Karfe A Wuta Chapter 109 By Ayshercool
Bin bayan Nabila yayi yana kiran sunanta, amma ba ta tsaya ba, ya cim mata a ɗaya bedroom ɗin, tana ƙoƙarin rufe ƙofa.Ya buɗe ƙofar ya tsaya yana kallonta, fuskarta ta koma ja, haka idanunta ma sun yi jawur.Jiki a sanyaye ya ce “Abla, dan Allah ki tsaya ki saurareni, na yi miki bayani ba yadda ki ke zato ba ne”Girgiza masa kai ta yi ta ce “No need, ba sai ka yi ba, na riga na fahimta””Ba ki fahimta ba abla, kin yi mini gurguwar fahimta, dan Allah ki tsaya ki ji”Cikin kuka ta ce “Ni ba sai na ji ba, na riga na fahimta, ba zan taɓa samun gurbi a zuciyarka ba, ni ka aureni ne kawai ka din ga kallon hoton jauhar, ba zaka taɓa so ma ba, this is the chance you ask me to give you, shikenan na fahimta”Diriricewa yayi ya ce “Ba haka bane, baki fahimce ni””Ba sai na fahimta ba, your actions show’s, da tuntuni ka bar ni na tafi a kan yadda na bar wa zuciyata, na aurenka shi ne sabuwar jarrabawar da zan fuskanta, ka yi mini maganganun da suka sanya na ji na aminta ina da kima a idonka, amma bakomai”Riƙota yayi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce “Ko ba zaki saurare ni ba, ki daina kukan nan dan Allah ba na so” fizgewa ta yi daga jikinsa, ta shige toilet, yana jin yadda ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.Har cikin ransa yake jiyo kukan nata, ya nemi wuri ya zauna jiki a sanyaye, tun yana sanya ran zata fito, har ya haƙura ya tashi ya fita.****””Na san wasiƙata zata iskeka a dai-dai lokacin da yakamata, kafin na jaka da nisa, bari na ɗan ja ka baya, zamanin da kana yaron ‘yan siyasa, kun zo garinmu wani sha’ani, aka kai mu wurinku, wai zaku bamu tallafi, aka haɗamu ‘yan matasan yara marasa galihu, aka kai wa uban gidanka, ya zaɓi wanda zai lalata, saɓanin cewar da aka yi za a bamu tallafin karatu da sana’a.Ina cikin waɗanda bai zaɓa ba, dan haka ban san me za ayi musu ba, na shiga damuwa burina ba zai cika ba na karatu, ba a zaɓe ni ba, ba zan samu tallafi ba. Ka yi amfani da wannan damar ka keta mini haddi, da sunan zaka saka ubangidanka ya bani tallafi.Matan da ka lalata da yawa, na san babu lallai ka tuna, sai dai shi irin wannan mikin, ba ya taɓa goguwa a zuciyar wanda aka illata.Naja’atu Bunkuren nan dai, da ka lalata da ƙuruciya a garin bunkure lokacin kana yaron ɗan majalissa, ni ɗin ce dai, ƙaddara ta sake haɗa mu, ba tare da ka gane ni ba. Sai dai ba tare da ka sani ba, ka cika alƙawarin da ka yi, na tallafar karatuna, kuma muka ɗora daga in da ka dasa aya.Ganin ina morarka, ya sanya na haɗiye mummunan ƙudurin fansar da nake da shi a kanka.Sai dai duk da haka, na yi shirin ko ta kwana ta kowace irin fuska, saboda sanin tsagwaron mugunta da zaluncinka.Lokaci ya yi da ka ke tunanin, ka ci moriyar ganga ka ya da kwauronta, ina! Idan har ka zauna a gida Nigeria, tonon sililin da zan yi maka ba zaka taɓa sha ba, haka zalika in da zaka ma ba zan bar ka ba, duk in da zaka shiga a faɗin duniya sai na kawo ƙarshenka, dan haka ya rage naka, ko ka dawo Nigeria, ko kuma ka tafi duk in da ka ke so, sai na kawo shafe tarihinka ta hanya mafi muni, zai zama daidai da ɗaukar fansar abin da