Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 35 Hausa Novel

Cike da doki ya shiga dakin amaryarsa rike da ledarsa ta kayan ciye-ciye; tana zaune a can a kuryar gado. Ko da ace ta amsa sallamarsa to shi dai bai ji ba, amma ya riga ya san yanda amare suke. Har inda take ya karasa ya sameta bayan ya ajiye ledar hannunsa a kan mudubi. Ga mamakinsa bayan ya daga fuskarta kuka takeyi sosai da hawaye kamar wadda aka yiwa auren dole, don haka nan take ya shiga aikin lallashi. Sai da suka kusan minti talatin sanna ya samu ta goge hawayen ta saurareshi.‘Wai me ya faru ne kike ta faman kuka haka sai kace wadda aka yiwa auren dole?’Ta balla masa harara ta dauke kai sannan tace ‘Ni da ka kawo na zabi dakin da nake so a sama kusa da nka dakin shine za a kawoni a ajiye ni a nan, ka sa ina nema nayi musu da masu kawoni.’Ya yi murmushin yake ya sake kamo hannunta wanda ta riga ta fizge yana cewa ‘Haba ke kuwa? Ai na zata da suka zo kafi sun gaya miki.’Ta zumbura baki ‘Ni babu wanda ya gaya min, sai da aka kawo ni kawai naga an ajiyeni a kofar gida kamar wata wadda ba a so zuwanta ba.’Nan ya shiga faman bata hakuri da bayani tana faman fizgewa har dai ya samu ta sauko. Ta kalleshi tace ‘Amma gaskiya ni fa ba zan zauna a nan ba, matarka da yaranka da kai kuna sama. Kenan fa duk ranar da ba kwana na ba ni kadai ce a kasa bakin kofa. Gaskiya wannan tysarin bai yi min ba, ko dai a bani sama ko kuma gaskiya ka nema min wani gidan. Wannan ai duk wanda ma ya zo ya san matsayina.’Ya kara matsawa ya janyota jikinsa ‘Kin ga, kada wannan ya dameki. Ko da ban kama wani gidan ba zaki iya komawa saman in ya so ko ni sai na dawo kasan ku kuma gaba daya kuyi zamanku a saman.’‘Ni dai ba haka nace ba, amma gaskiya ka cika min alkawari don ba zan yarda wata tana sama ni ina kasa ba.’Haka yayi ta lallabata har ya samu ta amince masa. Ya tattara musu kayansu suka wuce sama dakinsu wanda da farko ta so ta ki zuwa, sai kuma ta tuna gara itama ta hau saman ta ga yanda Khadeejan zata yi.……..Da yake dama Hammad bai saba barinta baccin safe ba yau din ma tun wajen 6am ya tashesu, bata bude dakin ba saida tayi wanka shima ta shirya shi. Ta riga ta ji motsinsu tun dare don haka ta san a dakin Mustaphan suka kwana. tana fitowa ta taso Hafsa suka shiga kitchen. Ya siyo burodi kamar yanda ya saba duk dare, don haka nan da nan ta soyawa kowa kwai ta hada kayan shayi tsaf ta bawa hafsa ta sauko da shi kasa. Kafin karfe takwasa ta jera komai da suke bukata ita da yara na breakfast a parlor din kasa. Tana shirin hawowa bene Hafsa ta biyota da wayarta ta mika mata tana ringing. Tana dubawa taga Baffa ne.Bayan sun gaisa ya kara yi mata nasiha sanna yace mata nan da awa daya Nabeela ta shirya Ahmad zai zo ya dauketa.Bata ji wata damuwa ba saboda dama ta san halin Baffa, ba tare da bata lokaci ba ta taso Nabila ta sanar da ita. Nan da nan ta hada kayanta don ko wanka cewa tayi idan taje gida tayi abunta, haka ma breakfast cewa tayi idan taje gida ta ci kosai don tabbatar yau lahadi kosai Mommy tayi.Wajen 9am suna zaune a dining table ita da yara in banda Afaf wadda bata tashi ba ko kuma bata fito daga dakinsu ba. Breakfast sukeyi suna ta hirarrakinsu Shukra sai labari take basu suna dariya gaba daya. Da sallama ya sauko daga benen ya karasa gaba table din yana cewa ‘Ina can ina nemanki a dakinki ashe kina nan ke da yara kuna ta jin dadinku.’Tayi murmushi ta kwara da kai. Ita da yaran duka suka gaishehi, bayan ya amsa ya dubeta yace ‘Idan kun gama cin abincin ki zo ki bani nawa breakfast din ni da kanwarki.’Tayi murmushin yake tace ‘Da yake mu ma bread da shayi muka sha ba wani abu ba, amma dama naga bread din da yawa ka siyo gashi can mun bar muku guda daya ka dauka ka haye muku da shi. Ko a nan zaku yi breakfast din?’Ya kalleta da dan mamaki ya cije lebe don baya son ya ja zancen a gaban yara yace ‘Um, idan kin gama dai kya hawo da shi.’