Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 36 By Ayshercool

Ya saki Sadik a ƙasa bayan ya caka masa almakashin, cikin tsananin tashin hankali, Al’amin ya yi kukan kura ya danƙi ɗan daban, amma wani daga cikin yaransa, ya lallaɓa ya sake maka masa gora a baya, ya gantsare yana wani irin ihu, suka yi gaba suka bar su.Ya din ga dukan gate ɗin gidan, yana ƙwalawa Abbu kira, ya koma kan Sadik, ya rungumo shi, yana jijjiga shi.Sai da garin yayi shiru, sai kururuwar Al’amin yana kiran Yaya.Maƙwabcinsu ya fito, na kusa da shi ma ya fito, aka din ga buga gidan su Al’amin, har aka tafi nemo mota, sannan Abbu ya buɗe. Sai dai ya shiga tashin hankali, ganin Sadik a kwance kamar mara rai.Cikin tashin hankali Abbu ya tafi kici-kicin fito da mota, Al’amin ya zuciya ya ɗauki Sadik a kafaɗarsa, kawai yayi gaba.Da ƙyar aka riƙe shi, aka saka Sadik a mota.Al’amin sai zubar da hawaye yake yi, ya na kiran “Yaya ka buɗe idonka ka kalleni, ka tsaya yanzu zamu je asibiti””A galabaice, Sadik ya motsa ya riƙa hannun Al’amin, sai kuma hannunsa ya saki. ko da suka je Asibiti, aka tabattar musu da Sadik ya koma ga Allah.Al’amin ya durƙusa a kan gawar, ya din ga rusa kuka, kukan da ko lokacin da umminsu ta mutu bai yi shi ba, maƙwabta na ta rarrashin Al’amin.Cikin kuka Abbu ya ce “Al’amin komai ya samu ɗa na kai ne sila, ka sa nayi rashin ɗa mai biyayya””A’a Alhaji Ibrahim, kar ka sake ka ɗorawa Al’amin laifi, kai ne babban mai laifi, kana sane sarai unguwar nan babu kwanciyar hankali, ka bar su a waje, da ka buɗe musu sun shiga gida, koman dare ai da haka ba ta faru ba”.A daren aka yi wa Sadik sutura, Al’amin gani yake yi kamar a mafarki, awannin da suka gabata suna tare amma a yanzu wai babu Sadik. Kodayeke Abbu yana da gaskiya shi ne sila, da bai ce zai bar gidan yayi tafiyarsa ba, da haka baya faru ba, dan kuwa Sadik ba ya yawon dare.Har jami’an tsaro sai da suka zo suka ɗauki bayanan abun da suka faru, sai dai Al’amin ya kasa magana.Sadik ya tara ɗimbin mutane, yara da manya matasa da dattawa wurin sallatar gawarsa, kasancewar sa mutumin kirki.Al’amin ya ji ina ma shi aka kashe, Sadik ya rayu, yayan nasa guda ɗaya tal da yake saukewa duk wata damuwarsa ya ɗauka babu ƙosawa ko gazawa, an kashe masa shi.Alhaji sammani, ya yi wa Ibrahim tatas, a kan yadda ya koma soko a kan gidansa, tare da ci wa Rahila mutunci tsaf, a kan abubuwan da take aikatawa.Ƙarshe ta shiga ta fita, ta raba abotar da aka yi shekaru ana ginata, suka rabu dutse a hannun riga, suka yi uwar watsi.Depression ya nemi ya kama Al’amin, babu wand yake ta tasa, gashi yanayin halayarsa idan ba wanda ya sanshi ya saba zama da shi ba, ba kowa zai iya masa ba, saboda miskili ne, ga nuƙufurci, ba zai taɓa cewa wani ga damuwarsa ba, shi ba abokai ba, haka ya din ga ragaita a layi, raɗaɗin mutuwar Sadik taƙi barinsa.Ya tafi wurin ‘yan sanda ya tambayi, ko sun kama wanda ya kashe yayansa, suka ce masa bincike suke yi a kai, dan har a lokacin ba su tabattar da wanda yayi kisan kan