Karfe A Wuta Chapter 23 By Ayshercool
Tun da ta hau adaidaita sahu, tunani take yi, yaya za ta yi ta samu dubu hamsin ta kai, a sako shi. Ta san muddin aka kai shi NDLEA case ɗin tsayi zai yi, ba zata musa an ganshi da kayan maye ba, tun da yana sha.Ta koma gida tayi salla, amma abun duniya ya isheta, ta kasa ko cin abinci, tausayinsa duk ya cika mata zuciya, jikinsa yayi ruɗu-ruɗu da cizon sauro, gashi almu sun nuna ba abinci ake ba shi ba.Baba kuwa abun duniya ya dame shi, yadda ya ji kunya a idon iyayen Alhaji mu’azzam, ace sun kawo kuɗi sun gama magana, amma ya aurar da ita ga wani, ko gaya musu bai yi ba, ya rasa me yake yi masa daɗi, har sai da zakiyya ta fahimta ta ce “Baban su Saifu, wai lafiya kuwa? Tun da ka yi baƙi jiya, gaba ɗaya ka rasa nutsuwar ka”Ya sauke numfashi ya ce “‘yan uwan Alhaji mu’azzam ne, suka zo suna bayar da haƙuri a kan jin su shiru da aka yi. Wai za ayi mata visa ayi auren a tura ta can”Waro ido tayi ta ce “Sai kuma ka ce musu me?”.”Na aurar da ita” yayi maganar a sanyaye yana sake jinjina wautar da ya yi.”Ba a haka fa, sai ka ce musu Allah ne ya ƙaddara a hakan, amma akwai yayyenta, ko hafsa ba sai a maye gurbinta da ita ba, hafsa ba ta fi jauhar komai ba ma? Ai bai kamata a bari ya tafi haka ya tsallake gidan nan ba”.”Zakiyya, kun saka na yi abun da yake damuna, na cuci ‘ya ta ba gaira babu dalili, na aurar da ita ga mutumin da ba na kirki ba, na rasa yadda aka yi, lamarin nan ya faru, kunyar haɗuwa da jauhar ma nake yi, na kasa komawa gidanta, zuciyata zafi take yi mini”Zakiyya ta ce “Jauhar fa an gama babinta, sai a fuskanci ‘yan uwanta, bai kamata a bari mutumin nan ya tafi haka ba””Zakiyya, dan Allah ki bari na samu nutsuwa, ni ban san ma meyake damuna ba, dan Allah ki bari na ji da abun da yake damuna”Ta kwantar da murya ta ce “Babu wani abu fa da yake damunka, kai ne ka ke neman ɗorawa kanka matsala, amma komai mai sauƙi ne, idan ya dawo ba sai a lallaɓa shi a bashi Hafsa ba ya aura”.Baba ya ce “Na ji, amma dai yanzu ki ƙyaleni” ya ɗauki hularsa ya saka ya fita.A tsakar gida ya tarar da su surayya, aiki duk ya kacame musu, aiki ba aiki, wanda da jauhar na nan, ita kaɗai take yi suna mimmiƙe kamar kifi a fridge.Suna ta yi masa a dawo lafiya, ya dawo da baya ya tsaya, ya kalle su ya ce “Surayya, kun je gidan ƙanwarku kuwa kun ganota?” Duk suka yi shiru, suka kasa amsa masa.”Yakamata ku je ku ga in da aka kaita, ita ma ta ji daɗ”.Mama ta fito daga kitchen ta ce “A’a fa, ka san dai yadda mijinta yake, ba zuwa gidanta ne ba za ayi ba, kar mutum ya je ya illata shi”. Yayi shiru bai ce komai ba.Jauhar kuwa kasa nutsuwa tayi, har sallar nafila tayi mussaman tana fatan Allah ya sa kar a kai Al’amin NDLEA.Duk yadda ta kai ga tunani, ta rasa mafita, bacci ya gagareta, a gidanma ya ta ƙare da sauro, ina ga shi da yake can, ta yi ta fatan Allah ya sa su saya masa buredin nan su bashi, sai kuma ta tuna ba ta bayar da kuɗin da