Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 19 Book 2 Complete Novel

Ita kanta Jalila setaji kaman tace A’a amma taji nauyin yin hakan, daddy yakuma cewa “Jalal maza kunna motar ku tafi karta makara” Jalal kaman yace bazashi ba amma yasan yana fadan hakan tasamu abunyi, bece komai ba ya bude motar ya kunna, Jalila ta tafi ta bude gaba ta shiga, “yawwa Allah yayi muku albarka sekun dawo” Jalila ce kawai tace Ameen, Jalal ya kunna motar yajata da gudun tsiya, yadda yake gudu yasa Jalila ta kalleshi “ni gaskiya in wannan ganganci za’ayi da rayuwata ka saukeni, akanme inkasaba kasada da rayuwarka to badaniba” banza yamata yacigaba da tukinsa, yadda yake ratsa tsakanin manyan motoci yasata runtse ido tana ambaton Allah, kallo daya yayi mata ya dauke kansa, “dan Allah ka tafi a hankali koka tsaya in sauka” jitayi an tsaya hakan yasata bude idonta, gani tayi yayi parking, yasa hannu ya yana dakko taba yana kokarin kunnawa, “kutmelesi meye haka ne?” banza yayi mata ya kunna tabarsa, sakin hayakin yayi fuuu a cikin motar, juyawa tayi zata bude kofar motar amma taji a kulle gam, yasa lock ta kalli agogon hannunta ta makara sosai ana daf da shiga exams,

“wai meye haka dan Allah nika budeni in tafi zan makara, ga warin hayaki ya isheni” Shiru yakumayi ya kwanta sosai a jikin kujerar yana busa hayakinsa, ji tayi kaman ta wanka masa mari, yanajinta amma yayi banza da ita kamar wani itace, dafe kanta tayi, wayarsa tafara vibration ya dauka yaduba message din Hanna ne danhaka ya ajiye wayar tareda fadin “wasu matan are just useless” Jalila ta dago ta kalleshi, “ai Useless din ba iya mata bane hada maza, dan gara mata da wasu mazan dabasa jin magana” wani dan guntun murmushi yayi, wanda shikadai yasan yayi shi, gani tayi ya shanye sigari kusan uku yakuma kunna wata, hannu tasa ta fizgeta ta jefa waje “wallahi baka isaba, akanme ina zaune zaka dinga shan taba ka cikani da hayaki salon inje aji a dauka ninasha tabar, ka budeni in tafi in yaso kaima kazama tabar, batareda ya kalleta ba yace

” warin taba ai kin dade kinayinsa, ba iya taba ba harda na giyama kinayi, kece baki saniba amma nakusa dake sun san hakan” kallonsa tayi alamar bata fahimta ba

“ya za’ayi nida bana shaye2 indinga warin giya, Allah ya kiyaye” “bakiyi addu’ar a inda ya daceba, dan kinriga kin makara, kuma ba lallai sekina sha zakidinga warinsu ba” hannunta ya kamo, ya nunamata “a jininki abun yake, akwai jinin yan giya a jikinki dan haka sekidena cika baki” ita Jalila sam batagane inda maganganunsa suka dosa ba, wayartace taketa ringing tasa hannu ta dakkota Alhaji Kabiru ne akan screen din wayarta, screen din Jalal ya tsurawa ido yai shiru kaman me nazari, ya kalleta ya kalli wayar, kashe wayar tayi ta mayar cikin jakarta, kallon tuhuma yayi mata na wani dan lokaci, sannan ya dauke kansa, “hmm Jawwad za aci amana, hakan yafi ai, dan baki dace dashiba gara ya auri mutuniyar kirki, dan duk jarabarki bazaki auri dan uwana ba, Jawwad da salihar mace ya dace ba irinkiba” kallonsa tayi sannaan tace “nice ma kai, aigarani da kai, kaima kasan hakan kuma duk bakin cikinka sedai kayi, dan nafi karfin ace za’a kyamaceni a matsayin mata, dan nasan nafi wannan doluwar kanwartaka”

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“Hmmm meye kuma nasakota a wannaan zancen? ” 

“kaika sani, nikawai ka budemin in fita” banza yayi mata yacigaba abunda yake, wasa2 kusan mintunansu talatin a tsaye Jalal yaki tafiya, hannu takuma sawa zata fizge tabar bakinsa cikin zafin nama ya hada da hannunta ya rike, ya juyo yana kallonta, wani mugun kwarjini yayi mata ta kasa magana ta sunkuyar da kanta kasa, “karki kuskura, bar ganin na kyaleki dazu” sakar mata hannu yayi, yacigaba da abunda yake, karfe tara hada rabi, amma Jalal yaki kaita makaranta, tarasa mezatayi kawai tafara kuka, seda Jalal yaga dama sannan yaja motar yacigaba da tafiya, wannan karon kuma a hankali yake tafiya kaman bayaso, hannu yasa ya kunna radio motar inda karatun Al qur’ani yake tashi, Jalila aranta tace “Tab dama yanajin karatun qur’ani” bata gama tunanin ba taji Jalal yanabin karatun a hankali, juyowa tayi tana kallonsa, danta tabattar anya kuwa shine yakeyi, sosai yakebin karatun cikin suratul Ibrahim, dan tabe baki tayi tana jinjina lamarin dama Jalal ya iya karatu haka, amma koda wasa bata tunanin ko bismillah ta tabajin yayi, se masifa da wake2, tana cikin tunanin taji yayi parking, “inkin gama kallon nawa seki fita” 

” Baka da abunda zan tsaya ina kallo, ko Meye amfanin zuwanama, tunda dai na makara nasan ba lallai inyi jarrabawar ba, kaida Allah in abunda kayimin dai2 ne, kodayake baka san darajar jarabbawa ba shiyasa kamin haka kuma Insha Allah se” “Ke!!!!” ya dakamata tsawar data tilasta mata yin shiru

“wallahi duk randa bakinki yai kuskuren yimin muguwar Addu’a akanki zata kare, gobe in ankuma cewa kibi namiji mara daraja irina sekikuma biyoni, fitarmin daga mota, inbahakaba na kunna motar nan senaje gida zan tsaya, kyasan yadda zakiyi” bude motar tayi tanata kunkuni gashi ta hade rai sosai, ta fice tabar motar a bude tai tafiyarta, ankai ruwa rana sosai kafin abar Jalila tashiga hall din exams saboda ta makara, Jalila ji take kaman tana komawa gida takama Jalal ta shakeshi seya suma, haka tai exams din ta fito cike da takaici, 

Tasamu guri ta zauna a karkashin wata bishiya, ta zauna babu dadewa Zahra ma tazo gurin “Jalila ya akayi kika makara haka yau?” dan tsaki Jalila tayi “kedai bari, wani ne yajamin wallahi, kuma ze gauraya dani” “hmm Jalila kenan me jama’a, Amma ke sir Hafiz fa yace ince miki kije, nifa nakasa gane meke shirin faruwa tsakanin ku” Jalila ta kalleta ta dauke “ki goge zuciyarki tsaf kidena bari tana kawomiki wani tunani” zahrah ta jinjina kai “ke ba wannan ba Jalila, ina mafita anawa lamarin? Ina cikin damuwa wallahi” 

“Nasani Zahrah, amma abubuwan dasuke kaina dayawa ga wannan jarrabawar ga sauran abubuwa” 

“to nidai kitemaka Jalila, karsuyi nasara akaina” 

“Ai yazama dole in temaka miki, sabida indai nayi nasara kikayi yadda nace to nikeda riba, zangaya miki yadda zamuyi, amma banason gaddama da taurin kai, duk abunda nace kiyi, bazan bari kiyi abunda zaki cutu ba” 

“to shikenan inajinki” Jalila ta gyara zama “zaki Amince da bukatar su Sameera” zaro ido Zahra tayi “Amma meyasa?” 

