miki ba saidai ina mai baki shawara dan Allah ki dubi halin da yaron ki yake ciki idan kina da masaniyar damuwar sa ina rokon ki gaggauta biya masa ko ki taimaka wajen sama masa mafita idan ba haka ba sorry to say zamu iya rasa shi gaba daya domin ni dake mun sani cewar tun tasowar yaron nan bai taba neman abu ya rasa ba shiyasa nayi tunanin koma meye abunda ya kwantar dashi ba karamin tasiri yake dashi ba a rayuwar shi dan Allah ki duba lamarin we have no time.Hawaye guda daya ta gefen dama ya silalo mata a fuska tasa hand-ki ta share kwallar tace kada ka damu Dr. Fahad insha Allah nothing will happen i will make sure nayi bincike a kan abunda ke damun shi ba tare da bata lokaci ba nagode sosai. Ta fada tare da mikewa ta fita daga office din ta nufi special room din da ake kwantar da manyan mutane a kwance ta same shi Yana bacci an jona masa karin ruwa ya rame kamar yakai sati yana ciwo. A hankali ta taka taja kujerar kusa da gadon ta zauna ta riko hannun shi tana matsewa cikin tsananin so da kaunar shi tana kallon fuskar shi data yi fayau da ita ta sauke ajiyan zuciya tace na maka alkawarin mallaka maka muradin ranka amma dan Allah kada ka raunana zuciyar ka na tabbata kana jina don haka ka kwarara kanka ina son ka ban taba tsammanin kin amincewata ga soyayyar ka zata iya jefa rayuwar ka cikin hadari ba da ban fara ba. Na maka alkawarin sama maka abunda kake so get well soon my love.Ta fada a zahiri amma kasan zuciyarta ita kadai ta san me take tunani game da wannan ballagazar yarinyar, tayi alkawarin sai ta sa tayi dana sanin shigowa cikin zuri’ar gidan ta. Sai ta sa tayi dana sanin haduwa da ita. Da wannan tunanin ta saki hannun shi ta koma gefe ta jingine bayanta a jikin kujerar tana wasu tunane tunane a cikin ranta har bata san lokaci yaja ba sai ji tayi ana kiran sallahr isha nan t farga fa da ko magriba bata samu ta gabatar ba saboda halin da take ciki duk ta sha’afa cikin azama ta tashi ta shiga toilet din dakin ta gabatar da alwala ta fito tayiwa daya daga cikin nurses magana domin su kawo mata sallaya babu bata lokaci aka kawo mata ta shimfida ta fara sallah ta idar ta zauna tana lazimi sai taga kamar ya motsa kafar shi ta kafe shi da ido taga dai da gaske ya farka da sauri ta isa gare shi lokacin yana kokarin mikewa zaune cikin ciccije baki da kama kanshi dake ciwo tamkar zai rabe gida biyu.Taimaka masa tayi ya zauna ta tallafa masa ya jingina ya mikar da kafafun shi sannan ta koma ta dau flask ta hada masa tea mai kauri daman duk tasa an kawo mata abubuwan bukata ta mika masa ya karbaya soma kurba da kadan da kadan har ya shanye babu wanda yace da kowa komai a cikin su.Sannu ammar ya kake jin jikin naka yanzu da sauki ko? Ta jera mai tambayoyin bayanta karbi kopin ta ajiye.Da sauki ammy kaina ne dai kamar zai tsage nike jin shi.Sorry my boy shi ma a hankali zai warware kaji ko kada ka damu.Gyada kai yayi tare da lumshe ido.Ammar ban taba tsammanin daidai da rana daya zan iya zama silar damuwar ka ba, banyi tsammanin cewar zaka kawo bukata in kasa biya maka ba ban kuma yi tsammanin girman soyayyar da kake wa yarinyar nan yakai ya iya tarwatsa rayuwar ka ba koda kazo mun da batun na hana ka ne saboda kokarin kare martaba da kimar ka amma banyi nufin in tilasta ka akan abunda baka so ba, Alhamdulillah tunda ka farka na tabbata da wani abu ya sameka bazan iya dauka ba ba kuma zan iya yafewa kaina ba. Zan yiwa wan mahaifinka magana sai aje can gidan su yarinyar a nema maka auren ta don haka sa ranka a inuwa kada ka illata mun kanka baban soyayya. Ta karasheda dan murmushi na zolaya wanda kuma yake na yake a wurin ta.A’a ammy kada kice haka ni ai tunda ma kika nuna baki so bazan yi abunda zai bata ranki ba don haka na hakura da ita har abada Allah ya hada kowa da rabon shi. Ya fada dakyar cikin tattaro duka karfin halin shi.Ammar kenan! Saboda kaji dadin mace