ba, kuma a ranar ba Sadik kawai aka kashe ba.Al’amin ya koma gida, yayi ta addu’a Allah ya sa a kama wanda ya kashe masa Sadik, duk da dare ne, amma a ko ina ya ga wanda ya kashe shi zai gane, dan kuwa ƙofar gidan su akwai security light.Duk bayan kwana biyu sai Al’amin yaje, tun suna sauararsa har suka fara korarsa.Ga matsi ya ƙaru daga gidansu, babu in da zai samu abinci, ya yanke shawarar fara zuwa kasuwa ya duba ko dako ya fara, sai da ya je ya tarar ashe dakon ma sai ka san wani, sai an san da kai, duk sana’ar da yayi tunanin farawa sai ya ga dole sai da jari, gashi Rahila ta cigaba da ziga Abbu, ya ƙara tsanar Al’amin wai shi ne silar mutuwar Sadik.Al’amin ya fara gajiya da yunwa da take neman tagayyara shi, ya fara zuwa gida ya ɗauki duk abincin wanda ya tarar ya cinye, idan ya tafka wannan tsiyar, sai ya gudu ya kwana a kangwaye, gashi ya koma HND tun Sadik na raye, dama shi ne yake ta fafutukar tara school fees ɗin sa kan ya rasu, yanzu kuma ga yunwa da rashin kuɗin transfort dan haka ya daina zuwa makaranta gaba ɗaya.Gashi ko a maƙwabta aka rasa wanda zai yi wa Abbu nasiha, ko su din ga taimakonsa, saboda ana ganin babansa yana da rufin asiri.Yana can garin yawonsa, kawai ya hango wanda ya kashe Sadik, a tsallaken titi, da tawagar matasa ‘yan daba, da gudun gaske Al’amin ya tsallaka titin, sai dai kan ya ƙarasa sun ɓace masa, cikin tashin hankali ya ƙarasa wurin wani mai ice ya ce “Malam dan Allah wanda ya wuce ɗin nan ina yayi?”Ya kalli Al’amin ya ce “Meye haɗinka da shi?””Yayana ya kashe da almakashi, bai yi masa komai ba, ‘yan sands suna ta nemansa””Taɓ, ka raba kanka da wannan. Madaki kenan gawurtaccen ɗan daba ne, hukuncin kisa ma aka yanke masa a gidan yari, amma muka ga an sake shi, duk ya gallabe mu, ya hanamu sukuni mu ma, sai dai ka bar wa Allah kawai” Ai Al’amin bai tsya jin ƙarshen zancen ba, ya shiga cikin unguwar ya din ga yawo, amma bai ga madaki ba.Washegari da sassafe, ya koma wurin ‘yan sanda ya gaya musu ya ga wanda ya kashe yayansa, su tafi tare da shi a nemo shi, an gaya masa sunansa madaki.Wani ɗan sanda ya kada baki ya ce “Ka san mutum nawa madaki ya kashe aka ƙyale shi?” al’amin ya ce “Ni ina ruwana da mutum nawa ya kashe, ku kama shi a kai shi kotu ni dai”.”Ko an kai shi ma, za a sake shi, ka je ka yi haƙuri haryanzu bamu tabattar da shi ya kashe shi ba”.Kasancewar Al’amin yana kan tashen balaga, ya sanya ya tsaya yana yi musu rashin kunya, aka saka wani sageant, ya zane shi aka kore shi. Hakan yayi matuƙar tunzura zuciyar Al’amin, ya din ga jin jinin ɗan uwansa ba zai tafi a banza ba.Ya din ga sintiri a unguwar da madaki yake, kasancewar ba su da nisa sosai, ya samu duk bayanin da yake son samu a kan madaki, da in da yake zama da shi da yaransa.Ya je gida ya shiga kitchen ya samo, wuƙa sabuwa gal, ya je ya ɓoye, ya saka a ransa shi ma sai ya kashe madaki, ko da kuwa za a kama shi a kashe.Sai dai aka yi rashin sa’a, Madaki bai fiye zama a unguwar ba, sai idan zai shigo yayi rashin