ka yi mini a baya, aikin da na yi maka tsawon lokaci ma kuma ya zama halacci ga ɗawainiyar da ka yi da ni, na barka lafiya” tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa haka take bugawa, sam bai san ta ina yakamata ya fara ba, ya koma Nigeria ko kuma ya ƙarasa Saudiyya?.Nan ya shiga lissafi, me take tunanin ta ƙulla masa, da har take iƙirarin kawo ƙarshen sa a duk in da ya shiga a faɗin duniya?Har labarin lalatar da ya taɓa yi da yarinya a garinsu ya taɓa bata, amma ba ta taɓa nuna masa cewar ita ce ba, ashe duk tsawon lokacin nan wani abu ne a ranta game da shi.Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, gaba zai yi ko kuwa baya, duk iya tunaninsa ya rasa wane irin tuggun take shirya masa.*****Abbu kuwa ya gabatar wa da maman ramma, abin da Viper ya zo masa da shi, gam da ya aureta, ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Alhaji Ibrahim, ni a wannan shekarun nawa, me nake nema da zan sake yin aure?”Ya girgiza kai ya ce “Ba fa ki yi hamsin ba, kuma auren nan duk in da aka je aka dawo, shi ne rufin asirinki, kuma sai hankalinki ya fi kwanciya, amma ki yi tunani a kai”Bayan tafiyarsa ta din ga tunani, ƙarshe dai maganar tayi ta cin ta, take gaya wa ramma.”Amma na ji daɗi mama, babu abin da zamu cewa yaya Aminu sai Allah ya saka da alkhairi, da har ya ce ki auri mahaifinsa””Ramma ni gani nake yi abin bai yi tsari ba, goɗai-goɗai da ni na hau yin aure?””Mama ai mu ma sai mun fi jin daɗi ace ki na da aure, aure security ne, dan Allah ki amince kar ki ce a’a”Ta ce “Ai abin ne sai a hankali, amma zan yi addu’a dai””To sai mu tayaki addu’ar, kin ga nan gidan ma, bamu sani ba ko Daddy zai yi amfani da abin sa, kin ga ya yi mana ƙoƙari, kalli shi yake ciyar da mu, yake yi mana komai, kin ga kuma yau da gobe sai Allah. Amma idan aure ki ka yi ai mijin ba zai gaji ba, tun da hakkinsa ne” shiru ta yi tana kallon ramma, tabbas maganganunta haka suke, ita ba ma tayi wannan tunanin ba, dan haka ta ce “Kuma fa da gaskiyar ki rahama, amma ni duk na fi son na ga kin tare tukuna a naki ɗakin””Eh, ya ce babansa ya bar ƙasar, ya kuma gama gyara in da zamu zauna, ya canza shawara yanzu, wai zan tare amma fa har kayan ɗakin duk ya saka”Mama ta ce “Ai ni wannan mijin naki, rigimarsa ta yi yawa, na ma daina ce masa ya bari, Allah ya taimaka” ramma a zuciyarta ta amsa da Amin.Nabila kuwa fafur ta daina sauraren Viper, duk rarrashin da ya so yi mata, fafur taƙi tsayawa ta saurare shi.Zata dafa abinci ta bashi, da duk wani abu da yakamata ta yi masa, amma ba ta zama in da yake, babu hira babu duk wani abu na soyayya da take yi masa.Duk yadda yake murnar hutun da ya samu, zai zo su samu isasshen lokacin da zai bata kulawa da soyaya, amma komai ya ɓaci.Zaman gidan ma ya daina yi masa daɗi ko kaɗan, duk ɗaukinsa da son kasancewa da ita, yanzu fargabar tunkararta ma yake yi, dan sam babu fuskar hakan, sai yayi ta maza yake iya tunkararta, shi ma sai dai yayi kiɗansa da rawarsa shikaɗai.Sosai yake jin tausayinta, sai dai taƙi ba shi damar ya fahimtar da ita abin da yake son ta sani.’yan gidan Nabila su suka zo mata wuni, har da Walida da baba