Halysaah Page 129 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 129…A hankali Khaleesat ta bude idonta wajen karfe shidda da rabi na asuba cause she slept like a baby, ta mike zaune da sauri don gari har ya ɗan fara washewa bata yi sallah ba, duvet ta jawo tana kara rufe jikinta da shi cause she is wearing nothing, abubuwan da suka faru jiya da daddare suka fara dawo mata daya bayan daya a kai, ta turo baki tayi saurin komawa ta kwanta ta rufe har kanta da duvet ta ji ina ma kawai tayi disappearing daga dakin ta ganta a dakinta saboda kunya, a hankali ta sauke duvet din tana jin wani sabon kunyan, sai kuma ta mike zaune tana dube duben inda zata ga towel da tayi wanka da daddare amma bata gansa a dakin ba, cikin rashin kuzari ta sauka daga saman gadon still covering her self with the duvet ta nufi bandaki, daya daga towels dinsa ta kara dauka sannan ta maida duvet din cikin daki ta koma bathroom din tana kallon sleeping dress dinta da inner wear da ya wanke ya shanya, wanka ta sake yi cause she felt the need of doing so, ta kuma yin alwala ta fito bandakin tana goge dogon gashinta da wani towel din daban, har lokacin ita dai a kunyace take sosai har bata son tuno abinda ya faru, nan ta fara tunanin yanda zata yi sallah saboda babu hijab a dakin, a hankali ta nufi wajen press din kayansa ta bude duk da bata ma san me take nema a ciki ba, ta ɗan bude ido ganin uban kayan da yake da shi kamar wani karamin boutique, haka ta dinga bude buden ko ina tana kallon kayansa, and the press was well organized, komai da inda yake ajiyewa, da mamaki take kallon well ironed hijab dinta dake ajiye cikin press din, nan ta tuna hijab din da ta saka ranan da Legend ya biyota har dakin ne, daukan hijab din tayi ta ajiye kan kujera ta tafi gaban madubi tana ci gaba da goge gashinta don bai bushe ba hair dryer dinta kuma na daki, ribbon dinta har biyu dake gaban madubin take kallo, sai kuma ta dauka ta daure gashinta da shi, kilan wa enda ta bari ne sanda ta kwana dakin, ta saka hijab dinta ta nufi kofa ta bude a hankali tana leka cikin parlon don so take ta koma dakinta, kwance ta gansa kan kujera yana bacci kuma bata ga alamar shi ma yayi sallah ba, ta fito daga dakin tana tiptoeing yanda bazata yi making ko wani sound ba ta fice daga parlon da sauri, tana shiga dakinta ta kulle ta jingina da kofa tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe idonta… Wajen karfe bakwai da rabi Khaleesat ta fita daga dakinta zuwa wanda Aunty Farida take, hijab ne har kasa sanye jikinta, a hankali ta bude kofar ta shiga ciki, ta tarar da Aunty Farida zaune dakin da littafin addu’o’i a hannunta, Khaleesat bata yarda ta hada ido da ita ba ta zauna kan Carpet ta gaidata a hankali, Aunty Farida ta kalleta ta amsa gaisuwarta dai dai sanda Ajay yayi sallama bakin kofar, Aunty Farida ta amsa ya shigo dakin, sosai gaban Khaleesat ya fadi jin muryarsa, yana shigowa suka hada ido daga ita har shi suka sunkuyar da kai kamar hadin baki, ya karaso dakin ya zauna suka gaisa da Aunty Farida, kamar munafuka Khaleesat ta mike har sannan taki daga kanta ta nufi kofa ta fita daga dakin. Throughout ranan Khaleesat bata sake haduwa da Ajay ba don kamar ma fita yayi tun safe, ba laifi yau Aunty Farida ta ɗan sake mata har suka ɗan yi hira kamar ba ita ta gaggaura mata mari ba jiya da daddare, wai sai yanxu ne take mata nasiha take nutsar da ita tana nuna mata Allah na fushi da ita idan ta ci gaba a haka tana matar aure amma tunanin wani na ranta tana shiga hakkin mijinta, ita dai Khaleesat na zaune ta sunkuyar da kanta amma ba wai hankalinta na kan maganganun da Aunty Farida ke yi mata bane, don babu abinda ya makale mata a rai ya hanata sukuni tun daxu sai incident din daren jiya, it’s making her to be so ashamed, duk yanda ta so kauda tunanin abun a ranta hakan ya faskara, gashi the thought of the incident alone send quivers all over her body, wani lokacin she will just be carried away with