za a saya masa ruwa ba, gaba ɗaya ta shiga damuwa, haka har garin Allah ya waye.Ta ji ƙarar babur ɗin malam lawan alamar ya fita, tana ta tunanin ko shiga za ta yi gidan, ta yi wa maman halimatu magana, ko akwai taimakon da za ta iya yi mata.Tana cikin tunanin, maman halimatu ta shigo, suka gaisa jauhar ta ce “Yanzu nake tunanin zuwa gidan wurinki”.Maman halimatu ta ce “Yaya kin same shi ɗin?””Eh yana can, sun ce na kai dubu hamsin a bayar da belinsa, amma wallahi bani da ita””To yanzu ya za ayi?”Jauhar ta ce “Wallahi ban sani ba, shi nake ta tunani””To ki kira gidanku mana ki faɗa” ta girgiza kai ta ce “A’a, daga yin auren sai na fara kai musu complain, a’a gara na rufa masa asiri na samu ya fito””Aikuwa Jauhar sai ki yi tunanin in da zaki samo kuɗi”.Tayi saurin cewa “Dan Allah ko akwai wanda zaki haɗa ni da shi, ya sai carfet ɗina?”Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Eh akwai wata dillaliya, kusa da titi gidanta yake”Cikin ɗoki jauhar ta ce “Mu je ki rakani maman halima”.”Shikenan, amma Jauhar kina me ki ka auri mutumin nan, gashi daga aurenku kin fara wahala, da kyanki da ƙuruciyarki, kin auri wanda zai wahalar da ke”.Jauhar ta yi murmushi ta ce “Maman halimatu ku daina aibata shi dan Allah, ku din ga yi mana addu’a””To Allah ya kyauta” Jauhar ta saka hijjabi, suka tafi gidan dillaliya, sai dai bata nan, aka kirata a waya, ta ce sai yamma zata dawo, zata biya gidan maman halimatu, su je gidan Jauhar ɗin.Wunin ranar jauhar kamar ta yi hauka, saboda dillaliya ba ta zo ba, sai tunanin halin da yake ciki take yi.Sai wajen ƙarfe biyar sannan ta zo, ta ga carfet ta ce zata saya dubu goma.Maman halimatu ta ce “Haba sahura, wane irin dubu goma, bai fi sati biyu ba ca carfet ɗin sabonsa dubu kusan sittin ne fa”.”To ku ɗauka ku mayar kasuwar mana, tun da an shimfiɗa ai ya zama taoho”.Jauhar ta ce “Bakomai na yadda” ba ta da burin da ya wuce ta ga Al’amin ya fito.Sahura ta ce ‘Saboda kin ban tausayi, na saya dubu sha biyu, bari na baki kuɗin.Maman halimatu ta ce “Wallahi sahura shiyasa da yawanku ba kwa arziki dillali, duk cuwa-cuwar ta ku, a tsiyace ku ke mutuwa”Sahura ta ce “Oho miki dai”Ganin ta fito da kuɗi da yawa, ya sanya jauhar shiga kitchen ɗin ta, ta ɗauko blender da set na tukwanenta masu kyau, ta cewa dillaliya su ma ta saya.Maman halimatu ta ce “Jauhar, idan ‘yan gidanku suka gane kin sayar da kayanki fa?”Sahura ta ce “Wallahi uwar su halimatu ke ‘yar baƙin ciki ce, ke kika saya mata?”.Jauhar kamar ta yi kuka ta ce “To ya zan yi maman halimatu, bana son zamansa a wurin nan, sauro ma kawai ya ishe shi” Sahura ta ce “Allah sarki yarinya, Allah ya mayar da alkhairi, idan an tashi sayar da wasu ma ki kira ni”Da ƙyar ta bawa Jauhar dubu ashirin da huɗu gaba ɗaya. Wanda a ƙalla sun kai kayan dubu ɗari da wani abu.