Halysaah Page 202 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 202…Ajay na komawa part dinsa ya tarar da Khaleesat zaune bedroom tana sanye da hijab dinta bata cire ba tana shan sauran fruits din da ya bari, kallonsa tayi tana murmushi tace “Amma yanxu kawai sai Mami ta ganta a dakin ya Jawwad gobe da safe?” Ajay yace “To ba dakin mijinta bane” Khaleesat tace “Uhmm, a can Palace fa ake son ta tare shi yasa zata bi su Aunty Faridah idan za su koma” Ajay yace “Nan ma palace ne” Khaleesat na murmushi tace “To bata gudo ba da ka kai ta dakin?” Ajay ya cire jallabiyan jikinsa yace “Ina wasa da ita ne” Er dariya Khaleesat tayi don har tayi imagining abinda Hadiyah zata mata gobe, she was soo happy maida auren da aka yi, ko ba komai Jay zai dena shigo mata Bedroom kai tsaye yanxu, murmushi kawai take tana shan grapes dinta tana kallon Ajay kasa kasa don he is just wearing short, sai kuma ta kauda kai, ya zauna gefenta yana kallonta yayi kasa da murya yace “Meye wannan kuma a jikin ki kamar labule wife” Khaleesat ta wani kallesa tace “Labulen ne” Bai tanka ta ba ya gyara zamansa ya dau remote ya maida tasha zuwa na football, a hankali ta cire hijab din jikinta ta ajiye, kamshin turarenta ya doki hancinsa, amma still yayi maintain bai dauke idonsa daga kan TV ba, ita dai kallonsa kawai take babu ko kiftawa amma yaki kallonta, by just looking at his muscular body she is feeling weak already, slowly ta matsa kusa da shi ta jingina jikinsa tana shafa broad chest dinsa tana kallonsa, can kasan ranta kuwa da ta sanin magungunan da ta sha take cause ita kadai tasan what is going on in her body, ganin bai cire idonsa a kan TV ba ta kasa daurewa ta shagwabe murya tace “Yaya” Ya kalleta a hankali yace “Slushie” Tuni nut din kansa suka kwance gaba daya ganin irin kallon da take masa, dagota yayi ya zaunar da ita jikinsa yana kallon kirjinta, ta lumshe ido cause she is feeling his quick reaction, gently ya sauke rigar jikinta, ita dai kallonsa kawai take da sexy eyes, ya daga idanuwansa ya kalleta suka hada ido, murya can kasa yace “I love you so much Jeeddah” Slowly tayi wrapping hannunta a wuyansa cikin sanyin murya tace “I love you too hubbyna” nan suka gangara zuwa wata duniyar daban yana bata hot romance, daga karshe kawai ganinsu a saman gado khaleesat tayi, duk da yanda gabanta ya fadi haka nan ta basa hadin kai yayi yanda ya so da ita a wannan daren cause she was also desperately in need, kuma bata masa gardama ko raki ba, sai ma hadin kai da ta basa. Da asuba Ajay na sanye da Jacket kan kayan jikinsa don snow sosai aka yi cikin dare, ba don sallan asuba ba babu abinda zai banbaresa daga jikin Khaleesat, ya fita part dinsa ya sauka downstairs as usual su yi sallan asuba tare da Jay kamar yanda suka saba tun sanda aka sallamesu a asibiti, ko a asibitin ma tare suke sallah, a duk sanda ya sauka kasa zai tarar Jay na jiransa a parlor, amma yau sai bai gansa a parlon ba, zaunawa yayi kan kujera ya lumshe ido memories din jiya da daddare na dawo masa, yafi 15 minutes zaune parlon yana jiran saukowar Jay amma shiru bai sakko ba, ganin lokaci na wucewa kawai ya tashi yayi sallansa shi kadai a parlor, still bayan ya idar bai ga Jay ya sakko ba, mikewa yayi ya wuce sama ya nufi part dinsa, Khaleesat na kwance cikin duvet din kan gadon, ya karasa ya zauna kusa da ita ya sauke duvet din yana kallonta yayi kasa da murya yace “Sanyi kike ji?” Taki yarda su hada ido tana kara shigewa cikin duvet, yana murmushi ya dagota ya kwantar da ita jikinsa yana shafa bayanta a hankali yace “Let me give you warmth” Ta lumshe ido tayi lamo tana shakkan kamshin jikinsa, ya kai bakinsa kunnenta kamar me rada yace “Yesterday night was sweet wife, thank you so