Hausa novels

A Sanadin Makwantaka Book 1 Complete Document

Description/Story:

A Sanadin Makwantaka Book 1 Complete Hausa Novel Document Written By Zee Laluh

 

Description

Unguwa ce mai dauke da Manya manya had’i da K’ananun Gidaje,sai dai kana kallon yanayin gidajen zaka fahimci cewa ba tsohuwar unguwa bace,don sam gidajen basu ji jiki ba,wasu gidajen Sababbi ne yayin da wasu kuma baza’a kira su da sabbi ba,ba kuma tsofaffi bane,akwae Manyan gidaje masu kyau wad’anda da ka kalla zaka fahimci masu gidajen nada arziki,yayin da wad’ansu kuma ke nuni da masu su,masu rufin asiri ne.Yanayin layin ba hayaniya sosai akwae mutane jefi-jefi,kallo daya zakae ma layin ka fahimci akwae masu arziki had’i da masu rufin asiri a wurin.

Wata mota ce k’irar Corolla S Navy blue ta shigo layin da matsakaicin gudu, K’irrrrrrr! Motar taci burki batare da shiri ba sakamakon wasu yara mata da basu wuce shekara 13 zuwa 14 ba, da suka shigo hanyar da gudu daga Lungun dake a bangaren dama,d’aya cikinsu na dauke da farin matsakaicin Bokiti mai d’auke da wani abu ciki hakan na nuni da tallah take yayin da dayar da ta biyo ta ita bata dauke da komae,lungun da ke opposite da wanda suka fito suka shiga a daidai nan kuma d’ayar yarinyar ta samu nasarar kamo hijab din yarinyar dake dauke da bokitin talla,tura ta tayi jikin bango tana kokarin 6arar mata da abunda take sayarwa, ita kuma ta rik’e bokitin gam,

Shi kuwa na cikin Motar still yayi da alamun bacin rai a fuskarsa yadda yaran suka fad’o masa all of a sudden,ba don Allah yasa bai gudu sosai ba da horrible accident ya faru a wurin don gaba dayan su zai dauke su da motar watakil ma ya take su,dan tsaki yaja”Mtsww”A hankali ya waiwaya yana kallon lungun da yaran suka shiga,hango su yayi sai faman kici kici suke alamar dai fad’a suke ga d’ayar yarinyar mai sanye da riga da skirt na atampa kanta d’aure da kallabi wanda daga bayan kallabin yayi tudu sosai alamun dai tana da gashi mai yawa ga gyalenta kuma daure a k’ugunta sai faman kokarin ganin ta 6aro da bokitin dake kan dayar yarinyar da ta matse a bango take,
Ganin yadda ta dage bilhakki sai ta 6arar ma d’ayar abunda ke cikin bokitin yasa shi sauke gilashin motar a hankali,”ke,ke” Ya fara k’okarin yima yarinyar magana sai dae ko waiwayo inda yake batayi ba,tunani yayi kilan bata ji shi ba hakan yasa ya k’ara dan daga murya duk da bai so hakan b “Kee sake ta!” ya kara fada,tana jinsa tayi burus da shi,yarinyar mai talla ce tace”ke Fatuu baki ji wancan mai motar na cewa ki kyale ni bane”kara k’ankame bokitin tayi ita kuwa wadda aka kira da Fatun ganin ta kasa 6aro da bokitin yasa ta fara dukan yarinyar don tasan in tayi hakan dole ta saki bokitin ai,
Ganin hakan yasa mutumin cikin motar fitowa,Wow! Masha Allah, Wani Kyakkyawan Mutum ne mai dan tsayi sai dae ba irin tsawon nn sosae b, sai dai kana kallonsa zaka shaida dogo ne,kalar fatar sa kuwa fara ce irin farin nan mai kyau mai tafia bai d’aya ba wai irin wanda zaka ga wani wuri yayi dan ja-ja ko yalo-yalo ba,gaba daya fatar shi sumul take,yana da matukar kyawun Fuska wadda da idanu sun kalli fuskar zasu shaida hakan,sumar kansa nada dan tsawo wadda take a nad’e yayin da daga tsakiya ta dan fi gefe da gefen tudu,sam bai tara kasumba ba sai dai akwae sumar kad’an zagaye da fuskar har zuwa saman dan madaidaicin bakinsa wanda labban sa suke kalar peach mai duhu,sanye yake cikin Suit Navy Blue yayin da yar cikin take Black color,Wuyansa na sanye da Necktie kalar suit din wato navy blue wanda yake kwance ak’asan bakar collar din yar cikin,k’asan necktie din kuma an rufe shi data saman ta hanyar sa Ma6allan rigar wad’anda suke bakake masu kyan gaske,hannunsa na sanye da Wrist watch silver mai d’an duhu kai da gani kasan zai yi kudi Agogon, yayin da K’afafunsa kuwa ke sanye cikin wasu dakakkun Takalma cover shoe bak’ak’e, ba k’aramin haduwa yayi ba,ba kamar da kalar fatar sa take fara sai yayi kaman ba irin mutanenmu ba na nan,yadda suit din suka amshi jikinsa cib ya bayyana sam ba ramamme bane yana da cikar kira ba kaman Kafadunsa da suke da fadi,da ka kalli kayan jikinsa da kuma motarsa zaka fahimci yayi shigan da ake kira too match,