Ƙoƙarin nemo wani abun take, maman halimatu ta hanata, ta ce ta bari gobe ta je station ɗin, ta basu haƙuri ta ce musu abun da take da shi kenan.Jauhar ta ce “Ki na ganin za su karɓa kuwa?””Za su karɓa mana, ai kin yi ƙoƙari” kamar ta janyo wayewar gari, ta din ga addu’a Allah ya sa su karɓa su sake shi.Da wuri ta gama komai, wurin ƙarfe goma da rabi ta fita, shi ma maman halimatu ce ta hanata fita da wuri, ta ce mata ba da wuri suke zuwa ba.Suna ganin Jauhar suka ce “Madam ya aka yi ne? Kin sake dawowa ganinsa ne?”Ta ciro kuɗin ta ce “Gashi dan Allah yallaɓai ku sake shi, sukaɗai na samo dan Allah ku yi haƙuri”Ya zuba mata ido ya ce “Shekarar ki nawa ne?”Ta ce “Na kusa shiga sha bakwai, dan Allah ku yi haƙuri””To ai ba zamu iya baki belinsa ba, kin ga mace ce ke, kuma yarinya, Allah ya sa ya daina abun da yake ko dan saboda ke, karɓi kuɗinki, ba zamu sake shi a kan wannan ɗan kuɗin ba, kotu ma zamu kai shi”Kawai ta saka kuka, “Dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba dan Allah kar ku saka a kai shi prison”Ɗaya daga ‘yan sandan ya ce mata “Yi haƙuri ki daina kuka, da wasa yake yi miki, an zo belinsa ma, ke ki ke tayar da hankalinki, ko mun kama shi zamu sake shi”Kasa daina kukan tayi, hannunta riƙe da kuɗin, wani ɗan sanda ne ya fito, da alama babba ne, bayansa kuma walid ne da Al’amin da wani mutum.Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta zubawa fuskarsa ido, da take a ɗaure babu walwala.Walid ya ce “Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a gidanka, tayi mini rashin mutunci””Wannan fa me aka yi mata take kuka?””Sir, matar Viper ce” ya kalleta ya ce “Hajiya me aka yi miki ki ke kuka?”.”Ce mini suka yi na kawo dubu hamsin za a sake shi, na kawo kuma suka ce mini wai kotu za su kai shi” ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka cike da yarinta.Ya kalli ‘yan sandan ya ce “Waye ya ce ta kawo dubu hamsin””Sorry sir, dan ta daina zuwa aka gaya mata haka”Nan ya hau yi musu faɗa, suka din ga bayar da haƙuri, Al’amin kamar bai santa ba, yayi gaba. Da sauri ta bi bayansa, tana ta yi masa magana yayi shiru.Walid ya ce “Haba mai dogon zamani, ka tsaya ka saurareta mana”A fusace ya waiwayo ya hau ta da masifa “Ban ce miki kar ki sake zuwa wurin nan ba? Kin san suwaye ake kawowa wurin nan? Mutuncinki ne a ganki a nan?” Sai da ta ja da baya a tsorace ta rufe fuskarta, saboda razana da masifar da yake yi mata.”Wai Aminu meyasa ka ke yin haka? Da uban waye ya damu da kai, yake ta taka? Macen kenan haka zuciyarsu take, ko dan matar gidanku ba ta da kirki kowa ma haka yake?” Tsaki ya yi yayi gaba.Walid ya ce “Yi haƙuri mu je, rabu da shi ya ƙarata, kar ki sake tayar da hankalinki saboda shi” suka tari a daidaita sahu suka tafi gida.Da suka je gida, ta shiga gidan ta bar shi da Walid.”Aminu, dan girman Allah ka rage jaraba, kalli yadda duk ta rikice saboda kai, kar ka yi wasa da damar da ka samu, ka saka ta tsaneka dan Allah”Ya tsaya ya ƙarewa ƙofar gidan malam lawan kallo, yayi ƙwafa ya shiga gidan, ba tare da ya tanka Walid ba.Jiki