Nan Jalila ta tsarawa zahra yadda abun ze kasance, zahra ta yadda da abunda Jalila tagaya mata. 

Zahra ta tashi ta dau wayarta zata tafi, Jalila ta dakatar da ita, ta dakko wayarta tasaka ta a tsakanin litattafan Zahrah daga sama, sannan ta kalli zahra” harkije ki dawo karki sake ki tabamin waya, jeki dawo ina nan ina jiranki”zahrah ta gyada  kai ta tafi, inda tasan zata samu su Sameera, tai sa’a kuwa suna gurin, tana zuwa tasamu guri ta zauna a kujerar opposite din su Sameera ta kalli Sameera tace “Sameera gurinki nazo” Sameera tamata wani mugun kallo sannan tace “fatan kinzo ki sanar dani kin Amince da bukata tane?” “A’a zuwa nayi in rokeki alfarma dan Allah dan annabi kirabu dani kiyi hakuri wallahi iyayena zasu shiga damuwa insuka gane gurbatacciyar hanyar dana fada” Saleema ce ta katseta “Ke saurar bama son shirme , kekinfiso aita nanata magana ko? To bari kiji bata sauya zaniba, koki yadda kokarki yadda bazaki kubucemana ba sannan sekinso iyayenki zasu san abunda kikeyi, abunda kezaki amfana kudi fa zaki dinga samu” Sameera ta dagawa Saleema hannu alamar tayi shiru, ta kalli Zahra “idan baki amince da bukata ta ba, wallahi kartin yan daba zansaka suyi miki fyade” A razane Zahra ta kalli Sameera “yes and i mean it, fyade na wulakanci na tozartawa kuma duk garin nan babu wanda ya isa yayi wani abu, inada yan daban dabakowa ke iya hayarsu ba, sannan inada manyan dasuka tsaya min, babu wanda ze gane ninasaka akayi miki haka balle adau mataki, bakida gatan da za’a iya kwato miki hakkin ki, kinga tarwatsewar rayuwa tagama, karatu ya kare se zaman gida jiran ajali danko waje baki isa ki fitoba saboda gudun kyamar da mutane zasuyi miki” da kyar zahra ta hadiye mugun yawu “shikenan dan Allah kar abun ya kai haka na yadda, na amince amma bana son mutane su gane” Saleema ta kyalkyale da dariya, “ashe bari ba shegiya bace yarinya da wata garan gara wata” Murmushi Sameera tayi, “kin temaki kanki” zahra ta share hawayenta “A ina zamu hadu?” nan Sameera taimata kwatancen wani gida, zahra tace “zanzo Insha Allah, sannan kibani lambarki incase ko zan bata” ba tunanin komai Sameera tabawa Zahrah lambarta, sannan ta karbi ta Saleema ma” har zahra ta mike zata tafi ta dawo ta zauna tace  “Amma dan Allah kujawa yar seat dina kunne, nayi2 tadena shiga harkata taki” Saleema tace “banni da ita zanyi maganinta” zahra ta jinjina kai ta wuce yayinda sukuma suka kyalkyale da dariya, zahra takoma inda tabar Jalila, tana zuwa tana niyyar labartawa Jalila abunda yafaru, Jalila tasa hannu ta zare wayarta, sannan ta kalli zahra “shikenan semunyi waya ina sauri zan koma gida” “Amma baki tsaya nagaya miki yadda mukayi dasu ba” “karki damu mu hade ta what’s app” cikin mamaki Zahrah ta kalli Jalila “to amma meye amfanin….. 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

” Shhhhh semun hade “Jalila tayi gaba abunta. 

Tana zuwa gida yaya Jawwad yana tsaye shida Abba, karasawa gurinsu tayi” Abba yana ganka a gida iyanzu? “yan makaranta ya jarrabwa” “Alhamdilillah Abba harka dawone?” 

“A’a tafiya ce takamani, zanje Lagos” dan hade rai Jalila tayi “Abba da tafiya zakayi ba sallama” “to ai gashi munyi sallamar” Jawwad yace “Abba muje karka makara, wannan babyn taka bazata bari ka tafi ba” 

“Nima zan biku Abba” Jawwad yace karatun fa? Naga kuna exams “

” Eh ai bakomai dan Allah ni zan biku” Jawwad yace “rigimammiya yanzufa kika dawo baki gajiba” “bangajiba Allah” Abba yai murmushi “taho mutafi shalelena, ai rakiya zakiyi min” da murnarta ta hau motar suka tafi raka Abba airport, suna tafe suna hira itakuma ta dakko wayarta tasaka earpiece tana kallon video, dazu wayarta data saka a agaban jakar zahra video ta saita ta kashe flash din wayar, duk wani magana dasukayi yayi recording, wanda ita kanta zahra bata Sani ba, aciki Jalila taji kwatancen gidan da akayiwa zahrah a dan bare, ita Jalila bata san ma inane dan bare a kanoba, hiding video din tayi a wani app ta ajiye wayar, suka raka Abba airport, seda Jawwad yabiya ya saimata ice-cream da tarkacen chocolate suna tafe suna hira har sukazo gida. Suna zuwa suka tarar da Maama a harabar gidan, kallon tuhuma takeyiwa Jalila da Jawwad “daga ina kuke?” Jawwad yace “dama Tafiyace takama Abba zeje Lagos kuma bakyanan shine muka rakashi airport” “in kayi salla kazo ina son ganinka” “to Maama insha Allah zanzo” Maama ta juya takoma cikin gida, Jawwad yajuya ya kulle mota, yaga Jalila a tsaye abayansa bata tafiba “ya dai?” “bangaji da ganinka bane” murmushi yayi mata “Babyna kenan, aini nakine zakita kallona sekin gaji” “bazan taba gajiya da kallonka ba, jekayi salla kazo kiran Maama” “to shikenan see u later” daga nan yafita ita kuma ta shige gida, a cikin gida bataga Nana a dakinsu ba, san haka tashiga tayi wanka tai salla. Tana ninke sallayar taji wayarta na ringing Alhaji Kabiru ne wani uban tsaki taja 

