Litattafan Yaki

Gwarzon Sadauki Littafi Na 1 Complete Document By Abdulaziz Sani Madakin Gini

Description/Story:

Gwarzon Sadauki Littafi Na 1 Document Written By Abdulaziz Sani Madakin Gini

 

Description

Kurkuku ne wanda aka gina dakunsa da katangarsa da zallan duwatsun wuta. Kofofin gidan gabadaya da tagoginsu an yi su ne da bakin mummulallen karfe mai kaurin kamu guda. Tsayin katangar wannan kurkuku kamu sittin ne don haka duk wani fursuna da ke cikinsa bai taba tunanin haurewa ba. Akalla akwai zaratan dakaru guda dubu daya da đari biyu. masu gadin wannan kurkuku wadanda su kansu ababen tsoro ne saboda kwarjininsu gami da surarsu ta manyan sadaukai domin ido ba mudu ba ne amma ya san kima.
A daidai wannan lokacin fursunoni na tsaitsaye a tsakiyar wannan kurkuku suna yar hada- hadarsu kamar yadda suka saba. Wasu suna wasan motsa jini wasu hira suke yi!wasu kuma suna kai kawo. Dama kullum an ware musu irin wannan lokaci domin samun nutsuwa. Kwatsam! Sai suka ji motsin bude katuwar kofar gidan wacce tsawonta da fadinta kamu sittin-sittin ne. Karar bude kofar ta cika dajin gabadaya da amsa kuwwa kai ka ce wani katon dutse ne ya mirgino da gudu. Ita dai wannan kofa ana budeta ne da wata irin na’ura mai dauke da kaca da kuma hakoran mawanin karfe mai juyawa. Dakaru ashirin ne ke iya juya mawanin sannan kofar ta bude a tsawon dakika dari uku da sittin.
Kofar na gama budewa sai fursunoni suka ga dakaru kimanin guda arba’in sun tuso keyar wani mai laifi wanda aka daure hannayensa da kafafunsa da manyan sasari kai ka ce giwa a ka janyo.
Shi dai wannan mai laifi ya kasance matashin saurayi wanda shekarunsa baza su haura ashirin da shida ba. Ya kasance kyakkyawa ne mai kirar sadaukai. Fuskarsa cike take da murmushi kawai sai kalle-kalle yake yi yana duban tsawon katangar gidan da kuma tsarin kofofin da tagogi.
Bayan an shigo da wannan saurayi tsakiyar kurkukun a lokacin da aka rufe kofar shigowa sai aka tsayar da shi cak aka fara kallon kallo tsakaninsa da Sauran fursunonin gidan. Kowa sai ya tsaya ya daina abin da yake yi. Su dai fursunonin gidan mamaki suke yi kuma suna tambayar junansu suna cewa wannan kuma wane takadari ne haka har da za a daure shi cikin manyan sarkoki. A saninsu duk wani gawurtaccen ma laifi a duniya idan aka kawo shi wannan kurkuku birnin Kisra risina yake ya kama kuka da nadama to amma shi wannan gashi da murmushinsa ya shigo ko kuwa bai san Irin masifar dake ciki ba ne.
Wata irin muguwar rayuwa ake yi cikin wannan kurkuku wacce mai karfi ne kadai yake tsira. Ba a raba abinci a cikin nutsuwa sai masu Karfi sun fara dibar nasu sannan in ya yi ragowa marasa karfi su diba. Idan mutum ba samu ba sai dai ya kwana da yunwarsa. A kullum akan dauki gawa guda biyu ko uku a cikin wannan kurkuku saboda bakin zaluncin da ke faruwa a tsakanin fursunonin.
Idan fursunoni za su kwana suna yaki a tsakaninsu ko kallonsu dakaru ba za su y ba. amma a da zarar fursuna ya karya doka guda daya take dakaru za su ufe shi da luguden duka sai sun ga ya suma sannan za su kyale shi kuma a dauke shi a kai shi wani kuntataccen daki wanda ko kwanciya zai yi ba zai iya mike kafafunsa ba kuma daki ne cike da shara, tsutsa ga doyi sauro da kudaje ma sun ishi mutum masifa.
Ana cikin wannan kallon kallo tsakanin bakon fursuna da sauran fursunonin gidan kenan sai wata kofa daga can wani bangare ta bude, shugaban dakarun gidan ya fito tare da wasu tsirarun dakarunsa masu take masa baya suka durfafo inda bakon fursuna yake.
Shi dai Shugaban dakarun wannan kurkuku ya kasance wani garjajen kato mai sura irin ta mutanen farko, Kallo daya za ka yi masa ka san cewa sadauki ne kuma jarumin gaske mai fasa taro. Shigarsa ta fita dabam da ta sauran dakarun gidan domin rigarsa, takalmansa da doguwar safar hannu duk na karfe ne, Takubba biyu ne rataye a bayansa.
Duk jikinsa a murde yake cike da kwanji ga jijiyoyi burdin-burdin. Sai da suka iso daf da bakon fursunan yadda tazararsu ba ta wuce taku biyu ba sannan suka tsaya cak, shugaban dakaru da bakon fursuna aka yi kallon kallo na tsawon dakiku biyar sannan Shugaban dakarun ya yi dan guntun murmushi ya dubi bakon fursunan ya ce.
“Sunana Gadaraz ni ne shugaba a wannan kurkuku Ya kai bawa Insam ina yi maka barka da zuwa gidan mutuwa. Labari ya iske ni cewa sau biyu kana samun nasarar guduwa daga can kurkukun cikin gari ana kamoka da kyar to ka sani nan ba a iya guduwa. Duk fursunan da aka shigo da shi nan sai dai a fitar da gawarsa amma bai įsa ya fita a raye ba. Yau tsawon shekaru goma sha hudu kenan da kafa wannan kurkuku ni da jama’ata muna gadinsa babu wani fursuna da ya taba karya wannan tarihi. Ka sani muna da dokoki guda tara a gidan nan. Dokoki biyar daga ciki idar ka aikata su za a yi maka hukuncin dukan kawo wuka gami da horo mai tsanani, Ragowar dokoki guda hudu kuwa hukuncin kisa ne a kan su. Ina mai yi maka gargadi da ka kiyaye wadannan dokoki wadanda za a sanar da kai su yanzu take idan kana son ka tsira da lafiyarka da rayuwarka.”
Koda gama fadin hakan sai shugaban dakaru Gadaraz ya dubi wani Badakare ya ba shi umarmi.
Badakaren ya bude baki ya ce.
“Doka ta farko a gidan nan ita ce. ”

File Name   Gwarzon Sadauki Littafi Na 1…
Title    Gwarzon Sadauki 1
Author    Abdulaziz Madakin Gini
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Advanture Story
Published Date    07/03/2024
File Size    40Kb
Format Size    TXT
Phone No
Download Gwarzon Sadauki Littafi Na 1 Document By Abdulaziz Sani Madakin Gini

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

  • Gwarzon Sadauki Littafi Na 2 Complete Abdulaziz Madakin Gini

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button