Ya mayar da Kofar motar ya rufe da hannunsa daya tafiya ya fara yi majestically,da ganin yadda yake tafiyar za kai tunanin irin mutanen nan ne masu ji da isa,gefen su ya tsaya fuskar nan a tamke cikin dan daga murya ya fara yima yarinyar magana”Sake ta!”burus tayi sai ma k’eya da ta kara juyo masa,cikin 6acin rai da daga murya yace”Am i not talking to u, idiot.” ya fada a dan harzuke,jin yace mata idiot yasata juyowa a fusace ta fara magana cikin masifa”Ni ba idio……sam ta kasa k’arasa maganar sakamakon hada ido da mutumin dake a tsaye fuska a d’aure,kwarjini yayi mata sosai,

“Get your hands off her”ya fada fuska a daure,a hankali ta saki Yarinyar mai talla da alama ta ji abunda ya fada da turanci,d’an ja da baya tayi kad’an,kasa-kasa tace “Don kana da kyau zaka wani daure ma mutane fuska ni ba ruwana da kyaun ka ehe” Still yayi yana kallon yarinyar don yaji duk abunda tace,lallai yarinyar bata da kunya ya ayyana a ransa,”Wuce kibar wurin nan before I slap ur face”ya fada tare da nuna mata hanya da hannu,A hankali ta fara tafia cikin lungun tana turo baki tana waiwayen su,kallon yarinyar da ke dauke da bokitin talla yayi”Wuce ki tafi” ya fada yana nuna mata hanyar da suka fito “To”,ta fada tana gyara Yellow din hijabinta da ta cukwikwiye ta fara tafiya,shima juyawa yayi ya nufi inda motarsa take,

