Daddyn Jalal ne a tsaye da yana rataye da ‘yar karamar Jaka, da alamu zeyi tafiya ne, Mummy na kan three seater ta kalmashe kafa tana danna remote. Daddy yace
“wai dagaske deeja bazaki bikin nan ba?”
Ya tsina fuska tayi tace
“Nifa bana son yin doguwar tafiya inba a jirgi ba kasani, kuma me zanje inyi musu, banda jaraba ayi biki a inda suke sun kwasa sun tafi wata uwa bauchi biki, ko meye amfanin hakan oho?”
Daddy ya samu guri ya zauna yace
“deeja, in duniya da gaskiya be kamata kiyi haka ba, duk gudunmuwar da Jawwad ya bawa Rayuwar danki, ga tsawon lokacin da kika dauka kuna makotaka, ga harkar kasuwanci da kikeyi da mahifiyar yaron nan, sannan koba komai kema Mahmud danki ne, shima kodan shi bazaki ba? “
“daddy a dawo lafiya, ka musu Allah ya sanya Alkhairi in sun dawo na musu Allah ya sanya Alkhairi, bani da lafiya bazan iya zuwa ba, ka tabattar sakona ya isa gurin Jawwad”
Ta juya ta cigaba da danna remote, haka ya mike ya fice daga palourn tabi bayansa da harara.
Ya fita ba dadewa sega Ilham ta fito daga dakinta, tazo ta samu guri kusa da Mummy ta zauna. Ji tayi Mummy tana tsaki ta dan kalleta tace
“Mummy lafiya kuwa?”
“barni da abun haushi, daddy ze batamin rai, wai se in bishi bauchi gurin bikin nan, ta yaya zanje gurin da Salma zata, ana Auren danta inje, ai na gama zubewa, ba dan ita ba da kodan Jawwad senaje bikin nan, Amma saboda Salma da wannan banzar yarinyar bazani gurin nan ba, Amma bayan biki har can Abujan zanje gidan Jawwad in masa Allah ya sanya Alkhairi, yanzuma na bawa Daddy sako ya bashi, Amma ai naga ke kawar Nana ce, meyasa baki bisu ba? “
Ya mutsa fuska Ilham tayi tace
“Tabdijan akan me zanje, Ai daga baya na gane da hadin bakin ta Wannan banzar take son janye hankalin Yaya Jalal daga kaina, dan haka ba abunda zanje in musu, suje can su karata”
Haka suka cigaba da hirarsu, Ilham na kara kushe Jalila a gurin Mummy.
Jalila Tana fitowa daga hall din ta samu jikin wata mota ta tsaya tana waya, Ahmad ya kirata, tasa wayar a kunnenta tace
“Hello my, ina jinka” ba”a iya jin me ake cewa amma tace “Shikenan in an nagama zan maka magana se mutafi tare” ta dan kumayin shiru tace “A’a idan na koma gida zanci Abinci, bazan iya cin Abinci yanzu ba, in aka tashi zan maka magana”
Ta kashe wayar, tana juyowa taji gabanta ya fadi, Jalal ne a tsaya a bayan ta, ya kura mata ido ko kyaftawa ba yayi
Dan tsayawa tayi itama tana kallonsa, tunda yazo ko sannu bata hadasu ba, ba karamin kyau manyan kaya sukeyi masa ba, gashi gaba daya ya cika gurin da kamshin turarensa, tayi kokarin bin ta gefensa ta wuce, ya kara tare mata hanya, dagowa tayi tana kallonsa ya hade rai kamar be san meye dariya ba yace
” Zoki wuce mu tafi”
Tai masa kallon ban gane nufinka ba tace “Kamar ya, mu tafi ina?”
“ban sani ba, ki wuce mu tafi nace” yayi maganar cikin fushi”
Zumbura baki tayi, tace
“Wallahi ba inda zani ba’a gama ba” yasan halinta da taurin kai, dan haka yasa hannu ya janyo ta har tana kokarin faduwa saboda takalmin ta me tsinine, ba shiri tabi shi be tsaya da ita ko’ina ba se gaban motarsa, ya bude motar yace
“Shiga”
ta kalleshi, cikin muryarta me sigar shagwaba tace
“meyasa zan shiga? Ina zaka kaini kowa yana can ana abun Arziki”
“Wallahi in baki shiga ba zan sakaki da kaina”
Zare ido tayi ta kalli idonsa, babu alamun wasa a abunda ya fada tabbas ze aikata, ba shiri ta shiga motar, ya za gaya ya shiga ya kunna motar, yafara tuki cikin nutsuwa ya bar harabar gurin, yafara tukin kenan aka kirashi a waya, ya daga wayar yasa a hands free, da’alama abunda ya shafi aikin suke tattaunawa shida wanda ya kira shin, dukda zuciyarta a kule take da haushi, Amma bayan ya gama wayar tace
“Ya Aikin kuwa?”
Kamar jira yake tayi magana yace
“ban sani ba, bakida kunya, saboda ke na tafi aikin nan for almost four months baki nemeni ba, Rayuwa ta kaman wanda yake cikin rijiya ne yake neman taimako, kin mikomin abu ina kokarin fitowa kin saki nakoma ruwa, dan kinga ina lallabaki kikemin wulakanci ko? “
” ni wani wulakancin nayi maka? Mekake so in maka kuma? In cigaba da bibiyar ka mahaifiyarka tana min kallon mazinaciya? Da kazo garin nan kana kallona shekaran jiya, har kusa faduwa nayi saboda dalilinka, ko kallona bakayi ba, so kake inta binka, kokuma goyaka zanyi? Ni kawai ana can ana Ta shagali nikuma ka dakko ni, duk gurin nan nika dai na tsole maka ido, ga Ahmad ma yama jirana, yanzu se yayi ta jirana, idan ya tarar bana nan bazeji dadi ba”
ya lura gaba daya a fusace take, yai mata shiru taita mita, yadda Jalila ke kuma fadar Ahmad yafi komai bata masa rai, dan haka yaja wani uban birki a kan titi da seda ta firgita, ya juyo yana kallon ta, ya matso da fuskarsa daf da tata, har suna jin numfashin juna, Jalila najin saukar numfashinsa a fuskarta, gaba daya Jikin Jalila ya hau rawa, taji numfashinta na kokarin tsayawa, gaba daya kamshin turarensa ya cika mata hanci, ga kuma wani mugun kwarjini da yayi mata, cigaba da matso da fuskarsa yake daidai tata, har dogon hancinsa na shirin taba nata, rintse ido tayi sosai jikinta na cigaba da rawa.
A hankali ya dauke fuskarsa, yace mata
“stop shivering, kina tunanin wani abun zan miki? Ba abunda zan miki, sedai ina kokarin nuna miki illar shigar da kikayi ne, look at yourself,”
Jin abunda ya fada, Yasa A hankali ta bude idonta tana cigaba da sauke numfashi.
Ya kuma kallon ta yace
“kalli jikinki babu mayafi, kin hau stage kina Rawa, kowa ya zubo miki ido kina rawa, kalli jikinki, kalli yadda kayan nan suka matse ki, hakan ya dace? “
Kallon kanta tayi, taga yadda rigar ta zauna a jikinta, taga irin yadda Jalal yasata a gaba da kallo, gaba daya seta ji kunya ta kamata, Amma ta maze ta dake, takuma hade rai tareda dauke kanta tace
“Ai dai bahaka na keyi ba, dan dai yau daya, ana biki zaka wani takuramin, naga kai da gajeren wando kake yawo a layi, waye ya dameka?”
Jalala seyayi kamar besan dashi take ba, ya fuskanci rigima takeji, idan ya biye mata fada za suyi a titi, banzan da yayi da ita, hakan ba karamin batawa Jalila rai yayi ba, wayarta ta fara ringing, tasa hannu ta ciro wayar daga jakarta, ta daga wayar tasa a kunnenta, beji me aka ce ba, sedai Jalila cikin shagwaba tace
“please my, na dan fitane yanzun zan dawo Insha Allah, ka jirani semu tafi tare”
Cigaba da wayarta tayi hankali kwance, ta gama tana kokarin ajiye wayar, Jalal yasa hannu ya fizge wayar daga hannunta yace
“Wallahi bazaki koma gurin nan ba”
“Saboda me? Ni gaskiya ka maida ni, wai meye haka?”
“Wallahi kika kuma yi min gaddama, Kano zamu nufa a daren nan, daga nan zuwa a Asuba ma isa kanon, babu abunda yayi min zafi da wani zargi ko wani abu daza’a ce akan hakan, kinsan ni bana gudun magana”
A firgice ta kalleshi, babu alamun wasa a idonsa, he mean what he said, yadda fuskarsa take murtuk din nan, ta tabattar ze aikata abunda yace dan haka taja bakinta tayi tsit, tana kallon wayarta tanata ringing, Amma Jalal ya share, ga shi tana tsoron abunda ya fada, dan ze aikata.
