Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 35 Complete Novel

*ASM Bk2035*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

 

……….Yadikko tayi zaton wayar suke tayi hakan yasa taci gaba da aikin ita kad’ai, sai da aka kira sallar Azahar su Amadu sun shigo yin salla ne ya ganta baje kan katifarsa tana ta sharar bacci d’an tsoki yay ya girgiza kan shi kaman bazai tashe ta ba sai kuma ganin lokacin salla yayi yasa ya tada ita yace ta je tay salla, tay matuk’ar yin mamakin yadda akai tayi baccin daga yin waya, Koda ta fito bata iske Yadikkon a cikin Kitchen d’in ba don tuni ta gama komae ta wuce d’aki don tayi salla itama Fatuu d’akin ta nufa, jibi su Yadikko zasu tafi hakan yasa washe gari talata suka hau shiri har Kasuwa gwaggo ta rakata tayo siyayya Fatuu duk ta damu bata son su tafi haka ma Mino tun ranar ta fara kuka Fatuu na bata hak’uri gwaggo ma tace mata in sha Allahu bada jimawa ba zata dawo da ita nan ta dae dage da karatun ta tace to, akwati guda na kaya Fatuu ta bata hakan yasa ta washe tana ta murna gwaggo ma tayi masu siyayya sosae shima Kamalu kaya sosae Amadu ya bashi, Washe gari da Asuba Abbas yazo kai su tasha dama tun jiya ya kira Fatuu sanin yau zasu tafin yace zai zo ya kaisu Fatuu ta so bin su tasha amman gwaggo ta hana don kar asa Abbas wahalar dawowa sai Fatan Allah yasa a sauka Lafiya, bayan tafiyar su duk kad’aici ya damu Fatuu don ma Haulat na nan, Ranar Juma’a da daddare bayan Isha Fatuu na zaune tare da gwaggo a Parlor gwaggon na zaune akan Carpet don ba kasaifai take son zama kan kujera ba har ta dad’e Fatuu ce zaune akan kujerar can ta tambayi gwaggon in jarabawar su ta fito a ina zata ci gaba da karatu, d’an jimm tay kafin tace a nan Katsina Fatuu ta d’an bud’a ido tace “amman gwaggo ai ba’a fa karatun Medicine anan sai Kano ko Zaria ko sakkwato” gwaggo dake kallonta ta d’an girgiza kai tace “ina tunanin ai kawae zaki canza abunda zaki karanta ne” da yar damuwa Fatuun ta tambayeta Saboda me tace “gaskiya banson ki tafi wani gari karatu ko ba don komae ba don abunda ya faru kinga yanzu idanun dangin mahaifin ki na akan ki abu kad’an suke jira tunda dama ba son karatun suke ba, ni a shawarce ki fara yin School of Nursing ta nan ala bashshi tunda naji ance gab ake da a fara karatun likitancin anan har an maida Asibitin Medical center na koyarwa don hakan kinga Ko kina cikin karatun aka fara sai ki koma shi in kuma har kika gama wannan d’in ba’a fara ba tunda shekara ukku ne lafiya lou ai shima duk aikin Asibitin ne kuma ko lokacin aka fara karatun likitancin zaki iya yi zaki ma fi jin sauk’in karatun tunda kin karanci abunda ya dangance shi” d’an shiru Fatun tay kamar mai yin tunani bata son abunda zai sa ta k’ara samun sa6ani da gwaggon har ta 6ata mata rai hakan yasa tace Shikenan Allah yasa haka yafi zama Alkhairi murmushin jin dad’i gwaggon tay tace Amin haka yakamata duk abu ya faru da mutum yay fatan kasancewar shi Alkhairi in har ba Alkhairin bane sai kaga Allah ya canza ma, cike da gamsuwa Fatun na yar dariya tace “Hakane gwaggo ni shaida ce” duk suka sa dariya kafin gwaggon tace “in ce dai kun rabu dashi yaron kwata kwata ko?” Fatuu ta gane Khalid take nufi hakan yasa yanayin fuskarta ya d’an canza ta ta6e baki tace “Eh, da dai Farko yana