magajiya, dama bata saka ran ganin Sauda ba, har da Anty.Ta ji daɗin zuwan na su, kuma babu wanda ya fuskanci tana da damuwa, suka wuni suka yi wasa da dariya, sai da ta ji kamar kar su tafi.Abu kamar wasa, Viper ya daina cin abincin Nabila, idan ma ta ajiye ba zai ci ba, ya koma kwana a ɗaya ɗakin, hakan ya saka a jere kwana biyu baya kwana a gida ba ma ta sani ba, sai kwana na uku, da bata ganshi a gidan ba, wunin ranar.Bayan magariba sai ga Walid, ta yi masa maraba ta karɓe shi hannu bibbiyu, bayan sun gaisa ya ce “Barrister, meyafaru ne tsakaninki da mai zamani, muna murna an yi aure komai kuma zai wuce, shi ma zai samu nutsuwa yanzu ya ji daɗin rayuwa kuma sai a fara rigima?””Wani abin ya ce na yi masa?””Bai faɗa ba, amma alamu sun nuna, kamar a gidan da muka zauna yake kwana, me yayi zafi haka?”Cikin mamaki ta kalle shi ta ce “Kwana kuma? A can yake kwana?””Wallahi Nabila da gaske nake yi miki”Kawai ta fashe da kuka ta ce “To ni ya zan yi ne? Duk iya ƙoƙarina baya gani, Jauhar ce kawai a ransa, ni ba ni da wani gurbi a zuciyarsa. Zuciya ce fa a ƙirjina, ina son ‘yar uwata, amma abin da yake yi mini yayi yawa. Muna tare da daddare har ya kwanta ya ce mini fita zai yi, sai ji na yi kuna waya, wai gidan da suka zauna ya tafi, a wannan daren ni bani da amfani kenan? Ba zan hana shi tuna Jauhar ba, amma ni fa? Kodayeke dama ni na ce ina son shi, dole na jure duk abin da zan gani”Walid ya ce “Subhanallah, kuskuren fahimta ne Nabila, tun yamma muka yi magana da shi, ya ce mini ya ji wani wa’azi, an ce gado nauyi ne a kan mamaci, har sai an raba ake sauke masa wannan nauyin.Shi ne ya ce mini tun da kema gaki, kina cikin magadanta, zai je ya duba gidan, yayi magana da su Baba, ina ga tun zuwan da ku ka yi, bai sake zuwa ba.Da safen ma, da muka yi magana ce mini yayi abin ne yake ta damunsa, ya kasa bacci, ya ji bai kyauta ba ace tsawon wannan shekarun ba a sauke wa Jauhar nauyi ba, kuma baba bai yi masa magana ba, kawai ya fita a daren, ya je ya sake dudduba gidan, ba wai dan baki da amfani ba ne ba Nabila.Wallahi kulawar da ki ka samu, Jauhar ba ta sameta daga gare shi ba shi fa yanzu duk wannan abin da yake yi, ihu ne bayan hari kawai, amma wallahi yana sonki Nabila.Kin san sunanki da nasa ya hargitsa ya fitar da sunan da yake kiranki da shi Abla? Ki din ga yi masa uzuri, a hankali zai daina, zamansa da Jauhar ba abu ne da zai manta lokaci guda ba, yarinyar ta sha wahala ne sosai, kuma ba ta wani more shi ba, an kashe ta a dalilinsa. Da bakinsa yake faɗar ki na da haƙuri matuƙa da kawaici, amma ina ƙara baki haƙuri, dan Allah ku sasanta”Tayi ajiyar zuciya, ta jinjina kai ta ce “Wallahi ina yi masa uzuri, shi ma ai ya sani amma In sha Allah zan ƙara, na gode sosai da sosai “”Yauwwa Nabila, ai wallahi tun da ya ce mini wai kin goyi bayan soyayyar liti da ƙanwarki na sara miki, ba ki da riƙo, kuma ki na da haƙuri sosai da sosai, Allah ya baku zaman lafiya ya ƙara muku fahimta juna”Ta amsa da Amin, tayi ta masa godiya, ya tafi.Kamar ta kira Viper a waya, sai ta ƙyale shi, sai da gari ya waye, tayi girki ta shirya ta fita.