Tanaji tana gani ya maida ita gida, yayinda ana can ana rakashewa, gaskiya Jalal ya kwafsa mata, suna zuwa harabar gidan taga motar daddy, da sauri tace “laa motar daddy yazo”
Nan ma shiru Jalal yayi mata, yana parking ta bude motar ta fice, cikin Sauri ta nufi wata kofa, da ya kasance bangarene da Daddyn Hanan yake saukar manyan baki idan suzo, kamar yadda aka nuna mata.
Tana zuwa ta bude kofar ta shiga da sallama, Daddyn Jalal ne, da Daddyn Hanan sekuma Abba, da wani babban mutum wanda Hanan tace mata baban Yaya Yusuf ne, suka amsa mata cikin sakin fuska.
Tana zuwa ta zauna a gefen Abba, ta kalli daddyn Jalal tace “Daddy sannu da zuwa ya hanya?”
“lafiya kalau Jalila ya taro?”
“lafiya kalau Daddy”
“to Masha Allah, Allah yasanya Alkhairi, Allah ya kaimu naki da rai da lafiya”
Suka amsa da Ameen amma banda Jalila da ta sunkuyar da kai.
Daddyn Hanan yace ” ‘yar baba, keko ganinki bana yi tunda aka fara bikin nan, ina kika shiga haka?”
“Baba ayyuka ne dayawa, kuma naga baka dawowa se dare”
“Hakane kam, sannun da aiki, Allah ya kaimu naki auren ‘ yar Baba”
Abba yace
“Baby ya akayi kika dawo ke? Naji ance kuna gurin walima, ina Kika baro Amaren?”
“Suna can ba’ a tashi ba, ba Yaya Jalal ne… Bata karasa ba Jalal ya turo kofar dakin ya shigo da sallama”
Shikan sa daddyn sa rabon da ya ganshi wata hudun kenan, ya sha manyan kaya yayi kyau, babban abunda ya daurewa daddyn sa kai be wuce yadda yayi sallama ba kuma ya risina yana gaishesu, suka amsa
Daddyn Hanan yace “ABDUL JALAL ashe kazo, Amma ban ganka ba, bamu hadu ba sam”
Jalal yayi murmushi yace “banfiye fitowa ba shiyasa baka ganni ba”
“Masha Allah, Yaya gurin Aikin na ka?
” Lafiya kalau, ina jin dadin Aikin, Amma nafison zama na a kano, gashi sunce sena kara watanni, bana son zaman lagos din nan”
Daddyn Hanan yace “Nayi farinciki ganinka ABDUL, kayi kalau da kai, me yasa baka son zaman lagos din?”
Daddyn sa yayi murmushi yace “baya son sabga da Mata, kasan kuma lagos babu ruwansu da Addini ko Al’ada, in munyi waya yana gayamin ;shi baya son Abunda matan kabilun nan sukeyi” suka kwashe da dariya, Abba yace “Karka damu Kaji Jalal, kana da gaskiya”
Daddyn Hanan ya kalli baban Yusuf yace
“Kaga yaron dana ce ka samarwa Aiki, Ansamu improvement kwarai a tattare da shi, gaskiya ‘yar Baba tana da kai sosai, ita tayi wannan tunanin a samo masa aiki, tace min in aka samo masa aikinyi hakan ze dauke masa hankali da ga barna da yake kuma ya rage masa damuwa da kadaici, a haka gata kaman bata iya komai ba se shagwaba da tsokana amma tafi Hanan kai”
Baban Yusuf yace “ABDUL JALAL karka damu kaji, haka sha’ anin Aiki yake, ba inda baya kai mutum, kai dai kayi gaskiya ka rike Addininka kuma kaji tsoron Allah”
Sukace hakane, daddyn Hanan yace
“Karka damu Jalal, za’a san abunyi, babban farincikin danayi, daga can lagos din sun kirani suna yaba maka, naji dadi sosai wallahi, Abunda yake kara shashi shaye2 da wannan phobia din na rashin son mutane, hadda psychological issues, yana bukatar me jansa a jiki, be kamata saboda halin da yake ciki na shaye2 ayi watsi da shi da lamarin sa ba, kokuma a dinga yi masa mummunan furuci ba, ko mutane su kyamace shi gaba daya ba, kuma wannan yana daya daga cikin matsalar society dinmu, wallahi wanima ko masallaci yaje baza’a hada sahun salla da shi ba, daga haka suke fara janye jikinsu daga mutanen kirki, se na banza su janye su, maimakon a jasu a jiki da nasiha da rarrashi”
Daddyn Jalal ya dan girgiza kai yace
“Wallahi you said it all sir, Jalal gaba daya gudun mutane yake se tsirari, musamman mata, saboda yarasa wani babban jigo a rayuwarsa da duk wanda yarasa dole yayi kuka, shiyasa da Wannan ‘yar tawa Jalila da Jawwad banida abunda zan biya su da shi, ko iya haka aka tsaya sun kawo gagarumin sauyi ga rayuwar ďana, bani da bakin godiya, ban taba tsammanin za’ a samu sauyi kwatankwacin haka akansa ba”
ya karasa maganar yana kokarin hadiye kwalla da ta taru a idonsa, gaba daya sukayi tsit cike da tausayin Jalal da mahifinsa, Jalal ya sunkuyar da kai, yana tuna Abubuwan da suka shude na rayuwarsa, Ya fuskanci kaddara daban2, gaba daya tausayin kansa dana daddy ya lullube shi.
Jalila kam cikin sanyi jiki, tace
“Haba Daddy, ni me nayiwa rayuwarsa dana cancanci wannan godiyar da kuke tayimin, wallahi banga abunda nayi masa dana cancanci hakaba, ni yakamata in baku hakurin cin zarafin sa dana dingayi a gabanku, nake kiransa da kalamai marasa dadi Amma….
Sekuma maganar ta kasa fitowa saboda kuka, dan Haka ta mike, da sauri tabar dakin.
Shikam baban Yusuf mamaki ne ya cika shi, ace kamar wannan yarinyar ta sauya akalar Rayuwar matashi da ya riga ya dilmiya a gurbatacciyar rayuwa, itakuwa wace irin baiwa ce da ita, ko dayake ance mata ‘yan baiwa ne, sedai kowacce akwai sigar da take Amfani da tata.
Jalal yace “daddy seda safenku, zanje in kwanta”
Abba yayi karfin halin cewa “to shikenan Allah ya tashemu lafiya”
Ya amsa da “Ameen” ya mike ya fito kaman wanda kwai ya fashewa a ciki.
Jalila takoma part dinsu ta canza kaya, tayi wanka, har tayi ta fito tausayin Jalal da daddy ne fal a ranta, se goge Hawaye take lokaci zuwa lokaci.
su Hanan suka dawo, suna zuwa suka tarar har tayi bacci.
Nana tasa hannu tasheta, Jalila ta mike zaune tana kallonsu tace “meye kuma na tashi na?”
Nana tace
“ya akayi kika taho ne? Tun a can Maama take nemanki, Ahmad se kiranki yake a waya baki daga ba”
Se yanzu ta tuna wayar tana gurin Jalal.
“Su Abba ne sukazo shiyasa na dawo gida” ta basu amsa
Hanan tace “keda wa kuka dawo, dan nasan baki san hanya ba”
“ban sani ba, uwar kwakwakwafi a isak na dawo”
Hanan tace “daga tambaya? Allah yabaki hakuri”
Siyama tace “Jalila wallahi Jalal ya hadu, kinata masa wulakanci, wani kallo da yake miki kamar ze cinye ki”
Sukasa Jalila a gaba da tsokana tayi musu banza ta kyalesu.
Jalal yana zaune yana ta tunanin abubuwan da suka faru dashi a baya, shi kansa yana sarawa namijin kokarin Jalila, ta iya lissafi gata da himma da kokari, duk rashin kunyarta da taurin kai, akwai kawaici da tausayi, duk zamansa da Jeje besan Cutar shi yake ba, Amma ita a ranar da suka fara haduwa ta gane hakan, ta saka rayuwarta a hatsari da dama saboda shi, besan mezeyi ya saka mata ba” kallon wayarta data ke faman ringing yayi, sunan My yana yawo akan screen din wayar, har wayar ta gaji ta katse, hotonta ne akan screen lock dinta tana murmushi, ya kurawa hoton idon na dan lokaci, ya sa hannu ya shara screen din, wayar ta babu key a kai, wallpaper dinma hotonta ne da Nana, kanta babu dan kwali, ta dan turo baki Nana kuma tana dariya, ya dade yana kallon wallpaper, yayinda kiran Ahmad ya shigo ba’a dadi, ya gaji sa wayar a silent ya ajiyeta ya cigaba da tunani,
Yana cikin tunanin ne, Angwaye suka dawo.
Jawwad beyi mamakin ganin Jalal a gida ba, dan ba karamin aikinsa ne gurin dinner din ma yaki zuwa gaba daya ba.