Ta daga wayar suka gaisa, haka ta dake ta boye damuwarta suka sha hira kamar gaske, Alhaji Kabiru ya matsa matuka akan se Jalila taje gidansa, taita lallabashi tana bashi hakuri daga baya ta kashe wayarta, fiowa tayi palour domin taje kitchen tasamu Abinda zataci, gani tayi anyi bakuwa a palour da alama gurin Maama tazo, suka gaisa da Jalila tace “bari inje in kira miki ita inaga tana daki” Jalila ta tafi dakin Maama danyimata magana Jalila ta jiyo kukan Nana tana cewa “Wallahi Maama gara in mutu da in auri Nura, wallahi yaya mairo kozata kasheni bazan aureshi ba” “nima ban goyi bayan hakanba, bazaki Auri Nura ba, amma yazama dole Jawwad ya auri Naja, intaga Jawwad ya auri Naja zata hakura inyaso kesekice ba kya sonsa” “Maama saboda me shima yayan ze auri Naja yakamata ayi masa adalci abarshi ya zabi wadda yakeso” “ke rufamin baki, dole ya auri Naja saboda bazan bari ya auri wannan yarinyar ba, indai ina raye baze auri Jalila ba saboda bana kaunar uwatta itama bana sonta dana baze auri yar Arniyaba karuwa” Jalila ji tayi kaman ansoka mata mashi a zuciyarta, tura kofar dakin tayi kaman bataji komaiba tace “Maama kinada bakuwa” hade rai Maama tayi “to naji jeki ina magana da yata” juyawa Jalila tayi ta fice tafasa cin Abincin, tafasar da zuciyarta take tasa takasa komai, ga hawayen yaki zubowa balle taji sanyi aranta, a hankali taketa karanto addu’oi domin zuciyarta tayi sanyi, gani tayi inta cigaba da zama bacin raine ze dameta gara ta fita ta rage wasu abubuwan dan haka ta dau hijabinta tasaka ta dau nikab da Jakarta ta fito palour, Maama tana gaisawa da bakuwarta “Maama dan Allah zan dan fita bazan dade ba zanje siyo kayan cake” “sekin dawo” shine kawai abunda Maama tace mata, tana fitowa harabar gidan Manu ya taso “A’a uwadakina ina zuwa haka daga dawowarki yamma tayi sosai” “Manu key zakabani na mota zanfita” “Ahh ai yayi wuri kifara tuki da kanki bakigama kwarewa ba kinsan tuki a kano se kwararren direba” “karka damu ba nisa zanyiba” Manu direba yabata key din mota, ta fita sannu a hankali take tukin da tambaya hartaje unguwar danbare inda su Saleema suka kwatantawa zahra sukace acan zasu hadu, abakin layin tayi parking ta fito sanye da nikab ta shiga layin, layin shiru ba mutane sosai, har kofar gidan taje ta tsaya daga baya, tana nan tsaye sega wata mata tazo wucewa, Jalila ta tare matar suka gaisa sannan Jalila tace “baiwar Allah dan Allah tambaya nake?” “ina jinki Allah yasa nasani” 

“Dan Allah ke yar anguwar nance” “meyasa kika tambayeni?” Jalila tace “kinga ba cutar dake zanba wasu yan tambayoyi kawai zanyi miki” matar tace “ina jinki” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“dan Allah waye me wancan gidan” Jalila ta nuno mata gidan “hmm wanna gidan da kike gani wai yan makaranta ne a ciki, kuma bawani yan makaranta taron yan iskane maza da mata bawanda basa zuwa gidan, ke kawaima gidan karuwai ne da yan shaye2 ” “Amma kuke zaune dasu a anguwar ina hukuma” “wace hukuma aiko ankamasu se an sakosu saboda ita ainihin me gidan wata yarinya ce, tanada manya a sama ba wanda ya isa yayi mata komai samfirin yan mata samari da yan daba babu wanda babu, har wasu manyan mutanen ma suna zuwa nan” 

“Nagode sosai yar uwa, da amsamin tambayoyina” matar tace “bakomai amma fa koda wasa karki sake kice nina gayamiki danba ruwana” “karki damu babu mejin wannan zancen”. Daga nan Jalila tayi godiya ta nufo gida, anata kiraye kirayen sallar magariba, tana komawa gida ta nufi cikin gida

“wallahi Jawwad da raina bazaka auri yar arna ba, ko ka auri Naja kokasamu wata ka aura amma ba wannan yarinyar ba, Naana dai zanyi yadda zanyi bazata auri nuraba amma kai kam sedai kayi hakuri bazaka aureta ba wallahi”

“Maama dan girman Allah kiyi hakuri Jalila batayi miki laifin komai ba, wallahi Maama ina sonta dan Allah karki rabani da ita, ina sonta dan Allah wallahi bazan iya auren Naja ba” 

“Au har ina fada kana fada Jawwad, nagama yanke hukunci, sedai ka mutu dan bana kaunarka da yarinyar nan baze yuwu jikokina su fito daga tsatson arna ba, wannan fitsararriyar yarinya mara tarbiyya to baka isaba ni na haifeka dan haka na isa da kai, bazaka aureta ba, tun kuna kanan akan uwatta ba irin wulakancin da ban fuskanta ba, ubanku yayi min shi Aliyun yayi min rashin mutunci akan uwatta dama shiba mutunci yacika ba, dan halinsa ta dakko, ga kakarku kowa ya hademin kai Allah ka dai yasan me tayi ta shiga ta fita ta rabani da dangin mahaifinku, suka tsaneni se yanzu kakuma jawomin jaraba baze yuwuba, zamanta a gidan nan ma ba yadda zanyi ne, amma bana kaunar ganinta kusada ku” sunkuyar da kai Jawwad yayi ya dafe kansa da karfi Jalila ta bude kofar palourn gaba daya suka juyo suna kallonta

