Hausa novels

Abban Sojoji Page 61 Book 2 Complete Hausa Novel

Abban Sojoji Page 61 Book 2

The Father Of Soldier

Written By: Boss Bature

komawa cikin bedroom ɗinta tayi tana ta faman sharar hawaye ranta na kuna,wuri ta samu ta zauna daga gefen gadonta tana ƙarashe kukan nata,babban takaicinta guntun gashin da Sgr ya bar mata da kyar in zaiyi parking da ribbom,koma yayin ba lalle ribbom din ya tsaya ba,ta jima tana azaune tana matsar kwallar bakin ciki,kafin daga bisani ta miƙe tare da nufar wurin dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta acikin madubin,cikin shessheƙar kuka tace”Meyasa bai aske gashin duka ba yabarmun kwalkwali?me zanyi da guntun gashin nan daya barmun?ban son gashin!na tsani ganin shi,’ita kaɗae take ta faman sambatu rai atsananin 6ace,

 

Kwankwasa ƙopar ɗakin nata akai,a tsiwace tace”Wanene”!

Muryar junaid taji daga waje yana cewa”It’s me junaid,tun ɗazu fa nake jiranki,ki fito mu tafi na sauke ki,’a ƙagare yake maganar don ya gaji da jiranta,

 

Ita gaba ɗaya ma ta manta da batun zuwa makarantar,sai da junaid ya tunasar da ita,

hannu tasa tana share hawayenta tace”junaid ka jira ni,acikin mota yanzun nan zan fito,”

Amsa mata yayi da”Okey,” sannan ya juya tare da barin kopar dakin nata,

 

Sai da tafara shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito tare da ɗaukar hijab ɗinta dake ajiye gefen gadon ta zura ajikinta

 

Cikin sauri ta fito ɗauke da school bag ɗinta,ta fice waje wurin harabar ajiye motocinsu,hannu tasa tare da buɗe motar junaid ta shiga daga ciki ta zauna,

ɗan kallon fuskarta yayi tare da cewa”Reesh,na jima ina jiranki,bansan me ya tsayar dake ba,gashi ma har kinyi late,ina fata dae lafiya?”

daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa”lafiya lou ba wani abu,mu tafi kawai ina ƙara makara,”

ajiyar zuciya ya sauke tare da jan motar suka bar gidan.

Ita kuwa Hayaam dama tunda taga Sehrish ta nufi part din sgr da coffeen ta sulale ta shige dakinta don kar a gano abunda ta aikata.

 

*HOSSANA*

 

Zaune take saman gadonsu ta takure kanta sai faman shessheƙar kuka takeyi,ta sanya uniform ajikinta amma taƙi tashi ta zura hijabin,ta hana kanta duk wani jin daɗi,

 

Fitowa jahad tayi daga cikin toilet tana kallonta gwanin ban tausayi tace”Hossana,dan Allah kidaina wannan kukan,duk kinbi kin takure kanki,ni nasan cewa ƴa omar ba hakanan ya daina zuwa wurin mu. Ba,Abubuwane suka yi mashi yawa shi ya sanya bai samu halin zuwa ba,’

 

muryarta na rawa tace”jahad ba zaki gane bane,bazan ta6a samun kwanciyar hankali ba in har bansa ya omar a idona ba,Allah in har baizo ba yau,zanci shinkafar 6era ne na mutu kowa ya rasa,’

dariya jahad ta fashe da ita,hakan yasa hosana ɗaure fuskarta tana jifarta da harara tace”jahad dariya kike mun ko?

tsagaitawa tayi da dariyar tana girgiza kai tace”hosana dole nayi dariya,shinkafar 6era fa kika ce?

ɗaure fuska tayi tana murguɗa mata baki,

Murmushi kawai jahad tayi tare da komawa wurin closet ɗinsu,ta buɗe tare da ciro uniform ɗinta ta shiga zura su ajikinta,shaf shaf ta kammala shiryawa,ta ɗauko school bag ɗinta,sannan ta dawo wurin hosana tace”tashi mu tafi kada mu makara,”

Girgiza kai hosana tayi tace”Jahad ku tafi kawai,ni zan zauna a gida,saboda ko naje ba gane karatun zanyi ba,’

Zuƙunnawa jahad tayi agabanta tace”pls hosana ki daina sa damuwa aranki kinji?ni da kaina yau zan nemo maki ya Omar,’

jin abunda jahad tace yasa hosana sakin murmushi tace”dagaske Jahad”?