the thought har sai tayi firgit ta dawo reality, karfe shidda saura na yamma Ajay yayi sallama kofar dakin da Aunty Farida take, sosai Khaleesat taji gabanta ya fadi don har sai da ta jingina da gadon dakin to calm her self down, ya shigo dakin ya zauna suka gaisa da Aunty Farida, kana ganinsa kasan he is not himself, Aunty Farida tace “Kamar kana bukatar kaje ka huta, you look stressed Junaid” Ya ɗan yi murmushi yace “Sure Aunty” Mikewa yayi ya fita daga dakin, sai da ya kullo kofar dakin ya jingina jiki for almost 10 seconds, haka ya wuni yau feeling so restless cause he realized he was actually double crossing a vow, and that is the work of the devil, yana tafiya a hankali ya nufi part dinsa…. Aunty Farida ta juya ta kalli Khaleesat ta hade rai tace “Sai ki tashi ki je ki kai masa abinci, ko abincin ma bakya basa?” Khaleesat tayi shiru tana kallonta, sai kuma ta marairaice a hankali tace “Aunty ai shi ba abincin kowa yake ci ba, shi yasa ni ban taɓa basa ba” Bude baki Aunty Farida tayi tana kallonta da mamaki, Khaleesat na ganin haka ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi kofa, Aunty Farida tace “Ban taɓa ganin mahaukaciyar yarinya gantalalliya kamar ki ba, wato baki ma taɓa attempting basa abincin ba kenan, sai dai kiyi ki ci tunda ke kika ajiye kayan abincin, tir da halin ki wallahi, ina ga wannan dole sai na gaya ma Umma abinda ke faruwa ba wani batun boye boye kuma” Tuni Khaleesat ta fice daga dakin ta sauka downstairs, ta rasa yanda zata yi gashi tana tsoron kar Aunty Farida ta taho kasa ta sameta, can dai ta tafi Laundry room ta kulle kofar ta nemi waje ta zauna don ita wallahi kunyan zuwa bangaren nasa ma take ji balle har ta kai masa abincin da ba lallai ya kalla ba ma. Sai da gari yayi duhu Khaleesat ta koma sama ta shiga dakinta tayi sallahn magrib, ta jira har lokacin isha’i shima tayi sannan tayi wanka ta dau doguwar riga ta saka ta koma dakin da Aunty Farida take. Karfe goma saura Aunty Farida tace mata sai da safe ta tashi ta tafi, ba musu ta mike tayi mata sai da safe sannan ta fita daga dakin, kamar munafuka tana waige waige ta sauka downstairs ta sake komawa Laundry room ta shiga ta kulle kofar…. Haka Khaleesat ta dinga yi a gidan duk idan dare yayi sai ta tafi Laundry room ta makale, ba ma da daddare kadai ba even during the day sai taje tayi zamanta a can ta yanda idan Aunty Farida ta duba dakinta taga bata nan zata yi zaton tana bangaren Ajay ne, yanda take avoiding Ajay shi ma dai kamar haka yake avoiding dinta a gidan kamar bai son su hadu, ko haduwa suka yi a dakin da Aunty farida ta sauka baya kallon inda take har ya fita daga dakin, a haka Aunty Farida ta gama kwanakinta a Maryland ta fara shirye shiryen komawa Nigeria with the hope that Khaleesat ta canza kenan for good don kusan kullum kafin ta kwanta da daddare sai taje dakinta ta duba sai taga bata ciki duk zaton ta tana bangaren Junaid, nan ko bata san tarewa tayi a Laundry room ba har da shimfida tayi ma kanta a can, ana washegari Khaleesat za su fara final exams dinsu suka kai Aunty Farida airport da daddare, tun basu isa airport din ba take ta matsar kwalla a gaban mota don tasan dole zata yi missing din Aunty Farida duk da zaman takuran da tayi a Laundry room all through her stay, but she is definitely going to miss her, bayan sun sauka Khaleesat ta jingina da motar tana share hawayen dake zuba idonta, Aunty Farida dai tayi kamar bata san me take yi ba balle ta fara lallashinta, tana kallon Ajay ta kara masa sallama tare da godiyar hidiman da yayi da ita, shi dai kawai yayi murmushi leading her inside the airport, Khaleesat ta fashe da kuka a hankali ganin Aunty Farida tayi tafiyarta without even saying a goodbye to her, tana ta tsaye jikin motar har Ajay ya dawo bayan wani lokaci, ba tare da ya kalleta ba ya zaga zai shiga motarsa ya ji ance “Yarima” Juyawa yayi yaga wani colleague dinsa da suka yi PHd tare, ya dawo yana murmushi ya basa hannu suka