na rawa ba tare da ta yi fushi ba, ta kawo masa tea da buredi.Ya gama baccinsa ya tashi, ya yi wanka, ya gama ya ga ta kafa masa ƙusar rataye soso a banɗakin, har zai rataye yayi tsaki ya yar da soson a kan sabulun ya fito.Ya canza kayansa ya fito falo, Satar kallonsa take yi, kamar ya ƙara kyau, kwana biyun da ya yi a tsare ba ya shan komai, kamar ya yi kyau sosai. Sai murna take yi ya dawo gida.”Ke!” Ta ɗago ta kalleshi.”Meye sunanki ne?””Jauhar”Ya kalleta ya ce “Me? Angela?”Murmushi ta yi ta ce “Angela kamar wata mage, sunana Jauhar”Guntun tsaki ya yi ya ce “A saka muku normal suna, sai dai a saka ƙaƙale-ƙaƙale da iyayi, ni ba zan iya ba””To ka kirani da fatimata fatima zahra” wani irin zirrrr ya ji a jikinsa, fatima zahra, sunan mace mai girma da daraja a idonsa, Ummansa abar ƙaunarsa, duk da ba ta duniyar, amma idan ya ji sunan har wata tsuma yake yi.Ya maze ya ƙarewa falon kallo, ya fita tsakar har zai wuce ya kalli kitchen ɗin ta sannna ya ce “Zo nan”Ta fito ta ce “Gani””Wa ki ka sayar wa carfet ɗinki da kwanukanki?”Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, yaya aka yi ya gane ko ya sani? Sai ka ce aljani?Ya ƙare mata kallo ya ce “Ina jinki, ya aka yi ki ka samu wannan kuɗin da ki ka kai? Ina kuma abubuwam da na tambayeki? Ki ka yi mini ƙarya kuma jikinki ya gaya miki”Kamar munafuka, haka ta zayyane masa komai.Bai ce mata komai ba, ya fita.Sahura na tsakar gida, tana hira ita da wasu coustomominta, kawai ta ga wasu irin zaratan matasa su uku, a tsakiyar tsakar gida da manyan gorori kamar za su farauta.Ta tashi ta ce “Lafiya malam? Me ku ka zo yi mini a gida. Wannan ai…. Haɗiye maganar tayi, da ya sako ƙafarsa cikin isa tsakar gidan.Yana shigowa idonsa ya sauka a kan carfet ɗin, a shimfiɗe a falonta.Ya ce “Liti, ku naɗo mini carfet ɗin nan”Ta waro ido ta ce “Malam lafiya?” Walid ya zaro wuƙa ya ce “Ki ka kuma magana, sai kin ɗaware daga sararin nan yanzun nan” daga ita har sauran matan, suka hau tsuma.Kamar abun banza, suka din ga yi mata cilli da kujeru, suka naɗo carfet.Viper ya ce “Dubu sha biyu ki ka saya ko?” Ta jinjina masa kai.Ya ce “Ɗaukko mini sauran kayan da ki ka karɓa a wurinta” jiki na tsuma ta shiga ta kwaso su.Ta ajiye masa a tsakar gidan, ya ce “Ɓarauniyar zaune, daga yanzu ki san abun da zaki din ga saya, ban da a nutse na zo miki, sai na saka an zana miki awarwaro a hannu, yadda gobe ba zaki sake zalunci ba. Liti ba ta kuɗinta”.Liti ya zaro kuɗi zai bata, Al’amin ya ce “Wait, ta riga ta shimfiɗa a ɗakinta, ka cire dubu uku a kai, sannan ka sake cire dubu biyu zan cika ku wanke mini carfet ɗin ku kai mini gida.Haka kuwa aka yi, suka cilla mata kuɗi, suka kwashe kaya suka tafi.Jauhar ta na yi wa wasu stone work, dan kuwa matar ta fara kawo mata kayan tana yi, hakan yana ɗebe mata kewa.Ba ta yi aune ba, ta ganshi a tsakiyar falo, hannunsa da kaya, ya dungurar mata da su a tsakiyar wurin ya ce “Daga yau, ko cokali ki ka kuma sayarwa, saboda ni sai na ɓata miki rai, fiye da yadda ki ke tunani”Baki buɗe ta ce “Master, karɓowa ka yi, kuɗinta suna wurina fa, Allah zai kaman…””Na ba ta kuɗinta, ko tsintsiya ki ka sake sayarwa, zan gane kuma ranki sai ya ɓaci”.A hankali ta ce “Na shiga uku”.