ta takura man da kira har da kina can ma sai yay ta kira na har message ya turo man yana rok’on wai don Allah in yi hakuri in saurare shi yana son muyi wata Magana ne ni kuma kawae sai nayi blocking d’in shi ma” jinjina kai gwaggon tayi tace hakan ya kamata tunda an rabu ba shikenan ba yaje kowa Allah ya had’a shi da rabon shi, can ta d’an kya6e baki tace wai da fa Mino za’a k’ak’aba ma shi, zaro ido Fatuu tay da Al’ajabi tace “Mino kuma!” gwaggon tace “Eh wllh duk tuggun Yaya ne Allah dai ya taimaka hakk’atta bata cimma ruwa ba, in ba don mugun nufi ba ba akwae sauran yara ba a gidan a bashi mana” ta6e baki Fatuu tay ta shiga fad’in ai dama ko itama tasan duk k’ullin su Yayan ne su suka tunzura komae Gwaggon tace “ai da yake da Allah muka dogara kuma shi ba azzalumin bayin shi bane gashi nan ai ya bamu mafita da basu ta6a zata ba” ta k’arasa tana sakin murmushi wanda da gani ba k’aramin dad’i take ji ba a ranta Fatuu dake kallon ta itama tana murmushin tace “Wllh Gwaggo ina son in ga kina farin ciki kyau kike sosae” yar harara ta wurga mata tace bayan ta gama sata kukan da rabon da tayi irin shi har ta manta da sauri Fatuu ta sauka daga kan kujera taje ta rungumeta tana fad’in “Am very sorry my lovely Kakus in sha Allahu bazaki k’ara zubar da hawaye Saboda ni ba zan ta saka ki farin ciki kuma zamu rayu tare har in yi aure inyi ya’ya harda jikoki” sosae gwaggo ke dariya tana fad’in anya bata so kanta ba da yawa ita ina zata kai wannan lokacin da sauri Fatun tace insha Allahu zata kai, jin tak’i ta d’aga daga jikinta yasa gwaggon ce mata ta d’agata ta fara d’aura mata gajiya shiru Fatun bata tanka ba kuma bata d’agata ba hakan yasa gwaggon ta kira sunanta da d’an k’arfi sai lokacin ta d’ago tana d’an murmushi ganin yanayin idonta yasa tace mata badae har tayi bacci ba tana muttsike idonta guda tace Wllh har ta fara gyangyad’i da d’an mamaki gwaggo tasa hannu ta ruk’e ha6arta tace “Wai ni kodae shawara ke damun ki ne Fatuu, na lura dake kwanan nan kin fiye bacci bunu bunu kin 6ingire bacci” tana yar dariya tace “Ramuwar baccin da ban samu yi da ina cikin damuwa ba ne” d’an ta6e baki gwaggo tay Fatuu ta k’ara cewa “Haka rannan ma fa Ya Haisam ya kira ni Video Call muna cikin yin Magana nay bacci ban sani ba” bud’a ido gwaggo tay alamar mamaki sai kuma tace “ashe kun yi Magana bayan kin dawo” Fatuu tace “Eh tun ma su Yadikko na nan” kai gwaggo ta d’aga sai kuma ta tambayeta suna lafiya dai ko Fatuu tace “eh lokacin yace Aunty Fanan ma na wurin aiki amman shi naga fuskarshi kamar ta d’an fad’a shine na tambaye shi ko bai lafiya ne yace eh baijin dad’i amman ya samu sauk’i” girgiza kai gwaggo ta shiga yi alamar jajantawa kafin tace “Allah sarki Allah ya k’aro sauki, amman to kin k’ara kiran nashi kin ji ya jikin ko” d’an bud’a ido Fatuu tay ta girgiza kai alamar a’a gwaggon tace “Amman baki kyauta ba gaskiya ai Kya kira ki ji ya ya k’ara ji ke in kece yaji baki lafiya kina tunanin zai dau kwanaki bayan jin hakan bai kira ki ya k’ara jin ya kike ba?” hannu Fatuu tasa ta rufe baki tana dariya sai kuma ta cire tace to ta kira shi yanzun gwaggon tace haka dae yakamata da sauri ta mik’e ta nufi hanyar fita daga parlon don wayar na d’akinta gwaggo ta bita da ido fuskarta da d’an murmushi har ta fice.