Kallo daya tayi musu ta dauke kanta ta wuce cikin dakinsu, itakanta Maama seda tasha jinin jikinta dan gani take kaman Jalila taji abunda tace, tashi Jawwad yayi ya fice, yayinda Nana da sauri itama ta mike da nufin bin bayan Jalila amma Maama ta hanata, “Ina zaki? Karki sake Kibi ta mayya” haka Nana ta hakura tafasa bin Jalila, Jalila tana shiga dakin tai jifa da jakarta da hijabinta akan gado ta zauna ta fashe da kuka me tsuma zuciya, dama tsanar da Maama take mata harta kai taci mutuncin mahaifinta haka shida baya doron kasar tsawon shekaru, ga kazafi datakeyi wa uwata, menayiwa wannan matar hakane meyasa ta tsaneni, banda albarkacin Abba dasu Nana da matar nan itada zuri’arta suka ganni se sun canza hanya, “zamana a gidan nan baze yuwu ba, bazan cigaba da jure cin zarafin iyayena ba musamman uwata ba dan kawai tubabbiya ce gara inshiga duniya, to amma inna tafi Jalal fa? Tabdijan wallahi matar nan tahana Jawwad aurena bata isa ya auri wata Naja ba, in ita Maaman bata san wacece Najaba to nina sani, Jawwad kuma dan uwana ne, intace baze aureniba baze auri Naja ba wallahi, bazan zauna a kasheni da bakin ciki a biyeba, ta karkashin kasa zan fara ramawa nagaji” “Enough!!!!” Jalila tafada da karfi idonta duk hawaye, guri ta nema ta kwanta hawaye na cigaba da bin gefen idonta to Jalal dinme ma? Nagaji tafiya zanyi sena bar gidan nan wallahi nagaji da wannan abun da akemin, hijab dinta tasaka ta mike. Nasihar ummi ta dinga tunowa wanda take yawan yi mata akan hakuri da rayuwa dakuma karbar kaddara, komawa tayi ta zauna ta fashe da kuka me ban tausayi. 

Jiki a sanyaye Jawwad yayi sallar magariba, gaba daya yarasa abunda yake masa dadi, Jalal ne ya shigo dakin da sallama, amma sam Jawwad bejiba hankalinsa baya jikinsa, dafa shi Jalal yayi cikin damuwa yace “Jawwad lafiya kuwa? Meyake damunka kake tunani haka?” Ajiyar zuciya Jawwad yayi, ya danyi shiru na wani lokaci sannan yace “Jalal ina cikin damuwa, narasa meyakamata inyi” “gayamin meya farune?” 

Nan Jawwad yagaya masa komai sanna ya dora da cewa “Jalal babban damuwana shine cin zarafin da Maama tayiwa iyayen Jalila ina kyautata zaton Jalila taji abunda Maama tace, amma ban tabbatar ba, data shigo ba wanda ta kula a cikinmu, wallahi bana zaton zan iya auren Naja bazan iyaba wallahi” 

Shiruu Jalal yayi, “Jawwad a duk lokacin da aka ci zarafin Ummi, har cikin zuciyata nakeji, raina yana baci, bana manta Alkhairi Jawwad, idan har a matsayinmu na hausawa zamu cugaba da aibata wanda suka karbi Addinin musulinci daga baya to tabbas wanda ba musulmi ba zasu dinga kyamatarmu da addininmu, Jawwad kayi hakuri, amma mahaifiyarka da yan uwanta basa kyautatawa, dukda ina gefe ina fadar rashin kunyar yarinyar nan bazan mata sharri ba tanada matukar biyayya wadda wanda dayawa aka haifa a musulincin basuda ita, kuma itama ai a musulinci aka haifeta, Ummi mace ce me karamci da ilimi riko da Addininta yasa ta baro iyayenta gidan jin dadi dau shekaru ba tareda ta waiwayesu ba, soyayyar datakewa mijinta da yan uwansa ce tasa nima naci Albarkacinku, Jawwad mahaifiyarka bata kyauta ba, kuma zigata akeyi amma kasani gara wanda ya tuba daga baya akan abunda yar mahaifiyarka take aikatawa”da sauri Jawwad ya kalleshi yana kokarin yayi magana, Jalal yace “karka tsananta tambaya dan bazan gayamaka komai ba amma lokaci zenuna komai, mahaifiyarka zatayi nadamar abunda tayi, kayi kokarin ganar da ita, tun kafin tasamu kanta a halin datawa mahaifiyar take ciki, nima da datawa damuwar nazo maka amma bari in kyaleka ka huta, kacigaba dayaimana addu’a kaji dan uwana, banason damuwar ka ina kaunarka dan uwana kadena damuwa” Jalal ya dan daddaki bayan Jalal alamun rarrashi, daga nan ya tashi ya fice. 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Jalila yadda taga rana haka taga dare, se tufka da warwara kawai takeyi, gashi tunda ta dawo Nana ko dakin bata shigaba, Maama ta hanata Nana bata kwana a dakin ba a can gurin Maama ta kwanta. 

Bangaren Jawwad ma hakane, juyi kawai yakeyi, ya daga waya zs kira Jalika yaga inya kirata ma mezece mata, tunda be tabbatar Jalila taji abunda Maama taceba. 

Washegari Sam Jalila bata nuna da wani abu a ranta ba, sedai ko karyawa batayiba ta fita domin tafiya makaranta, a kofar gida tasamu Manu yanata goggoge mota, suka gaisa takoma gefe tana jiransa yagama su tafi, Jalal yana cikin motarsa a kofar gida, zeje wani guri, daga cikin motarsa yana ganin yadda ta rame, da ganin idonta kaman bata samu bacciba ta kwana cikin damuwa, lokaci2 tana goge idonta da handkerchief, Jalila tanada yawan fara’a bata fiye hade raiba, musamman in ta samu abun tsokana, amma yau fuskarta sam babu annuri, setayi kaman wadda ta dade tana jinya, har cikin ranaa seyaji babu dadi ganinta a haka, haka manu ya dauketa ya kaita makaranta. 

Hannah abun duniya ya dameta tarasa ta ina zata bullowa lamarin Jalal, amma tanason sanin matsayin Jalila a gurinsa, yazama dole taga Jalila, amma kafin taga Jalila kokuma bari in bari tukuna, amma bari inje gurin wannan garan sena hadu da Jeje, Hannah ta shirya tsaf ta dau mota, ta tafi inda tasan Zata hadu da Jeje, Jeje na ganin Hannah yafara murmushi yana tafa hannun sa “barka da dawowa Gimbiya Hannah” daga masa hannu tayi alamar bata son surutu, guri ta nema ta zauna tana facing din Jeje, Jeje ya rigata magana ta hanyar cewa “dama nasani Hannah zaki dawo, zaki cigaba da aiki damu kin temaki kanki da kika gane hakan, don Jalal baze taba aurenki ba, ni kaina yau rabon da Jalal yazo mashaya ya dade, shiyasa wani shirin muke sakeyi akansa zuwanki a yanzu kinzo akan gaba” “kaga dan Allah kayi shiru kaji meyake tafe dani se surutu kake, kai ka isa inyi magana in janye saboda wani banzan me gidanka baku isaba wallahi ka tsaya ka saurareni, nazone in gaya maka wanda yasa aka dauke Jalal ranar birthday dinsa ba kowa bane face wannan yarinyar data  kawo cake” a razane ya kalleta “are you serious?” “sekaje kayi bincike, da bakinta tagayamin haka, sannan kasani in har tana raye to baka isa kuyi nasara akansa ba, seku sake shiri sannan nima bazan bari kuyi nasara akansa ba saboda aurensa zanyi, mataki ya rage ku dauka akan wannan yarinyar, danni nafi karfinku kasani” “Amma hannah……..” kaga ni na riga nagama magana” ta mike ta bar gurin, jinjina kai Jeje ya dingayi yana tuna abunda Jalila tagaya masa daren da yafara ganinta akan Jalal, tabdijan yazama dole ya dau mataki akan yarinyar nan. Yazama dole anjima inje gidansu Jalal da kaina, inbahakaba akwai yuwar wannan yarinyar tamayar mana da aiki baya, bazan bari oga KB yaji wannna zancen ba mara dadi”