gaisa yace “Longest time Usman” Usman yace “Wallahi kun buya kai da Jawwad, ba a jin motsin ku” Ajay yace “Kai ma ai ka buya, me kake yi a Maryland?” Usman yace “Na samu aiki a nan” Ajay yace “Maa sha Allah, Congratulations Usman, ka dawo da family din ka nan kenan?” Usman yace “A’a tukunna dai in sha Allah, ina processing din hakan very soon” Sai kuma Usman ya kalli Khaleesat da ta kauda kai tun zuwansa wajen tana kallon wani direction daban, Usman ya bude baki da mamaki yana kallon Ajay yace “Kar dai kayi aure babu labari ko a social media Yarima?” Ajay ya ɗan bude ido yace “Aure kuma? Haba dai, kanwata ce wannan, me zai hana a gaya maku idan aurena ya tashi, but na kusa soon in sha Allah, za a gayyace ku” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalli Ajay jin abinda yace, Usman yace “Ohh maa sha Allah, karatu kanwar taka take a nan ne?” Ajay yace “Yeah, final exams zata zana a John Hopkins” Usman na kallon Khaleesat calmly yace “To Allah ya bada sa’a yan mata, or should i say Gimbiya, don kanwar yarima ai princess ce” Khaleesat ta ɗan kallesa kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace “Ina wuni” Bude front seat Ajay yayi ganin yanda Usman ke kallonta maimakon ma ya amsa gaisuwar da tayi masa, Ajay ya kalleta for the first time in many days yace “Get in” Sauke idonta tayi don suna hada ido sai da gabanta ya fadi, tana tafiya a hankali ta shiga motar ya kulle, Usman yace “Ai kuna nan gidan nan naku har yanzu, in sha Allah ko zuwa gobe idan na gama abinda nake yi zan zo” Bai rufe baki ba Ajay yace “A’a bana gidan yanxu, i got a new apartment” Usman yace “Haba, to za dai mu yi waya, sai ka bani address din apartment din” Ajay bai kallesa ba yace “Ohk” Sama sama yayi masa sallama ya zaga ya shiga motarsa ya ja motar ya bar wajen, sai da suka yi nisa sosai Khaleesat taji yace “Ana maki magana ki dinga wani yauki kamar kubewa, to wa za ki burge? Did you know him from anywhere ne yana maki magana kina jujjuya ido kamar owl” Khaleesat taki ce masa komai kamar bata ma san da ita yake ba, bai sake cewa komai ba a motar har suka isa gida, yana parking ta sauka a motar tayi wucewarta cikin gida ta shiga dakinta ta rufe, ta gama shirin kwanciya ta dau wayarta taga miss calls din Safiyyah, zaunawa tayi gefen gado ta kirata, Safiyyah ta ɗaga tace “Ina kika shiga ina ta kiran ki?” A hankali Khaleesat tace “Mun je kai Aunty Farida Airport” Safiyyah tace “Ayya shi yasa nake ta kira inji ko she is still leaving today, nasan kina nan kina kuka ko” Khaleesat taki cewa komai wasu hawayen na taruwa idonta, Safiyyah tace “In gaya maki daxu sai ga kiran Ajay a wayana…” Khaleesat tayi shiru na kusan 5 seconds kafin tace “Kiran me? Kuma ina ya samu number ki?” Safiyyah tace “Tab, ai ina da numbersa shi ma yana da nawa da dadewa, kin tuna shi ya turo min receipt din 10M da aka tura account din ki bayan Maman Abdul sun je sun amshi kudin Abdul dake account din ki? Ai tun sannan ni dai nayi saving number sa” Khaleesat tace “Ohk, kiran me yayi maki?” Safiyyah tace “He requested for Ya Musty’s number, wai yana son yayi masa magana ko zai amince mu zauna dake a apartment din ki har mu gama Exams don zai ɗan yi tafiya” Khaleesat bata ce komai ba bayan taji abinda Safiyyah tace, can tace “Zai yi tafiya zuwa ina?” Safiyyah tace “Ikon Allah, ke kina matarsa baki san inda zai je ba sai ni?” A fusace Khaleesat tace “Ta yaya zai tafi ya bar ni ina final exams?” Dariya sosai ta ba Safiyyah, can Safiyyah tace “To ni dai kar yace na kwaso gulma na gaya maki, kar ki sa sauran mutuncina ya zube a idonsa, ki bari idan ya maki magana da kansa sai kice ta yaya zai tafi ya bar ki, ke baza ki iya zama babu shi ba gaskiya, kuma baza kiyi concentrating a exams din ba idan ba so yake ki fadi jarabawan ba” Khaleesat tace “Ni dai sai da safe” Daga haka ta katse wayar. Kamar yanda Safiyyah ta gaya ma Khaleesat hakan ne ya faru don tare suka zauna su biyu a apartment dinta for their