ɗaga mata kai tayi alamar eh tace”nayi maki alkwarin,duk inda yake indae yana acikin garin nan saina nemo maki shi,”

Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hosana,jiki na rawa ta tashi ta ɗauko hijabinta bayan ta zura safarta da takalmanta suka fuce atare,

 

A waje suka samu motar osman na jiransu,bayan sun shiga ya tashi motar ya fuce dasu daga cikin gidan,hosana sai murna take jahad tace zata nemo mata Omar,batasan cewa ita da wasa ta faɗa mata ba don ta sanyata farin ciki ne kawai,

 

Wuraren ƙarfe 12 na rana,jirginsu hajiya azeema yayi landing daga lagos,kanal yousouf ne tare da su irfan suka je tarbosu,a lokacin hayaam suna a kitchen tare da azmee suna shirya lunch ɗin gidan da kuma na tarbar baki,daga kasa ƙafarka acikin main palour ɗin zaka ji daddaɗan ƙamshin abincin da suke girkawa ya gauraye ko’ina,

 

Cike da son jin gulma hayaam tace”Aunty azmee,wai Uncle ɗin nan nasu da zaizo daga ƙasar turkey,yana da aure ne”?

Azmee tace”a’a bai ta6a aure ba,ina tunanin ma ko budurwa bai ta6a ajiyewa ba,”

jinjina kai hayaam tayi tare da cewa”tabɗijancen amma da alama zaiyi ji da kai,”

murmushi azmee tayi tare da cewa”yarda kike tunani ba haka yake ba,Abusufyan wayayyan mutun ne,ta wani 6angaren ma bai ɗan jin magana amma dai nasan yanzu ya kimtsu tunda girma ya kama shi,amma lokacin baya da yake zuwa mana nan, yarda kikasan junaid haka ɗabi’unshi suke,da yake shi rainon goggonsu ne,’

murmushi hayaam tayi tana ɗan ta6e baki tace”Amma aunty azmee,ita wannan yarinyar sehrish,yakamata ace aikinta ya qare acikin gidan nan,tunda gani nazo kuma zan jima anan ne,ni a ganina bai kamata tana yawo acikin gidan nan ba,ita kaɗae ƴar matashiyya da ita,ya kamata ace tana gaban iyayenta yanzu,’ta ƙarasa maganar tana faman yatsina fuska,ta zuba ma azmee ido tana jiran jin me zatace,

 

shiru azmee tayi saboda bata da amsar da zata bata,

Cigaba da magana hayaam tayi”Yarinyar ta cika rawar kai sosai,yakamata ta tsaya a iya matsayinta na ƴar aiki mana,ni ina ganin akwai abunda take hari acikin gidan nan shiyasa ta liƙe har ta samu matsayi a wurin babban yaya,”

 

“Hayaam muyi sauri mu kammala aikin girkin nan,lokaci yana ƙure mana,”da gangan azmee tace mata haka,don ta dakatar da ita daga yi mata zancen Sehrish,don ita ta tsani gulma arayuwarta,

ta6e baki hayaam tayi,aranta kuma taji haushin yarda azmee ta katse mata hanzarinta batare da ta ƙarasa maganarta ba,daga bisani kuma ta saki shu’umin murmushin nan nata,tana tunanin ko ya Sehrish ta ƙare da sgr,don tasan cewa dole yaga gashin nan kuma zai hukuntata akan hakan,taso taje tayi masu la6e amma tsoro ya hanata gudun kar wani ya kamata asoma zarginta,