***Matasa ne a ƙalla su biyar, dukkanin su, babu wanda ya gaza ko ya wuce shekaru ashirin da biyu, suna sanye da tufafi masu nuna datti, gashin kansu da yanayin fuskarsu kuwa, babu tambaya sun bayyanar da tsantsar rashin ji a tattare da su, sai bushe-bushe suke yi, suna shewa.Wani matashin ne ya diro ta saman katanga, gaba ɗaya suka nutsu, suna yi masa sannu da zuwa.”Kai gayu akwai matsala wallahi” gaba ɗaya suka tattara masa hankalinsu suna sauraren sa.Ya ce “Kaii, wai ashe mai zamani ne ya tare a unguwar nan kusan sati biyu bamu sani ba?”Ɗaya daga cikin su ya miƙe ya ce “Ƙarya ne wallahi, me yake yi mana a unguwa”.”Nustu, ni ma ban sani ba sai ɗazu, mai unguwa na ji yana maganar, sai za su je police station, ko a sasanta ayi zaman lafiya da shi, ko ya bar unguwar nan”.Ɗayan ya yada sigarin hannunsa ya tashi ya ce “Guduma gaskiya kar dagus ɗin ka ya janyo mana matsala, ya san waye mai dogon zamani kuwa?”.”Guys mafita ɗaya ce wallahi, kun san ba a sarki biyu a zamani ɗaya ko?””Me ka ke nufi?”Guduma ya ce “Dole ɗaya ya bi ɗaya””To waye zai bi wani?””Kwanciyar hankalinmu da nustuwarmu, shi ne mu yi mubayi’a, samunsa ma a unguwar nan wani security ne, zai sa a din ga jin tsoranmu”Wani matashi ya ce “Ƙarya ne wallahi, babu wanda ya isa ya zo unguwarmu mu yi masa mubayi’a ba a isa ba”.”Kai Kwano, bari na yi maka wani lissafi, duk sarkin da ya zo garinka ba da ziyara ba, ya shafe awanni arba’in da takwas, a irin harƙallarmu, to ɗayan biyu, ko dai ɗaya ya bi ɗaya, ko kuma a yaƙi juna, a kama sarki ɗaya da mutanensa a matsayin ganimar yaƙi, mu rayu a matsayin bayinsa, harƙalar da Mai zamani yake yi, ta ci uban tamu, ba sa’anmu bane ba, mu yi abun da ya dace, idan kuma mu ka bari rigima ta ɓalle, wallahi a unguwar tamu, zamu rayu kamar bayi ne amma ku yi tunani”.Can Al’amin kuwa yana zaune a station, ga mai unguwar da yake da sauran mutanen unguwa.Yana zaune yana kallonsu, suna ta ɓaɓatun gaskiya ya tashi ya bar musu unguwa, saboda bad record ɗin da suka samu, a kansa daga in da ya baro, kuma nan ma ya zo yana yi musu shaye-shaye kar ya ɓata musu yaran unguwa.Suka yi suka gama, yayi shiru kamar mai zancen zuci, suka yi suka gama, D.P.O ya ce “Malam Aminu, ka ji abun da mutanen unguwar da ka tare suka ce, me za ka ce?” Sai da ya ja wasu seconds, sannan ya ɗaga kai, ya kalle su da jajayen idanunsa masu matuƙar kwarjini, duk suka yi shiru, suna sauraren sa, ya ce “Haryanzu ban ji an ce ga abun da na yi ba ai. Ba zan ce komai yanzu ba, gobe in Allah ya kaimu, mu haɗu a nan ƙarfe huɗu na yamma, zan faɗi abun da na yanke”.D.P.O ya ce “Ina fatan ba wata ɓarnar zaka yi ba?””Ba na sara sai an zo