Gaba daya Ahmad ransa a bace yake yana ta tunanin ina Jalila ta shiga haka? Ya kira har ya gaji amma bata dagawa, kuma ya duba hall din nan be ganta ba, sukayo wa Angwaye rakiya yana shirin fita daga dakin yace
“Jawwad zan tafi seda safe, Dan Allah ko Jalila ta dawo ne ? Nakirata har nagaji bata dagawa”
Jawwad yace
“Aini tunda ta sauka akan stage din nan ban kuma ganinta ba, Amma ka kira wayarta mana”
“Aina kira wayarta ta bata dagawa”
Jawwad yace
“Idan ma ta dawo yanzu nasan tayi bacci, Amma bari in kira wayar ta ta”
Jalal yana jinsu amma be tanka musu ba, Jawwad na kiran wayar Jalila yaji ringing dinta a dakin, da yake yasan tone din wayarta, Jawwad ya kalli inda ringing din wayar ke tashi, tana kan teburin dake gaban Jalal tareda wayoyinsa,
Jawwad ya tafi gaban tebur din, yaga tabbas wayar Jalila ce, Jawwad ya kai hannu ze dau wayar, yace “ya akayi kuma wayarta tazo nan?”
Jalal ya sa hannu ya dauke wayar ya kashe wayar gaba daya yace
“wayar tana gurina, tare muka taho”
A fusace Ahmad yace
“Amma dan wulakanci kanaji ana maganar kayi banza? Meyasa zaka dakko ta? Na lura tunda kazo kake wani jin kai da nunawa mutane gadara, ubanwa kafi? Zaka dinga nunawa mutane jin kai, meye naka na shiga sabgarta? Waye dinta kai? Dama ana fadin kana shaye2 wallahi kamin hauka kurata zansa sumaka duka”
Jawwad da sauri yace
“yi hakuri Ahmad, baka fahimci Jalal bane, shima yayanta ne yana da iko akanta, Bekamata ka dinga wannan maganganun ba, an riga an zama daya”
Zuciyar Jalal wata irin tafasa take, ba dan Dalilin Jawwad ba wannan banzan ya isa ya tsaya gabansa yana zaginsa, dan takamarsa yanada kaki, idan takamar Ahmad kakin soja, shikuma yana da abunda ze siye shi da kakin nasa yasa Aljihunsa
Kawai Jalal ya jingina da kujera ya zaro karan sigarinsa ya kunna yana kada kafa.
Karshen kuluwa Ahmad yayi, wai uban me Jalal ya taka yake wannan gadarar.
Abdallah ne ya shigo dakin da sauri yana fadin “Jawwad ana nemanku a part din daddy, kaida Ahmad”
Jawwad yace “Allah yasa ba wani abun mukayi ba?”
“ba abunda kukayi ance dai in kiraku”
Jawwad yace “Amma a daren nan haka?
” kuzo dai muje, ko menene kwaji a can”
Seda Ahmad yayiwa Jalal wani banzan kallo, yayinda shikuma Jalal yakara yawan hayakin da yake fesarwa a iska, yana lumshe ido Ahmad ji yake da da bindiga se ya harbe Jalal, haka suka fita suka tafi.
Su Jalila kam, babu alamar zasu kwanta yanzu, hira kawai suke suna shewa, Maama ta shigo dakin tace “har yanzu baku kwanta ba?”
Hanan tace
“Wallahi Maama, mun kasa baccin ne, shiyasa muke ta hira”
Maama tace
“lallai kam, ke Nana magana fa ta canza, da mun zata nan da sati biyu zaki tafi, Hajiya Salma tace; dake zasu tafi maiduguri, visar ki ta samu, in aka daura Aure gobe in Allah ya kaimu ranar Asabar zaku tafi maiduguri, litinin zaku tafi can England keda Mahmud, dan haka za’a kawo miki kayanki da zaki tafi dasu, bayan kun tafi”
Take jikin Nana ya hau rawa, cikin rawar murya tace
“Maama litinin fa, yayi kusa da yawa”
Jalila tace “dan Allah Maama a barmin ita se nan da sati daya”
Gaba daya suka fashe da kuka daga Nana har Jalila, Maama taga bazata iya zaman rarrashi ba ta tafi ta kyalesu, Ai Jalila har tafi Nana shiga damuwa, Hanan da Anty fiddo ba yadda basuyi ba amma suka ki yin shiru musamman Jalila, kwana tayi tana kuka, bata taba tunanin zataji haka ba in Nana ta tashi Aure,
Kamar wasa har wayewar gari ranar daurin Aure kuka take, hakan ya saukar mata da ciwon kai da zazzabi me zafi.
Hajiya Salma ta samu labarin halin da Jalila ke ciki, tazo ta dinga rarrashin Jalila, aka nemo likita yabata magunguna, aka samu tayi wanka.
Daddyn Hanan yace akai Jalila bangaren sa ta samu ta huta saboda hayaniya.
Haka kuwa akayi, wunin ranar bata fito ba daga bacci se salla, ta sha kuka shikenan Yaya Jawwad ya tafi da Hanan lagos, Nana ta tafi England, shikenan se ita kadai.
Har aka gama wunin ranar tana kwance saboda zazzabi ga ciwon kai, ita kanta Nana wunin ranar da kuka ta yi shi, se bayan magariba, Mummyn Hanan ta shigo dakin da Jalila take dauke da Akwatin Jalila tace “Jalila maza tashi ki wanke fuskarki, ki sa hijjabinki ki biyoni ana san ganinki”
Jalila tace “Nikuma? Amma me za’ayi da trolley dina anan”
“in munje zakiji, tashi maza” jiki a sanyaye ta mike ta saka hijjabi, har yanzu kanta ciwo yake, dukda zazzabin ya sauka.
Tabi bayan Maama har wani katafaren parlour da yake wani bangare na gidan, suna shiga taga Angwayen nan gaba daya da Amare, sekuma iyayensu maza. Jalal na gefen Jawwad a zaune.
Ta samu guri kusa da Mummyn Hanan ta kwanta a jikin Maama saboda dikinta ba kwari. Sukai tai mata sannu.
Da alamu an dade ana tattaunawa ita kadai ake jira, Maama ta rage murya ta radawa Jalila Daddyn Jalal ya gabatar da kyautar da Mummy ta bayar abawa Jawwad, kyautar gida a Kano, sannan ita ta bayar da sadakin da’aka biyawa Jawwad naira dubu dari.
Jalila tayi mamakin hakan kwarai
Kowacce aka mika mata sadakinta a hannunta, akayi musu nasiha da fada sosai tareda Addu’oi, aka sallami su Hanan, da Nana, Siyama bayan daurin Aure suka koma Kaduna, daddy yace Jalila ta tsaya, Jalal ma yana zaune a gurin.
Abba ya mikowa Jalila bandir din kudi, Mummyn Hanan ta mika mata, ta sa hannu ta karba cike da mamaki
“Abba wannan na menene?” ta tambayeshi tana juya kudin
“Sadakin ki ne” a tsorace ta zare ido ta kalli kudin
“Sadakina kuma? Waye mijin?” ta fada a firgice
Daddyn Hanan yace
“kwantar da hankalinki gashi nan a gefenki ABDUL JALAL ne ba wani ba!!!!
Ai a zabure ta zubar da kudin ta ja da baya tana kallon Jalal da ya sunkuyar da kai tana zazzare ido.
Jalal ya dago yana kallon Jalila, cikin kuka Jalila tace
“Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Abba me yasa? Laifin me nayi a kayimin haka?”
Abba yace
“kwantar da hankalinki, nasan bazaki watsa min kasa a ido ba, ba laifin da kikayi, ganin da cewar hakan mukayi shiyasa muka yanke wannan hukuncin”
Girgiza kai ta shiga yi tana kuka, daddyn Hanan yace
“Calm down my daughter, kinga bakida lafiya, meye abun damuwa? Jalal ne kin sanshi ba wani aka Aura miki wanda baki sani ba, bakomai kiyi hakuri, Allah yabaku zaman lafiya, Kuma nasan kina sonshi ai ko?”
Girgiza kai tayi da sauri tace
“Ni wallahi bana sonshi, Allah bana sonshi haba daddy, duk ‘yan uwana ba wanda akayiwa haka seni, daddy Why? Wallahi ni ba son Jalal nake ba tausayin sa kawai nakeji”
Abba yace
“ba cinya ba kafar baya”
Daddy yace
“to wa kike so”?
“Ni Ahmad nakeso” ta fada kanta tsaye tana kuka.
Jalal yasan za’ a rina, yasan setayi daru, Amma be taba zaton Jalila zata iya furta bata sonsa ba agabansa haka”
Mummy tace
“Ke rufewa mutane baki, kaunar da’ake miki yasa aka zaba miki Jalal din, in kun zauna zakiji son, kar in kara jin wannan maganar a bakinki, Ahmad yana da mata, ko yanzu yaga dama ze iya neman wadda yakeso a bashi, kamar yadda kikace tausayin Jalal kike, to kiyi hakuri kicigaba da tausayin sa”
Maama kanta jikinta yayi sanyi, seda ta bada shawarar a ji ta bakin Jalila kafin a yanke wannan hukuncin amma basu bi shawarar ta ba.
Jalila ta mike da sauri ta fice daga palourn tana kuka.