Ƙasa ƙasa tayi da murya tare da cewa”Koda ace bai hukunta ta ba,nasan cewa zai fara tsanarta ne,kuma zai gane cewa ƙazama ce ita,zanci gaba da shirya mata makirci har nasamu na maye gurbinta a wurin sg……’bata ƙarasa maganar ba,saboda jin shigowar Hajiya Azeema tare dasu kanal yousouf da sauran da suka je ɗaukota,zuba ido hayaam tayi tana kallonta,ganin irin ruwan wankan gwala gwalan data ɗauka,

jikinta na sanye da material launin sararin samaniya,mai tsadar gaske sai faman ƙyalli yake yi,rigar takai mata har wurin guiwarta,sai zane data ɗaura,ta yafa gyale asaman kafaɗarta,yayin da ta kashe ɗaurin ɗan kwalin nan ture kaga tsiya,amma ita nata sunan shi ture kaga arziƙi,don akwai abun arziƙi,gaba daya earrings dinta da awarwaron hannunta da kuma sarƙar wuyanta duk gold ne,ta wanku iya wankuwa,Hajiya azeema kenan ɗaya daga cikin biloniyas din family nasu,idan aka cire shugaba kuma jagora wato Surgeon General Rafayet,

 

Sai faman sakin murmushi take yi,tsantsar farin cikine ya lullu6eta yau gata agidan ɗan uwanta hussein,anjima ba’a haɗu ba,harkar kasuwanci ta 6oye ta,saboda bata cika zama a nigeria ba,kunsan business woman bata nan bata can kullum cikin hawa jirgi take wurin zuwa harkar kasuwancinta,

Atare suka ƙarasa cikin main palour ɗin,Kanal yousouf na ruƙe da Trolley ɗin da tazo dashi,

Anatse take bin ko’ina na gidan da kallo komai ya canza mata,ba kowa take muradin gani ba,face Junaid don har mafarkin shi tayi,shiyasa ta ƙagara tazo don tagan shi,juyawa tayi tare da kallon irfan tace”wai ina yaya hussein ne?naga kamar ba kowa gidan ko”?

“Abban mu ya ɗan fita garden tare da babban yayan mu da kuma ya Omar,amma ina da tabbacin cewa nan bada jimawa ba zasu shigo ciki,”ya ƙarasa maganar tare da nuna mata wuri yace”Aunty ki zauna mana,bari nayi ma Aunty azmee magana ta haɗa maki farfesun nan nata,nasan baki manta ɗanɗanon shi ba,”

dariya tayi tare da dan bugun kafadarshi tace”wato kallon acici kakeyi mun ko?daga zuwana ko hutawa banyi ba zan fara neman farfesu,kamar wata mayya,ni duk bama wannan ba,nifa hankalina bazai kwanta ba in har bansa junaid acikin idona ba,’

Kanal yousouf yace”Aunty gaskiya nafara kishi da junaid,haba kowa junaid junaid,ko hutawa ba kiyi ba amma kin fara ambaton sunanshi kamar shi kaɗae ne ɗa acikin gidan nan,”cikin zolaya yayi maganar tashi,

Kafin Azeema ta kuma cewa wani abu,sai ga azmee ta fito daga cikin kitchen fuskar nan ɗauke da murmushi tana cewa”wata sabon gani, hajiya azeema,Sai yau zamu sake sanyaki acikin idanunmu”?tayi maganar a yayin da take ƙarasawa wurinta suka rungume juna,dama suna ɗasawa da ita,mutuniyarta ce kodan saboda iya girkin azmee yasa take shiri da ita sosai,don ita bata wasa da abinci,akwai son cin mai daɗi,kullum tazo Abuja wurinsu burinta tasha farfesun azmee,

Raba jikinsu sukayi dana juna,Azmee taci gaba da cewa”Hajiya azeema kece kika koma haka?

Dariya azeema tayi tace”kinji ki da wata magana,kamarya na koma?nasan halinki fa azmee yanzu kince na ƙara ƙiba,’

Azmee tace”kin tsargu kenan,tunda gashi nan kin rigani faɗin abunda zance,’

Ta ƙarasa maganar tare da ruƙo hannunta tace”nasan kin kwaso gajiya sosai,shiyasa na gyara maki shinfiɗa inda zakije ki yada gajiyar da kika kwaso,sannan akwai special suya da kuma wannan farfesun da kika fiso na shirya maki shi,da zarar kin kammala hutawa zan shiryo maki shi,kici ki ƙoshi,nasan mutuniyar tawa bata wasa da cikinta,akwai bama ciki haƙƙinsa,”

 

Download>>> Deen House Complete Document

 