Anfito daga exams Jalila tana tafiya kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, daka ganta kasan bata cikin walwala, gani tayi an sha gabanta tana daga ido taga saleema, matsawa tayi da niyyar wucewa, takuma shan gabanta “Ke magana zanyi dake” Jalila ta kalleta “ina jinki” “Kashedi na karshe zanmiki akan Zahrah, ta kawo mana kararki dan haka ba ruwanki da rayuwar da takeso tayi, dan haka kidena mana shishshigi, bake ba zahra” Jalila ta dakko wayarta tana dannawa sannan tacewa Saleema “tsakanin nida zahra wakika haifa da kikemin wannan kashedin?” “haka kikace to kicigaba karki fasa zakiga abunda ze biyo baya” 

“bazan dena ba, mekika isa kiyumin meze biyo bayan?” cikeda da gadara saleema tace “Abunda ze biyo bayan abune mafi muni da bakinciki a rayuwarki abu mafi kunya da asara” murmushi Jalila tayi 

“shikenan ina jira, nabaki nan da yan kwanaki in har abun da kika fada be faru daniba to ke ze faru akanki, sha3 kawai” binta da kallo Saleema tayi, yayinda itakuma ta wuce, office din sir Hafiz taje, yanata marking, ya kalleta “hmm Gimbiya yar senaga dama se yau kikazo kiran danayi miki” shiru tayi batace komai ba “well ya exams din” “lafiya kalau Alhamdilillah” 

“meyake damunkine? Naganki kaman bakida lafiya” “lafiya ta kalau” ta bashi amsa a takaice

Mikewa yayi ya tattare takardun gabansa yasaka a drower yace mata “biyoni” ba musu tabi bayansa, sun danyi tafiya me nisa sannan sukazo bakin wani office, Sir hafiz ya bude kofar yamata alama yace “bisimillah” Jalila ta kalleshi “fara shiga zanbiyoka abaya” murmushi yayi “kina zaton zan cutar dakene anyway biyoni a baya” suka shiga office din, office din babbane sosai ya hadu matuka, se kamshi da sanyin Ac ne ke ratsa ko’ina a cikin office din, kallo daya tayiwa mamallakin office din yana kashingide yana dannan laptop dinsa, sallama sir hafiz yayi, da fara’a wanda ke danna laptop ya dago tareda amsa sallamar, musabiha sukayi da sir hafiz suka gaisa, ita dai Jalila kallonsu kawai takeyi Sir hafiz yace “kalleta ina fatan ita kake nufi” mutumin ya kalleta “eh itace Hafiz nagode sosai Allah yasaka da alkhairi” suka kuma gaisawa sir hafiz ya kalli Jalila yace “to game son ganin naki nan” batace komai ba sir hafiz ya juya ya fice, mutumin ya kalleta “bisimillah ga kujera nan kizauna mana” ya mike ya yaje fridge ya dakko mata ruwa da lemo ya ajiye a gabanta, “wai meyasa kake nemana, ni dai ban sankaba menayi maka” murmushi yayi ki kwantar da hankalinki dolece tasa na nemeki saboda naganki da abunda na dade ina nema ” kallonsa tayi irin ban fahimta ba

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“dan Allah a ina kikasan ABDUL JALAL, meye alakarki dashi?” kallonsa tayi cikeda mamaki sannan tace “waye kuma hakan?”

“Naganki a motarsa jiya yakawoki school shiyasa na tambayeki”

“kai mene alakarka dashi?” “Abokina ne, mun dade bamu hadu ba sena ganku tare, shiyasa na tambayeki saboda akwai wani muhimmin abuna a tare da shi?”

“shiya kamata ka tambaya alakar dake tsakanina dashi tunda abokinka ne, kokuma inbaka lambarsa seka tambayeshi” “to shikenan bani lambar tasa” mikewa tsaye Jalila tayi sannan tace “Sena tambayi izininsa tukuna” ta juya tai ficewarta daga office din tana zancen zuci “wannan wane irin abune kawai kawani fara tambayata waimeye alakata dashi mtseww” wata Jalila ta tsayar ta tambayeta sunan me office din, tagaya mata sunanshi malam Sagir Ahmad, Jalila taimata godiya ta tafi, 

Koda ta fita tsaki yayi, ya dauki wayarsa, ya dan daddana sannan yasa a kunnensa “hello, ke gaskiya yarinyar nan tanada matukar wayo, taki yadda tacemin komai a game da alakarta Da yayanki” Ajiyar zuciya Ilham tayi “kai duk dabarar naka da iya maganar amma ka kasa” “lallai Ilham, yarinyar tana da lissafi batacemin komai ba akan alakarsu” “shikenan nagode sosai” “yawwa to se anjima” Ilham ta aje wayar ta jinjina kai “shikenan tunda kinki fada, bari in je gurin malam inji meze cemana, Allah ya kaimu goben” 

yauma seda Jalila tasa nikab taje dan bare gidan dasu Saleema suke sheke ayarsu, ta tsaya daga waje, maza da mata ba wanda baya zuwa gidan nan, seda ta tabbatar su Saleema suna zuwa gidan nan kuma babu kalar yan iskan da babu. Ta dau lokaci a labe tana kallon masu shiga da fitaa a gidan sannan ta tari abun hawa takoma gida.

Ko a gida ma tunani taitayi, ko Jalal zatayiwa zancen wannan Sageer din cab toma tayaya zan tari wannan jarabbabben da wannan maganar ko ina, tana cikin tunanin ne Nana ta shigo dakin da fara’arta tace “kindawo ashe?” “Eh na dawo Nana” “yaya Jarrabawar” “Alhamdilillah” 

“Jalila taso zomuje ankawo sabon order na laces da turaruka, zomuje mu zaba”