Baban Hanan yace
“Jalal sekayi hakuri, kasan yarinya ce karama, kuma an shammace ta, ba zato ba tsammani aka daura mata Aure, kuma tana ganin duk ‘yan uwanta su suka kawo wanda suke so, kayi hakuri da abubuwan dazata yi maka ze wuce kamar ba’ayi ba, gata nan Amana ka rike ta da amana”
Sallamar Hajiya Salma, da kannen Mahifin Jalal, da shi kansa daddyn Jalal, ya katse wa Daddyn Hanan maganar da yakeyi, suka amsa musu sallamar.
Suka karaso suka zauna, daddy yafara magana
“Dukkan yabo da godiya da jinjina da kirari sun tabatta ga ubangiji ma daukakin sarki, me kowa komai, Alhamdilillah anyi taro lafiya an gama lafiya, muna fatan Allah yasa anyi kenan, Allah yabasu zaman lafiya, sannan Alhaji Usman, bazan gaza gurin kuma nuna godiya ga dawainiyar da iyalanka suka dingayi da ďana ba har kawo wannan lokacin da kukayi masa ko ince kuka yimana wannan karamcin, iyalanka sun Rungumeshi lokacin da mutane kowa ke gudun sa, Mungode mungode Allah yasaka da alkhairi, Allah yabiya ku da gidan Aljannah ya jikan magabata, Kuma Insha Allah bazamu baku kunya ba”
Abba yace
“Masha Allah, Alhaji Habib duk abunda nayiwa Jalal tamkar Jawwad nayi wa ne, ABDUL JALAL tun tasowarsu da Jawwad yake kaunar sa, kusan kaso mafi yawa na Rayuwarsa a gidana yayi ta, dan haka yiwa kaine Allah yabasu zaman lafiya”
Itama Hajiya Salma godiya takuma yi da nuna farincikinta akan wannan lamarin.
Jalila kam tana zuwa ta zube a jikin Hanan tana wani irin kuka me sauti, Hanan ta kalli Nana suka hada ido ta dan jinjina kai, sannan tace
“Wai Jalila lafiya kuwa? Meyafaru ne haka?”
Jalila ta dago idonta da tuni yayi Ja tace
“Hanan wai an daura min Aure nima”
Nana tace
“Aure, dawa aka daura?”
“Nana wai Jalal aka auramin, meyasa a kayimin haka? Takuma fashewa da kuka
Hanan tace
” kece baki sani ba, mu mun riga munsan za’a daura muku Aure”
Zumbur Jalila ta tashi zaune ta kalli Hanan
“Amma meyasa baku gayamin ba?”
“Saboda ana gudun wannan shirmen dazaki yi, aka gargade mu karmu sake mu gaya miki, kuma ni banga aibun abunda akayi ba, hakan shine dai2”
“Haba Hanan meyasa zakimin haka? Ko dan na tsaya tsayin daka kin samu wanda kikeso, shine ni zakimin haka?”
“Jalila abunda ya dace akayi, nasan abunda akayi miki babu dadi, Amma iyaye basa zabawa yaransu abunda ze cutar dasu, wallahi Jalila sekin fi kowa Alfahari da shi nan gaba, Yana sonki, kuma kema kina sonshi, sann……
” Dan Allah dakata Hanan “
Jalila ta katseta
” dan bake akayiwa ba ko? Ina da wanda nakeso amma an Auramin wani daban, shine ya gaya miki yana sona, babu wani abu makamancin soyayya a tsakanin mu, ta yaya zan fara rayuwar Aure da Jalal, bahagon mutum me wani irin murdaden hali,
Mahaifiyarsa bata kauna ta, ko kinsam tana zargina da ďanta, Mahaifiyarsa tana da wanda takeso ya Aura, ta yaya zanyi zaman Aure da wanda mahaifiyarsa bata sona, Hanan nasha wahalar Rayuwa, yakamata ace lokaci yayi da zan huta, wannnan Auren tamkar kara jefa Rayuwa ta cikin wata wahalar ne, nasha wuya Ina bukatar zuciyata ta huta Nashiga uku ni Jalila “
” Subhanallah ke Jalila meye hakane kikeyi? “
Muryar Mummyn Hanan ce take magana, da suka shigo ita da Maama, tace
“duk Nasihar da’akayi miki baki jiba kenan? Meyasa bazaki dauki kaddara ba, ko ba’ayi haka ba dama Allah ya rubuta shine mijinki”
Kuka Jalila takuna fashewa da shi maama tace
“Jalila kidena kukan nan haka, batun mahaifiyarsa bata sonki ze wuce, musamman idan ta gane mahinmancin ki ga danta, Jalila tunda kika iya jure rayuwar gidana duk taren kalubalen da kika fuskanta daga gareni da ‘yan uwana, bana tunanin akwai wani kalubale daze tsoratar dake, Anmiki ba dai2 ba tabbas, Amma kiyi hakuri ki rungumi kaddara ki riki mijinki, ki masa biyayya, idan kikayi hakuri kikayi biyayya se Allah yayi miki Rahama saboda hakan”
Mummy tace
“wannan gaskiyane, kuma shi Ahmad da kike magana, ai Daddy ne yace ya bashi da farko, yanzu kuma ya bashi hakuri, Jalila na tabattar nan gaba sekin fi kowa jin dadin zama da shi”
Jalila sam bataji nasiharsu na shigarta ba, ita kawai an gama da ita basu san waye Jalal bane shiyasa suke fadar hakan.
Maama tace
“Nana ki shirya kayanku, gobe in Allah ya kaimu hadda ita zaku tafi maiduguri”
Jalila na jin haka ta kuma rusheewa da kuka.
Yusuf ne ya shigo dakin shima a fusace yana fada
“haba Mummy, meyasa daddy zeyi haka dan Allah? Yaza’ayi a Aurawa yarinya wanda bata so, kuma bayan yasan ďan shaye2 ne, a family din nan ba wanda aka taba yiwa Auren dole meyasa za’a fara akanta?ga shi sam wannan yaron bashi da mutuci, ga gadara da girman kai”
Mummy tace
“Sannu jagoran marasa kunya, meyasa bakayiwa daddyn ba seni? Kafi su sanin abunda yakamata ne?”
Hanan Kallon yaya Yusuf kawai take yadda yake zakewa yana masifa
Jawwad nai yai sallama a dakin shima fuskarsa dauke da damuwa, ya hango Jalila ta takure a gefe idon nan kaman gaita saboda ja, ga fuskarta duk ta kumbura. Bebi takansu Maama ba gaje gabanta ya tsuguna yace
“Baby why? Meyasa kike kuka haka? Gashi baki da lafiya? “
“ba dole yarinya tayi kuka ba, an mata Auren dole, an Aura mata ďan shaye2 wanda bata so”
Jawwad yace
“Yusuf meye haka? Ana kokarin hankalin ta ya kwanta kana son ka kunna wata wutar, koma dai meye an riga an daura Auren nan, ayi musu Addu’a da fatan Alkhairi mana” Jawwad ya kalli Jalila yace
“We are sorry Baby, kaddara ta riga fata, dana san ba kya son Jalal bazan bari ayi Auren nan ba, saboda nasan Jalal baze ban kunya ba shiyasa na amince”
“Yaya Jawwad ni bana sonshi”
“Jalila kulawar da kike bashi da babu so bazaki yi ba, na miki Alkawarin Jalal baze bada kunya ba, kuma shi Alkhairi ne a rayuwarki, dan Allah Jalila ki kula da rayuwar Jalal kamar yadda kike yi abaya, Nabaki amanar ďan uwana please Jalila” ya karasa maganar kamar zeyi kuka.
Girgiza kai Jalila ta shiga yi
“Yaya Jawwad….
“Shhhh kiyi shiru, ki karbi Amana ta kidena wannan kukan”
Hanan tace
“Jalila son da Haidar yake miki baze bari a baki abunda ze cutar dake ba kiyi hakuri da kaddara Queen”
Jalila shiru ta musu ba tace komai ba, ita ka dai tasan me takeji a ranta.
Jawwad ya mike yace
“Mummy seda safenku” sukayi sallama.
Yusuf dai ya cigaba da banbami da mita.
Su Maama suka cigaba da rarrashin ta tareda Nasiha.
Hanan kuma ta shiga hadawa Jalila kayanta dukda tarin gajiyar biki dake tare da ita.
Jawwad yakoma masaukin Jalal, ya tarar Jalal yana shirin kwanciya, Jawwad yace
“Ango ka sha kamshi”
Jawwad ya lura kaman Jalal baya walwala
“Jalal Lafiya kuwa? Naga kaman baka walwala, ko baka son Auren”?
“Jawwad ba wai bana son Auren bane, idan inason Auren itafa?”
Jawwad ya dafa kafadarsa yace
“brother karka damu, nasan zataji babu dadi da farko, saboda an mata bazata ba tareda masaniyarta ba an daura mata Aure, Amma nasan tana sonka, kuma a hankali zaku daidaita cikin kankanin lokaci”
Jalal yace
“Hmm haka dai kake gani”
“Hakane ze kasance, ni dai gata nan Amana Jalal, kayi hakuri da ita”
Jalal bece komai ba ya danyi murmushi, daga nan suka shiga wata hirar.