Sai faman murmushi hajiya azeema ke saki,da alama taji daɗin karramawar da azmee tayi mata sosai,atare suka wuce ciki izuwa bedroom din da zata sauka,dama already azmee ta gyara mata ɗakin sai ƙamshi yake,

bayan sun shiga bedroom din,Sai da suka ƙara gaisawa sosai,kafin daga bisani Azmee tabar cikin ɗakin ta koma kitchen,

Ajiyar zuciya hajiya azeema ta sauke tare da cire mayafin cikinta ta ajiye shi saman gadon,sannan ta wuce cikin toilet,

Bayan shigarta kanal yousouf ya shigo cikin bedroom din hannunshi ruƙe da trolley dinta,jingine mata shi yayi ajikin wardrobe,sannan ya juya ya fuce,

fitowa azeema tayi daga cikin toilet din har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi a fili tace”oh ni,koya junaid ya koma yanzu?nasan cewa ya ƙara girma sosai,gaskiya nayi missing shagwa6ar shi,nasan cewa da zarar yaji cewa na ƙaraso,zaizo ya ishe da rigima yana cewa Ina tsarabar shi,’ta ƙarasa maganar tare da hayewa saman gadon ta ɗan kishingiɗa donta runtsa,

 

Bata jima da kwanciya ba,Abbansu ya shigo cikin gidan tare da sgr da marshal atare suka ɗunguma zuwa masaukin nata,a hankali abba ya tura ƙopar ɗakin suka shiga da sallama,

Jin muryar ɗan uwanta,yasa ta yunkura tare da miƙewa daga zaune tana kallonsu fuskarta ɗauke da murmushi,

Ƙarasawa ciki su kayi,sgr da omar suka samu wuri saman doguwar sofa din dake dakin suka zauna suna fuskantarta,yayin da Abbansu kuma ya samu wuri gefen gadon kusa da ita ya zauna fuskar nan awashe sai faman farin ciki yake yi na ganin ƴar uwarsa daya jima basu haɗu ba,

gaisawa suka shiga yi da junansu,don ba ƙaramin kewar juna sukayi ba,

Abba yace”ina fata dae da shirin zama kika zo mana,dan wannan karan bazan bari ki koma ba,nagaji da kewarku da nake ta faman yi,’

“Yaya hussein,nasan ban kyauta ba,na rashin zuwana wurinku,abubuwane sunyi mun yawa shiyasanya na jima banzo ba,amma Insha Allah wannan karan har sai kun gaji dani,zan zauna ne har sai an ɗaura auren junaid,’

Fashewa sukayi da dariya gaba dayansu,banda Sgr wanda tun shigowarsu,ya jingina bayanshi ajikin sofa din tare da lumshe idanunshi,sarai azeema ta lura dashi dama sai da ranta ya bata cewar bazai tanka mata ba,

Omar yace”ae ni fushi nake da Auntyn tawa,haba aunty azeema yau kusan wata nawa kenan?yaushe rabon da mu sanyaki a idanunmu,baku son zuwa ganin ƴa’ƴanku,kuma babu damar mutum yace zaizo ganinku saboda kullum baku a ƙasar,’ya ƙarasa maganar tare da ɗaure fuskarshi,

dariya azeema tayi tana cewa”kwantar da hankalinka mutumina,ae wannan zuwan daka ga nayi,bazan koma ba har sai naga an shafa fatihar auranku,kai da wannan namijin zakin,’

tayi maganar cikin zolaya tana kallon Rafayet,aikuwa ya ƙara ɗaure fuskarshi alamar baiso,

Murmushi Abbansu yayi tare da cewa”kada ki samu damuwa,ae kuna anan ma zamusha biki,Abusufyan kawai nake jira ya ƙaraso,don nafison ya shaida wannan ɗaurin auren,ayi komai tare dashi don shine waliyyi”

Jin wannan maganar ta Abban nasu yasa shi buɗe idanunshi tare da miƙewa daga saman sofa ɗin ya nufi hanyar fita,duk suka zuba mashi ido,

Sai da yakai bakin kopar fita sannan ya ɗan juyo tare da kallon inda Hajiya azeema take zaune yace”Allah ya huta gajiya,”yana faɗin hakan yasa kai ya fuce daga ɗakin,