much” Ɗan murmushi tayi taki bude idonta shi dai sai kallonta yake kamar zai hadiyeta, cikin sanyin murya tace “Good morning My prince” ya kara rungumeta yace “Good morning Slushie” A hankali tace “Should I make you some tea?” Yayi kasa da murya yace “Are you not stressed already wife” Sai a sannan ta ɗan kallesa, da sauri ta kara rufe fuskarta a jikinsa don wani sabon kunyansa take ji, and this immediately turned him on cause he just can’t get enough of her, ta zame jikinta daga nasa a hankali tace “Bari in kawo maka shayi” Daga haka ta mike ta dau hijab dinta dake kan kujera ta saka sannan ta fita daga dakin ya bi ta da kallo, Khaleesat na fita daga part dinsa ta dinga mamakin jiya da daddare, the pain was just for some seconds bayan nan kuma ita kadai tasan abinda tayi experiencing jiya, it’s something she can’t get over cause it’s stuck in her brain, yanxu ma tuna hakan kadai is making her feel so weak, gashi ko kadan bata ji wani gajiya ba kamar yanda take ji always, downstairs ta sauka tana isa kofar kitchen taji alamar akwai mutum a ciki, ta ɗan koma baya, sai kuma ta leka kitchen din ta yanda wanda yake ciki bazai hangota ba, Jay ta gani tsaye yana making cup din tea, juyawa tayi da sauri ta koma sama, direct ta nufi bedroom dinsa tayi knocking gently, jin shiru ta ɗan bude kofar slightly tana leka ciki, kwance taga Hadiyah a saman gado idonta lumshe, hakan yasa Khaleesat ta shiga cikin dakin, Hadiyah ta juya a hankali suka hada ido, murmushi Khaleesat tayi ta karasa har bakin gadon tace “Amarya kin tashi” Hadiyah ta hade rai taki ce mata komai, Khaleesat sai gintse dariyarta take ganin yanda Hadiyah ta daure fuska, Khaleesat tace “To shikenan, dama na shigo mu gaisa ne, tunda baza ki kulani ba byeee” Hadiyah ta mike zaune da kyar, ta jingina jikin gado, sai a sannan Khaleesat tayi noticing idonta da suka ɗan kumbura alamar tayi kuka, kana ganinta kasan she is stressed, Hadiyah bata yarda su hada ido ba da kyar tace “I trusted you but you betrayed me Halysaah, me yasa kika min haka?” Hawaye ne suka ciko idonta, Khaleesat ta zaro ido ta marairaice tace “Let keep joke aside Hadiyah, da gaske ban san an maida auren ku ba fa, duk abinda na gaya maki jiya to abinda Ya Junaid ya gaya min ne, i know nothing, kilan boye min yayi kar in gaya maki, haba er uwa, kinsan baza a hada baki da ni ayi maki haka ba ai” Magana Khaleesat take yi amma saura kadan dariya ya kwace mata ganin yanda Hadiyah ke matsar kwalla, cikin rawan murya Hadiyah tace “Wallahi Ya Jawwad mugu ne….” Da sauri Khaleesat ta dakatar da ita tace “A’a ni dai kar ki zagar min yayana a gabana….” Dai dai nan aka bude kofar dakin, Khaleesat ta juya da sauri bata yarda su hada ido da Jay ba ta karasa bakin kofar tace “Ina kwana Ya Jawwad?” Ko jiran ya gama amsawa bata yi ba tayi maza ta fice daga dakin tana murmushi ta kullo masu kofa, Hadiyah ta hade rai, ya ajiye shayin hannunsa ya cire jallabiyan jikinsa, tana kallonsa sau daya taji gabanta ya fadi sosai, da kyar ta fara kokarin sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta tana cikin sakawa taji sa kusa da ita, ta gama saka hijab din ta marairaice zuciyarta na bugawa tace “Don Allah ka bar ni zan fita in je in gaida Mami ne….” Ba abinda yace mata, zata nufi kofa ya tafi ya rufe kofar, Hadiyah tayi da ta sanin saukan da tayi daga kan gado, sai yanxu da ya damke ta a edge din gado ta gane ashe daren jiya Jay bai yi komai ba somin tabi yayi, although the first 20 minutes of yesterday night tare da shi sai da yasa ta mance kasar da take tsabar yanda ya sarrafata ta tafi wata duniyar, amma daga baya da ya canza salo sai da ta gaya ma yan garinsu don babu sassauci a al’amarinsa, it’s just 2 years and some month of