Hatta Inna ba’a barta a baya ba gurin rarrashin Jalila da yi mata nasiha, dan ita Inna har cikin ranta Jalal yayi mata, dan seda ta zage Yusuf tsaf saboda masifar da yakeyi akan anyiwa Jalila auren dole.
Jalila dai yau tayi kwanan bakinciki, dan sam bacci ko na minti goma batayi ba, Ga Jalal ya kwace mata waya balle ta kira Ahmad, gaba daya tausayin Ahmad takeji, yasaka rai akan Aurenta, yana da matukar kirki ya nuna mata soyayya, shiko wannan Jalal din da magana se ya ga dama ta ina ze nuna mata wata soyayya. Har akayi kiran sallar Asubah batayi bacci ba se sakawa da kwancewa, bayan tayi salla ta koma ta kwanta tana jin yadda kanta ke sarawa, ga kirjinta da yayi mata nauyi, se karanto Addu’oi take daban2 ko zuciyarta tayi sanyi.
Wajejen karfe bakwai da rabi, Mummy tazo ta kira Jalila suka tafi cikin gida, dakin da’aka sauki hajiya Salma ta kaita, mutane sun ragu sosai duk an watse, se tsirarin mutane da zasu raka Hanan Abuja, sekuma ma’aikata da suke ta kokarin gyara gidan.
Bayan sun shiga Jalila kanta a sunkuye ta gaida Hajiya Salma da Antin Jalal, Suka Amsa mata Antyn Jalal tace
“Sannu Amaryar mu, Kin tashi lafiya?”
Take Jalila ta kuma jin wasu hawayen suna zubowa daga idon ta, Mummy tace
“Ikon Allah, har yanzu baki gaji da kukan nan ba?”
hajiya Salma tace
“haba Jalila, banyi zaton haka daga gareki ba, mun san an miki laifi amma kiyi hakuri, Jalila zakiyi Alfahari da mijinki, yana sonki fiye da yadda kike tunani, gaba daya hope dinmu yana gurin Allah kuma yana gurinki, dan Allah ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ki gode Allah, Jalal baya kule kulen mata, ke kadai ce macen dana san yana saurara, kiyi hakuri Jalila “
Cikin kuka Jalila tace
“Mummynsa fa bata sona, tace in rabu da shi, kuma ba irin maganganun da ban gayawa Ilham akan sa ba, na kirashi da sunaye marasa dadi, kuma kawai ace shi na aura”
Hajiya Salma tace
“to shine me? Mahaifiyarsa bata sonki ni ba’a gaya miki abunda tayi min ba, ita da Saudat, gidan mijina abun kaunata seda ta rabani da gidan hankalin ta ya kwanta, ko kin fison a ya auri Ilham din ne? Jalila kece zakisa zaman gidan Aurenki yayi dadi in kin so, ki manta da abunda ya riga ya wuce kinji yarinya ta, Allah ya Albarkaci rayuwar Aurenku, kije ki shirya anjima kadan zamu tafi”
“wai a maidugurin zanta zama? Makaranta fa?”
Antyn Jalal tace “A’a ba’acan zaki zauna ba, Se a inda yakeso zaku zauna, amma akwai dalilin zuwanki can ďin”
Jalila dai ba tace komai ba suka cigaba da rarrashin ta. Haka Maama tazo ta ja hannunta domin fara shirin tafiya.
Daddy ya samu Hajiya Salma a masaukinta, shar da ita bakace ita haifi Mahmud ba, sekace kaninta, har yanzu tana tare da Gayunta,
Daddy yace “To Salma kinga abun Allah ko ba zato ba tsammani danki ya samu matar Aure, kodayake na dade ina burin Jalal ya Auri yarinyar nan”
Hajiya Salma tace
“Hakane, yarinyar tana da nutsuwa da kirki, dangin yarinyar nan sun gama yimana komai, Amma daddy wai ya’akayi abun nan ya kasance”
“hmm ai shekaranjiya dana zo, yazo ya ganni muna tare da iyayen Jalila, shine suke tambayarsa ya aikinsa? yace bayason zaman lagos, nake ce musu yanayin sabanin Addini da al’adun mutanen garin ne yasa baya son zaman garin, bayan ya tafi ne, kawai Captain Abdurrasheed yace ; inyana da wadda yake so ai masa Aure ya tafi da matar can lagos, se nake ce musu bana tunanin yana da budurwa, saboda yace yasan babu me bashi ‘yarsa yana wannan halin, se captain Rasheed yace; indai yana son Jalila ya bashi ita, shine aka kira Jawwad da yaron daza’ a bawa ita da, aka tambayi Jawwad yana ganin in aka Aurawa Jalal ita ze zauna da ita? Jawwad yace “ai Jalal yana sonta, dan haka suka kira shi wancan yaron suka bashi hakuri, shikansa Jalal be saniba se jiya a gurin daurin Auren”
Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace
“Allah me yadda yaso, kaga Al’amarin ubangiji, ba zato babu tsammani my Son yasamu mace ta gari”
“Hakane amma yaushe zaku bashi ita? Naji kince da ita zaku tafi maiduguri”
Tai murmushi tace
“Daddy kenan, yadda aka daura aure a bagas ba tareda ya sha wata wahala ba, bazan bashi yarinyar nan a bagas ba, bazamu bashi ita ba se mun tabattar da irin Son da yake mata, dagaske yana sonta kokuwa? Zata zauna damu tasanmu, sannan muyi mata shiri irin namu na ‘yan barno”
Daddy yai murmushi yace “haba Salma, a takaice dai ta wani bangaren kuna son ku wahalar min da yarone kawai”
Tayi murmushi tace
“Zamu temake shi dai, yawwa sannan Jalila tana kukan matarka Khadija bata sonta har tana zarginta da Jalal, wannan karon bazan lamunci duk wani nau’i na rashin mutunci daga gareta ba, idan baka dau mataki akan wannan lamarin ba, Zeyi wuya mu bawa Jalal matarsa anan kusa, saboda nafi kowa sanin khadija nasan abunda zata iyayi, a wannan karon bazan bari ta cutar da ‘yar mutane ba kamar yadda ni tayimin ba”
Ta mike tsaye tace
“daddy bari inje in karasa shiryawa, da wuri zamu tafi”
Ta wuce cikin dakin, Daddy yabi bayanta da kallo, har yanzu Salma tana nan da gayunta da iya kwalliya, nan ya dinga tuna abubuwa da dama da suka wuce a baya.
Wanda zasu yiwa Hanan rakiya tuni sun shirya dan yiwa Hanan rakiya can gidan Jawwad dake babban birnin tarayya, Hanan tasha kuka, da kyar aka banbare Hanan daga jikin Mummyn ta, daddy yayi mata nasiha Sosai, suka hau motoci sukayi gaba.
Da kyar Maama ta takura Jalila ta ci Abinci aka bata magani, Karfe dayan rana Aka gama kintsa Jalila da Nana, suka fito domin tafiya, Jalila ko ganin gabanta batayi saboda kuka.
Tunda su Jalila suka fito Jalal ya sauke idonsa akanta ta rame sosai ga idanuwanta sunyi Jawur, gaba daya tausayinta ya kama shi, ko ya takeji a ranta oho? Sosai yake jin tausayinta a ransa.
Yadda Jalila da Nana suke kukane yasa jikin Maama yayi sanyi, shikenan Nana zata bar kasar se lokaci2 zata dinga ganinta, duk kiyayyar da tayiwa Jalila a baya, bata taba zaton zataji babu dadi haka ba, Zatayi missing din yarinya me kara da kawaici, ga Jawwad shima ze tafi, zasu bar mata gidan se ita kadai, yadda Jalila ta rirrike Maama tana kuka kamar mahaifiyarta yasa Maama ta kamu da matsananciyar kunyar muzgunawaa Jalila data dinga yi, ba tayi aune ba taji itama Hawaye na bin idonta ta kuma rungume Jalila a hankali tace “ki yafemin Jalila” . Jalila ta kankame Mama tana cigaba da kuka
Abba yace
“haba in kina kuka zaki karya musu gwiwa ne, kiyi hakuri, ki gode Allah da ya nuna miki Aurensu kuka rabu lafiya”
Antyn Jalal tace
“Ai dole tayi kuka, kowace uwa haka takeji a lokacin da take bankwana da ‘ya’ yanta, yaranta uku zasu tafi su batta lokaci daya, maman Hanan ma tana can ta nayi”
Daddy yace
“ya za’ayi se hakuri”
Haka aka sa su Jalila a mota, ana musu fatan Alkhairi.
Mota daya Jalila, Nana da hajiya Salma suka hau, kanin Mahmud ne ze jasu, sekuma tawagar Angwaye da sauran ‘yan uwansu dazasu biyo bayansu, Hajiya Salma tace Jalal ya biyosu a tasa motar, Jalila naji na gani suka ďaga suka nufi borno.
Tunda aka kira Ahmad aka bashi hakuri akam Aurensa yarasa ina zesa ransa yana matukar kaunar Jalila, sannan duk yadda zeyi yaga Jalila be samu damar yin hakan ba har suka tafi.
Yusuf kam ko sallama beyi musu ba saboda bacin ran abunda akayiwa Aminin nasa, haka kurum an hana mutumin kirki an bawa wannaan sakaran.