mutunci, Al’amin ya din ga fakonsa, har ya yi wataran sa’a ya tarar yana nan.Gadan-gadan ya ratsa tarin matasan da suke ɗauke da makamai suna shaye-shaye, ya nufi madaki da wuƙa.Matasan suka mimmiƙe, amma madaki ya ɗaga musu hannu, a kallo ɗaya madaki ya gane Al’amin.Kafin ya ƙarasa gaban madaki, sani ya sanya ƙafa ya taɗiye Al’amin dan haka ya faɗi a gaban madaki, suka kwashe da wata irin dariya.Al’amin ya yinƙura zai tashi, madaki ya saka aka take masa kafaɗun Al’amin da ƙafa, yana ƙoƙarin tashi, amma cikin ƙarfin Al’amin ya tashi, madaki ya tako gaban Al’amin ya shaƙe wuyansa. Take Al’amin ya ji kamar an shaƙe shi da wata muguwar sarƙa mai nauyin gaske, a take ya ji numfashin sa na neman ƙwace masa. Al’amin ya saki wuƙar ya koma kokowar raba hannun madaki da wuyansa, madaki ya tsare shi da jajayen idanunsa da ya rambaɗa musu farin kwallin tsafi, yana ƙyaƙyata wata uwar dariya, daga bisani kuma ya tsuke rai tamau, ya ƙara tsananta shaƙe Al’amin, sai da ya ga ya daina motsi, sannan ya watsar da shi a wurin, ya kalli wani ya ce “Ku kai shi arear su ku watsar””Ba za a saita ma hanya daga duniyar ba ya ci bulus kenan?”Madaki ya girgiza kai ya ce “Yana cikin tsananin ɗacin rashin ɗan uwansa, idan aka yage shi daga sararin nan, hutawa zai yi, sai ya gane kuskuren da ya aikata na yinƙurin da yayi”Suka ɗauki Al’amin suka kai shi unguwar su, suka jefar da shi a sume a gaban wani mai kayan miya, suka ce wa mutanen wurin “Gashi nan, ajiyarmu ne, zamu din ga bibiyar sa ku kira tsohonsa ya ɗauke shi idan yan buƙatarsa”.’yan unguwa suka ɗauke shu, suka kai shi gida, Abbu yana nan, aka kwantar da shi a tsakar gida, ana shafa masa ruwa, mai kayan miya ya gaya wa Abbu abun da yaran madaki suka ce, aka shawarce shi a kan ya kai maganar wurin jami’an tsaro, amma Abbu ya ce babu ruwansa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, shi bai aike shi wurin ‘yan daba ba.Tun daga nan madaki ya mayar da Al’amin kamar karen farautarsa, ya saka rayuwarsa a gaba, wataran har cikin unguwar su yake aikawa, a nemo masa Al’amin, a kai masa shi har dabarsa, su casa shi da zalunci kala-kala, wai sa ya saduda ya nemi afuwar abun da ya yi wa madaki, dan ba a taɓa samun wanda ya yi abun da Al’amin yayi ba, ya rasto har dabarsa ya nemi ya kashe shi, yana ƙanin ƙanin bayansa.Al’amin ya kalli madaki ya ce “Ka yi kaɗan na nemi afuwarka, baƙin kare kuma in sha Allah sai na zubar maka da jini, kamar yadda ka zubar da jinin ɗan uwana da bai yi maka komai ba”Ya durƙusa ya soka wa Al’amin wata kibiya a cinyarsa, cinyar sa na zubar da jini, amma saboda azabar taurin kai, ya datse haƙoransa ya ƙi ihu.”Na fuskanci zaka yi mini amfani, na saka ka cikin yarana daga yau, zaka din ga yi mini aiki”Al’amin ya girgiza kai ya ce “Ni fa kallon kare nake yi maka, da na bika gara na yi mutuwar wulaƙanci”Ya ce “Shikenan zamu gani, dafin ciwon da nayi maka na fili da na zuciya ya isheka ka saduda”.Al’amin ƙafa taƙi takuwa, sai da kyar, ya din ga tagayyara a gari, yaran madaki