*****Cikin matsanancin tsoro da fargaba, indabo ya sauka a airport, yana ta tunanin abin da ka iya faruwa, na sharrin da Bunkure ka iya ƙulla masa.Sai dai ya ga ya wuce airport lafiya, babu abin da ya faru, har ya isa masaukinsa, bai haɗu da wata matsala ba.Ya kira abokansa ya sanar musu takardar da Bunkure ta aiko masa da ita, suka bashi ƙarfin gwiwar ka da ya damu, barazana ce kawai ba wani abu ba, yayi zamansa zuwa lokacin da komai zai daidaita.Kankarofi kuwa yana ta campaign ɗin sa, na takarar sanata, kujerar da Indabo yake kai.Kuma yana ta ci gaba da samun karɓuwa ta kowace kusurwa.Jidda ƙanwar indabo kuma tana ta nacin sai ta koma ɗakinta.***Kamar daga sama haka Viper ya ji sallamar Nabila, sai dai bai iya amsa mata ba, cikin ɗakin ta shiga, aikuwa ta same shi a zaune a kan katifa.A ranta take mamakin halinsa, daga samun saɓani yayi yaji, ƙasan zuciyarta, take addu’a Allah ya sa bai sha wani abu ba.Ba ta ce masa komai ba, ta ajiye flask ɗin, ta ƙarasa kusa da shi ta zauna, bai kulata ba, ta saka hannunta ɗaya a bayansa, ɗaya kuma ta juyo fuskarsa ya kalleta, ta marairaice ta ce “Na zo biko ne, am sorry Vi, son da nake yi maka ne ya janyo komai, kuma tunanin da nake yi, ba ni da matsayi a wurinka ne ya sanya nake shiga damuwa, but am sorry” bai yi magana ba ya ci gaba da tsareta da idanunsa.Ta shafa fuskarsa ta ce “Talk please” kamar gunki yaƙi magana.”Please talk Vi””I love you” yayi maganar yana tsareta da ido.Idonta ne ya ciko da hawaye ta ce “And you mean it?” ya jinjina mata kai alamar eh.Rungume shi ta yi, hawayen farinciki na zubowa daga idanunta, gadon bayansa take shafawa zuwa kansa ta ce “Dama zaka iya bani gurbi a zuciyarka?””Na daɗe da baki Abla, baki yadda da kanki bane ba, shiyasa ki ke ganin kamar ba da gaske nake ba. Tashin hankalin da na shiga, da na ji an ce gado nauyi ne, ya sanya na kasa jurewa na tafi a daren, communication gap aka samu a tsakanin mu, dole mu zama masu saurarar juna da yi wa juna uzuri domin zaman auremu ya ɗore kuma ya yi daɗi.Na yadda ke ba Jauhar ba ce ba, kuma ina ƙoƙarin na rayu da ke a Nabilanki, amma sai kin yadda da kanki, kin kuma rage zargi.Abla ina yawan gaya miki Al’amin ba butulu bane ba, bana manta halacci komai ƙanƙantarsa kuwa. Balle ke naki da ceto raina, hankalina kacokan ki ka yi, rayuwarki ki ka saka a hatsari mai ban tsoro ki ka ceto ni, tayaya zan zama butulu, a ɗakin nan na kusa ajalinki, amma bai hanaki ci gaba da bibiyata ba, wane irin butulu ne ni da zan kasa buɗa miki zuciyata ki shiga? Ki manta da matsayin Jauhar a zuciyata, ki kalli kanki ke ɗaya kawai, wasu lokutan wasa nake yi miki a wasu abubuwan, amma tun da ba kya so, in sha Allah na daina, amma ina ƙaunar ‘yar sugar, wannan kalaman ko ‘yar madara ban taɓa gaya wa ba, sau ɗaya na taɓa furta wa jauhar ina sonta a rayuwata, daren da za a kasheta, amma ke ba na son na maimaita wannan kuskuren ina sonki Nabilatul arfa, Ablana kuma ‘yar sugana” Ita kanta ba ta san takamaimai kukan me take yi ba, ya ci gaba da rarrashinta, da duk kalaman da shi kansa bai san ya iya su ba, tare da ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa.A hankali ta ce “Vi ba fa a gida muke ba””Eh, ai ke ki ka ɓata mana honeymoon a gida, sai mu yi a nan””Honeymoon a kango?” Tayi maganar tana murmushi, bai san lokacin da ya tuntsure da dariya ba, ya tashi zaune yana kallonta ya ce “Gidan gwaurontakar namu ne kango?”Tana daga kwance ta yi murmushi ta ce “Kogon da macijina ya din ga ɓuya ba”Ya gyaɗa kai ya ce “Ke ce jarumar da ki ka samawa wannan maciji ‘yanci, ya ci gaba da rayuwa da cikakken ‘yanci.Abla a lokacin da ake nemana ruwa a jallo, ba ki duba kamani tare da ke barazana ne a gareki ba, ba kya lissafa wannan, ‘yanci kawa ki ke nema mini, na bar kogon da yake tamkar kurku a gare ni, wai duk tayaya zan manta wannan ne?” Ya ƙarasa maganar yana kwanciya a jikinta.Ta rungume shi sosai, tana sauke numfashi.A nan suka karya, hankalinsu kwance kamar su na gida, su ke gudanar da soyayyar su.Har Dutsen da ta kan je ta same shi, su ka je, ta din ga tuna masa wasu abubuwa da suka din ga faruwa, suna nishaɗi.Har yamma suna can, sannan suka tafi gida.Viper ya tambaye ta, a raba kayan jauhar a bata, ko a sayar a raba kuɗi kawai a bata.”Ba zan iya amfani da kayanta ba”Dumm ya ji a ƙirjinsa, amma ya daure ya ce “Meyasa?””Zan daɗe ina kallon kayan ina tunata”Ya ce “Ko dai kishin ne?””Ko kaɗan, rayuwarta da yadda ta rasu, ba zai taɓa barin ƙwaƙwalwata da zuciyata ba, ba zan iya amfani da kayan jauhar ba, rashin haɗuwa da jauhar a rayuwata wani miki ne za ba zai taɓa warkewa daga zuciyata ba. Idan ma an raba, ayi amfani da abin da na samu a sai wani abu da ladan amfani da shi zai isketa da mahaifiyarmu a makwancinsu””Shikenan, zan yi magana da Abba abin da ya ce shikenan”Gidan Major kuwa, Mama ta takurawa Nasir a kan ya auri ‘yar ƙawarta da take so ya aura tuntuni.Aka fara shirye-shiryen biki, aka yi masa transfer a wurin aiki, zuwa kudancin Najeriya, kuma aka rage masa matsayi sosai da sosai a in da aka kai shi.Walida kuma sosai suke soyayya da liti, dan kuwa akwai shi da shiga rai.Sosai Viper yake ƙara ganin kimar Nabila, saboda rashin riƙonta, maganar bikin Sumayya ita ma ta taso, Nabila su na ta shirye-shirye.Viper sai da ya samu Liti, shi ma ya ja masa kunne, a kan abubuwan da yake yi wa Nabila.Nabila ta sake komawa duba mama, an sallamota daga asibiti tana gida, sai dai wata irin wahalalliyar jinya take yi, gaba ɗaya yaran babu mai tausayinta.Har gidan su Shahida ta je, ta zazzagaya ta sada zumunci.Bayan ta dawo, ta tarar da Viper yana ta mita.Ta ce “Meyafaru ne?””Kuɗin da muke rabawa na ribarmu, na wurin shayin nan, wai ba za su bani ba, wurin refilling ɗin gas, Walid zai din ga zama idan ya dawo daga kasuwa, zai din ga zama”.Ta ce “To menene a ciki, idea ce mai kyau””To ai ni kuɗi nake so, harkar bikin nan na kashe kuɗi sosai, na sakankance na saka rai, suka ɓullo da wannan maganar”Ta ce “Vi ai idea ce mai kyau, zaman haka ka dogara da aikin gwamanti kawai, ba zai yiwu ba, gashi shiru an ce za ayi maka ƙarin girma amma haryanzu shiru””Wannan ƙarin girman duk matsala ne””A’a ina fatan mu samu ci gaba, a kan komai”Cikin ikon Allah aka saka ranar tarewar ramma, kuma maman ta amince da batun auren baban Viper.Nabila ta