 

Tana shiga ta nufi gado ta fad’a saman shi tay rubda ciki, bayan ta kai hannu ta d’auki wayar tay sending mashi kira saidae har wayar ta katse ba’a d’aga ba tana kokarin sake kiran sai gashi ya kira picking tay ta kara a kunne gudun kada yay complain kamar ranar nan na k’in yin Magana yasa tace “Hello Assalamu alaikum” cikin cool voice en shi ya amsa mata, d’an murmushi tay tace “Ya Handsome ina kwana nasan ku nan safiya ne ko?” d’an murmushi ya saki jin sunan data kira shi dashi ya bata amsa da eh, tace “Dama na kira in ji ya jiki rannan da kace baka jin dad’i” shiru ya d’an yi sai kuma slowly yace ta damu da ciwon da yake ne, tura baki tay a shagwa6e tace “A’a nifa kawae na tuno ne shiyasa na kira”,

 

“Dat’s mean baki damu da ciwon ba kenan” ya tambaya tace “a’a….na damu ba kai ne ba…” Sai kuma tay shiru ya tambaye ta shine mi tace sai yace ta damu, d’an murmushi mai sauti yay yace to ba gashi tace ta damu ba miya fad’i ba daidai ba, shiru tay ta rasa mi zata ce ma har saida ya kira sunanta a shagwa6e ta amsa yace mata ya warke ya gode da kulawa tace to, bai cika son ya kara waya a kunne yay ta Magana ba hakan yasa ya maida kiran video call yana zaune da gani a Office ne jikinshi sanye da Maroon suit yayi kyau har ya gaji ganin bai ganinta sosae yasashi tambayar ta ba wuta ne tace eh amman ai akwae sola bari ta kunna wannan hasken na rechargeable globe ne ya amsa da Ok, bayan ta kunna haske ya gauraye d’akin ta koma kan gadon ta zauna ta d’age k’afafuwan ta ta jingine wayar ajikin su, tambayar shi tay ya Aunty Fanan yace tana nan lafiya da bud’ar bakinta sai cewa tay wai tana da ciki shiru yay kawae yana bin ta da kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ita kanta hakanan taji tayi tambayar ba tare da shiri ba su6utar baki ce, duk ta kame kanta sai nonnoke fuska take ganin yadda take yi yasa shi yin d’an murmushi yace zata zo ne kallon shi tay kaman bazata ce komae ba sai kuma tace tazo ina yace nan in Fanan d’in ta haihu da sauri ta girgiza mashi kai alamar a’a fuskar shi a sake yace “Why ba sai ki mata rainon ba” tana tura baki tace ita bazata yi karatu ba sai raino, yar guntuwar dariya yay sai kuma ya tambayeta yaushe zata ci gaba da karatun ta kwashe yadda sukae da gwaggo ta fad’i mashi a tunaninta ko zai ce zaiyi Magana da gwaggon kan a barta taje tay Medicine d’in amman sai taji yace hakan yayi yace amman ai kaman dole saida Jamb tace a’a taji ana cewa Basic Nursing ba saida Jamb ba yace Ok tace mashi yanzu result kawae take jira yace Ok Allah yasa aga Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d’an yi can tace mashi yaushe zai zo idon shi akanta ya tambayi tana son ganin shi ne da sauri tace a’a ba gashi ko yanzu tana ganin shi ba kawae ta tambaya ne yay nodding kai kafin yace mata bazai samu zuwa yanzu ba tunda bai dad’e da yazo ba kuma Hajiya daga Abuja zata zo nan ta d’an zauna dasu Saboda ganin likita tace Allah ya bata lafiya ya amsa da Amin daga baya da kanta tace bari ta k’yale shi ta hana shi aiki yay d’an murmushi kawae yace mata take care ta d’aga kai daga haka ta katse kiran, d’akin gwaggo ta nufa