suka matsawa unguwar su Al’amin, duk da suma suna da ƙasurguman ‘yan daba, amma ba sa shiga harkar faɗan matasan ‘yan daba.Al’amin ya ƙi ya karaya ya saduda, ga ƙafa yana ɗingisawa, ga yawon neman in da zai ci abinci, kullum rahiila cikin gaya wa Abbu take, Al’amin abubuwan da yake da yadda ‘yan daba suke kawo masa farmaki, sun tabbatar da cewar shaye-shaye ya fara yi, dan haka lallai ya kori Al’amin daga gidan, ya daina zuwa kan ya kuma janyo musu wata masifar, ta ce a kama masa shago a cikin unguwa ya bar kwana a cikin gidan, duk da dama ba kullum yake kwana a gidan ba.Wata ranar juma’a da yamma, Al’amin yana tafe yana ɗingisa ƙafarsa, yaran madaki suka shigo, da wasu irin mahaukatan karnuka, kuma kai tsaye suka sakarwa Al’amin su, gashi ba zai iya gudu ba, saboda ƙafarsa, suka dirar masa da cizo, ya din ga danƙar karnukan nan yana jifa da su, manyan karnuka ne sun kai biyar, wannan ya yage shi ta nan, wancan ya kai masa cizo ta nan, sai da suka ga yana neman fara halaka karnukan, ko su yi mutuwar kasko da su, sannan suka nufi Al’amin suka fito da makamai. Dan madaki cewa yayi, su kai masa wani sashe na jikin Al’amin sun cire masa.Karnuka sun yi masa kaca-kaca da kayansa, da fatarsa da cizo da yakushi, jikinsa duk jini, amma ya yinƙura ya tashi, ganin sun tsaya a kansa da makamai.Ɗaya ya shammace shi, ya sara masa wuƙa a cinya ta baya, ya hankaɗa shi ya faɗi, yana faɗuwa suka ga ɗaya daga cikinsu ma ya faɗi ƙasa jini na zuba daga jikinsa.Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon wanda ya yi aikin.Wani gabjejen mutum ne, baƙi mai jiki sosai, da jajayen ido, a yaran madaki wani ya yinƙuro, amma ya caka masa wuƙa a ciki shi ma, ya faɗi.Ya durƙusa ya ɗago Al’amin, jikinasa jina-jina, ya kalli wanda suke tare ya ce “Samo abun hawa, a kai yaron nan asibiti” ya kalli sauran yaran madaki ya ce “Ku je ku gaya wa madaki, ya zo dabata ni dodo babban sarki, ina nemansa. Na ji labarin irin ɓarnar da yake shigowa unguwar nan yana yi, kasancewar bana shiga shirgin shirmen ƙananan matasa, ya sanya ban damu ba. Sai dai na wuce a mota, a wancan lokacin na ganku kuna dukan yaron nan, wannan karon ma na ganku kun saka karnuka na cizon sa, kamar ba ɗan adam ba awanni ashirin da huɗu na bashi, ya zo yayi mini bayani, idan ya bari na taka na je in da yake sai dai uwarsa ta haifi wani. Ku ɗauke mini wannan mushen, ku ɓace daga gabana” jiki na tsuma, suka ɗauki wanda aka cakawa wuƙar suka tafi da shi.A asibiti ɗan wando kawai aka bar Al’amin da shi, jikinsa sai tsatstsafar da jini yake yi, saboda cizon karnuka da yakushi, ga raunin da yake ƙafarsa, sai da aka yi dressing raunukan jikinsa, sannan aka yi masa rigakafin cizon mahaukacin kare, dan ba a san wane irin karnuka ne suka ciji Al’amin ba, aka saka masa ruwa, sannan aka kawo masa lafiyayyen abinci daga restaurant.Dodo babban sarki, bai sake bi ta kan Al’amin ba, sai bayan magariba, ya je Asibiti da shi da yaransa, aƙalla dodo ya kai shekaru arba’in da biyar, ya girmi madaki