mayar da hankali wurin gyara ramma ma, ta biya kuɗin yi mata gyaran jiki, sannan ta saka maman yusuf likitan mata haɗata.Viper ya yi ta mita, saboda Nabila ta koma aiki, haka abubuwa suka yi wa Nabila yawa, zama matar gida babu sauƙi ga komawa aiki.A haka lokacin hutun Viper ya cika, zai koma bakin aiki.Daga shi har ita kamar su cinye juna, dan tun bayan da suka shirya, yake ta ƙoƙarin kare duk wani abu da zai sanya ta ji babu daɗi, ita ma daga nata ɓangaren tana ta ƙoƙarin kiyaye abubuwan da zai janyo su samu saɓani.Tun dare ta haɗa masa jakarsa, ta yi masa snacks, ta yi masa cincin da dambun nama, yadda zai daɗe yana amfani da shi.Sun sha soyayya ranar, kamar kar su rabu.Da safe wurin ƙarfe goma, ya tafi duk sai ta ji babu daɗi, gidan yayi mata wani iri.Kwanan Viper biyu da tafiya, Walid ya rako liti har gida, ya zo ba wa Nabila haƙuri.Nabila ta ce “Da zan riƙe abin da ka yi mini a raina, hatta alaƙarka da Vi sai na rabata, duk da tasirin shekarun da ku ka yi tare. Kawai da ka din ga iya bakinka, wani idan ka cutar da shi da harshenka, har abada duk aikin alkhairin da zaka yi masa, ba zai shafe tasirin abin da ka gaya masa ba, Allah ya shiryeka” duk da ya ji haushin kausasan maganganun da tayi amfani da su a kansa, amma ya danne.Bayan sun fito yake cewa Walid “Yanzu da gaske sai ta raba alaƙata da Viper, duk tsawon lokacin da muka ɗauka tare?”Walid ya ce “Macece fa, wallahi sai ta raba””Kai ƙarya ne ba zai yiwu ba, ba wata mace””Galibinmu uban meye ya koro mu daga gidan iyayenmu, idan ba tasirin kaidin mace ba, ka daina cika baki malam”Sai kuma ya ce “Kai haka ne fa, to Allah ya kyauta”Nabila ta samu labarin mutuwar Madaki, ya mutu an rasa wanda zai zo ya karɓi gawarsa, ga jikinsa babu ta in da za a saɓa shi ayi masa wankan gawa, saboda duk ya ruɓe, haka aka yafa masa ruwa aka binne shi.Da Nabila suka yi waya da Viper, ta din ga godewa Allah, da Allah ya dawo da su hanya madaidaiciya lokaci bai ƙure musu ba.Nabila ta kai wa madam Halima ma ziyara, dan sai da ta kwana biyu a wajenta, Viper ya bata damar hakan.Nabila ba zata taɓa mantawa da matar nan ba.Aka gama shiri tsaf, ramma ta tare a gidan Abdul, a lokacin tana cikin hutun makaranta.Gidan ramma ya yi kyau sosai da sosai, ana gobe zata tare ya sanar wa mummynsa, a lokacin Anty Jidda tana gidan.Ta ce “Abdul ka yi asara, ‘yar matsiyata talakawa da suka tagayyara rayuwarka, yau ita ka bi kake wannan rawar kan a kanta”Abdul ya ce “Anty Jidda ban yi asara ba, gyara kuskurena na yi, kuma ke ma yakamata ki nemi yafiyar ramma, abin da ya faru da ita a gidanki, amma ki ka nuna halin ko in kula, ba zan gaji da sarawa Alhaji mu’azzam kankarofi ba, ya cika uba, kuma ni abin da yayi mini taimakona yayi”Mummy ta ce “Jidda ba fa zai gane ba, a kan yarinyar nan zai iya ci miki mutunci ma, ai ni na cire hannuna daga kan Abdul na saka masa ido, kina kallo halin da mahaifinsa ya tsinci kansa a ciki wanda har saka hannunsa bai dame shi ba, ya haɗa kai da abokan adawar ubansa ba abin da ya dame shi”.Jidda ta ce “Amma kuwa Abdul ka yi asara””Wallahi ban yi asara ba, tun da kema abokin adawar ta sa ki ka aura