Daddy ma ya shirya kayansa tsaf, yayi musu Sallama ya koma kano, yayinda Abdallah ma da tawagar abokansa suka tafi yi masa rakiya kaduna kasancewar a can ze zauna.
Tuni Labari yafara karade unguwar su Nana cewar an ďaura Auren Jalal da Jalila, da yake Akwai wanda sukayiwa Maama kara sukaje mata biki ‘yan anguwarsu, Labari ya zaga unguwa inda wasu suke ganin an kwari Jalila da aka Aura mata wannan mara tarbiyar dan shaye2, bayan ita kamila ce, me kirki da faran faran ga kowa, Amma duk abun nan ba wanda yaje ya Tari Mummy ya gaya mata.
Bayan la’ asar Daddy ya je gida, da ya koma gida be gaya mata ba, seda yaci Abinci yayi wanka yai salla.
Suna zaune da Mummy tana ce masa “ya hanya? Ya kabaro su?
” lafiya kalau Alhamdilillah, Jawwad da iyayensa suna godiya “
Ya mike ya debo goro da alawowi dayawa ya zube a gabanta.
Ta kalleshi tace
“wannan kuma na menene? “
” Na Auren ďanki ne”
“ďana kuma? Wanne ďan nawa, daza’a abani wannan kayan haka?”
“Aike yaran naki ukune, ga Jawwad, ga Mahmud, ABDUL JALAL”
“Jawwad din dai, Mahmud ba ďana bane, sannan ba wanda ya isa yayiwa Jalal Aure ba da izinina ba, idan ma anyi ko ‘yar uban waye se an fasa shi, kodayake wace mace ce zata yadda ta Auri wannan ďan naka?”
Daddy yace “to shikenan tunda baki yarda ba”
Ya dau remote ya kunna tv abunsa. Ta shi tayi tabar masa palourn ta koma dakinta, tunani ta fara yi, tasan daddy da zolaya wani lokacin, Amma kamar in serious tone yayi maganar, tana cikin tunanin ne wayarta ta fara ringing, seda ta kusa tsinkewa hankalin Mummy ya kai kan wayar taje ta ďaga
“Salamu Alaikum”
Mummy tace “wa’alaikum salam, hajiya Rahama barka da yamma”
“yawwa Mummy ya gida ya taro?”
“taro kuma?”
“Au tambayata ma kikeyi? Baban su yacemin ;yaje ďaurin Auren ďan gidan Alhaji Usman a bauchi, ashe bayan na Mahmud har dana Jalal amma baki gaya mana ba, na miki magana ta what’s App bakiyi responding ba”
Ai Mummy bata jira me zata karasa cewa ba ta kashe wayar ta kunna data aikuwa messages suka dinga shigowa ana mata Allah ya sanya Alkhairi, wasu na mata mitar bata gayyacesu ba, jifa tayi da wayar kan gado ta nufi part din daddy
“dama dagaske kayiwa Jalal Aure ba da izinina ba? Akan me? Saboda me?”
“haba Deejah, kefa kikace Jalal ya isa Aure, to menen laifi a ciki dan namasa Auren? Kuma ma yana son matar da’aka Aura masan”
“Sekuma nace kayi masa Aure ban saniba, wane irin wulakanci ne wannan? Wallahi baku isa ba daga kai har munafukan da kuka hada kai aka masa Auren”
Sintiri tafara yi a dakin, wani irin gumi yana tsatstsafo mata ita Daddy ze yiwa haka?
A fusace Tace
“Tukuna ma ‘yar gidan ubanwa aka Aurawa masa ba tareda masaniyata ba? Kowace’ ya ce wannan ta tarowa kanta abunda bazata iya ba, dan sena ga bayan Auren nan Wallahi, sena murkusheshi, bazan taba bari Jalal ya zauna da matar da bani na zaba masa ba, dan babu yarinyar da zan yadda ta juya min ďa, nasan baya son Ilham shiyasa na dage ya Aureta, Amma yanzu Ace an min bazata an rusamin shirina baze yuwu ba wallahi “
” Shikenan deeja abunda kike gudu akan ďanki fa se ya faru, Sannan koma wacece zatazo har nan ta gaisheki seki ganta.
Da Sauri Mummy ta sha gaban Daddy tace
“Wallahi Habib seka gayamin dan me zaka yiwa Jalal Aure ba tareda nasani ba? Sannan kuma ‘yar ubanwa aka Aura masa? Wato kaje kun haďa kai da wannan munafukan’ yan uwan naka aka Aurawa ďana yarinya ban sani ba, to wallahi baze yuwu ba, ďa dai nawane nina haifi abuna, dan haka ba’a isa a yanke masa hukunci game da rayuwarsa ba tareda sani na ba”
“sekuma kiyi, naga yadda zaki raba Auren ai, indai Jalal ne gaki nan gashi, dai dai yake dake, Akan kira bashi da yarinyar nan zaki kuma lalata alakarki da shine kawai, dan nagaya miki yana sonta”
“karyane Wallahi, Jalal bashi da wata yarinya da yake so, Yarinyar dana zaba masa ita ze Aura”
Dama daddy yasan ze fuskanci wannan kalubalen daga matar tasa, dan haka ya ture ta daga gabansa yabar mata palourn.
Se magariba Su Jalila suka isa garin maiduguri, koda sukaje sun gaji sosai, musamman su Jalila, su da suka sha hidimar biki, basu huta ba akayo wannaan uwar tafiyar.
Gaba daya Jalila ji take jikinta kaman ba nata ba saboda gajiya, har suka je maiduguri kanta a kasa yake, se dai ta jimgina da jikin Nana, ko mota tayi bacci, in aka jima ta shige cikin mayafinta tayi kuka, har sukaje Jalila bata kula kowa ba seda taji an tsaya ance sufito.
Gidan da akayi parking din motar ne yayi awon gaba da tunanin ta, sekace ba a duniya ba, kallo daya zakayiwa gidan kasan mamallaka gidan sunyi hannun riga da talauci, ko da suka fito daga motar Se guďa akeyi, Jalal idonsa gaba daya yana kan Jalila da take a takure, Suka nufi cikin gidan, tun daga harabar gidan wani irin sassanyan kamshi ke tashi, har zuwa cikin gidan, cikin gidan da’a akwai mutane a gidan da sukazo domin karbar Amaren.
Cikin gidan ma kamshin da yake na musamman ne, fiye da na harabar gidan.
Aka basu ďaki, suka gabatar da sallolin da suke kansu, Sannan aka kawo musu Abinci, Jalila da Nana ne kawai a dakin dan haka Nana tace
“Jalila ki daure kici Abincin mana”
Girgiza kai Jalila tayi tace
“Na koshi, ke dai kici kawai, ni kaina kemin ciwo”
“to ko inyi musu magana a nemo miki magani?”
“A’a base kinyi hakan ba, A yanzu dai babu wani magani daze warkar min da wannan ciwon kan”
Suna cikin wannan mujadalar ne Anty ta shigo da tray din fruit a hannunta tace
“Jalila kuci Abincin mana, ga dangin baban Jalal can suna son ganinku kafin su tafi”
Nana tace
“Anty Jalila taki cin Abincin, wai kanta ke ciwo”
“Subhanallah har yanzu kan ke miki ciwo? To daure kici Abincin se a kira likita ya dubaki”
Da kyar Jalila ta cakali Abincin nan ta barshi.
Suka fito parlour inda dangin Daddy keson ganin Amare, se hausa suke suna hadawa da yarensu, sunga fuskar Nana yayinda Jalila ta dukunkune a mayafi taki bari su ganta, dare ya farayi sukayi musu nasiha da Addu’oi, tareda jadadda godiyarsu ga Jalila sannan suka watse a hankali.
Dakin da’aka bawa Su Jalila yana da kyau da matukar girma, suka koma suka canza kaya, Hajiya Salma da kanta ta kawowa Jalila magani ta sha, tana shan maganin ta nemi guri ta kwanta tayi lamoo akan gado, tana missing din wayarta, tun randa Jalal ya kwace be kuma bata ba, tana son tayi amfani da wayarta amma ya rike a gurinsa sekace shi ya saimata.
Nana na kwanciya Mahmud ya kirata a waya, Suka dinga hira suna soyewa, kaman ba gobe zasu tafi ba, suna ta soyayya gwanin sha’awa, Jalila ta tuna kowacce ta samu zabinta, ta auri wanda take so suna cikin farinciki amma banda ita, an haďa ta da wanda be damu da kansa ba ma balle wani, take taji wasu hawayen na zubo mata, ta tabatta Auren Jalal wani sabon shafi ne na kaddarar Rayuwarta.