“kai Nana wane irin lace kuma? Duk kayan damuke dashi” “to Ai Abba ne yayo waya yace muje” “to bari indakko hijjabina” “kai Jalila ingo mayafin nan dora, banaso wasu su rigamu zuwane a zabe abarmu” Jalila ta karbi mayafin hannun Nana ta yafa, ta kalli Nana “Nana gaskiya mayafin nan yai kadan dubi kayan jikina fa?” “wallahi watakila har muje mu dawo bazamu hadu da kowaba taho kawai” Nana taja hannunta suka tafi gidansu Jalal, Mummy bata babban palour dan haka sukaje part dinta, tana palourn ta tana kallo, Ilham tana kwance tana gyara dogayem faratan ta cikin girmamawa suka gaisheta ta amsa, Ilham bata kulasu ba, Nanace taitayiwa Ilham korafin ta dena nemanta yanzu zumuncinsu ba kamar da ba, nanma Ilham batayi wani responding ba a zuciyarta tace “kina tareda babba makiyata zan dinga sauraranki, taanar danake mata yanzu ai harda ke” Nana tace “Mummy anuna mana kayan mu zaba tun kafin azo a kwashesu” murmushi tayi tace “to hajiya Nana, dankuwa kinsan akwai costumer da Jalila ta hadani dasu sunce zasuzo da sun rigaku zuwa da sun kwashe” Jalila tai murmushi “Mummy ashe har yanzu suna zuwa” “muna hulda sosai suna siyayya a gurina, Jalila maza shiga bedroom dina ki dakkomin mukullaye acikin wardrobe dina, se muje a bude store ku gani” Jalila tana mamakin yadda Mummy batajin komai take turata kan kayanta, Ilham seda ta dago ta kalli Mummy, Mummy ta dauke kai, meyasa Mummy bata yadda da ita akan irin wannan lamuran nata, tsabar haushi Ilham ta tashi takoma baban palour, Jalila taje ta dakko keys, sukaje store suka gama ruwan idonsu suka dauki kaya” Mummy tabiyosu sun fito babban palour sega Daddy ya shigo shima suka gaisa daddy yace “Jalila na kuwa tura Jalal nace masa yace inason ganinki sega faduwa tazo dai2 da zama” murmushi tayi “ai bansaniba Daddy dana zo” yace hakane ya kalli Mummy yace “yan borno zasuzo next weekend Insha Allah” 

A razane Mummy ta kalleshi, Ilham ma seda ta tashi zaune, Mummy tace “yan barno kuma? Meza suzo suyi?” “Zumunci mana, dan haka Jalila naga kin iya wannan kayan dadin Abincin naku na yan zamani da irin namu na yan da, dan Allah inban takuramiki ba inaso za’ayimin zamuyi baki ne nasan Madam bazata iya ba ita kadai” Jalila ta dan rusuna “bakomai Daddy Insha Allah ba damuwa za’ayi”

Nana tace “daddy dama Abincin hada wani na kwadayi” murmushi yayi “Eh mana Nana irin naku na zamani ba” Jalila tace “amma wani irin Abincin kakeso ayi musu sannan su nawane”? “Yawwa takwarar son, nagode sosai, yanzu kije gida kiyomin list din Abunda za’a bukata, kiyi musu kawai Abinci me dadi, nasan zasuzo da dan yawa ina jiranki kiyo list din, wanda muke dashi shikenan in babu se a siyo, inkin tashi kizo kiyi anan karki bata muku gida “

“to Daddy bari inje yanzu zan kawo maka Insha Allah”

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Su Jalila suna futa Mummy tace “dan Allah dagaske kakeyi koda wasa!”

“daga snake shiyasa ban takuraki nace kiyi musu girkin dazaki karbesu ba gara nasa na waje suyimin tunda ke ba lallai kiyi ba, bayan shekaru yan uwana zasuzo sukawomin ziyara” daga haka ya wuce part dinsa, dafe kai Mummy tayi tanemi guri ta zauna ita kanta Ilham kanta ya kulle,

Jalila tana zuwa gida, ta zauna tayi list din abunda take bukata ta fito domin kaiwa Daddy, amma tundaga kofar gida taci karo da motar Jeje, “Wannan annamimin mayen yazo kenan” tana shiga taga Jalal da Jeje a harabar gidan, suna zaune akan fararen kujeru suna hira, suna shan wata irin taba me girma sosai dan tafi wadda Jalal yake sha girma, zuwa tayi ta wucesu cikin gida, Jeje da kyar ya iya dauke idonsa akan Jalila, saboda karamin mayafine ajikinta gashi doguwar rigarta cif jikinta

“Waime kake kallo hakane?” Jalal yaima Jeje tsawa cikin inda2 Jeje yace “ohhh am sorry J, nothing, dan samomana kayan washi mana, tunda kwana biyu bamu hadu ba” Jalal yace “to jirani ina zuwa” Jalal ya mike yaje part dinsa ya kawo musu kwalaban giya da wayne cups ya ajiye akan table din”Jeje yace “yauwwa nace meyasa kadena zuwa club, friends nata tambayarka yane? Ga beb dinka Hannah duk tana cikin damuwa irin sosai kagane eh”

“kai bari kawai, haka nan bana son zuwa club din nan, a gida nake dura duk abunda nakeso normal ne ai nan da can” “A’a akwai banbanci, nan  ba wasu zafafan mata, bawani sauti me ratsa kunnuwa, kodayake bebs din dake ratsawa a gidan nan naku ma sun isheka kallo, especially wannan zazzafar baby girl din, komai nata me kyaune,” hade rai Jalal yayi, a fusace yace”kamanta kashedin danayi maka abaya ko” Jeje ya sauri yace “ohh No am sorry bazan karaba Insha Allah, yanzu kaga dakkomin wani product din wannan ta isheni, kusan kullum ita nake sha, nasan bazaka rasa na manyan kai ba, dan Allah kabani wani product din” “bazanje ba sedai karka sha” “please am sorry nasan kanada masu tsada dan Allah ka dakkomin” banza Jalal yaiwa Jeje, sekuma can jumawa ya tashi ya tafi dakko masa wata giyar

Jalila ta shiga palour bakowa, Seta jiyo sautin maganar Mummy a bangaren daddy, kaman sa’insa sukeyi, dan girgiza kai Jalila tayi, be kamata taje musu a yanzuba, tana jiyo muryar daddy yana “yan uwanane gurina zasuzo ba gurinki  ba, insunzo sedai kibar gidan”

“Amma kamanta abunda yafaru ne? Har kake wannan tunanin?”

“ni ba abunda ya faru tsakanina dasu sedai tsakaninki dasu” Jalila juyawa tayi tafito da sauri dan karma su fito su ganta su gane taji sa’insar da sukeyi. Koda ta fito harzata tafi, ta juyo Jeje cikin wannan muryar tasa mara dadin ji  yana cewa “hi beb i like your confidence, akwaiki da fada da cikawa, ” tsayawa tayi cak ba tareda ta juyo ba, yacigaba da cewa “kin fada kuma kincika, kinyi nasarar batamin aikina na wannan rana wanda na dora raina akaki, amma ki saurari hukuncin dakuma abunda ze biyo baya” juyowa tayi ta kalleshi, kawai taga kwalaben giya akan tebur, take taji ranta yabaci koya daddy zeji in yafito yaga dansa yana shan giya a cikin gidansa, shida wani dan iska ta kalli Jeje “ai fada da cikawa baka ga komai ba, se randa sharrin ka yakoma kanka, se ranar dana ga karshenka, asararrae dan wahala, kalle ka sekace karen arna tir da kai da halinka, kuma shi zalunci in abunyine kacigaba, nima bazan gajiba” 