ai”Duk da bai ji daɗin abin da ta faɗa ba, amma yana Addu’ar Allah ya sa kar furucin mahaifiyarsa yayi tasiri a kan aurensa.Hankalinsa kwance ya kasance da ramma, cikin jin daɗi da farinciki, saboda yadda yake ji a yanzu yana da cikakkiyar dama a kan matarsa.Babban abin da ya basu mamaki, har da akwati bakwai na lefen ramma, suka tarar a gidan.Store ɗin ta na abinci shaƙe da abinci, duk wani abin buƙata da na amfani ya saka mata.Kafin ta tare ta sha nasiha, kuma sai da aka yi walima sannan ta tare.Ko sabon ango fil bai kai Abdul rawar ƙafa ba yau, a baya duk da auren ramma yake yi, ya kan ji kamar yana wani abu ba dai-dai ba, amma yanzu hankalinsa kwance, kasancewar duniya yanzu ta san ramma matarsa ce.Daren bai gushe ba, sai Abdul yana nanata wa ramma, irin matuƙar ƙaunar da yake yi mata, tare da neman afuwarta a kan abubuwan da suka faru a baya.Duk daga shi har ita ba baƙin juna bane ba, amma daren yau ɗin ya ƙara zama na musamman a cikin zukatansu, duk da a ƙarƙashin zuciyar ramma, ta na jiyo raɗaɗi da zafin rasa mutuncinta, da kuma rayuwar da ta yi, ita ba karuwa ba ita ba mai aure ba. Amma ba ta fatan sake tayar da wannan maganar, dan ta yi masa alƙawarin komai ya riga ya wuce, domin yanzu Abdul gaba ɗaya tausayi yake bata.Da safe Nabila suna Video call da Viper, ko saukkowa ba ta yi daga kan gado ba, ta kira shi ta gaishe shi.Ya zuba mata ido ya ce “Fito daga bargon sai mu gaisa” ta fito ta tashi zaune ta ce “Good morning Vi””Morning darling, ya aiki ya gidan kuma”Cikin shagwaɓa ta ce “Am missing you””Next week zan shigo in sha Allah, ni kaina ina kewarki like crazy, kin rame ma fa, ya aka yi ne?””Hidimar tariyar ramma ce da na yi ta zirga-zirga, jiya dai ta tare Alhamdilillah “Viper ya ce “Masha Allah, an sha gwagwarmaya Allah ya zaunar da su lafiya ina fatan dai maman ba ta ɗaga hankalinta ba?””Ba ta ɗaga ba, baka ga gidan rahama ba, har lefe yayi mata, ka ga rawar kai, sai dai babu kowa daga danginsa””Tun da dai shi ya ji ya gani, aishikenan ina yi musu fatan alkhairi, yaron ma ni tausayinsa nake ji, a idonsa zaka ga yadda yake ƙaunarta. A yadda na san shi yaro ne ɗan gata mai ji da kansa. Tun da na ga ya sauke yana magiyar a bar masa rahama, na gane lallai yana son ta”Nabila ta ce “Vi ba dai son girma ba, wai yaro, mijin rammar ne yaro?””Ban girme shi ba?”Cikin dariya ta ce “To kuma sai ka ce masa yaro?””Eh mana, an gaya miki ni na yau ne, na kama hanyar 40yrs fa”Tayi dariya ta ce “Sannu dattijo””Eh faɗi ki ƙara beb, Allah ya sa ki samo mana baby da wuri, kin ga na kama hanyar tsufa, in ga babyna, gashi ke ki na can ni ina nan, da mun ƙara effort kuma mu yi ta addu’a”Ta tura baki ta ce “Duk effort ɗin da saka bai isa ba sai ka saka wani? You won’t kill me”Ya ƙanƙance idanunsa ya na kallonta, yana yi mata wani miskilin murmushi.”Menene kuma?” Ta tambaye shi a shagwaɓe.”Maganarki ce ta bani dariya, Abbu ma fa end of this month zai angwance in sha Allah”Waro ido Nabila ta yi ta ce “Aure zai yi?”Ya ce “Eh mana, za a ɗaura aurensu da maman ramma in sha Allah, ni na nemi ya aureta, ita ma ta fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali””Au