‘Ok.’ Ta amsa cigaba da cin abincinta.Sai da suka gama cin abincinsu tsaf sannan ta dauki bread din ta haye sama, tana shiga babu kowa a parlor din don haka ta karasa kan dining table ta ajiye bread din ta shige dakinta.Kamar tare suka shiga dakin don ko zama bata yi ba ya shigo ya tura kofar, yana daga tsaye a jikin kofar yace ‘Wai ya na ganki a nan ina breakfast din namu ni da kanwarki?’Ta karasa ta zauna a kan gadon ta jingine ta mike kafarta tana cewa ‘Oh, ga bread din can na ajiye muku ai ko akwai wani abun ne?’Da mamaki yace ‘Ai na zata zaki dan dafa wani abu ko don saboda ganin ga bakuwa kin kwana da ita a gidan.’Bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, haka kawai maganar tashi sai ta bata dariya musamman da ta kalleshi kuma yana cewa wai “kin kwana da bakuwa”Ta dan gintse tana kokarin saita fuskarta sanna tace ‘Na kawana da bakuwa ko ka kwana da ita? Tea and bread muka ci fa kuma gashi can na ajiywmata ita bakuwar tawa, ina ga kamar ai dafa ruwan zafi bai kamata ya zama matsala ba ga wanda aka bawa burodi ko?’Ya bata rai saboda kwat-kwata bai zata haka ba; a iya saninsa sai sun kwana bakwai da amarya Khadeeja tana yi musu girki sannan sai araba kwana amma gashi tana nema ta kawo masa raini. ‘Ba fa na son raini Khadeeja, duk wanda ya kara aure matarsa ta gidan itace take yiwa amarya girki har sai ta kwana bakwai amma zan zo ina miki magana kina min wani zancen banza. Ai ko bazawara na aura kin san ya kamata kiyi mata abinci na kwana uku balle budurwa.’Ta kalleshi ta kawar da kai; babu yanda za ayi ta yiwa Naja girki sai dai duk abinda zai yi ya yi; ta tsani Naja ta tsani jin sunanta. Watakila da ace ya biyo ta hanyar da ta dace wajen sanar da ita zai kara aure da wadda zai aura da haushin da take ji bai kai haka ba, amma gaskiya babu abinda zai sa ta yiwa wata Naja girki. Ya auro matarsa ya gama more kwanan amarci sanna ita kuma bayan bacci da bata yi cikin nutsuwa ba kuma ita yake so ta tashi da sassafe ta hada musu breakfast na warware gajiya, bata taba ganin rainin hankali irin wannan ba. Ta bata rai sannan tace ‘Ba a biya mana wannan hadisin ba a islamiyya.’Mamaki ya kamashi ya bude baki amma ya rasa abinda zai gaya mata. Yana kallo ta zame ta gyra kwanciyarta ta juya masa baya. Bai shirya da wannan mahaukacin taurin kan nata ba wanda idan ta fara shi sai duk garin kowa ya ji. Ya dan tausa muryarsa yace ‘Bana son wasa Khadeeja, don Allah ki tashi ki samarwa yarinyar nan abinci. Next week ai zaku raba girkin kowa ta dinga yin nata, amma for now ki tashi ki bamu breakfast.’Ta sake gyara kwanciya ba tare da tace masa komai ba. Ya kalli kasa yana jijjiga kai don ya san ta gama magana; takaici ya kamashi. To yanzu ya za ayi tana amarya ya bata bread ruwan zafin ma ace sai ta dafa. Haka ya fice daga dakin yana wasi-wasi.Yana ficewa ta juyo ta harari kofar kamar yana wajen ta ja dogon tsaki tace ‘Dan rainin hankali!’

Back to top button