“Jalal, shike kama da kare amma ba dainiba shike kama da karnuka, kuma kisa ido, zakiga yadda ze koma ke, zakiga yanda zan maida shi, senacika alkawarin da na daukarwa me gidana, se Jalal ya lalace fiye da tunaninki seya kare rayuwarsa a prison a wulakantacce, ke asuwa naganin bayana karya kikeyi, dukda bangane meye nufinki akansa ba amma zanyi maganinki wallahi, senamiki tabon da harkibar duniya bazaki manta ba” 

“Shikenan naji nakuma yadda, koni ko kai duk wanda yasamu dama yaga bayan dan uwansa, sena wulakantaka daga kai har megidannaka, ainasan waye megidannaka zaka gani, banda ai sam Jalal be dace da tarayya da tababbe irinka ba tunda kaikayi sanadiyar yazama haka, ka cutar da rayuwar sa, sannan kacigaba da wargaza masa rayuwa, nikuma zancigaba da bashi kariya dayi masa addu’a har zuwa numfashina na karshe kuma insha Allah seka wulakanta kafin in bar duniya, sanna kasani…….. Shiru tayi ganin Jalal yafito da wata katuwar kwalbar, yaje ya zauna, tana tsaye tana kallonsa ta gefen flours Jeje yaimata wani shu’umin murmushi, Jalal sam be kula da itaba, saboda tana bayan inda yake a zaune, Jeje ya bude giyar ya zuba, sannan ya zubawa Jalal a cup ya mika masa, Jalal ya karba ya kai bakinsa ze sha, Jeje kuma idonsa na kan Jalila, yanaso yaga yadda zatayi da hanzari ta kaaraso inda suke, Jalal ji kawai yayi an kwace kofin hannunsa ta kalli fuskar Jeje ta watsa masa ruwan giyar nan a fuskarshi , gaba daya suka bita da kallo, ta kalli Jeje cikin zafin rai tace “Asararre tababbe mara zuciya, wallahi inbaka ji tsoron Allah ba, mushen jaki seyafi karshenka kyan gani, saboda rashin mutunci a cikin gidan mahaifinsa zaka biyo shi kuyi shaye2” ta kalli Jalal tuni idonta yacika da hawaye “kaima saboda rashin zuciya Jalal mahaifinka na cikin gidan nan kana nan kana sha masa giya a gida, kowane lokaci ze iya fitowa yazeji in yaganka a haka? Memakon ma kuyi a dakinka amma kake shan giya a bainar jama’a ko kunya bakaji, kodayake bakaji kunyar Allah ba sena mutane, bakaji dadin halinka ba wallahi” 

Jalal sam ba abunda Jalila tayi bane ya bata masa rai illa irin kallon maitar da Jeje yakemata, ta juya ta hankade tabur din da giyar take kai, suka fadi kwalaben suka fashe, tana kuka tana fadin “Jalal kaji tsoron Allah, Allah ya tsinewa me shanta, da duk me ta’amali da ita, amma giya a cikin gidanku, gidan mahaifinka”  ta kalli Jeje “kafita kabar gidan nan, wallahi bantaba tsanar mutum a rayuwataba kamarka, idan na ganka jinake kaman naga shedan natsaneka wallahi, kallon nan danake maka kaman zuciyata ta fashe haka nakeji, in baka bar gurin nan ba sena maka illa da kwalba” ta durkusa tana kuma fasa kwalaben dabasu fashe yadda takeso ba, Jeje ya kalli Jalal “J man, anya yarinyar nan ba mahaukaciya bace ba, kalli fa abunda takeyi” kafin ya rufe bakinsa tafasa hannu da kwalba, da sauri Jeje ya durkusa ze tabata, cikin zafin nama Jalal ya janyeshi, “meye haka kake kokarin yi” Jalila gaba daya ta hargitse kaman mahaukaciyar, Jeje yace “haba J kalli yadda beb din nan takeyi inta illata kanta ba karamar asara za’ayi ba, kallon Jeje yayi,”get out from here” da mamaki ya kalli Jalal “me kake nufi?” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“kafita ka tafi yanzu ka bar gidan nan” “Amma Jalal…… 

” kafita nace bakaji menaceba ne, kosokake seta illata kanta” Jeje ji yayi gaba daya duniyar tamasa zafi jiyake kaman ya mutu ya huta yau shi Jalal yakewa wannan tsawar saboda mace, ya juya ya fice daga cikin gidan, da sauri Jalal yasa hannu dago Jalila daga durkushen da take, ya jinginata a jikin bango sannan yasa hannunsa ya dafe gefe da gefe, ya kalleta yace “baki da hankali ko?, sekinyiwa kanki Illa tukuna, ji yadda kika yanke hannu meye amfanin hakan da kikeyi ne? Ina ruwanki dani dolene sekin shiga shirgin rayuwata” idonta duk hawaye tai masa wani irin kallo, shima kallonta yayi daga sama har kasa, ya karewa rigar jikinta kallo sannaan ya kalleta 

“Idan kika kuma bari naganki da kaya irin wannan sena bata miki rai, sena yaga kayan ko agaban uban waye, sena miki rashin mutincin da bakya tunani” idonta duk yayi ja tace “au yanzun meya hanaka yagamin rigar, tunda baka da hankali, Jalal baka da hankali na fada kuma zan fada ko agaban waye baka da hankali, ai daka sani ga yagamin riga seka tabbatar min lallai giyar daka sha tafara aiki, yanzu kagama cemin ina ruwana da rayuwar ka, nima ina ruwanka datawa rayuwar, kanwarka wace irin shigar ce batayi seni zaka dingayiwa shouting haka, ko tsirara zan tafi ba ruwanka dani, in kafasa yagamin kaya baka kaunar Allah, sannan ka gayawa abokinka zan gauraya dashi, dagani kabani guri in wuce ko in hankadeka akan kwalaban nan, koka mutu banda asara” banza yayi mata ya cigaba da kallonta, “Nine banida hankali ko? “eh baka da hankali, ka matsa in wuce nace ka tsaya kana karemin kallo, duk ka cikani da warin giya, da kaurin hayaki, kaman zanyi amai. Jitayi kaman wani abu yana shanshana mata kafa, dubawatayi taga menene, ihu tayi, ta rungume Jalal tana” wayyo Allah na mene wannan” dubawa Jalal yayi seyaga ashe dan karensa dayake cewa bobby ne  kiwata shiyake  a part dinsa ya bar kofa a bude shine yafito, karen dan guntune da kadan yafi mage tsayi, ga jikinsa buzu2 da gashi gashi kato sosai amma ba tsawo, daga England daddy yakawo masa shi, Jalila bata taba ganin kare irin wannan ba, kuma batasan dashi a gidan ba. 

Ilham se kiran layin Maminta takeyi ta labarta mata abunda yake faruwa a gidan, amma wayar taki shiga ba network, dan haka ta yanke shawarar bari ta fito waje kozata samu network. 

Koda bobby yaga Jalila ta tsorata sekara zuwa kusada ita yakeyi, yana shanshana mata kafa, sosai take ihu tana kara shigewa Jalal, hmm dariya ma tabashi tagama zaginsa kuma yanzu abun tsoro yazo ta rirrikeshi, dan haka ya kyaleta Bobby se zagaye mata kafa yake, 

“Nashiga uku, Dan Allah a temakeni, wani abu ze cinyemin kafa, waimeye haka bazaka hanashi ba banaso, dan Allah banason mage fa” duk ta yamutsa masa kaya gashi ta goge masa jinin hannunta duk a rigarsa, janyota yayi ya tsayar da ita “meye haka? Kare ne fa kalli” itadai bata taba ganin Kare a haka ba, Jalal ya dago bobby a hannunsa yana nuna mata, aikuwa Bobby yai tsalle yakoma jikinta, ihu takumayi tana nema fita a hayyacinta, tana kokarin cire Bobby a jikinta, dan tsoro yakebata, sosai takuma rike Jalal tana ihu, Jalal ya riketa ya dauke Bobby a jikinta,

Abunda Ilham tagani ne yai matukar tayar mata da hankali, tarasa idonta biyune kokuma mafarki takeyi, Jalila ajikin Jalal, abunda bata taba ganin yayi ba, nan take taji kirjinta ya buga da karfi, tama rasa me zatayi, ta juya takoma cikin gida da gudu. A hankali yacewa Jalila “Nutsu mana is just a dog, ba abunda ze miki, kalli yadda kike nema ki firgita kanki, duk tsiwar taki kalli yadda kika rikice akan kare, seki dagani ai, tunda ba jikin Jawwad bane, jikin makakke ne mara daraja, kokindena kyankyamin gashin jikin nawa” tsaki Jalila tayi ta juya, girgiza kai Jalal yayi, Jalila tai tafiyarta gida. 

Nana tazo ta zauna a kusada Jalila tace “Jalila kamshin wani turare kikeyifa” “kamar ya?” “kamar yadda nagaya miki, kamshin me dadi” “turare na dai dayane kuma kinsanshi sekuma me?” “hmmm bakomai, yaushe zamu kai dinkine?” “ko yaushe ne kikaimana, ni har yanzu bamu gama jarrabawa bane” “to shikenan” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Daren ranar Ilham ko na minti daya bata rintsa ba ta dau wayarta ta kira malaminta

“hello malam ina cikin damuwa fa, yarinyar nan da alamun soyayya suke da Jalal, tashin hankali na ma kar inje Aikin da akayi masa ya karye” “Aikin da akayi masa har yanzu yana jikinsa, amma kibari zuwa gobe kizo” “to shikenan nagode zanzo goben” sukayi sallama, saboda tunani da bacin rai, tarasa meyake mata dadi, sabida abunda idanunta suka gane mata yau amma gaskiya Jalila tacika yar rainin hankali taita nuna ita batason Jalal dan munafunci ashe soyayya da suke harta kai ta rungumeshi, taita nuna ita ta Allah ce amma abun bahaka yake ba, Allah2 kawai take gari yawaye ta tafi gurin malamin nan ayi duk me yuwuwa ayita ta kare!. 

Jawwad har ya shirya ze kwanta, Hanan ta kirashi, kamar ya share ta sekuma ya dauka

“barka da dare abun kaunata fatan kana lafiya” “lafiya kalau hanan yaya mutanen gidan?” “duk suna lafiya kalau Alhamdilillah, kwana biyu ko nemana bakayi meyasa” “bakomai Hanan abubuwa ne sunmin yawa kawai, gashi muna daf dagama school” “Allah sarki nayi murna sannan inamaka fatan Alkhairi, Allah ya sanya Albarka a ilimin ka yasa al’umma su amfana” 

“Ameen Hanan naji dadin Addu’arki nagode sosai” “No bekamata kayimin godiya ba, tunda ina sonka zanso duk wata karuwarka Jawwad, amma na lura kaman ina takuramaka ni kadai nakesonka nasan kana guduna saboda Jalila, amma nima yakamata ka tausayamin Jawwad, Abunda kakeji game da Jalila shinakeji game da kai, bazanso incigaba da takurawa rayuwarka ba, bazan so saka ka a cikin damuwa ba, zanso ka kasance a cikin farinciki koda zezama ni narasa nawa”

“Hanan yakamata ki……” “A’a Jawwad base ka gayamin komai ba, karka damu, amma kasani bazan dena sonka ba har karshen rayuwata, inasonka Jawwad, amma Insha Allah wannan shine kira na karshe da zanyu maka, bana son rusa maka farinciki, tunda na fuskanci ina takuramaka, ka gaishemin da masoyita kuma yar uwata” kafin yayi magana ta kashe wayarta, jiyayi daga karshe kaman kuka take, seyaji sam beji dadin hakan ba, dan haka yai kokarin bin layinta amma a kashe haka yaita trying har ya hakura. 

Da wuri Jalila ta shirya dan tafiya makaranta, sam bata jin dadin jikinta, ta kwana da ciwon kai wadda tasan damuwa ce datayi mata yawa, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa dan duk ta rame, tana fitowa ta tarar manu yana goge mota, suka gaisa ta shige gaban mota ta kifa kanta, tana jiran manu yazo su tafi, har ya shigo ya kunna motar bata dago kanta ba, seda taji gudun yayi yawa ba tareda ta dagoba tace “Manu mutafi a hankali mana, kaina ciwo yake sosai, wannan gudun kaman zamu bar gari” shiru be amsaba kuma be dena gudun ba, dagowa tayi kawai taga Jalal ke tuka motar ba manu ba 

“kaiii meye haka kuma? Ina manun?” shiru yayi yacigaba da tuki “magana fa nake maka, yauma ka dakkonine don kamin wulakanci, inkuma makara wallahi baka isaba ka ajiyeni kawai in sauka” still bekuma cewa komai ba

“wai baka jinane? Nika ajiyeni, bana son adinga gani tareda kai kar wannan shashan yan matan naka su dinga min hauka, gashi har wani yafara titsiyeni sena gaya masa alakar dake tsakanina da kai ni ka ajiyeni” “Ke!!!” seda ta tsorata, saboda yanayin da yayi maganar “idan na ajiyeki duk abunda yasameki kika sani, ba cewa kikayi kanki yana ciwo ba, amma se surutu kikeyi, wallahi kika kuma magana sena baki mamaki, in an ganmu tare duk wanda ya tambayeki kigayamasa abunda kika gadama” ba shiri taja bakinta tayi tsit, ko minti biyar beyi, da wannan maganar da Jalal yayi ba, wata mota tasha gaban tasu motar a guje, wanda ya tilastawa Jalal yin parking. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

Back to top button