ramina” daga haka bai kuma cewa komai ba, ya tashi ya fice, ba tare da ya jira iznin hakan ba.D.P.O ya ce “Abun da nake so da ku shi ne, ku bi yaron nan a sannu a samu maslaha, kar ku yi wani abu da zai tunzura shi, ya fara yi muku fitina a unguwa, ku bari mu bi a hankali mu sasanta, ɗan ƙasa ne yana da damar zama a in da yake so, ku bi a hankali ayi musu sulhu”.Shi kuwa yana fita, ya kira wayar liti, bugu biyu ya ɗaga. “Liti, nan da mintuna arba’in zuwa awa ɗaya, ina son ka tattara mini, duk wasu yara marasa ji a arear unguwar nan da nake da kewayenta, duk wanda ya yi gardama, ayi masa ɗaurin igiya da swizaland gaba da baya, a layin gidana nake son su taru”.Liti ya amsa da “An gama shugaba”Sahura kuwa, sai da ta je har gidan maman halimatu ta ƙare mata cin mutunci, a kan yadda Al’amin ya je har gida, ya ƙare mata tanadi, a kan ta sai kayan matarsa, maman halimatu ta din ga ba ta haƙuri, ta ce su shiga gidansa su yi magana da jauhar ɗin, amma ta ce ai ba mahaukaciya ba ce ita, da zata shigar masa gida ya ritsata ya kashe.Jauhar tana ta aikin stone, ta ji ana wata irin busa a unguwar, kamar da ƙaho ake yin busar, irin bushe-bushen da aka din ga yi, ranar ɗaurin aurenta, dan haka gabanta ya faɗi ta shiga cikin tsoro.Sannu a hankali, hayaniya ta fara cika layin nasu, da surutan matasa, ɗaki ta gudu ta rufe ƙofar falo, dan tunani ta fara yi, ko yaran madaki ne, gashi ba waya ce da ita ba, balle ta kira Al’aminKafin ya ƙarasa layin gidan, liti ya kira shi a waya, ya sanar masa sun fara taruwa matasan, dan haka bai bi ta cikin ba ya bi ta baya.Jifff! Ta ji dirar abu a tsakar gida, ta katanga ya diro gidan, ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar falon, amma a rufe ya jijjiga ya jijjiga amma ya ji a rufe. Ya shiga bugun ƙofar kamar yaƙi, ƙulewa tayi a ɗaki, ta hau addu’a, tare da tunanin ta ta ta ƙare, yaran madaki sun zo neman Al’amin, ko sun zo sassarata.”Ke malama ki zo ki buɗe mini ƙofa” sai da ta ji muryarsa, sannan ta fito ta buɗe, ta kalle shi, ta leƙa tsakar gida ta ce “Ai ban san kai ba ne, biyoka aka yi ne?” Wani irin kallo ya yi mata, ya ce “Matsa ki bani wuri” ta matsa ta bi bayansa tana surutu “Master ka daina dirowa ta katanga dan Allah, gaba ɗaya na tsorata wallahi, na zata madaki ne, suka zo nemanka na ji sai busa ake yi ga warin kayan shaye-shaye…… Haɗiye maganar tayi, da ya waiwayo yana yi mata kallon warning.Ta ce “Yi haƙuri, ka ga abokanka sun dawo da carfet ɗin, wai wanke shi suka yi, amma dai yakamata na je na bawa dillaliyar nan haƙuri, ai ka ga an shiga hakkinta, har gida ta zo tayi wa maman halimatu masifar abun da ka yi” ɗakinsa ya shiga, ya kulle ƙofar ya saka sakata ya bar ta a bakin ƙofa.Sai abun ya bata dariya, kafin awa ɗaya matasan nan sun kusa cika layin nan, sai hayaniya suke yi.Malam lawan kuwa, a waya matarsa ta kira shi, ta ce kar ya kuskura ya dawo yanzu, ‘yan daba sun cika layin nan.Jauhar na ɗakinta, tana