don ta fad’i mata ya warke ta iske har tayi bacci. Fatuu an samu natsuwa har ta koma islamiyya washe gari yan islamiyyar sunyi farinciki da ganinta sai tambayarta ake yadda akai ta dawo tace an fasa auren ne kawae Malam Nazifi har ke6ewa yay da ita ya tambayeta Allah yasa dae lafiya ta dawo tace mashi lafiya lou dama bata son auren na dole ne za’a mata to kuma an fasa daga yanayin fuskar shi ta fahimci yaji dad’in hakan yace ba komae bane ya ja hakan face Addu’a shiyasa ake son bawa ya mik’a lamuransa wurin Ubangiji to kuwa a komae zai samu mafita Fatuu ta jinjina kai tay mashi godiya sosae har yana tsokanarta yace sai a dasa rashin ji ko tana dariya tace ai ta daina wannan yanzu ta girma, Washe gari bayan ta dawo daga islamiyyar safe ne Amadu ya shigo d’akinta lokacin tana cikin gyara wardrobe d’inta ta kalleshi tana murmushi shima murmushi yake mata yace “Amaryar mu” tura mashi baki tay tace don Allah ya bari bata so, wayarta ya kawo mata yace ta bashi tashi tace a’a Ya barta kawae yace don me ai itama tana son abunta ko kuma ga Makaranta zata fara tace ai tashin ma lafiya lou daga baya ta canza, duk yadda yay da ita k’in amsa tay k’arshe yay mata godiya ya tafi, acikin satin da ya kama Haulat ta koma Nijar don bikinta bai fi saura sati biyu ba, ranar Laraba sai ga Baffan Fatuu sun kawo Kayanta na kitchen kamar yadda yace Fatuu tay farincikin ganin shi sosae, a d’akin Fatun can gefe akai masu wuri manyan kuma su freezer aka kai su d’akin Amadu bayan sun zauna da gwaggo ta tambaye shi yadda akai da furniture d’in yace wad’anda suka yi su sun fanshe su duk da sun rage kud’in gwaggo ta girgiza kai tace Allah ya kyauta bayan Gwaggo ta tafi Fatuu taje wurin shi d’akin Amadu da aka sauke shi sukai fira anan ya bata kud’i dubu d’ari yace ta d’auki 50k d’inta da ta bashi tay amfani da sauran dubu hamsin d’in gun shirye shiryen fara karatun ta dama cikon dubu d’arin data bashi kud’in sadakin ta ne, k’in amsa tay tace ai ba sai ya maido mata ba itama ai Saboda auren aka bata yana dariya yace to ai ba’ai auren ba ko ta dingi zuba mashi shagwabar bazata amsa ba yana dariya daga baya da k’yar ya sata ta amsa kwanan shi biyu ran Friday ya tafi, Bayan sati guda suka shirya zuwa Niamey K’asar Nijar bikin Haulat harda Kawu Amadu gwaggo tayi masu hidima sosae don kayan kitchen d’in Fatuu ta d’ibar mata masu yawa harda zannuwan gado da labulaye innarsu haulat d’in kafin su tafi lokacin tay tsananin farinciki da yake su da wuri suka tafi su kuma su Fatuu saida bikin ya zo, Tafiya yankin Azaba Fatuu an ji jiki sai lokacin ta gane daga Katsina zuwa Adamawa ba komae bane akan wannan tafiyar da sukae don farko Marad’i suka fara zuwa daga can suka hau luxurious bus suka kwana suna tafiya don ma Motar nada dad’in hawa akwae su Ac harda Tv, lokacin da suka isa da k’yar take iya taka k’afafunta don tafiyar tayi daga Katsina zuwa Lagos in ma bata fi ba, Haulat tay tsananin farinciki da zuwan nasu haka danginsu sun tarbe su hannu bibbiyu an sha shagali an ci an sha anyi wadaqa da nama don mutan Nijar badai cin nama ba bakamar in suna hidima gashi ba Laifi dangin mijin nada