final exams with the permission of Ya Mustapha, babu abinda Ajay bai siya ya ajiye masu a apartment din ba, sannan ga isasshen kudi da ya tura ma Khaleesat sai dai ita bata yarda baya kasar ba jikinta na bata yana nan, duk da gata ga Sophie amma duk zaman apartment din baya mata dadi, she was so bored ta rasa dalili, kullum babu wani walwala zaka sameta don ma dai karatu suke ba dare ba rana da Safiyyah, a haka har suka kare jarabawarsu ta final. Washegarin ranan da suka gama exams da yamma Safiyyah ta shirya zata tafi African Store wai tuwo da miyar vegetables zata dafa ita ta gaji da cin junk food, ita dai Khaleesat na kwance gefen gado tana danna wayarta kamar bata ma ji abinda take cewa ba, a haka Safiyyah ta bar gidan da shopping bag dinta, bayan tafiyarta da kusan minti sha biyar Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali taje jikin window ta tsaya tana kallon neighborhood din unguwan, babu abinda ya tsaya mata a rai irin yanda ko sau daya Ajay bai taɓa kiranta yaji ya exams ba har suka kare exams din sai dai ya kira Safiyyah, har daga karshe tace ma Safiyyah kar ta sake gaya mata idan ya kira bata son sani, bude kofar dakin aka yi ita dai tana kallon waje don duk tunaninta Safiyyah ce ta fasa zuwa shopping din ta dawo, amma jin Safiyyah bata fara jero excuses din dawowarta ba ga kuma kamshin turaren da ya cika dakin yasa ta juya da sauri, tsaye ta gansa ya jingina jikin side din kofar dakin ya rungume hannu, idonsa sanye da glasses baƙi irin no respect, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, a takaice yace “Congratulations” Ta wani hararesa tace “Ka ce min Allah ya bada sa’a sanda zan fara ne balle kace min congratulations yanxu, bana bukata” Tana fadin haka ta juya kamar zata yi kuka, shi dai kallonta kawai yake, can ya karasa cikin dakin cike da kasaita ya tafi har inda take tsaye, tana jin alamarsa a bayanta ta juyo da sauri ta manne da jikin window din ta kasa kallonsa, yana kallonta ta cikin Glasses dinsa yace “Rashin kunya za ki yi min?” She couldn’t say anything because he was very close to her ga kamshin turarensa da ya cika mata hanci, and her heart was racing very fast amma ba na tsoro ba, calmly yace “Ni kin ce min Allah ya kiyaye hanya da zan yi tafiya?” Ta wani kallesa ta turo baki sai kuma ta kauda kai tace “Ai ni nayi zaton auren ka tafi kayi” Ajay dake ta kallonta yace “Ohk, kawarki bata gaya maki ba kenan?” Khaleesat ta maido kanta tana kallonsa, Yace “Ur Aunt, ur Mom, the Jawwad you are chatting with, duk basu gaya maki ba?” Yanda take kallonsa haka shi ma yake kallonta directly in the eyes, speaking calmly yace “To aure naje nayi, so now ki hada kayan ki, you will be leaving for Nigeria tomorrow at noon, I will send you ur flight ticket via Whatsapp” Yana fadin haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, har Safiyyah ta dawo gidan Khaleesat na tsaye inda Ajay ya bar ta ko motsawa bata yi ba daga wajen, Safiyyah tayi cilli da mayafin jikinta tana cewa “Tirr sai kin ga ganyen duk ya langwabe kamar na yan iska, in ba dole ba me zan yi da wannan ganyen, ni da nake son fresh vegetable soup” Jin Khaleesat tayi shiru, Safiyyah ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace “Me kike yi jikin window ke kuma?” Khaleesat tayi shiru taki ce mata komai tana tafiya a hankali ta karasa gefen gado ta zauna, Safiyyah dai bata sake bin ta kanta ba ta fita daga dakin zata je tayi girki don dama duk kwanan nan Khaleesat ba wani kulata take ba tun da Ajay ya fara kiran wayarta, ita dariya ma abun ke bata sosai ba kadan ba, wani lokacin da gangan take ce mata Ajay ya kira ko da kuwa bai kira din ba. Karfe shidda saura na yamma Khaleesat ta sauko downstairs, Safiyyah dake zaune parlor tana jiran miyanta ya karasa tace “Ina za ki?” Without looking at her tace “Zan ciro kudi ne” Daga haka ta nufi kofa ta fita daga parlon ta nufi Lyft dake jiranta.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