aikinta, ta ji yana buɗe gate, a razane ta fito saboda yanayin bushe-bushen da ake yi, ya tabattar mata da akwai matsala.Yana fita wurin yayi tsit, kamar ba su ne suke hayaniya ba da.”Sai da kai sarki, ƙaramin dodo magajin babban, ko ma in ce ka ɗara shi. Mu na yi maka maraba da zuwa wannan unguwar, mun fito ƙwanmu da kwarkwata domin yi maka mubayi’a”. Cewar guduma yana geɓare baki, yanayin yadda yake maganar kawai a buge yake.Viper ya goya hannunsa a bayansa, ya ce “Manyanku sun kai ƙarata a kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai ni da ku zan yi wannan yarjejeniya.Abu goma a cire bakwai a tara da ɗaya zan gaya muku, a bi iyaye, ayi caji kaɗan saboda lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa, a kiyayi taɓa kayan wani. Babu zubar jini a tsakanin ku, ko duk wani wanda yake unguwar nan, abu na ƙarshe mafi muhimmanci da fari salin alin na so zama a unguwar nan, wataƙila na ɗan lokaci na baku wuri, amma tun da abun ya zo da haka, sarki biyu ba zai yi sarauta a zamani ɗaya ba. Ko dai mutum ya yi mubayi’a ko ya bar unguwar nan. Kar kuma a kuskura a matsi ramina idan ba haka ba, zan yi ɓarna. Mu haɗu da shugabannin dabar Unguwar nan da kewayenta gobe a station ɗin unguwar nan, domin yarjejeniyar zaman lafiya. Kuna iya samfewa”Su ka din ga yi masa kirari, yana jin kansa yana sake fashewa.Bayan sun watse, maman halimatu ta shigo, tana ba ta labarin abun da sahura ta zo ta yi mata.Jauhar ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri maman halimatu, dan Allah ki bata haƙuri, ba yadda zan yi, na so mayar mata ma da kayan, ya ce idan na sake sayar da wani abu, zai ɓata mini rai. Wallahi yana ankare da komai, ko cokali na sayar zai gane, ni har tsoro yake bani, bari na baki dubu goma a kuɗin, ki kai mata ta ƙara ki bata haƙuri dan Allah”Maman halimatu ta ce “To shikenan, Allah ya kyauta” ta bata dubu goma ta kaiwa dillaliya, ita kuma ta bata kyautar dubu biyu, sauran kuɗin kuma ta ɗan yi musu cefane dan kuwa shi babu ruwansa.Washegari tun ƙarfe biyu, su mai unguwa suka koma police station, suna jaddada dole a kori Al’amin, dan jiya kafin su je gida ya rigasu zuwa, ya tara musu dandazon ‘yan daba a unguwa.Al’amin bai je ba, sai ƙarfe huɗu tare da rakiyar su walid, da kuma matasan yara ‘yan shaye-shaye da sun kai ashirin da wani abu.D.P.O ya ce “Lafiya, waɗanan fa?”Al’amin ya kalli mai unguwa, ya nuna masa guduma ya ce “Ka san wannan? Ko ba ka bani amsa ba ɗanka ne, meyasa ba ka kore shi daga unguwarka ba? Ko dan shi ɗanka ne?. A wannan ba wannan matasan wakilai ne da suke jagorantar wasu yaran a ƙarƙashin su, wanda duk a cikin unguwarka suke, kana nufin a sati biyu da zuwana duk ni na lalata su? Har na tare a unguwar nan, ba su san waye ni ba, sai jiya da na saka a tara mini su.Dama can kuna da lallatun yara, harƙallata nake, ba na lalata ɗan kowa, duk ɗan wanda ya lalace, dama lalataccen ne. Ina sake maimaitawa ba na harbi