d’an hali saidae wani Abincin fa su Fatuu kasa ci sukae sai wanda yay irin namu na nan, Alhamdulillah ranar Asabar aka d’aura auren Haulat da Angonta wanda yake d’an uwanta ne wato Nuraddeen suna zaune Fatuu na dariya tace mata da rabon dae sai ta rigata yin aure duk sukae dariya, Sosae Fatuu akai kasuwa don wanka na Mutunci ta rink’a d’auka da bikin don ma gwaggo na taka mata burki har samari ta hanata saurara tace ba wannan ne a gabanta ba to itama dai dama ba mai kula samarin bace, bayan biki da kwana biyu suka sake d’aukko hanya aka taita yi har Allah ya maido su Lafiya Fatuu cike da kewar Aminiyarta, tun suna can aka saki result d’in Waec suna dawowa Abbas yazo ya dauketa suka je dubawa gaba d’aya ta samu credit saidae chemistry ne ta samu pass tun can ta fara k’walla don bata tsammaci hakan ba sakamakon tasan ta maida hankali lokacin da sukae exams d’in gashi dole saida shi zata iya yin School of nursing din Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali yace a jira Neco ta fito in sha Allahu yasan zata samu, koda ta dawo gida ma gwaggo duk da bata ji dad’i ba amman bata nuna mata damuwa ba sosae itama tace a jira d’ayar daga baya ma sai ga Haisam ya kirata don Abbas ya fad’i mashi komae harda yarda ta tashi hankalinta sosae ya kwantar mata da hankali yace ai akwae alternative so a jira Neco fuska jage jage tace mashi to anan ma saida ya k’ara ce mata lazy ta tura mashi baki daga baya sai gashi har saida yasata dariya, bayan sati biyu Neco ta fito wannan karon k’in zuwa tay dubowar saidae Abbas ne yaje, a k’opar gida ya tsaya bayan ya dawo ya kirata ta fito tunda ya tafi dubowar dama gabanta keta fad’uwa duk ta sha jinin jikinta ba kamar da taga fuskar Abbas d’in bai dariya a gefe ta tsaya ta gaida shi a sanyaye ya amsa duk ya d’an damu kaman zatai kuka tace mashi itama akwae matsala ko ya d’aga mata kai alamar eh nan da nan tasa hannu zata fara matsar kwalla ya fiddo result d’in daga gefen shi ya mik’a mata, k’in amsa tay tace ita mizatai dashi tunda bata ci abunda ake so ba saida ya d’an matsa mata sannan ta amsa ta amman ta k’i dubawar yace ta duba mana, hannunta har rawa yake ta d’aga da ido d’aya ta d’an kalli paper d’in da sauri kuma ta ware idanun a tunaninta ko abunda take gani gizau ne ba gaske ba, tabbatar ma da kanta tay da sauri ta kalli Abbas taga yana murmushi a rud’e tasa hannu ta rufe bakinta ganin ta cinye duka harda su A (distinctions) nan da nan ta fara murna tana yarfa hannu sai faman fad’in Alhamdulillah take Abbas na mata dariya, koda ta shiga gida gwaggo ta gani tay matuk’ar murna harda duk’awa wai Fatun ta hau ta goyata ta kuwa haye aikuwa da k’yar ta mik’e don ma gwaggon k’akk’arfa ce dik’ir take, ganin tana ta nishi yasa Fatun saukkowa tana ta kyalkyatar dariya,

 