kai ka bashi shawara ya yi wa maman Shahida kishiya, na ji daɗi amma ta wani fannin, baka tunanin yadda zamansu zai kasance da maman Shahida, gata ba ta da cikakken hankali?”Viper ya ce “Wacece ita da ba za ayi mata kishiya ba, haifarsa tayi?””A’a Allah ya baka haƙuri, na ga haryanzu akwai wani abu a ranka, game da matar nan, yakamata komai ya wuce””An gaya miki kowa irinki ne, wallahi ba zan taɓa yafewa matar nan ba har abada, ina ɗaga mata ƙafa ne kawai saboda ‘yar uwata, amma ko da me take yawo ba zan yafe mata ba, ke sai anjima ma kin ɓata mini rai””Allah ya baka haƙuri ” bai jirata ba ya kashe wayar sa.Hafsa ta fara shiga damuwa, tun da ta koma gidan Alhaji mu’azzam, ko canza date na period ɗin ta ba ta taɓa samu ba, ta duƙufa da addu’a Allah ya sa tana da rabon samun haihuwa a rayuwarta, gashi kusan kullum sai Anty ta kirata tana tambayarta, ko ta samu ciki, har abin ya fara ba ta haushi.Sosai Abdul yake nuna wa ramma soyayya da kulawa, sai dai ta fara fuskantar ƙalubale daga dangin Abdul, babu wanda ya zo tariyarta, amma suka fara zuwa wai ganin ‘yar ƙauyen da ta yi wa Abdul asiri.Abbu kuwa gidan da zai ajiye maman ramma daban, ba zai haɗata da Rahila ba.Sai dai tun da ya sanar mata da zai yi aure, hauka ya ƙaru tuburan, kamar ta yi masa duka saboda azabar kishi, har da iƙirarin zata cinna musu wuta a cikin gidan.Viper ya zo gida hutu, ya samu labarin abin da matar Abbu ta ce, ya ce sai ta koma gidansu an nema mata magani ta dawo, ba za ta ƙona masa uba ba, ace ba ta da hankali, idan ba haka ba ruwansa da haukanta, zai saka a fitar da ita daga gidan ta ƙarfin tsiya.Har gida Shahida ta zo tana kuka, ta na bawa Viper haƙuri, a kan yayi haƙuri, idan ta fita babu in za ta je.Viper ya ce “Shahida ba ina ƙoƙarin tozarta mahaifiyarki ba ne ba, amma da alama haryanzu karatun da duniya ta yi mata ba ta ɗauke shi ba, amma ki yi haƙuri daga ke sai mahaifina ku ka rage mini, idan ta ƙona shi ban san ya zan yi ba. Idan ba haka ba kuma a kaita asibitin masu rangwamen hankali, har sai ta warke.Shahida ta yarda da hakan, dan ita ma gani take, larurar ta mahaifiyar ta ta, ƙara gaba take yi. Abbun ma ya amince a kan a kaita asibitin ƙwaƙwalwa. Bayan kaita kuma su ka ce gado za su bata, har sai ta warke, a can zata zauna.Indabo hankalinsa ya kwanta sosai, jin ya zarta wata guda, yana zaune lafiya a ƙasa mai tsarki, ya miƙe ƙafa ya ɗora da tsula tsiyarsa.Nan gida Nigeria kuma aka ce, Indabo ya je neman lafiya ne, bashi da lafiya, amma duk wasu allowances ɗin sa suna shiga account ɗin sa.Wajen ƙarfe sha ɗaya, ya farka da kyar, kansa yana yi masa wani irin nauyi, ya duba ɗakin ya nemi yarinyar da ya kwana da ita ya rasa.Ya tashi da kyar yana dube-dube, duk ta kwashe masa abubuwa masu muhimmanci ta gudu da su.Ya duba gefen da ta kwanta, ya ga wani ƙaramin note.”Ina mai farincikin sanar da kai, samun saƙon Naja’tu Bunkure, ta ce ayi maka fatan girbar abin da ka shuka, a nan duniya da ma can in da zaka”Yana bankaɗa pillown da ta kwanta, ya tarar da ɗaurin hodar iblis, kafin ya yi wani yinƙuri, ya ji ana buga ƙofar ɗakinsa.
Ayshercool 08081012143