Girgiza kai Abbansu yayi tare da cewa”Rafayet sai addu’a abun nashi ƙara gaba yake yi,”murmushi kawai azeema tayi aranta tace”Jinin Alexandra kenan,in har rafayet baiyi mun haka ba,bazan tabbatar da cewa nononta ya sha ba,

Ganin rafayet ya fice yasa Omar miƙewa tare da yi masu sallama ya fuce yabarsu donsu samu damar tatttaunawa atsakaninsu yasan sunyi kewar juna sosai,

 

Bayan fitar Omar,azeema ta kalli abban nasu tare da cewa”Yaya hossein,ya maganar zuwan Abusufyan din?dagaske ne yau ɗin shima zaizo?kasan fa ya jima yana samana ran cewa zaizo sai kuma yaƙi zuwa daga baya,abun na damuna sosai,”fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,

“ya tabbatar mun da zuwan nashi,kuma ina da tabbacin cewa wannan karan dagaske yake mana ba wasa ba,inaso yazo saboda akwai abubuwa da dama da nake son muyi magana akai,na damu dashi sosai,na damu da halin da yake ciki,”

Jinjina kai tayi tace”amma abba,akwai wata alfarma da nake nema awurinka,”

“Wace alfarma kenan”?acewar abban nasu,

Cigaba da magana tayi”idan Abusufyan yazo nigeria wannan karon banso ku bari ya koma turkey,dan Allah ka ruƙe shi anan,ya zauna akusa dakai,banason yanayin nesa dakai,har yanzu akwai sauran yarinta atattare dashi,shi ne ƙarami acikinmu akwai buƙatar mu janyo shi ajikinmu,don muji menene ke damunshi,meyasa baya son zama ƙasar nan,ni nasan akwai dalilin da yasa abusufyan yake gudun zama anan,tabbas akwai damuwa atattare dashi,”

Abba yace”dama ni bazan barshi ya koma can ba,bazan ƙara yin gangancin barinshi yayi nesa dani ba,koda can daya bar ƙasar batare da sanin mu ya tafi ba,narasa gane mashi ni kaina,ba yarda banyi dashi ba akan yadawo nan gida amma yaƙi saurare na,wannan karan dae mun ci sa’a ya amince zaizo,kuma insha Allah idan yazo bazan barshi ya koma ba,zan ruƙe shi awurina,’

Ajiyar zuciya azeema ta sauke,hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,dama ita burinta Abusufyan yadawo kusa da Yayansu hossein su zauna atare da ƴa’ƴanshi,tafi son taga sun haɗa kansu wuri ɗaya,ita kanta ba da son ranta take zaune a lagos ba,sabo ne kawai sai kuma harkokin kasuwancinta da suka fi yawa acan,

Sun jima suna fira tsakaninta da ɗan uwanta,kafin daga bisani yayi mata sallama tare da fucewa daga ɗakin,komawa azeema tayi tare da kwantawa saman gadon,nan take bacci yayi awon gaba da ita,

 

A 6angaren sehrish kuwa tunda taje school,fuskarta babu annuri ko kaɗan duk tabi ta takure kanta asaman seat ɗinta,ko magana batasan yi,juyowa Amrish tayi ta kalli fuskarta tare da cewa”wai meyake damunki ne Sehrish?duk kin bi kin canza,ki faɗamun mana in akwai damuwa,may be ina da shawarar da zan iya baki,”

 

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

 

shiru tayi na wani lokaci kafin tace”Zan faɗa maki,but pls kada ki sanarwa kowa,”

“Insha allah,i will keep ur secret bazan bari kowa yaji ba,”amrish tayi maganar tare da mayar da hankalinta kan sehrish,

matsowa sehrish tayi kusa da amrish tayi ƙasa ƙasa da muryarta sannan tace”Amrish,babban yayanmu ne ya datse mun gashin kaina,dana kwallafa rai akanshi,na jima ina gyara gashin kaina,sai da yayi tsayi sosai yayi kyau,shi kuma ya datse mun shi da almakashi,baki ga wanda yabar mun ba,ɗan guntu ko parking ma bayayi,in nasa ribbom ma zamewa yakeyi,baya ruƙe gashin,’