“Wayyo Allahna! ta 6arar man da Awara…!” Yarinyar ta fasa kuka tana fadi da sauri mutumin ya juyo,da wani irin expression yake kallon yarinyar da ta 6arar da awarar,Ashe ba tafiya tayi ba tana ganin ya nufi motarsa ta fito da sauri tasa hannu ta ture bokitin Awarar,ganin yadda yake mata wani irin kallo yasata jin tsoron shi rugawa tayi a guje cikin lungun ita kuwa mai awarar muryar ta kawai ake ji sai faman ihu take tana fadin”Wllh bazan yarda ba sai an biyani gidanku zan biyo ki,Muguwa,Azzaluma kawae”d’aukko bokitin tayi wanda ya rigada ya fashe ganin haka yasa ta sakin wani sabon kukan,
A hankali ya juya ya koma inda take tsugunne tana d’ibar awarar tana zubawa cikin bokitin sai faman kuka take,tsayawa yayi a kanta,d’ago kanta tayi cikin kuka tace”kagani sai da ta 6arar mn da awarar ko,kuma wllh bashin waken soyan da mai Innarmu ta amso sai na sayar za’a kai kudin gashi ma har bokitin ya fashe wllh gidansu zani sai an biya ni” ta k’arasa maganar da matsanancin kuka.
“Is okey,just leave the rest” Ya fada,dagowa tayi tana kallon shi da alama bata fahimci mi yace ba,”tashi kibar sauran, baki ga yayi k’asa b” Ya fad’a gently, mik’ewa tayi tana ta sheshsheka cigaba da magana yayi a hankali”Miya hada ki da ita? “Wllh ba abunda nayi mata kanwata ta tare rannan wai sai ta bata alakoro ita kuma tace bazata bata b,shine ta buge ta,kuma ta d’ebi awarar,da Innarmu taji shine taje gidansu da kanta don ayi mana tsakani don ba lokacinne na farko ba da take taremu tace mu batan,to shine aka bugeta yau tana ganina tace tunda Innarmu tasa aka bugeta sai taja mata asara sai dai in tasa a kasheta,ba yad……..”its okey”ya katse ta, da alama ya gaji da sauraronta,”Ina ne gidan ku? ya tambayeta a takaice,”Acan layin baya muke gidan Alhaji Sani karofi anan babanmu yake gadi cikin gidan muke acan baya”takae maganar tana goge kwallan idonta.

“Shi abun naki na nawa ne? ya tambaya.”Awarar dubu da dari biyar ce gashi ta zubar da ita duka yar kadan ce bata baci da k’asa ba,inaga ma ko ta d’ari biyu bata wuce ba,wllh gidansu zanje sai anbiya mu ta k’ara fashewa da kuka,da alama taji zafin abun sosai, Sigh yayi kafin yace”You know what,ku kyaleta kawae tunda bata jin mgn in kun k’ara zuwa kun kai karanta zata k’ara zubar maki da abu,calmly yayi maganar,Hannu yasa a cikin aljihun wandon suit din jikinsa bak’ar Wallet ya fiddo mai kyaun gaske ya bude,Kudi ya kirgo sababbi fil kamar lokacin aka buga su,mik’ama yarinyar yayi wadda ke tsaye ta kafe sa da idanu tasa hannu da sauri ta kar6a,aje fasassan bokitin tayi a kasa ta fara kirga kudin dubu ukku ta gani da tsananin mamaki ta d’ago lokacin har ya juya da sauri tace”Yallabai kudin sunyi yawa ai” Hannu yad’an daga ba tare da ya juyo ba yace”ku siya sabon bucket da sauran” ya cigaba da tafia wurin da motarsa take,
Mai tallan kuwa har lokacin juya kudin take da mamaki hakanan bai santa ba ya bata har dubu ukku da sauri tabi bayansa tana fadin “Yalla6ai,yalla6ai…” lokacin har ya kama k’ofar motar zai bude jin yadda take ta faman kiransa da yallabai yasa shi juyowa”What again? Ya tambaya da kosawa,”umm dama²…. ta kama inda-inda sakamakon kafeta da ido da yayi,ya lura da yadda ta dabarbarce,dan sakin fuska yayi yace”Uhum ina jinki dama me? Dama so nike in tambayeka in innarmu ta tambayi wanda ya ban kudin wa zance mata? ta k’arasa maganar tana sunnar da kai k’asa”just tell her wh….ki fada mata abunda ya faru kawai”ya juya zai shege cikin motar, da sauri tace “ai tana iya cewa k’arya nike ni na tsara hakan kullum tana ce mana kar wani ya bamu kud’i bamu san shi b,ko yace zai siye mana yayi mana abunda bai dace ba”ta gama maganar kanta a kasa…

Download A Sanadin Makwabtaka Book 1 Complete

Proceed with your download by clicking the below button

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button