sosai, madaki kuma ya girmi Al’amin.Ya tarar da Al’amin a zaune, hannunsa ana saka masa ruwa, ya ƙarasa gaban gadon Al’amin ya ce “Sannu ka ji” Al’amin ya jinjina masa kai.”Yaron nan ba shi da imani ko kaɗan, tayaya zai saka a sakarwa yaro karnuka su je shi, zai ci ubansa da ni yake zancen, zan gani zuwa dare idan bai zo ba, sai na kashe shi wallahi” ya sake kallon Al’amin ya ce “Kai ba kai ne kuka tare a unguwar nan shekarun baya ba? Kuna zuwa islamiyyar dogon bene, kai da ɗan uwanka ba?””Ni ne””Ina ɗan uwan naka? Meya haɗaka da madaki kuma, na ga kai ba irin su bane” Al’amin ya yi shiru, sannan ya ce “Kashe mini Sadik yayi, ba abun da yayi masa, ni kuma na ga ba zan haƙura ba sai na kashe shi nima”Dodo ya ce “A’a dama yayanka ne aka ce mini an kashe a layin dawaki? Madaki yana fama da gigin daba, tun da ya samu masu tsaya masa, ya je prison ya haɗu da wanda suka fi shi rashin mutunci yake abun da ya ga dama. Zan ci ubansa kuwa yanzu me ka ke son ayi masa gaya mini”Al’amin ya ce “Kawai sonake shi ma ya mutu, in soka masa almakashi kamar yadda ya yi wa Yaya” yayi maganar cikin damuwa.Dodo ya dafa kafaɗarsa ya ce “Kwantar da hankalinka, yanzu dai fatanmu ka samu lafiya, za aje a sanar da babanka, ya zo asibiti ya duba ka, a samu mai jinyarka”Ya girgiza kai ya ce ‘A’a kar a gaya masa, zan koma gida kawai””Na ji ba za a gaya masa ba, amma sai ka zauna an kula da kai tukuna”.Madaki hankalinsa ya tashi, jin an kashe masa yaronsa na hannun damansa, a hannun wanda ba zai iya ɗaukar fansa ba, dan gaba da gabanta.Yana tsuma, suka tafi in da Dodo yake zama, aka ce sai dai su bishi asibiti, baya nan.Asibitin gwamanti ne, Amma amenity dodo ya biya aka kwantar da Al’amin.Madaki cikin girmamawa ya ce “Na amsa kira ranka ya daɗe”.”Ka san wannan ai?” Dodo yayi maganar yana nuna masa Al’amin.”Na san shi””Daga rana mai kamar irin ta yau, idan kai ko wani daga cikin yaranka, ya sake taɓa shi, ko tsoratar da shi, wallahi sai na ƙarar da tarihin mutum a bayan duniya. Bana shiga harkar ƙananan dabarku, amma aka kuma ratso unguwar nan, aka taɓa shi, wallahi sai na yi abun da ba a zata ba. Ka durƙusa ka bashi haƙuri a kan cin zarafin da ka saka aka yi masa, ka sanya karnuka suka yi masa illa, yana ɗan adam ba dabba ba, sauran abun da ka yi masa kuma kai da shi ne”.Madaki ya kalli Dodo ya ce “Ni zan bashi haƙurin?”Wani wawan mari, dodo ya ɗauke madaki da shi, da sai da ya kife ƙasa, “Ka shiga hankalinka, ka san da wa ka ke magana kuwa? Har ka mutu ba zaka yi iskancin da nayi ba, shekarata goma a ƙiri-ƙirin lagos, ba wani ɗan iskan da ban gani ba, ko ban sani ba, ka bashi haƙuri, ko na ciyar da macizaina namanka”Madaki ya kalli Al’amin, shi ma ya kalleshi, ya kalli dodo sannan ya ce “Ka yi haƙuri, bisa abun da na saka aka yi maka da karnuka”.Al’amin ya ce “Ko ka bani haƙuri ko baka bani ba, gaba da ni da kai sai ranar da na rama zubar da jinin ɗan uwana da ka yi” sai da duk suka kalli Al’amin, Al’amin ba dai taurin zuciya ba.Madaki ya fice a