Hankali tashe Amrish tace”Are u serious!shi da kanshi yayan naku ya yanke maki gashi?baisan cewa gashi tsada yake yi ba,?amma garin yaya hakan ya faru?ta tambaya tana jiran amsarta,

shiru ta ɗanyi kafin tace”ni kaina bansani ba Amrish,da safe ne naje kai mashi coffee,yana cikin sha wani abu ya sarƙe mashi a throat ɗinshi,ashe gashi ne ya faɗa ciki,kuma ni banawa bane,nayi ƙoƙarin nayi mashi bayani akan hakan,amma bai saurareni ba,kawai yasa almakashi ya datse mun gashin,’ƙarasa maganar tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka,

hannu amrish tasa tare da dafe goshinta tace”Ya salam,amma banji daɗi ba wlh,ni babban abunda nafi takaici shine,wazai aure ki a haka da guntun gashi,kinsan fa mazan yanzu sunfi son mace mai dogon gashi,”cike da zolaya amrish tayi maganar tana ƙumshe dariya abakinta,

Harara sehrish ta watsa mata tare da cewa”Oh abun ya zama na zolaya ko?ina faɗa maki damuwata maimakon ki tayani jimami shine kike mun dariya,’

“No,ba haka bane sehrish,nadamu nima sosai,rai na ya 6aci amma kada ki sa damuwa aranki,zan iya taimaka maki da hular gashi in kinaso,’

Cike da farin ciki sehrish tace”dagaske kike ko wasa”?

Amrish tace”am serious,ina dasu ajiye a gida zan ɗauko maki ɗaya daga cikinsu,amma bisa sharaɗin zaki kawo mun gashin kanki da babban yayanku ya yanke maki,inaso zanyi amfani dashi wurin haɗa wata hular gashin,ba ƙaramin kuɗi zamu samu ba,’

murmushi Sehrish ta saki tare da cewa”shikenan insha Allah,zan kawo maki gashin gobe in zanzo school,’

“Allah ya kaimu lafiya,”Amrish ta amsa mata,ci gaba da fira su kayi atsakaninsu har sae da malamarsu ta shigo sannan suka dakata da yin surutun nasu,

 

_💋Boss Bature💋_

 

Ana gab da za’a tashe su daga school,ciwon ciki yazo mata mai tsananin gaske,gaza jurewa tayi hakan yasa ta miƙe tare da zuwa wurin Aunty ɗinsu ta nemi izinin fita a wurinta,bayan ta amince mata ta fito daga class ɗinsu,sai faman sauri takeyi,hannunta ɗauke da school bag dinta,wani corridor ta nufa inda toilets din makarantar suke a jere,ɗaya daga cikin toilet din ta buɗe tare da shigewa ciki ta rufo shi,juyawa tayi tana kallon cikin toilet din komai na cikinshi fari ƙyal atsaftace,hannu tasa tare da zuge zip ɗin jakarta,ta ciro pad din da tazo da ita guda ɗaya,dama tun last week take jin alamun zuwan al’darta amma baizo ba,sai dae stomach pain da take ta fama dashi,wannan dalilin ne yasa take yawo da pad a jakarta just in case,

 

ajikin towel hanger,ta rataya jakarta,sannan ta zame dogon wandon jikinta,pant ɗin ta curo tana dubawa taga ko ya fara zuba,babu ajikin pant ɗin,amma da taje wurin yin tsarki bayan tayi fitsari sai ga ɗigon jinin ya fito,cikin sauri ta sanya pad din ajikin pant dinta,sannan ta sanyashi ajikinta,ta ɗauko dogon wandon ta mayar ajikinta,sai da ta zura shi ajikinta,ta ɗauko jakarta tana ƙoƙarin fita daga cikin toilet din kenan,cikinta ya murɗa mata,wani irin raɗaɗi mara daɗin ji,nan take ta zukunna ƙasa hannunta dafe da cikinta,zufa ce ta shiga gangaro mata agefen fuskarta,daƙyar take fitar da numfashi,lokaci guda gaba daya ta galabaita ta fita hayyacinta,anan ta faɗi kwance saman tiles tana juyi ita kadae acikin toilet ɗin,babu wanda yasan abunda ke wakana.

 

Back to top button