Hausa novels

Wace Ce Ita (Who is she) Chapter 68 Complete Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY-EIGHT📍

Daga idon da zatayi sukayi ido hudu dashi daidai ya zauna akan kujerarsa, mamaki ne ya bayyana karara akan fuskarta saboda bata taba tinanin ganinsa ba, inko hakane toh waya kirata dan sam muryar batayi kama da tasa ba, babu shakka kuma address din office dinnan aka bata, mazewa tayi tace;
“Yaya dama kai ke kirana?”…
Hade girar sama da kasa yayi kamar be santa ba yace;
“Koma kiyi sallama!”….
A sanyaye ta koma tayi sallaman sannan ta sake shigowa, bataji ya amsa sallamar ba taji yace;
“This is not yaya, this is your supervisor, mind the way you talk”….
Gyada kai tayi tanajin kanta na sarawa, har mamakin yanda bata iya masa musu takeyi yanzu, tabbas ta yarda she’s a different person now, da a lokacin da take fatima zainab dinta ne shima yasan be isa yace ta koma tayi sallama ta koma ba saidai suyi duk balakin da zasuyi, amma wannan baby tee din is too cool, ko hayaniya bataso ayi a gabanta…
“Sit!”….
Maganar daya dawo da ita hayyacinta kenan, zama tayi a kujerar daya nuna mata tana gyara mayafinta….
Batareda ya kalleta ba yace;
“I assume kinyi gaban kanki ne da baki kawo research proposal dinki ba, now I want to see a sample of your research”….
Wani irin banbarakwai taji zancen saboda tasan yakamata ace ya sani in tayi ko batayi ba hasalima shine yake tsaye akan rashin lafiyarta shine ze zo yana tambayarta kamar wacce be sani ba, bata fuska tayi tace;
“Ban fara ba”…
Wani mugun tsawa ya daka mata yace;
“You’re very stupid! Ni kike gayawa baki fara ba? What are you even doing in this school”….
Ranta ne taji ya soma baci ta tsuke fuska cikin halin ko in kula tace;
“Toh karya kakeso in maka ince nayi?”….
“Ni kike yiwa rashin kunya zahrah?”…
Murguda baki tayi a ranta tace ashe dai ka sanni tinda kake kiran sunana….
Takardu taji an watso mata a fuska ta dago da sauri tana kallonsa, wasu ya sake watso mata sannan cikin masifa yace;
“Na baki 24hours ki kawomin research proposal dinki, wannan kuma handouts ne na courses dinku shi kuma na baki 48hours ki karanta kizo kiyi resiting exam din da kikayi missing, wallahi ko abu daya kika kuskure sai kinyi danasani, kwashe ki ficemin daga office unserious element kawai!”….
Fashewa da kuka tayi saboda tsabar takaicin yanda ya watso mata takardun ta mike ta zubar da takardun ta juyo ta kallesa cikin shesshekar kuka hade da daga murya tace;
“Menayi maka? Why did you change so bad? Meyasa kake min wulakanci yanzu? Kai ba yayana bane? Nace mena maka?”….
Jikinsa ne yayi mugun sanyi yana jin zubar hawayenta har cikin zuciyarsa, Allah yasani bada wata manufa ya mata hakan ba, kawai so yake tayi concentrating sosai, yaga kuma in ya bita a hankali sai ta kiyi, amma datace kai ba yayana bane sai yaji maganar ta mugun tabasa, fita yayi daga office din ya barta a tsaye tana cigaba da kukan…
Ko 5mins beyi da fita ba yaji hankalinsa ya kasa kwanciya, ba ze iya jure barinta a haka ba, dawowa yayi ya koma cikin office din ya sameta a durkushe tana kuka, tattara handouts din daya watsa mata yayi sannan ya dagota cikin rarrashi yace;
“Stop crying zahrah”…
Fuzge hannunta tayi ta matsa gefe….
Kamo hannun ya sakeyi cikin lallashi yace;
“Haba yar kanwata bakisan ba kyau mutum yana fushi da yayansa ba”…
Hawaye ne ya silalo a idonta ta turo baki tace;
“Ba yayan bane ya fara fushi dani yana min masifa ba”…..
Dayan hannunsa yasa ya goge hawayen sannan ya ja hancinta yace;
“Tuba yaya yake, kece bakyaji and your yaya wants you to have a good future”…
Shiru tayi ya dauke guntun hawayen daya zubo mata ya lakaci kumatunta yace;
“Be kamata hawaye yana zuba akan pretty face dinnan ba, karki kara kuka kinji ko?”….
Gyada masa kai tayi tanajin wani dadi aranta, har ta manta yaushe rabon da magana me dadi ta shiga tsakaninsu, sai take jin yau din kamar rana ta musamman….
Sakin hannunta yayi yana tattara sauran takardun yace;
“Muje in kaiki shopping yar kanwata”…
Murmushi tayi tanajin kamar tafi kowa sa’a ranar, sai ta matsa jikin kofa tana jiransa ya gama su tafi…
Dagowan da zeyi yaci karo da abubuwa a tsattsaye suna kallonsa ko tamtama kuma bayayi bata saka bra ba, dauke kansa yayi bece komai ba ya cire jacket din dake saman rigarsa ya yasaka mata, hakan be masa ba sai da yayi buttoning jacket din sannan ya gyara mata zaman mayafinta ya dan sauko ya rufe kirjinta, tsayuwa tayi kamar gunki tana kallonsa har ya gama batace komai ba ya kama hannunta suka fita….
Tinda suka fito harabar makarantar ake binsu da kallo, babu inda zasu gifta ba’a dago an kallesu ba saboda balakin dacewan da sukayi, a haka kuma wasu gani suke kamar yan uwa ne saboda dan kama da sukeyi saidai kuma duk wanda ya sansa gani yake matarsa ce saboda sun san ba yanda za’ayi ya ruko hannun wata haka, wa’yenda sukaga shigarsa ma sunfi kowa gasgata hakan saboda jacket dinsa da yake jikinta gashi dama duk basu san fuskarta ba sai hakan ya tabbatar musu da matarsace ba yar makarantar ba…..
Sai da ya tambayeta wanda ya kawota tace a motarta tazo sannan ya karbi key din yace su shiga nasa su tafi zesa a mai da nata gida, suka shiga yaja motar suka tafi…
A daidai Payless Hypermarket yayi parking suka fito a tare, sai da ya zagayo ya sake gyara mata mayafinta sannan suka jera suka nufi cikin mall din…..
Suna shiga ya kamo hannunta yace;
“Yauwa mu fara da perfumes, I really don’t like the ones you’re using”…
Okay kawai tace tana biye dashi, karasawa gurin turarukan sukayi ya fara daukosu yana shinshinawa, duk wanda ya dauko sai yaji yayi karfi yana sane kuma ya hanata zaba da kanta….

Download>>>

Kamar ance ta dago idonta ya sauka akansu, kasa gasgata abinda idanuwanta suka gani tayi, saida ta kara matsowa kusa sannan ta tabbatar da shi din take gani, mutumin da tun ranar data fara ganinsa a airport a Iran bata kara samun nitsuwa a rayuwarta ba, tin ranar kuma take bibiyarsa saidai bata wani samu information akansa ba, abu daya kawai ta samu shine dan Nigeria ne, babban dalilin daya kawota kuma kenan dukda kasancewarta yar Nigeria itama dama karatu ne ya kaita Iran, yau watanta daya a Nigeria ta kasa samun ko sunansa sai gashi yau Allah ya yanke mata wahala ya nuna mata shi, ita ko ina zata bari damarta ta wuce ta, sannan kome ze faru sai ta tabbatar ya zama mijinta kota halin kaka, tashin farko ta yankewa zuciyarta wacce take gefensa kanwarsa ce saboda kama da taga sunayi, ta kuma kudirci yiwa kanwarsa magana saboda bazata iya tunkararsa kai tsaye ba dan bata manta da marin daya mata wancen karan ba, nufarsu ta farayi cike da karfin gwiwa, luckily kafin ta karasa taga ya bar gurin sai yarinyar ita kadai..
“Hello beautiful”..
Ta fada tana sakarwa baby tee murmushi..
Juyowa baby tee tayi ba yabo ba fallasa tace;
“Hi!”…
Murmushi tayi tace;
“I’m suhaima, you?”….
“Fatima”..
“What a nice name for such a beauty like you”..
“Thank you”..
Murmushi ta sakeyi tace;
“Please can you do me a favor fatima?”…
“What favor?”…
Cewar baby tee tana dauko wani turare da deen ya ajye…
“Number yayanki nakeso ki bani dan Allah”….
Zaro ido baby tee tayi tace;
“Number yayana kuma?”…
“Yes please, wanda na ganku tare yanzu”..
Wani dogon tsaki taja ta hade rai tace;
“Bazan bayar ba”….
“Saboda me bazaki bata ba”…
Suka jiyo muryar deen akansu, kafin wani daga cikinsu yace wani abu ya zaro business card dinsa ya mikawa suhaima sannan ya kalli baby tee yana shirin magana yaga tabar gurin, bin bayanta yayi da sauri ta fita daga mall din a guje, ko kafin ya fito ta shige napep sunja, giftawar me napep kawai ya gani yayi saurin shiga motarsa yabi bayansu….
Ganin yana binsu a baya tacewa me napep din ya bacewa wanchan da yake binsu ko nawane zata basa, me napep na jin haka ya kara speed suka shiga wata kwana, a haka a haka har deen ya nemesu ya rasa…
Sosai hankalin deen ya tashi especially dayaga sun bace masa, babban abinda yafi daga masa hankali kuma shine abinda yasa tayi hakan, yasan dai bada number dayayi be kamata ya zama wani problem ba, infact shi bema gane yarinyar ba haka kawai yaji sha’awar bata number amma da yasan baby tee bazataji dadi ba da be bayar ba, yanzu ta ina ze fara nemanta?, tinani yayi ai wannnan ba fatima zainab din da bace mara tinani bare yayi tinanin zatayi wani gurin, yasan wannan baby tee din dole gida zata tafi, hakan yasa ya dauki hanyar gida yana addu’ar Allah yasa yana shiga ya ganta…..
Tin a gate ya tambayi gate man ko baby tee ta dawo yace gaskiya bega shigowarta ba besani ba dai ko dazu daya je kama ruwa ta dawo, shiga ciki yayi zuciyarsa cike da positive thought na ganinta a cikin gidan….
Twins ya tarar a parlor suna hira ya tambayesu kota dawo, hada baki sukayi gurin bashi amsar ‘bata dawo ba’…
Kin yarda yayi sai da yasasu zuwa su duba masa sama, dawowa sukayi suka sanar masa da batanan, dafe kansa yayi yana tinanin ina taje, part dinsa ya tafi da tinanin zata dawo zuwa anjima tinda yasan duk inda taje dole zata dawo kafin dare, chan kuma sai yaji hankalinsa ya kasa kwanciya, kawai ya dau waya ya kirata, saidai kiran duniya taki dagawa yasan kuma tana gani, kyaleta yayi inta wuce ta dawo da kanta…
Sai da taga sun bacewa deen gabadaya sannan tayi directing me napep zuwa gidansu khaleel, a hanya ta kirawo khaleel ta tambayesa yana gida yace mata eh, tace toh ya fito ya jirata a waje kuma ya tawo mata da twenty thousand, ‘angama wifey’ ya fada sannan ta kashe wayarta….
A gaban khaleel dake tsaye sukayi parking, fitowa tayi ya mika mata kudin datace yazo mata dasu, karba tayi ta mikawa me napep kudin yayi saroro yana kallonta, ajye masa tayi tacewa khaleel su shiga ciki, me napep na ganin haka ya daka tsalle yabi bayansu yanata godiya kamar ze kwanta mata a kasa, shigewa sukayi me napep yaja ya tafi cike da nishadi na babban sa’an da yayi ranar dama fitowarsa kenan…..
“Wifey kin ki cin komai?”…
Cewar khaleel cike da kulawa, tinda suka shiga yasa aka cika mata abubuwa a gabanta saidai bata taba ko ruwa ba..
“I’m okay”…
“Daga gida kike wifey?”…
Ya jewo mata tambayar dake cin ransa, ba wai beji dadin zuwanta bane, kawai yasan babu abinda zesa a barta tazo gidansu in bada dalili ba…
“Daga school nake”…
“Okay wifey”….
Shiru tayi tana tinanin abinda ya wakana a hypermarket dinchan, ko za’a kasheta batasan meyasa ta tawo tabarshi ba tasan dai bataji dadi daya bawa yarinyar business card dinsa ba, zatayiwu kuma taji haushi ne saboda ta riga ta cewa yarinyar bazata bayar ba shi kuma yazo ya wani bata….
Haka suka cigaba da zaman kurame duk yanda khaleel yaso suyi hira taki basa hadin kai, bayanda ya iya haka ya kyaleta, sallah kawai ke tashinsu daga shi har ita bayan nan ko tv basu kunna ba, a haka har akayi sallar mangariba suna zaune lokacin baby tee ta dade da kashe wayarta….
Kasa hakura khaleel yayi lokacin dayaga karfe tara tayi kuma be ga alamun tafiya a tattare da ita ba, mikewa yayi yace;
“Muje in kaiki gida wifey, naga dare yayi”
“Ni anan zan kwana”…
Ta bashi amsa kai tsaye…
Hakan sai ya tabbatar masa da akwai abinda aka mata, zata yiwu lefi tayi aka mata fada shine taji haushi, a tausashe yace;
“Kiyi hakuri in mai dake gida wifey, kinga be kamata ki kwana ba”….
Cike da masifa tace;
“Da bana kwana a gidan ne? Ka gayamin in korata kake in tashi in tafi, ai ba nan kadai bane inda zan iya zuwa”….
“No ba haka nake nufi ba wifey, ni ban isa in koreki ba, kawai su umm da mami bazasu ji dadi bane kuma zasuyita nemanki, dan Allah kiyi hakuri in kai ki gida”….
“Look khaleel! Nifa gidan ne bazan koma ba, anan kuma nakeson zama, kuma ka sake ka fadawa yan gidanmu ina nan wallahi a bakin aurenka, I mean it!”…
Shiru khaleel yayi be kara tanka mata ba, karshema cewa yayi ta zabi dakin da take son kwana tace bata shirya bacci ba su zauna a parlor…

Karfe shida na yamma mami ta dawo daga aiki, dakin umm ta fara zuwa ta tarar da ita tana aiki akan system har lokacin, sannu da gida ta mata ta dora da fadin;

Deen House (Romantic Story) By Oum Hairan

“Jam tun safe, waii sannu”….
“Hmmm yauwa yaya sannu da zuwa, wallahi wani yaro akayi diagnosing in a critical condition, anyi tests kala kala amma ankaso gano abinda ke damunsa, shine muke zoom meeting akan tin safe”….
“Oh Allah sarki, Allah ya basa lafiya yasa a gano abinda ke damunsa”….
“Ameen ameen, mun gama ma”…..
“Okay bari in je in watsa ruwa”….
Cewar mami tana barin dakin, fita umm itama tayi ta nufi dakin baby tee, tun dazu take ranta ganin bata shigo ba tun safe, bata sameta a dakin ba ta sauka kasa, twins ta tarar suna kallo, suka mata barka da saukowa tace musu;
“Ina baby tee?”….
Hussy ce ta bata amsa da fadin;
“Bata dawo ba”….
Da mamaki tace;
“Ina taje?”….
“Wallahi bamu sani ba, she went out in a rush”….
“Tun yaushe kenan?”…..
“Tun safe”…
Suka hada baki gurin bata amsa….
“Tun safe ta fita shine haryanzu bata dawo ba? Meyasa baku fadamin ba?”….
Rasa abun fada sukayi suka sunkuyar da kai, komawa sama tayi ta dau wayarta ta shiga kiran baby tee, saidai duka wayoyinta a kashe, hankalinta ne ya tashi ta tafi gurin mami ta bata labarin abinda ya faru, kiran baby tee mami tayi a wayarta nan ma a kashe, mai da akalar kiranta zuwa layin deen daya fara garari a titi yana nemanta tayi, bugu daya ya dauka ta fadamishi baby tee ta fita tun safe bata dawo, ce mata yayi ya sani yanzu haka ma ita yake nema, su kwantar da hankalinsu ba bata tayi ba, amsa masa kawai mami tayi badan hankalinta ya kwanta ba…..
Suna zaune har akayi isha’i deen be dawo ba, minti minti suke kiransa yace su kwantar da hankalinsu Insha Allah za’a ganta, karshe da suka damesa da kira ya daina dauka sai dai ya musu text message yace karsu damu….

Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Deen be tabbatar da dagaske baby tee ba dawowa gida zatayi ba sai da yaga sha biyun dare yayi, lokacin ji yake kamar yayi hauka saboda babu inda be duba ba be ganta ba, sosai lissafinsa ya jagule saboda tinanin inda taje gashi dare yayi, har transcorp hilton saida yaje ya sasu a gaba suka bincikamasa duka wanda ke hotel din dukda basa bada information akan mutum, amma babu yanda suka iya dole sukayi abinda yace, har a wayo sai da yaje gidan abby ya gaishesa yaga ko tana nan amma bata nan, babu inda be zagaye ba a garin abuja amma kwata kwata brain dinsa be kawo masa gidansu khaleel ba….
Kallo daya zaka masa ka gane how frustrated he is, ga damuwa bayyane karara akan fuskarsa, ga su mami dake damunsa da kira yaki dauka gashi ya hanasu fitowa, abun duniya ne ya ishesa ya kirawo sudais dan ya gayamasa halin da yake ciki ko ze dan ji sanyi a ransa…
Sudais na daga wayan ya basa labarin duka abinda ya faru , be boye masa komai ba tindaga zuwansu mall zuwa shigewarta napep da bace masa da sukayi da irin neman daya mata amma haryanzu be ganta ba…..
Sai da sudais ya gama sauraransa tsap sannan yace
“Saboda me zaka bada number bayan tace bazata bada ba?”….
“Wani irin tambaya kake min haka sudais?”….
“Yes, ai sai kabi abinda tace”….
“A wani dalili kamar wanda yake tsoranta?”….
“Saboda kana sonta kuma…”…
Dakatar dashi deen yayi da fadin;
“Sudais ba abinda na kiraka ka fadamin ba kenan, solution nake nema na inda zan ganta, sudais idan aka kwana banga zahrah ba zuciyata zata iya tabuwa saboda ni kadai nasan irin mugayen sake saken da nakeyi araina”..
“Dole kayi kam yarinya gata nan masha Allah, ga zamanin nan da muke ciki na yan iska, da anga mace me kyau da sura shikenan ta zama nama”…
Cikin tashin hankali deen ya sake dakatar dashi da fadin;
“Na shiga uku ka kara dagamin hankali sudais, wallahi sai na nemota ko ina tashiga a daren nan, ko hannunta wani ya rike sai na yanke hannun meshi wallahi”….
Dariya kasa kasa sudais yayi yanda deen baze jiba yace;
“Kwantar da hankalinka babu abinda ze faru da ita Insha Allah, yanzu ina da ina ka nemeta”….
Bayanin duka guraren da yaje ya masa beyi skipping ko guri daya ba, sai da sudais ya gama sauraronsa sannan yace;
“Gidansu saurayinta fa? Ko kana ganin bazata iya zuwa ba”…..
Buga steering din dake gabansa yayi yace;
“Shit!!! How comes na manta da nan, yaron da suka taba guduwa tare, kai suna tare ma wallahi, thank you sudais, bye”…
Kashe wayar yayi sannan ya figi motarsa sai gidansu khaleel!!!…

Mata 25 da ke takarar gwamna a Najeriya

 

Back to top button