muzance, a gaban yaransa aka saka ya bawa Al’amin haƙuri, an wulaƙanta shi ƙarshen wulaƙanci, dan haka ya ƙullaci abun a ransa.Al’amin har ya kwana huɗu a asibiti, Abbu bai neme shi ba, kullum abincinsa mai rai da lafiya yake samu ya ci, ga dodo shi ma kullum sai ya zo duba shi, ya yi ta yi wa Al’amin hira, har yaransa suka fara mamakinsa, dan Al’amin ba wani sakin jiki yake da shi sosai ba.”Al’amin da gaske kana son ka rama abun da madaki yayi maka?”Al’amin ya ce “Eh””Tunani mai kyau, amma ka sani shi ƙarfe dole sai da ɗan uwansa ƙarfe, yanzu an sallameka, mu je mu kai ka gida, sai ka din ga zuwa dressing, na biya kuɗin dressing ɗinka, duk abun da ka ke buƙata zan baka adress ɗina, a nan cikin unguwar, ka je ka same ni”Al’amin ya jinjina kai ya ce “Na gode sosai” ya dafa kafaɗarsa ya ce “Kar ka damu Aminullahi”Da ya koma gida, babu wanda ya tambayi ina yaje, tsawon kwanakin nan, ga jikinsa duk raunuka,  amma babu wanda ya tambayi ya yake, sai ƙanwarsa shahida da suke uba ɗaya.Tun da dodo yayi wa madaki iyaka da Al’amin, ya samu sassauci, ya cigaba da sabgoginsa, bai kuma sake bi ta kan dodo ba.Da ƙyar ya samu aiki a wurin wani mai shayi, yake yi masa wanke-wanke da abun da ba a rasa ba, idan ba ya nan, da shi da ƙanin mai shayin ne suke riƙe wurin, hakan ya sanya ya fara rage damuwa da halin da yake ciki.Sai dai ƙanin mai shayin ya nemi da su haɗa kai da Al’amin, su ɗan din ga ɗaukar wani abu, Al’amin ya ce ba zai yi ba, ba a jima ba, yaron ya yi wa Al’amin sharri wai yana ɗebar masa kuɗi, kuɗi kusan dubu talatin, mai shayi ya kai Al’amin wurin ‘yan sanda aka daka aka yi rarrashin ya ce shi bai ɗauka ba, ba kuma zai amsa yayi ba. Aka yi ta kai ruwa rana, da ƙyar case ya mutu, bayan ya shafe kwanaki a hannun ‘yan sanda.Yamma liƙis, ya je ya samu ƙanin Habu mai shayi, har rumfar mai shayi, ya karya shi a hannun dama, aka kuma cafke shi zuwa wurin hukuma, aka nemi Abbu, amma ya ce ba ruwansa, tun da kangarewa ya ɗauka.Ɗaya daga cikin matasan da suke yi wa dodo aiki, wato Walid, shi ya gaya masa halin da ake ciki. Da kansa yaje station ya karɓo Al’amin.Ya saka shi a gaba, yana yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, ya aikata abun da yayi. Ya kwashe komai ya gaya masa.Dodo ya ce “To daga yau, kar ka sake zuwa ka nemi wata sana’a, duk abun da ba ka da shi, ka zo na baka. Na fuskanci tsohonka baya yinka, ni kuma ehhh kawai ka kwanata mini a rai, tausayi kake bani, kana rayuwa da kai da wanda aka bugoku cikin samfurin jini ɗaya, an ɗaye maka shi, ta ƙarfin tsiya. Amma ba komai, zaka rama ne”Tun daga lokacin Al’amin ya zama yaron dodo, wurinsa yake zuwa ya karɓi kuɗin abinci, ya biya masa kuɗin registration, ya mayar da shi makaranta ya cigaba da HND, dama shekarunsa ba su kai shiga University ba, shiyasa ya fara zuwa poly.Dodo harkar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi yake yi, babban distributor ne, har garuruwa yake rarrabawa kaya.Bai damu da harkar daba ba, sai wannan sana’ar, Abbu bai taɓa