mun a gida ko? Tunda dai kai yanzu ka zama shahruk-khan, kaga bar wani batun bana son ta ko kuma na fasa duk babu abunda zai magance ince dai a sanadinta kake nan a kwance yanzu? Kuma ina so ka sani duk duniya idan kaga ka nemi abu baka samu ba toh ka dauka haka Allah yaso sannan abun ne yafi karfi na ka sa a ranka cewar da izinin Allah Ameenatu matar kace don bazan bari soyayyarta ta kashe ka ba alhalin ina da damar taimakawa.Murmushi yayi mai dan sauti yana lumshe ido ji yake kamar ya daka tsalle ya tashi ya rungume ta tsabar dadin da yake ji yana suffanta yadda zasuyi rayuwar su a gidan su daga shi sai ita ya gwada mata tsantsar so da kulawa ya goge mata hadda akan kowa ya zamto babu wanda zata sake tunawa sai shi kadai, zuwa yanzu ya gama gasgata maganganun data fada masa a kanta gaskiyane saidai shi babu ruwan shi da duk wani abu da za’a fada akan rayuwarta ta baya kawai abunda ya amince da shi shine ita kuma kalar tata jarabawar kenan sannan ma ba yanzu ne ta aikata ba tun da ne kuma tayi nadama kuma idan akace baza’a mu’amalanci wanda ya aikata zunubi kuma ya tuba ba toh da dama mutane zasu koma ruwa wadanda kuma ke da niyyar tuban zasu ji gwiwar su ta sage duba da irin kallon da ake musu da kuma irin mu’amalar da ake nuna musu.*****Kamar yadda ammy ta mishi alkawarin suje sun nemawa ammar auren Ameena inda babu bata lokaci baba malam ya amince duba da cewar su din ba boyayyun mutane bane bincike akan su bazai bada wahala ba bayan nan kuma mutanen suna da suffa ta kamala shiyasa baiyi wata wata ba yace dasu idan sun amince yana da bikin ‘yar uwar ita ameenar a sati biyu masu zuwa don haka yana da bukatar a hada bukin saboda ya saukaka wa dangin su jeka ka dawo da zasuyi.Iyayen ammar sunyi matukar jin dadin wannan al’amari musamman ma wan mahaifin shi da duk yafi kowa bukatuwa da ganin auren ammar ko domin ganin ya damka duka sauran kadarorin shi gare shi a cewar shi aure cikon kamalar dan adam.Nan take suka bada sadaki da kudin sa rana aka sanya rana daidai da bikin fateema kana suka yi sallama cikin aminci kamar sun jima da sanin juna suka tafi.Koda labari ya riski Ameena kan ranar aurenta da aka sanya ba tare da an shawar ceta ba a matsayinta na bazawara wacce take da damar zaban mijin da zata aura, taji babu dadi saidai jin dawa aka sanya mata rana sai ta kasa tantance farin ciki take ciki ko akasin haka.Basarwa tayi kawai ta ci gaba da tsabgogin ta amma duk motsi takan tsinci kanta da yin murmushi a cikin zuciyarta.Alhamdulillah ammar ya samu sauki sosai, yana zaune a falo da safe yana kurban ruwan lipton mai citta a ciki ammy ta sauko daga steps ta zauna kusa da shi yau basu hadu ba sai yanzu.Daga ido yayi ya mika hannu ya ajiye cup din a center table din dake kusa da shi yace ammy barka da safiya!.Yauwa barka dai ya karfin jikin?.Alhamdulillah ammy ai na samu sauki sosai.Yauwa toh masha Allah ni yanzu ina so in tafi asibiti akwai patient din da ya kamata in duba amma kafin nan ina so muyi wata magana da kai.Gyara zama yayi ya tattaro duka natsuwar shi ya mikawa ammy yace ina jinki ammy Allah yasa ba wani laifin na aikata miki ba.Girgiza kai tayi tace ko kadan! Kawai so nike insan yanda shirye-shiryen bikinka zai kasance musamman gidan da zaka zauna.Murmushi yayi yace kai ammy har kin tsorata ni na zaci laifi na miki.Bata kulashi ba tace ina sauraren ka lokaci na tafiya.Eh Toh ammy shiri kam na barwa Ahmad gidan da zamu zauna kuma wannan gidan saman dake shagari cortex nan nike sa rai insha Allah tunda a gyare yake iyakar furnitures kawai za’a saka a ciki.Gimtse fuska ammy tayi tace toh naji shirin dai ka barwa ahmad amma gidan da zaku zauna umurni zan baka ba shawara ba ka gyara wancan bangaren na gidan nan anan nike so ku zauna zuwa nan da wani lokaci.Faduwar gabane ya shige shi ya shiga binta da kallo ita ma shi din take kallo……………. *EESHERT ADAMU*