Lokacin da aka fara saida Form na Makarantar Abbas ne yaje Bank ya siyo mata ya kawo mata suka cike tare suka maida can School d’in bayan wani lokaci suka je don yin jarabawar shiga wato Entrance exam a lokacin ne ta had’u da wata da suka zauna tare har ta fad’a mata sunanta Fauziyya Ahmad ta tambayi Fatun itama ta fad’i mata nata Fauziyyar tay masu Fatan Nasara Fatuu ta amsa da Amin, bayan sun gama ne tace ma Fatuu ta bata phone no d’inta ta bata don ta lura tana da kirki ga fara’a bunu bunu tayi murmushi, bayan kaman sati biyu da yin jarabawar aka kafe lists d’in wanda suka ci Fauziyya ce ta kira Fatun ta sanar mata ta samu itama haka don taga sunanta cikin yan Katsina local Government itace ma ta biyu sosae Fatuun tay murna duk da da sauran rina a kaba don dama farko sai su d’auki Mutane fin d’ari cikin mutane wurin 500 koma fi da sukai applying sai a hankali za’ai ta zubar da su don bai wuce Mutum 130 ko 150 bane zasu ci entrance exam d’in suma kuma wurin interview za’a k’ara zubar da wasu haka Bayan an fara karatunma, cikin Nasara Fatuu taci interview da sukae ta samu Admission d’in Kasimu Kopar Bai School Of Nursing Katsina dake acikin General Hospital, kowa yay farin ciki karma dae gwaggo taji haka Abbas ma har Haisam saida ya kira ya tayata murna daga baya suka fara Class ranar farko har Video call sukai da Haisam tana cikin fararen Uniform d’inta da takalma sai faman zabga dariyar dad’i take ya k’ara tayata murna ya kuma ce sai ta d’age don still bata zama cikakkar daliba ba har sai tayi passing Intro Exam tace in sha Allahu, tun ranar da suka je interview Fauzy kamar yadda Fatun ta fara kiranta dama kuma tace haka ake ce mata ta tambayi Fatuu Day zatai ko Boarding tace mata Day Fauzyn tace mi zai hana tayi Boarding don itama ita zatai Fatuu ta tambayeta ba’a nan garin take bane tace eh ita yar Funtua ce amman akwae Yayarta dake Aure nan Katsina a Goruba Road, Fatuu tace to ba sai ta zauna a wurinta ba Fauzyn tace ita tafi son zama a school don mutum yafi samun time na karatu balle wannan Makarantar da ba’a wasa da karatu dole sai Mutum ya dage zadai ta rink’a zuwa wurinta weekend, to bayan sun fara shiga Class ma saida ta k’ara yi ma Fatuu Maganar tace an bata d’aki dama akwae wata yar garinsu da suka gama a d’akinsu zata zauna Don Allah ta dawo boarding sai su zauna tare ganin yadda ta dage tana ta nuna mata Muhimmancin zama a cikin Makaranta ne yasa Fatuu tace to in ta koma gida zata tambaya in an barta sai ta dawo Fauzy harda yi mata Addu’ar Allah yasa a barta ita dae Fatuu yar dariya kawae tay, A ranar da daddare bayan sallar Magrib ta iske gwaggo a d’aki ta gama salla ta zauna gefenta bayan tay mata sannu ne tayi mata Maganar komawarta boarding, shiru gwaggo tay tana kallonta can ta nisa ta tambaye ta miyasa take son zama a Makarantar Fatun tace an fi samun lokaci kuma ko Assignment aka bada mai wuya za’a taru ayi tare sannan ana tattaunawa game da abunda aka koya, d’an jimm gwaggo tay kafin tace “Gaskiya ni banson zaman Makarantar nan don yana da illoli ba kuma wai don ban yarda dake bane amman nafi son ki rink’a zuwa kina dawowa” gyad’a kai Fatuu tay tace Shikenan Gwaggo ta fahimci yanzu duk inta nuna ga yadda take son abu bata gardama mata hakan yasa tace mata in kamar an basu aikin ko zasu tattauna kan karatun zata iya tsayawa can amman ba wai ta koma gaba d’aya ba Fatun tace to ta tashi ta koma d’akinta…………

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button