tuhumar ya aka yi Al’amin ya koma makaranta ba, wace sana’ar ya fara duk bai tuhume shi ba.Dodo yana da manyan yara da matasa, ciki har da sa’an Al’amin mai suna Walid. Sai dai Walid ya tsani Al’amin ganin yana neman ƙwace masa fada a wurin dodo babban sarki.Ko aike babu wanda ya isa ya aiki Al’amin, dodo ne kawai yake sa shi ko ya hana shi, haka zai zauna a cikin su, su yi ta shaye-shaye suna ƙuƙƙula kayan maye, amma ba ruwansa da su, ko sigari bai taɓa gwada sha ba.Idan yayi dare a yawonsa, sai ya tafi gidan dodo, yayi kwanansa, dodo har safarar makamai yake yi, babban criminal sosai da sosai.Komai Aminullahi, komai Aminullahi, lokaci lokaci, ya kan tuntuɓi Al’amin, ko zai iya yafe wa madaki, amma ya ce har abada, har sai ya rama abun da yayi masa ya kan yi murmushi ya ce “Aminullahi kenan, in dai zaka zauna a haka, ba ka shirya ɗaukar fansa ba, ƙarfe dole sai da ɗan uwansa ƙarfe, roba ba ta tasiri a kan ƙarfe” baya gane mai dodo yake nufi, dan haka sai dai ya bi shi da toAl’amin ya ce masa dan Allah ya samo masa sana’a, ko wace iri ce zai din ga yi. Dodo ya ce masa zai duba.Duk abun da Al’amin zai yi, dodo bai yadda yaransa su yi masa wani abu na horo ko cutarwa ba, hatta kaya idan Al’amin ya cire, sai ya ce Walid ya wanke masa, wanda kan zuwan Al’amin shi ne na gaban goshi.Sannu a hankali, ya fara aiken Al’amin kai kayan shaye-shaye wasu wuraren, cikin dare idan motar kaya ta isao, haka zai ɗauke shi, su tafi su karɓo kaya.Wataran ya aike shi, hukumar hana sha da fataucin, suka kama shi, aka din ga tuhumar Al’amin, ya ƙi faɗan wanda ya aike shi da kayan, sai da aka kwana biyu ana nemansa, hankalin dodo ya tashi, aka bincika aka gano masa shi a hannun hukuma.Ya je ya karɓo Al’amin, sannan ya ce “A bashi kayan da aka ƙwace ayi musu kuɗi zai saya, idan suna da wasu ma a haɗa masa ya saya. Kuma hakan aka yi.Ya yi ta yi wa Al’amin faɗa, a kan dan me, ya zauna a hannunsu, bai saka an neme shi, ya fito da shi ba?.Ta kai ta kawo, Dodo yana tafiya da Al’amin wurin ‘yan siyasa, dan a nan ne suka haɗu da Indabo, a lokacin baya shan komai.Duk da wannan abubuwan da suke wakana, Al’amin yana zuwa gida, ya ga Abbu, ko da kuwa zai yi masa faɗa ya kore shi, yana zuwa ya ganshi.Yaran dodo sun sha attempting koya masa shaye-shaye, amma ya ƙi, tun Walid yana jin haushin Al’amin, har ya haƙura, manyan yaran dodo suka saka masa mai zamani, ya kori gwamantin Walid dan haka idan yana son zaman lafiya ya kiyayi mai zamani”Dodo ya din ga dariya, ya ce “Kuma zamanin Aminullahi dogo ne a wurin dodo ba, bana tunanin akwai wanda zai ture gwamantin sa a wurina, dan mai dogon zamani dan haka mai laya” yayi maganar yana kallon Walid.Aka haɗa baki aka ce “Ka kiyayi mai zamani” suka yi abun da sigar raha.Al’amin ya je gida, domin ganin Abbu, amma ya tarar baya nan, Rahila kuma tayi baƙi, ya shiga kitchen ya ga an yi uban abinci, ya kwaso fulasan yayi gareji da su, ya zauna ya hau ci, duk da ya san na baƙin ne.Yana cikin ci, sai ga wata ‘yar yarinya ba