not having intimacy amma ji take kamar bata taɓa yi ba wannan ne karon farko, gashi yaki bin ta a hankali, yanda ya saba wujijjigata a baya yanxun ma hakan yake bi da ita babu sararawa, ko jin magiyarta baya yi don idonsa sun rufe, yanxu ma kuka sosai Hadiyah ta dinga yi masa tana rokonsa yayi a hankali amma bai ma san tana yi ba, duk da azaban da take ji hakan bai hanata jin sumbatun da yake ba, kana ganin yanda yake yi da ita kasan he misses a woman so much, haka ya tara mata sabon gajiya bayan ko gama recovering daga na jiya da daddare bata yi ba, sai kusan karfe bakwai da rabi ya samu nutsuwa, seeing how exhausted she was hawaye sai gangarowa yake ta gefen idonta ya lumshe idonsa ya dora forehead dinsa a nata, yana sauke numfashi a hankali murya can kasa yace “I’m sorry, I missed u so much” Gefe ya koma ya kwanta ya rungumota jikinsa ya kankameta tana shesshekan kuka, duk kukan da tayi jiya bai ce mata uffan ba har bacci ya dauketa, yanxu kam lallashinta ya dinga yi calmly, ya dago kanta suka hada ido, a hankali yace “I love you so much” a haka bacci ya dauketa a jikinsa don dama bata samu isasshen bacci jiya ba. Wajen karfe goma Ajay ya fito zai je gaida Mami, he just woke up from sleep ya tuna bai gaida Mami ba, yana isa kofar dakin da take yayi sallama sannan ya bude kofar ya shiga, bai ganta a dakin ba, ya karasa ciki ya zauna don duk tunaninsa tana bandaki, after sitting for 10 mins ganin bata fito ba ya mike ya fita daga dakin, yana isa main corridor sai ga Jay ya fito daga dakinsa, daga sama har kasa Ajay ya dinga kallonsa, can yace “An samu fitowa kenan su Jawwad, sallan asuban za mu yi yanxu ko kuma mu bari mu hada da na gobe kawai don naga kamar lokaci ya wuce” Jay yaki kulasa har ya wucesa sai kuma ya dawo yace “Kuna da pain reliever a bangaren ku?” Ajay yace “What pain are they relieving?” Jay yaki tankasa ya nufi bangaren sa, knocking kofar parlon Jay yayi, Khaleesat da ta fito daga bedroom zata je gaida Mami amma duk kunya take ji don tun da ta zo bata taɓa zuwa gaisheta this late ba, walking slowly ta karasa ta bude kofar parlon, tana ganin Jay tace “Ai baya ciki Ya jawwad” Jay yace “Ba wajensa na zo ba, wajen Halysaah na zo” Tana murmushi tace “To ina jin ka Ya jawwad” Yace “Dubo min pain reliever a ciki pls” Tace “Ohk, tohm” Juyawa tayi ta koma cikin daki, ba a dau lokaci ba ta dawo da maganin ta mika masa ya amsa yace “Thanks” Daga haka ya juya ya tafi, ta zauna kan kujera tana murmushi ita kadai, after a while ta mike ta fita daga part din zata je gaida Mami sannan taje ta masu breakfast. Ajay na zaune downstairs Khaleesat ta sauko tana kallonsa tace “Kasan Mami bata gidan nan kuwa?” Ajay ya juya ya kalleta, sai kuma ya mike yace “How?” Tace “Ba gashi na je gaisheta ba ina zaton tana bandaki ina ta zaune dakin, kawai sai nayi noticing babu box dinta a dakin” Ajay yayi shiru yana kallonta, Khaleesat ta karaso cikin parlon ta zauna tace “Uhmmm kilan fa ta gane Hadiyah har ta tare ne, tunda dakin Ya jawwad isn’t far from her’s ai, innalillahi ni dai wallahi har naji kunya” Ajay ya zauna yana dariya, Khaleesat ta wani kallesa don da kyar ka gansa yana dariya in ba na shakiyanci ba ko na mugunta. Mikewa Khaleesat tayi zata bar masa parlon don har cikin ranta taji kunya duk da ba ita bace, jin Footsteps a sama ta daga kai taga Jay ne ke saukowa kasa, juyawa tayi ta wuce kitchen tun bai karaso cikin parlon ba, Jay na saukowa ya nufi Ajay yace “Where is Mami, naga bata dakinta” Ajay yayi keeping serious face ya gyara zama yace “To gida da ango da amarya ba dole tayi tafiyarta ba, da na sani kawai hotel na kai maka ita, kaga da har yanxu tana gidan nan bata je ko ina ba, yanxu ina za mu fara neman Mami Jawwad….”