sai an matsi ramina ko in da nake.Ga mafita zan bayar, wadda ba zan ƙara ko rage wani abu daga abun da zan faɗa ba.Mafita biyar ce ba uku, ko dai a haɗa a kore ni, da ni da yaran nan, ko kuma ku yi wa gidana kuɗi ninki uku, yadda zai isheni na sai wanda ya fishi, na bar muku unguwa, idan ba haka ba……. Ba na ƙarasa magana sai dai na aikata.Duk sai suka yi ɗif D.P.O ya ce “Mai unguwa mai ku ka yanke?”Shiru suka yi ba su ce komai ba, D.P.O ya ce “Tashi ka ja zugarka ka tafi, babu wani abu in sha Allah”.Ya miƙe ya ce “Galibi yaran nan secondary school drop out ne, wasunsu idan son zuciya ne ya kai su wannan halin, wasun su laifinku ne, ko dai ku nutsu ku gyara rayuwar matasan yaran nan, ko kuma su cigaba da lalacewa kuna rusa al’ummarku da hannunku” yana gama maganar suka fice da shi da su.D.P.O. ya ce “Yaron nan fa ya san abun da yake yi, jiya kuna barin wurin nan, daga can unguwar su, Aka kira ni aka ce a gargaɗe ku, babu ruwanku da shi, yaron ‘yan siyasa ne, dan Allah ku lallaɓa ku zauna lafiya da shi.Bayan sun bar station ɗin, wani irin ɓacin rai ya din ga cizon zuciyarsa, a duk lokacin da aka samu matasa ire-iren sa, al’umma ba su da wani burin da ya wuce, yin watsi da shi, da nesanta kansu da ire-iren su, bayan su ne ƙashin bayar lalacewar ta su.Yau abun na sa ya fi na kullum, domin kuwa a buge ya dawowa jauhar, wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, ya wuce ɗakinsa, ba ta kula shi ba ta koma gefe ta zuba masa ido.Washegari da safe shiru bai fito ba, ta leƙa ɗakinsa, ta tarar da shi a kwance yana bacci, gefensa ga kwalin ashana da na taba, ga kwalabe.Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, a hankali ta fara magana “Sun san da haka suka aura mini kai, Allah na roƙi ka bani mafita ka zaɓa mini shi, Allah ka kawo mini mafita, Allah ka shirya mini shi, Allah shiriya taka ce, Ni da shi duk bayinka ne, Allah bai gagari ikonka ba, Allah ka shirya min mijina. Allah ka sa ya daina abun da yake yi, Allah kar ka sa ya mutu yana saɓa maka” ta yi maganar tana kuka.A hankali ya yi juyi, satchets ɗin ƙwayoyi, suka zubo daga aljihun gaban rigarsa, ta saka hannu ta kwashe su, da kwalaben, ta hau caje ɗakinsa, duk wani nau’i na abun da ba ta yarda da shi ba, sai da kwashe daga ɗakin.A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa, ita kuma ta fice daga ɗakin.Da ƙyar ya iya tashi, dama bayan sallar asuba, ya sake yin shaye-shayen.A yunwace, ba tare da ko wanke baki yayi ba, ya hau cin abinci, saboda kayan shaye-shayen sun rarake masa ciki, ji yaya ko tsayuwa ba zai iya yi a kan ƙafafuwansa ba, sai da ya gama ci ya dawo dai-dai.Ya shiga banɗaki, ya wanke bakinsa ya fito falo, ko ɗaga jauhar ba ta yi ba, balle ta kalleshi.Ya je gabanta ya miƙa mata hannu.Ta ɗago ta kalleshi. “Bani abun da ki ka caje mini ɗaki ki ka ɗauka” gabanta ne ya faɗi, mutumin da yake bacci ya aka yi ya san ta ɗauka?.”Bani mana””Na zuba a shara an zubar!”