ta fi shekaru biyu ba, ta zo in da yake tana kallonsa, ta tsuguna ta saka hannu a kwanon, tana tsintar abincin tana ci.Ya kalleta, sai ya tuna jaririyar ummi da ta rasu, yanzu ga shi duk su ukun babu su.Sai ya din ga bata abincin a baki, amma hakan bai hanata saka hannu a kwanon miya ba, haushi ya kama shi, kamar ya kwaɗe ta, ya kama rigarta yana goge mata hannun, kawai ya ji salatin Rahila.Ya ɗaga kai ya kalleta ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, na shiga uku jama’a ku taimake ni, zai lalata ‘yar mutane, Allah ya sa ba yi mata komai ba” Sai yayi saroro yana kallonta, ya rasa gane mai take nufi, wanda ta yi hakan ne, dan huce takaicin tozarcin da yayi mata, na cinye abincin baƙi.Shahida ta ce “Mama wanke wanke nake yi, ina hango su ba abun da yayi mata, abinci kawai yake bata””Ƙarya ne rufe mini baki dan ubanki, ke kin taɓa ganinsa yana ɗaukar yara ne, balle ba da abinci a baki, ni na ga abun da na gani” dama ‘yar ta maƙwabta ce, uwatta ta kawota ta fita.Ta tara wa Al’amin jama’a, wai ya saka wa yarinyar hannu a wando, da idonta abun da ta gani kenan.Duk dakiya da dauriyar Al’amin, jikinsa ya hau rawa, ya kasa ko motsi daga wurin, mutane suka taru a garejin gidan, Abbu dama sallar la’asar ya fita, a masallacin yana lazumi aka je aka kirawo shi.Cikin tashin hankali ya danƙo Al’amin, ya kwaɗa masa mari ya ce “Me ka yi wa ‘yar mutane? Al’amin lalacewar taka har ta kai ga haka? Ni zaka zubarwa mutunci a idon duniya”Shahida tana kuka za ta yi magana, Rahila ta hanata, wata mata ta cire pampers ɗin yarinyar ta duba ta, ta ce “Wannan yarinyar fa babu abun da aka yi mata, lafiyarta ƙalau da ya taɓata ma, ba za a ganta a haka ba”Al’amin ya ƙwace rigarsa daga hannun Abbu, ya fice, yana jin zuciyarsa zata tarwatse, bai zarce ko ina ba, sai gidan dodo, suna ganin sa suka din ga tambayar sa, menene saboda yadda idonsa ya yi jawur, amma ya yi shiru ya ƙi kula kowa.Walid ya kira dodo a waya, ya sanar masa ga mai zamani ya zo, cikin ɓacin rai da tashin hankali.Ba a ɗauki lokaci ba, sai gashi, ya ce “Waye ya taɓa zuciyar magajin dodo, wa ya taɓa mini Aminullahi?””Al’amin ya ƙi magana sai huci da ajiyar zuciya, ga wani gumi da yake yi”Dodo ya ce “Walid””Allah ya taimaki babban sarki””Narka jan tablet, ka bani” Walid ya narka ya bashi, ya miƙa wa Al’amin.Ba tunanin komai, ya karɓa ya shanye ya ajiye kofin, wani zuuuuu ya fara ji a kansa, ya fara ganin hazo-hazo, a hankali ya fara ganinsu bibbiyu, daga haka bai sake sanin abun da ya faru ba, sai sha biyun dare ya farka.Yayi sallolinsa, ya ci abinci, dodo ya ce “Magajin dodo, ba zan takuraka na ji menene ba, amma ya ka ke ji yanzu damuwar ta tafi gaba ɗaya?”Al’amin ya girgiza kai alamar a’a.”Duk wannan dogon zangon da ka yi? Bari na baka wani haɗin”Ya naɗa masa wiwi, ya kunna ya bashi, sai dai zuƙa ɗaya Al’amin ya hau tari, kamar zai shiɗe ya ce “Ƙara gwadawa, ba zaka yi ba” ya din ga zuƙa a hankali, tun yana tarin har ya daina. Ayshercool 08081012143

Back to top button