Hanan kam gidanta yana da girma amma ba can ba, Amma ya tsaru anyi masa gini na zamani, dauke da wadataccen gini, an kashewa gidan kudi sosai, Sannan daddy ya zuba mata kaya yadda yakamata. Wanda sukayi wa Hanan rakiya suna zuwa a ranar suka juyo gida, suka barota tanata rikici, Seda kowa ya watse bayan sallar magariba sannan Jawwad ya shigo gidan, ya sameta tayi zaman dirshan a kasa ta jingina da gado, ta takure kanta sosai, tayi kuka harta gaji, dan girgiza kai yayi ya karaso gabanta ya tsuguna se kamshin turare yake, A hankali yace
“Haba Hanan, kukan ya isa haka, i know you miss home, Amma ba gani ba, sekace wadda akayiwa auren dole, ko kin dena sona ne?”
Girgiza masa kai tayi alamar A’a
“Yawwa my love 😍, kukan ya isa haka, yau ranar daza muyi farinciki ne, kar kanki yayi ciwo, ko nima kina so ki sani kukan ne?” ya fada yana goge mata hawayen fuskarta.
A hankali tace “A’a ni karkayi kuma nadena kukan” tai maganar cikin shagwaba
Murmushi yayi mata yace “Yawwa ai nasan baza kiso ki ganni ina kuka ba, shiyasa nima bana son ganin kukanki”
Haka ya cigaba da rarrashin ta har ta dan saki jiki tana hira, Jawwad da kansa yaje kitchen ya dakko plate da cups, ya bude musu kazar da ya shigo da ita, ya cika mata kofi da youghut me sanyi, yace “Bismillah”
Ta kalli kazar ta kalleshi tace “Ni na koshi”
“me kika ci da kika koshi?”
“bakomai” ta bashi amsa, ya lura gaba daya a firgice take, har hakan yaso ya bashi dariya amma ya maze ya ďan bata fuska yace
“in baki ci ba, zan kwana da yunwa ne, kuma ni inajin yunwa sosai, tunda aka fara biki bana samun cin Abinci fa, se Ulcer ta kamani ko?”
Yai maganar a ďan shagwabe, dariya ya bata tace
“in Ulcer ta kamaka ba rabin zamce ai, Dama haka ka iya shagwaba, wallahi tayi maka kyau”
tai maganar tana dariya, cikin hikima yanayi ya namata hira ya dinga bata kazar tana ci, seda suka kammala, Jawwad ya jagorance su sukayi Sallar nafila, domin nuna godiyarsu ga Allah da kuma fatan zaman lafiya me dorewa a cikin Rayuwar Aurensu.
Se Hamma take tana lumshe ido, da alamun gajiya da kuma bacci a tareda ita, Jawwad ya kalleta yace
“Wannan hammar da kike karki hadiyeni mana”
Tayi dariya ta Mike, tana cewa “gara in hadiyaka in huta ai”
fita Jawwad yayi domin rufe kofofin gidan, da kuma tabattar da komai lafiya.
Hanan ta canza kaya, ta nemi guri ta kwanta, wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin nata ne tana kokarin yin juyi ta jita a jikin mutum, a hankali ta bude ido tace “Haidar”
“My love” ya amsa mata
“bakayi bacci ba?”
“Banyi ba”
“meyasa?”
“ina tunani ne”
“Nasan me kake tunani, be wuce su Jalila ba, ni na gaya maka komai ze wuce, zasu koma normal, Jalila tana son Jalal, kawai dai kasan ta da taurin kai”
A jiyar zuciya yayi, ya kuma kwantar da kansa a jikin ta yace “Naikaina na san Jalal yana sonta sosai, daga baya na yadda da maganar ki soyayyar ‘yan uwatanka ne tsakanina da ita, hankalinta akan rayuwar Jalal take, a tunanin ta tausayinsa take ji, amma da haka sonshi yayi mata illa bata sani ba, kaman yadda ban fargaba naki son yakusa karasani”
Ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata
“I Love you my Hanan”
Makalkale shi tayi tace “I love you too Haidar”
Daga nan hirar kuma ta canza salo zuwa wani abu na daban, tun Hanan tana daurewa tana biye masa, taji abun ya wuce tunanin ta, ta fara neman taimako, ‘yan gidan su ba wanda be sha kira ba dama an hadu da uwar shagwaba, A wanna daren Jawwad ya saukewa Hanan wannan rawan kan nata.
(nima me rahoto naga abun yafi karfina dan haka na dawo da baya, na fito 😜😜😂😂😂)
Gaba daya Nana ta takurawa Jalila da waya, har sha biyun dare tana manne a waya seka ce wata mara aikinyi, haushi duk ya ishi Jalila tana ganin ta fiye zakewa, ji ta ke kaman suna karama ta takaicin da take ciki, ta ja bargo ta rufe har kanta dan ta dena jin abunda Nana take fada.
Washegari tunda safe Su Nana suka fara haramar tafiya.
Wayar Nana Jalila ta karba sukayi waya da Maama, har daki aka kawowa su Jalila breakfast, Nana kanta ba ta sake taci ba, saboda gaba daya ji take ba dadi, zata daga tabar kasarta ta haihuwa Aure kenan.
Karfe sha dayan safe su Nana suka gama shirinsu, suka shirya domin tafiya airport, nan ma seda aka sha daru Da Jalila saboda kuka, haka sukayi Sallama Nana da Mahmud suka tafi.
Hajiya Salma bata bisu ba ita seda ga baya zata koma.
Bayan tafiyar Nana Jalila dakin ta koma ta kwanta gaba daya ji take duniyar tayi mata fadi, ba abokin hira an kawota inda ba wanda ta sani. Ta lura nan gidan Antyn Jalal ne, tana da yara ‘yan mata guda biyu, daya zata girmi Jalila, Husnah da Amal, Amma sam basa san mutane basa shiga harkar mutane, dan haka ko sannu bata hadasu da Jalila, sedai sukan gaishe ta.
Hajiya Salma ta shigo ta samu Jalila a kwance tace “Jalila har yanzu jikin ne?”
Jalila tace “A’ a naji sauki kaina ne kawai be dena ciwon ba”
“ko dai likita za’a kira”
“A’a Anty naji sauki”
“to shikenan, Amma Jalila ki kwantar da hankalinki, ki cire duk wata damuwa a ranki, Kicigaba da raguwarki kaman yadda kike yi a da kinji”
Jinjina mata kai kawai Jalila tayi.
Koda Hajiya Salma ta fita dakin da Jalal yake taje, yana zaune yana kallon labarai a tashar CNN.
“Sannu Jalal kana nan kana kallo, kai ko tambaya matarka bakayi, ka sameta a sauki, dan haka baka damu da ita ba ko?”
“to me zance? Kokuma me zanyi? Nima ai bata nemana”
“Au hakama zakace ai shikenan, yaushe zaka koma?”
“gobe insha Allah”
“zakaje kano ne kokuwa?”
Jalal ya dan yamutsa fuska yace “daga nan gurin aiki zan koma, bazanje Mummy ta hargitsa min kai ba, lagos zan wuce”
“Shikenan Allah ya kaimu goben” Jalal yace “Ameen Amma, se yaushe Zaku bani ita mu koma kano”?
Hajiya Salma tace
“ita wa kenan?”
“Matata mana” ya bata amsa
Hajiya Salma tace “au ashe matarka ce, baka da kunya Jalal, se lokacin dana shirya yayi tukuna, ashe dai ka damu da ita”
Dan dage kafada yayi irin i don’t care din nan.
Jalal idan ya tuna yadda Jalila ta ce bata sonsa a gaban kowa da kowa, yana tunanin wani irin zaman Aure zasuyi? Tsawon lokacin nan dama bata taba sonsa ba kenan? To meze sa ya cigaba da bibiyar ta tunda tace bata sonsa.
Bayan Hanan tayi sallar Asuba komawa tayi kan gado, wani wahalallen bacci ya kuma dauketa. Koda Jawwad ya dawo ya tarar ta koma bacci, ya hau kan gadon ya ďan tsira mata ido, baccin ta take hankali kwance, tuno darun da tayi jiya yayi, ya danyi murmushi ya janyo ta jikinsa ya kwanta shima baccin ya dauke shi.
Wajen karfe tara Jawwad ya tashi, Amma Hanan bata farka ba, ya je ya dafa musu tea ya fita, ya fita ba dadewa Hanan ta tashi daga baccin, taje tai brush tai wanka ta saka wata doguwar riga mara nauyi, ta fito parlour amma bata ga Jawwad ba, ta nemi guri ta zauna a kan kujera, befi mintuna goma da fitowarta ba se gashi ya dawo hannunsa dauke da kaya, yayi sallama ta juyo ta amsa suna hada ido ya kashe mata ido, hakan yasata sunkuyar da kai tana murmushi, ya karaso ya ajiye kayan yace
“good morning dear, kin tashi lafiya?”
“lafiya kalau, kaima ka tashi lafiya?” tai maganar tana kokarin kaucewa hada ido da shi
“lafiya kalau na tashi lafiya, How was your night?” ya kuma jefo mata tambayar.
Pillow ta dauka ta rufe fuska tana murmushi haka Jawwad ya cigaba tsokanarta yana bata kunya.
Ya dakko cups yana kokarin hada musu tea tace “Haidar waye ya dafa tea din nan?”
