Novel Document

Maciji Ne Complete Novel Document

Maciji  Ne Complete Document

By Mammy Kabir

Bismillahir rahmanir rahim,Ina godiya ga Allah daya bani damar fara wannan littafi ,bayan kammala littafin soyayyata. Allah kasa yadda na fara lafiya naga bayansa lafiya ameen.

 

Gargadi banyarda wani ko wata ya juyamin wannnan littafi ta kowace sigar ba.

 

______Wata kyakkyawar yarinya na hango sanye da kaya irin na Fulani ,wato rigar saki dakuma zaninta,duka duka rigar da kadan ta wuce cibiyar ta,saidai kuma ta daura zanin ya rufe mata cikinta ta yadda ba wanda zai ga jikinta awaje.

Farace irin mai sirkin yallow -yellow din nan,tana da doguwar fuska mai kyan tsari dauke da dogon siririn hanci har baka,bakinta dan karami kamar gidan tsutsa,tana da irin manyan idanunnan masu kamar tana jin barci,ga gashin ido zara -zara.
Girarta kuwa ,kamar wacce aka dora Mata ita dan saiti,gaban goshinta wasu yan kananan gashine kwance lub lub kamar na jarirai.
Masha Allah yarinyar ta ko ina ta hadu ,dan doguwace marar jiki saidai fa Allah ya hore mata hips Kai kace wata babbar macece Sannan akwai alamun girma akirjinta , ma’ana dai akwai dukiyar Fulani dasuka fara tasawa akirjin nata.

Duka duka wannan yarinyar bata wuce shekara 15/16 ba ,amma kallo daya zaka yi mata kasan Allah yayi halitta agurin.

Sandace irin ta Fulani ahannunta tana dagawa sama ,da alama tana son hada kan wasu tarin sha’nun dake kiwone wani kayataccen jeji ,dan kuwa ciyawace agurin Kore sharr da ita ,sha’nun suna ta cin abarsu .

Tafiya ta farayi gurin shanun dake dan nesa da ita ,dan ita tana daga jikin wata bishiya ne tana kallon yadda suke kiwo abinsu.

Kanta ta daga ta kalli yadda garin ke hada wani irin hadari baki kirin dashi ,kuma da alama koda yaushe ruwa na iya saukowa.
“Kuzo mu tai gida abokaina kada ruwan nan ya sauko ya taba mu banin son nai mura aradu”
Cikin Yaren fulatanci take musu magana ,tana daga sandarta .aikuwa kamar wanda suke jin me take fadi suka fara yin hanyar gida .
Murmushi tayi tana mai binsu tana kara daga sandarta .

Tafiya suke cikin jajen ita kadai daga ita sai wadannan garken shanun ,sam ba alamun tsoro tattare da ita,yar wakar tama take tana daga sandar sama.

Kusan tafiyar minti biyar sukayi ,sannan na fara hango bukkokinsu dake can gaba kadan .
AHankali naga duk wani annurin dake kan fuskar yarinyar ya dauke ,nan da nan damuwa ta maye gurbin nishadi da take ,sosai naga jikinta yayi sanyi har suka karasa wata bukka dake farkon rigar da alama nan ne gidansu.

Garken shanun ta fara zuwa ta daure su tsaf sannan ta nufi cikin gidan,bakinta dauke da sallama.
Lokacin har anfara yayyafi .

Ba kowa a tsakar gidan nasu ,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar wata bukka cikin sauri.
Saidai kafin ta karasa kofar bukkar aka daka mata wata uwar tsakar da saida sandar hannunta ta fadi kasa.

Afirgice ta juyi jikinta na rawa sosai kamar dan mazari.da sauri ta karaso gurin matar data daka mata tsawar,
“Gani gwagwgo”ta fada cikin rawar murya. Kallon matar nayi sai na tarar da
matar farace saidai kuma kazanta da rashin kulawa yasa tayi wani irin baki baki fari fari,sannan tana da jiki sosai sam fuskar ta ba alamun rahama a cikinta.
Tana tsaye a kofar bukkar ta tana hararar yarinyar dake durkushe gabanta.
Cikin masifa da bala’i matar ta fara magana da hausarta marar kyau.

“Da kake kokarin shigewa dakin,ubankane zai debi ruwan?
Ko kin ajiye bawanki ne a gidan?matar ta fada cikin zaro ido.
Kan yarinyar akasa jikinta na rawa ta fara magana
“Allah hukkumu hakuri gwagwgo naga ruwa na don sauka ne shiyasa ban deboba”ta fada cikin rawar murya da tsoro.

Wani wawan mari matar ta kai mata cikin rashin imani da tausayi cewar yanzu ta dawo daga kiwo kuma ko abinci bata ci amma take kokarin sake turata rafi.

“Shegen yaro mai bakin hali wllh yanzu koke kidobo min ruwan nan dan ubanki karuwa kawai”matar ta fada tana mai hankade yarinyar .

Faduwa tayi sosai hannunta ya bugu da wani dutse dake ajiye tsakar gidan da alama na zama ne.

Kara ta saka cikin azaba tana mai dafe hannunta dake mata wata irin azabtar zafi.
“Wayyo handi ɗin boni lalashewa gwagwgo hannu na ta ɓalle” ya rinyar ta faɗa cikin azaba.

“Shege wllh dama zai karye danafi kowa jin dadi yarinya kamar aljana,ace kinfi kowa kyau arugarnan? Na tsaneka fatto saina bata wannan shegen fuskan baki.maza ki tashi kona shakeki agurin ki mutu kowa ya huta” cewar matar cikin bala’i da tsantsar nuna tsana ga dattin.

Cikin hanzarin ta mike ta zari wani boket din roba ta fice tana kuka sosai.

Tafiya mai nisa tayi kafin tazo rafin, har zuwa lokacin kuka take hannunta sai zogi yake mata, ruwan ta debo cike da sauri dan kuwa ruwan da ake ya fara karfi.

Saidai me ?tana juyawa tayi arba da wani murtukeken maciji katon gaske ya fasa kai yana huci.

Wani irin mugun tsorone ya kamata nan da nan jikinta ya kama rawa har batasan lokacin da boket ɗin ya fadi kasa ya fashe ba.

Tashin hankali kenan wanda ba’a sa masa rana ,iyakar rushewa da tashin hankali yarinyar nan ta shiga.
Hannu ta ɗora aka tana mai kara ƙarfin kukanta.

“Wayyo ni fattu bukar na mutu na lalashe ya zanyi da rayuwata nashi zai karni wayyo baffana wayyo Allah ,taimaka min”
Ta faɗa tana kallon boket ɗin dake tarwatsa,dama kuma rana ta gama cin ubansa.
Shi kuwa macijin nan ganin yadda ta tsaya tana kallon sa kuma tana kallon fasashshen boket ɗin ta ,sai taga kamar neman makami take, dan haka afusace yayi kanta

Ihu ta kwalla mai karfin gaske tare da zubewa agurin sumammiya dan ganin yadda macijin nan yayi kanta baki bude.

Masu karatu ya kukaji?
Meye ra’ayinku akan wannan Nobel ɗin?
Ina bukatar comment dinku idan buk din nan yayi muku dadi muci gaba.

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Danna Inda Aka Rubuta Download

 

Back to top button