“ni na dafa” ya bata amsa
“Allah yasa dai baka bari yayi kanzo ba, dan na san baka iya girki ba”
Dariya ta bashi sosai
“Ai nafi ki iya girki in gaya miki, zaki kuma gani”
“to ai shikenan hada min yunwa nakeji”
“Ai wannan tea din nawane ni kadai, bazaki sha ba ke kazarki zaki warming a oven ki cinye”
Zare ido tayi tace
“gaskiya bazan ciba na koshi”
Jawwad yayi dariya yace
“se kin cinye ta kuwa”
“aikuwa bazan ci ba, tsaya in baka a baki” ta dinga bawa Jawwad Abinci a baka, yana bata haka sukayi breakfast cike da kulawa da kaunar juna.
Wunin ranar yau Jalila ji tayi duniyar ta kara mata fadi, ga har yanzu Bata kuma sa Jalal a idonta ba balle ta sa ran karbar wayarta.
Bangaren Jalila ma tunanin ta yaza’ayi tayi zaman Aure da Jalal be damu da kansa ba balle ita, tana ganin shima an cusa masa ita ne kawai baya sonta, banda haka kwanan su nawa da zuwa be nemeta ba ga rashin lafiya tanayi amma ko keyarsa bata gani ba balle tasa ran ze mata sannu.
Ko parlour bata fita tana ďaki, Hajiya Salma da Antyn Jalal suna monitoring din Jalal da Jalila domin ganin actions dinsu, Amma abun mamaki kowannensu yana nuna be damu da ďan uwansa ba, tunda sukazo kwana uku ba wanda ya nemi wani a cikinsu.
Antyn Jalal tana zaune suna hira a parlour su Husnah suna cin Abinci Jalal ya shigo, su Amal suka gaisheshi a ciki ya amsa, dan sun fidda ran ze amsa musu, suka cigaba da cin Abincin su.
Anty tace “Jalal ina zuwa haka?”
“Zan koma lagos ne”
Anty sukayi ido hudu da Hajiya Salma.
Hajiya Salma tace “to wannaan tafiya haka kaman wanda ake kora? Ka gayawa matarka yau zaka koma?”
Cikin ko in kula yace “in kun ganta ku gaya mata”
Anty tace “dan kaniyarka mu zamu gaya mata ka tafi, Anya Jalal ka shirya rike yarinyar nan?”
A ransa yace “ita zaku tambaya in ta shirya zaman Aure dani?”
Hajiya Salma tace “nima dai haka nagani, tunda muka taho bata da lafiya, Amma yaron na ko ta kanta bebi ba, balle in sa ran ya duba ta, ya mata sannu” da sauri yace “bata da lafiya kuma? Me yasa me ta?”
Hajiya Salma tace “ban sani ba” mikewa yayi ya kalli Husna yace
“ina ne dakinta”?
“tana upstairs kusa da ďakina” ta bashi amsa, be kuma bi takansu Anty ba ya haura saman.
Kai tsaye ya bude dakin ya shiga, ya sameta ta dukunkune a cikin bargo, a hankali ya karasa gaban gadon nata ya kai hannu ya janye bargon.
Wata sleeping dress a jikinta blue me matukar kyau, kanta babu dan kwali, dukda tayi parking din gashin nata amma gashin ya hargitse, bacci takeyi sosai, Amma tayi rama a baccin ma se ajiyar zuciya take.
Ya kura mata ido fatarta se sheki take, a hankali ta motsa ta mike hannyen ta wajen kirjinsa, hannayenta sun sha ado da jan lalle, hannunsa yasa a nataa ya rike yana kuma kallon fuskarta, bacci take amma tayi kyau sosai. Ya bata lokaci sosai yana kallon ta. A hankali ya saki hannunta
Ya dakko wata ‘yar takarda a Aljihinsa da biro yayi rubutu ya ajiye mata akar kashin pillow dinta, ya mayar mata da hannun ta kan gado ya lullube ta ya fice.
Koda ya sakko bekuma ce musu uffan ba yayi waje abunsa.
Anty tace “kinga danki ko?”
Hajiya Salma tace “ai bari kawai, Jalal Akwai taurin kai, suna son juna amma taurin kai neke damun su, se nunawa suke kaman basu damu da juna ba, Allah shi yabarwa kansa sanin dalilin dayasa ya hadasu, Amma wannan zaman Auren nasu da kallo”
“hakane amma zamu cigaba da yi musu Addu’a, zasu dai daita, bari kiga sukoma gidansu da zama, bazaki sake jin kansu ba”
“hakane Allah ya tabattar da alkhairi, Amma bazata koma kano yanzu ba, sonake hankalin ta ya kwanta ta sake nustuwa, daga nan ma waccan jarababbiyar watakila ta sakko”
Anty tace “tab haba sister Salma, kin manta wacece khadija kenan, ai babu batun ta sakko yanzu, kawai dai mu tayasu da Addu’a” haka suka cigaba da hirarakin su.
Koda Jalila ta tashi ji tayi gaba daya dakin ya gauraye da kamshin Jalal, dan tabe baki tayi ta shiga toilet tayi wanka ta sa kaya, tazo tana kokarin gyara gadon tana cire bedsheet din taga takadda ta fado, ta dauka ta bude, wani tsararren handwriting tagani a jiki.
Am going back to lagos, get well soon
ABDUL JALAL se signing dinsa da date
Juya takaddar tayi ta jefar da ita a gurin tayi tsaki, “kwana nawa bani da lafiya, tunda aka daura auren ko ta kaina bebi ba, se yanzu ze wani rubuta min wata banzar takadda, ya tafi abunda yafi lagos ma ni be shafe ni ba, kuma maimakon ya ajiyemin wayata amma yakuma tafiya da ita sekace tasa.
Haka Jalila ta cigaba da mita, har ta gama gyaran gadon.
Parlour ta fito dan ta gaji da zaman dakin ga shi ba waya a hannunta balle ta debe mata kewa.
Anty na ganin Jalila tayi murmushi tace “Jalila kin fito? Ya jikin naki kuwa?”
“naji sauki Anty”
“to Allah yakara sauki, dazu Mijinki ya shiga dubaki ai”
Dan tabe baki Jalila tayi tai shiru.
Tundaga Ranar kullum cikin turara Jalila suke da samfurin turaruka daban2, a rana se ayiwa kayan sawa turare kusan sau hudu, banda wanda ake tuarar mata jikinta, hatta ruwan wankan Jalila akwai turaren da’ake zubawa, sabulun wankan ta ma na musamman ne aka hada mata, ga mayukan shafawa dana kai, nan da nan Jalila jikin Jalila yara canzawa, duk inda ta gifta kamshi take, duk rashin son kitson Jalila wani na tsufa me kitso take zuwa tayi mata wani, hakama lalle, gaba ďaya wannan gidan sun maida Amfani da turaruka kamar ibada, babu wani aiki da takeyi sedai taci ta kwanta, ko ta yunkura zatayi aiki se a hanata, ga kyan gyra da’ake bata dan haka har wani kiba tayi abunta tai kalau da ita. Jalila idan tana son yin waya sedai ta ari ta Anty tayi, ta mata magana akan wayarta tace tabari Jalal yazo.
Tunda Jalal yazo ko a waya be kuma neman inda Jalila take ba itama ba ta nemi jin inda yake ba.
Mummy ta cigaba da tayarwa da Daddy hankali akan maganar Auren Jalal, amma sam yaki saurararta, ya tattara ya koma Dubai, duk abun nan da ake Ilham bata sani ba.
Daddare Ilham na kwance tana chatting, ta shiga Twitter kamar wadda aka saka ta shiga profile din Jalal Alhamdilillah got married to Jalila Aliyu Imam shine abunda Ilham ta gani zumbur ta tashi Zaune tana kuma mutsukke ido, Amma still taga ba mafarki take ba.
Da sauri ta kira layin Nana, Amma bata shiga, se lokacin ta tuna ai Nana Mahmud ta aura, a England zasu zauna.
Fitowa tayi da sauri ta tafi ďakin Mummy tana kwala mata kira
“ke lafiya kuwa kike min wannan kiram, meya faru ne?”
Nunawa Mummy wayar tayi, mummy tace “me zan gani?”
“Mummy wai dagaske ne Jalal yayi Aure”
Ajiyar zuciya Mummy tayi tace “tun satin da Daddy yaje daurin auren Jawwad, ya hada baki da ‘yan uwansa suka masa Aure, nayi2 ya gayamin wacece yaki”
Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Mummy kin san wacece kuwa? Jalila ce fa, kalli Abunda ya rubuta ita ya aura Mummy, na shiga uku, Mummy ki kashe Auren nan kafin sun tare, Wallahi idan suka tare na kade, zan rasa komai, komai nawa ya rushe”
Gaba ďaya Mummy tsayawa tayi tana kallon Ilham
“dolene in kashe Auren nan, baze yuwu ba, wallahi ko yana so koba ya so sena kashe auren nan, ni Hajiya zainab zata munafunta, a hada kai da ita a Aurawa ďana wannan makirar yarinyar, in abun gaskiyane ta aurawa nata ďan mana, indai nina haifi Jalal seya saketa, a ďaura masa Aure ko ya nemi inda nake, rabona da shi wata biyar kenan, baze yuwu ba wallahi”
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool