Zakuna Biyar Page 28 By Princess Teema
Hands gloves ɗin hannunsa Dr James ya gyara tare da tsayawa a gaban ɗaya daga cikin kwalaben, idanunsa a kan na’urar dake nuna gudun buguwar zuciyar babyn. Hannu yasa ya yi pressing wani number dake jiki, ɗan jim ya yi kafin ya ɗauko wani leda dake jikin kwalbar. Hannu yasa ya yage ledar, wani farin abu mai kama da towel ya fitar.A gefe ya ajiye tare da ɗauko almakashi da sauran abin da zai buƙata suma ya ajiyesu a jefe. Wasu nurses ne suka fara shigo da gadajen babys a jere, shirya beds ɗin suka fara yi a kusa da kowani kwalba. A cikin wannan na’urar dake jikin kwalba ɗin Dr ya danna open control. Take jikin kwalbar ta ɗan motsa, kafin wani ɗan lokaci kwalbar ta buɗe daga ta sama, yadda kuka san ana yiwa cikin mace tiyasa a fitar da baby, haka suka yi, yasa hannu ya fito da jariri, like seriously! Babyn da cibiya a jikinsa, sak yadda uwa take haihuwa, babu wani banbanci, watau basu fito ba sai da suka shirya, karya ne su kyankyashe yara a iya banbantasu da waɗan da uwa ta haifa tsabar kwarewa!.Wannan abin da ya fitar a leda kamar towel ɗin ɗauko ya naɗe babyn a ciki, jikin yaron har da jini-jini, da kuma fari-fari haka. Naɗe babyn a ciki ya yi tare da kwantar da shi a saman bed ɗin, sannan ya ɗauko wani leda ya yaga ya sake fito da wannan zani mai kama da towel ɗin, goge yaron ya fara yi tare da ɗauko cutton ya cigaba da goge kunne da tafin hannun yaron.Daga bisani ya yanke mashi cibiya, bayan ya yanke ya ɗauko olive oil, man zaitun dai tamu ta gargajiya, dan a kayan kowani baby da aka kawo akwai man zaitun ɗin. Jikin yaron ya shafe da man tare da ƙara kudundunesa saboda ya ga yana rawan sanyi sosai.Kafin ya matsa daga wajen sai da ya tabbatar yaron ya yi kuka, sannan ya gama mashi komai ya matsa izuwa kwalbar gaba. A haka suka ciro dikka yaran nan, amma fa kwanaki biyu suka ɗauka, dan yara sama da 150 ba wasa ba, sun ɗauki kwanaki biyu suna wannan aiki. Bayan sun kammala tsab aka shigar da yaran wani ɗaki dake gefe, yaran sai kuka wasunsu suke yi. A wannan ɗaki ƴan matan nurses sun fi 20 a ciki, yadda kuka ga ungorzoma ke yi wa jarirai wanka haka nurses suka wanke yaran gabaɗaya. Cikin tsadaddun kayan sanyi aka shirya yaran. Dikkansu aka kwantar da su a kan gadajensu, amma sun ɗauki kwanaki huɗu suna wannan aiki, idan kuka haɗa da kwanaki biyu na fito da su ya haɗu kwanaki 6 kenan.Ya ALLAH, idan kuka ga yaran nan sai kun sake kallonsu, wlh lafiyayyu da su, ga wayau, dan sai ɗaga hannaye da kafafu suke suna buɗe baki alamar neman abinci suke yi, wlh yaran sun haɗu, gwanin burgewa, tamkar ka zauna ka yi ta kallonsu kada ka daina. A kwanaki na bakwai da fito da su da daddare 3D suka shigo ɗakin da jajiran ke kwance, dikka nurses dake kula da babys ɗin suna barci, akwai gadon nurses guda 10 a ɗakin, su 20 ne kuma suke kula da yaran, dan haka gado ɗaya mutum biyu suke kwana.5 na yamma 3D suke tashi daga aiki su koma gidansu, amma yau da misali karfe 12 na dare sai gasu a cikin hospital ɗin, kuma a SECTION D wajen babys ɗin. Kunna ainahin light na ɗakin suka yi, dama nurses ɗin sun kashe haske suka kunna dim. Take haske ya gauraye ko’ina, dikkansu 3D suna sanye cikin shiga iri guda, sleeping dress mai kyau da tsada, amma hannayensu sanye da hands gloves, sannan face mask a fuska, iya idanunsu kawai kake gani. Wasu irin gadaje suka shigo dasu wanda yake tamkar kwai, yana da marfi, sannan akwai oxygen a cikin gadon, ko an rufesa babys zasu yi numfashi. Tin da suka shigo babu wata nurses da ta iya motsawa, dik suna barshi tamkar waɗan da suka sha maganin barci.Wasu babys ɗin idanunsu biyu suna wasan dare da yara suke yi da ƴan kafafunsu da hannayensu gwanin burgewa. Daga layin farko suka fara selecting yaran suna ɗauka su sanya a cikin wannan gado mai kama da incubator da suka shigo da su.Abin mamaki kuma ba kowani baby suke ɗauka ba, da alama akwai abin da suke dubawa kafin su ɗauka, dan sai su tsallake yara uku ku ga sun ɗauki baby na huɗu, haka suka dinga bi suna zaɓa, sai da suka zaɓi yara guda 100 ciff, suka shiryasu a waɗan nan gadaje, sannan suka fara turawa suka fita da su waje. Tin da suka fara aikin nan babu wanda ya yi magana a cikinsu. A tsakiyar babban filin SECTION D suka dinga shirya gadajen, suna shiryawa guards na cikin hospital ɗin suna ɗaukarsu su kai parking lot na hospital ɗin, akwai wasu kattin motoci guda uku masu kwantaina a bayansu, a cikin bayan ɗaya daga cikin motocin guards ɗin suke shirya yaran.Guards guda 5 ne suke wannan aiki, guards ɗaya sai ya ɗauki babys biyu da gadajen nasu, abin mamaki kuma babys ɗin tin da aka sanyasu cikin wannan sabon gadon nasu dik wanda bai yi barci ba ma ya yi, basa motsi har aka shiryasu tsab a cikin, mota ɗaya ya ɗauki dikka gadaje 100 a bayansa. Su kuma 3D suka koma cikin baby safe room ɗin suka gyara sauran babys ɗin, suka cire gadajen da aka ɗauke babys ɗin kai, suka gyara saura babys 55 da suka rage, suka shiryasu tsab, sannan suka kwashi gadajen dake empty ɗin suka fita da shi.Sannan suka dawo suka kashe wutar ɗakin, suka kunna masu dim light ɗin. A tare suka jera izuwa parking lot ɗin, already guards ɗin sun gama shirya komai. Dr Mark ne ya karɓi wata katuwar rigar sanyi mai kauri da tsawo daga hannun guards dake tsaye a gaban motar da aka shirya babys ɗin. Sanya rigar ya yi a jikinsa kafin ya karɓi p-cap ya sanya, ya gyara nose mask ɗinsa kafin ya karɓi glass ya sanya.Sannan ya shiga gidan gaba driving seat na kwantainar, da alama shi zai ja motar, guard guda ɗaya ya shiga gidan gaba shi ma…….. “Safe journey”. A tare Dr Kamal da Dr James suka faɗa. Kai kawai ya jinjina masu tare da tada motar, a lokacin karfe 4 na asuba ta yi. Sai da suka ga fitarsa ta wata katuwar gate dake wajen parking lot ɗin, sannan suka juya izuwa gidansu. TO FAH, INA AKA KAI BABYS ƊIN KUMA? ME ZA’AYI DA SU!. Ni kaina tsoron abin da alƙalamina zai rubuta nike yi!.Washegari da safe kamar yadda suka saba haka nurse’s ɗin suka tashi, tin asuba suka fara yi wa babys ɗin wanka game da haɗa masu madara masu ɗumi, dik wanda suka yi wa wanka suka shirya shi sai su haɗa mashi madara, akwai wani na’ura dake jikin gadonsu, an yi shi kamar hannun mutum, a jikinsa ake maƙala masu fidar madara ya sa masu a baki su yi ta ja kamar nonon uwa bayin ALLAH. Basu san uwarsu ba, basu san uba ba, su dai kawai yaran kwalba ne da aka kyankyashe, basu san daɗin nonon uwa ba sai dai madara, ya ilahi, ko wannan musifa bai isa yasa tausayi a zuƙatan masu sayar da sperm and eggs da mahaifarsu ba? Ko dan rashin madogara da yaran nan zasu tsinci kansu bai isa ku ji zuciyarku ta karaya ba? Bama ku san me ake yi da yaran ba tukun nan!.Ko kaɗan nurses ɗin nan basu damu da babu raguwar babys ɗin ma, da alama sun saba kowai shekara za’a kyankyashi jarirai kuma bayan watannin da basu kai uku ba dik jariran suna zama babusu, so kunga ba zasu damu da cewa an kwashi wasu babys ɗin ba.Suka shirya yaran tamkar yadda suka saba, dik babys ɗin babu wanda yake kuka sai wani jariri guda ɗaya wanda tin da aka haifi ɗan nan yake tsala kuka, da alama yana da rikici, dan wani lokaci sai nurse ta ɗaukesa ta yi ta faman jijjiga shi, yana da rikici sosai fiye da yadda ake tinani, kuma yana da mugun wayau sosai, dan shi yana jin madara a baki yake damkewa ya fara sha, but sauran yaran sai sun ji yana zuba su dinga lashe baki, basu iya tsotsa sosai ba.Wani abin mamaki kuma wlh yaron ya fi kowannensu kyau, ya fita daban a cikinsu, yana da violet eyes sak irin na Seraphina, yaron fari tas tamkar madara, ya fi saura dikka haske, ɗan bakinsa nan sak na Seraphina, kai a taƙaice suna mugun kama da Seraph tamkar an tsaga kara, ni da kaina sai da na girgiza da ganin wannan yaro, wlh kamar ka sacesa ka gudu da shi, wayau kamar Seraphina, ga rikici ma kamar ita yadda take rikita mana Aryan Champion namu.A ɓangaren 3D kuma yau su biyu ne a zaune a office na Dr James, Dr Mark bai dawo daga kai babys da ya tafi ba, suna zaune suna hira, Dr Kamal ya ce. “Lazy tana wasa da hankalinmu sosai fa, amma meyasa ka yi mata shiru ne?”.Dr James dake faman cike form da rubuta jariran da ake fita da su ne ya amsa da. “Taimakona ta yi ai”…… “Ban gane ba”. Dr Kamal ya faɗa cike da mamaki a kan face ɗinsa…… Ɗagowa Dr James ya yi, a kansa ya sauke idanu kafin ya amsa da. “Dama ina neman hanyar da zan wahalar da su Zinta ne ai, su saba da juriyar da kwarin zuciya, kasan bana son mutum mai rauni, kuma I love Zinta more, shiyasa nike son horata ta zama mai taurin zuciya”. (ALLAH yasa ka horata ta zama mai taurin zuciya ta fara cin ubanka! Jama’a ku ce Amin, shege tsinanne!)Wani shu’umin murmushi Dr Kamal ya saki kafin ya ce. “Shiyasa kake fakewa da ka yarda da karyar Lazy kana soke masu aiki ko? Gaskiya mutumin baka da kyau fa”……. “A tinanin Lazy ita ta mum wayau ai, I will continue using her to achieve my goals, but one day one time”.Dr Kamal ya karisar mashi da. “The game will be over”…….. Shiru ya ɗan yi tare da mayar da hankali kan rubuce-rubucen da yake yi. Bayan ya kammala ya cire wasu fareren takarda guda biyu. A saman keyboard laptop dake gabansa ya ɗaura su, sannan ya ɗauki table phone ɗinsa, sister Lazy ya dannawa kira.Bugu ɗaya ta ɗauka tana wani karya murya. “Jeki turo mun Maya da Zinta”. Ya faɗa ba tare da jiran amsarta ba ya katse kiran. Takaici tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu, wani irin dogon tsaki ta ja tare da miƙewa tsaye. Fuuuu ta fita tana wani huci tamkar zata kama da wuta. Kai tsaye SECTION C ta nufa, yau suka kammala aikin haɗa chemicals da aka rubuta masu a document ɗin, dik sun gama haɗawa, a yau suka koma ainahin office ɗinsu sai ga sabon sammaci, ko hutawa bai bari sun yi ba.Sai da Lazy ta zagesu fes kafin ta ce su wuce 3D na kiransu. Da sauri suka miƙe, dama kiran suke jira, sun kammala aiki suna jiran su ji result ɗinsu. Sai masifa sister Lazy ke zazzaga masu, amma basu wani damu ba. Suka bi bayanta, a office ɗinta ta tsaya tare da ce masu su wuce ciki.Da sauri suka shige ciki suna dafe kirjinsu dake bugawa da karfi. Tin da suka shigo ta ƙasar ido Dr James ya fara satar kallonsu har suka iso in da yake, har ƙasa suka durkusa suka ɗaga masu gaisuwa.Basu amsa ba, cike da bada umarni Dr James ya miƙo masu paper ɗin tare da cewa su yi sign. Jikinsu na rawa suka miƙe suka fara sign da pen ɗin da ya basu. Sai da suka yi sign ɗin suka gama sannan ya miƙe tare da ce masu su ɗauki paper ɗin su biyosa.Ya faɗa tare da wucewa gaba, da sauri kowacce ta ɗauki nata paper ɗin suka rufa mashi baya. Miƙewa Dr Kamal ya yi ya rufa masu baya yana cigaba da yaba kyau irin na jinin Muhammad, yaran sun haɗu, a cikin ransa ya ce. “Gaskiya karshen Muhammad bai yi kyau ba! Ya yi mana aiki cikin ruwan sanyi yaki, ga shi ya jawa kansa, mun saka shi yin aiki dole, mun kashe banza, mun kuma cire abin da yake taƙama da shi, sannan yau in mun ga dama zamu sake kyankyasan Muhammad sabo tin da muna da spem ɗinsa, mun kashesa kuma muna shirin mallakan ƴaƴansa, su haifa mana masu irin ƙwaƙwalwar tasa, ya zo a banza kuma ya koma a banza, ja da 3D baa haifi mai yin wannan ba!! Mutuwa da kanta tsoron 3D take ji bare ɗan adam”.Ni kam na ce mu faɗawa Dr Kamal cewa IRON FIST jinin daddy Muhammad ɗin ne ko kuma dai mu yi shiru su faɗa mashi? Mu faɗa mashi Lion watau Zayra’an first born of daddy Muhammad yana numfashi a doran duniya ne ko mu yi shiru? Na ce mu faɗa mashi daddy Muhammad ba zai mutu a banza bane ko dai mu yi shiru? Na sake cewa mu faɗa mashi cewa Lion shi kaɗai gayyace, shi kaɗai bataliyar runduna guda ne ko kuma dai mu yi shiru? Na sake cewa mu faɗa mashi Lion ya dame daddy Muhammad a dik abin da suke zato ne ko kuma mu yi shiru?. To ku ba don abubuwa da suka sha kan IRON FIST ba kuna tinanin izuwa yanzu ba zasu zaƙulo 3D bane? Abubuwa sun masu yawa, ba ƙasa ɗaya ba, suna cikin ƙoƙarin warware wannan basu gama ba wata ta kunno masu kai, amma very soon zasu samu natsuwa, zasu juyo ta kanku ne! Kuna ganin kamar ba wanda zai iya zaƙuloku, to sai dai idan ba jinin daddy Muhammad ba!!Kai tsaye cikin SECTION D Dr James ya shiga, su Maya na biye da shi. Ɗakin da babys ɗin suke ya shiga da su. Tin daga bakin kofa suke jiyo kukan wannan baby mai kama da Seraphina namu, hakan yasa da Dr James ya shiga ya umarci a miƙo mashi yaron. Da sauri nurse dake rike da babyn ta kawo mashi shi. Maya tsabar son yara har ta kai hannu zata karɓesa, tamkar zata kwacesa ma, ta manta cewa 3D ne ya ce a miƙo mashi shi. Karɓarsa Dr James ya yi tare da ɗagasa kaɗan yana kallon babyn. Da ya haɗa ido da babyn sai da ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya yi tinanin saboda violet eyes na yaron ne yasa ya ji hakan.A saman shoulder ɗinsa ya saɓa babyn tare da kallon nurses da suka zube gwiwowinsu a ƙasa suna zuba masu gaisuwa……. “Dik ku kwashi komai naku ku koma hostel ɗinku, daga yau aikinku ya kare a nan”. Cewar Dr James.Dik da suna son sanin meyasa, amma basu yi gigin tambaya ba, saboda babu fuska. A hanzarce suka kwashe komai, da sauri suka fice. Zinta da Maya sai kallon babys ɗin suke yi suna jin tamkar su je da gudu su rurrugumi babys ɗin. Amma babu dama, sun natsu saboda 3D dake wajen. “Daga yau ku zaku dawo kula da wannan sashe, zan turo nurse ɗaya ta faɗa maku yadda zaku kula da babys ɗin”…….. Cike da mamaki Dr Kamal ya ce. “Su biyu kacal? Babys ɗin sun yi yawa ai”……… A dake ya ce. “To aikin me suke yi? Sai su wuni aikin babys ɗin! Dama ban kawosu nan dan su huta ba!”. Babban magana, ta ya za’ayi su iya kula da babys guda 55 su biyu kawai? Kuma ba wai sun iya bane, hasalima basu taɓa koda rike baby ba sai yau zasu fara, amma da yake basu san wahalar aikin ba sai daɗi kamar ya kashesu suke ji, har da murmushi.Miƙawa Zinta babyn hannunsa ya yi yana faɗin. “Kada ki bari ya sake yin kuka!”. Tin da ya karɓi babyn yaron ya yi tsit…… Jikinta na kerma ta miƙa hannu zata karɓesa, a lokacin da hannunta ya haɗu da na Dr sai da ta ji wani irin narkakken kaunansa ya ratsa mata zuciya, take ta ji ta kara tsananin son shi. Shi ma wani irin spark ya ji zuciyansa ta yi, amma ya ɗauke kai tare da sake mata babyn. A natse ya juya ya fita ya barsu tsaye kamar wasu dolaye, bayansa Dr Kamal ya bi yana waigo Maya dake ta faman sakin cool smiling tana leƙa fuskan babyn da Zinta ta rike, basu iya rike baby ɗin sosai ba, sun lankwasa mashi wuya kaɗan. Suna fita sister Maya ta ce. “Sister Zinta kina ga babys dayawa, to yaran waye? Ko dai a nan sister Lazy ta ɗauko wancan babyn dama? Yanzu kullum zamu kasance da babys ɗin nan? Wayyo daɗi”. A kiɗime take magana tana zaro idanu, irin she was so surprised na ganin yaran. Murmshi tamkar bakinta ba zai rufu ba, da gudu ta nufi wajen sauran babys ɗin, ta zama tamkar zarariya, tana ganinsu tana murmushi, sai tattaɓasu take yi tana tsalle, dik yaran suna ta wasa na ɗaga kafafu da hannaye, gwanin burgewa, yarinyar nan Maya dik kiɗime ta zauce a kan yaran nan. Ita kuwa Zinta sai faman jijjiga babyn hannunta take yi amma yaki yin shiru, Dr James na bata shi ya fara kukan again, yana ta irin feket-feket kamar yana son yin kukan mai karfin nam, baiwar ALLAH bata taɓa aikin yara ba sai yau, ta ma rasa me zata yi mashi ya yi shiru, sai cewa take yi sorry my baby. Amma ina babu alamar zai natsun nan fa.Kafin ta farga ya fashe da kuka mai sauti, hakan ya jawo hankalin Maya a kanta, idanun Zinta ne ya cicciko da kwallah wai babyn yaki ya yi shiru, har ta gaji, kuma tausayinsa take ji, bata son ya yi kuka.Da gudu Maya ta dawo gareta, a gabanta ta tsaya tare da miƙa hannu ta karɓi yaron, haka kawai suka ji wani irin tsananin kaunar yaron, sai suke jin tamkar jininsu ne koma ɗan cikinsu, har cikin ransu suka jisa. Rungumesa sister Maya ta yi a kirnjinta, ta fara jijjigasa, amma yaki yin shiru. Hakan yasa ta ɗan yi ƙasa da shi, ta haɗe fuskokinsu, tongue ɗinta ta zura mashi a baki. Ai da sauri ya capke ya fara tsotsa tare da yin tsit.Aikuwa Maya sai ta hau tuttula mashi yawonta a baki, shi kuwa yana tsotsan harshenta yana shan yawun nata. Tsalle sister Zinta ta yi, tana farinciki wai sun samo hanyar saka babyn yin shiru, kullum idan yaron ya yi kuka haka zasu dinga yi mashi. Wlh kan ka ce me yaron nan barci ta ɗaukesa, da alama shi nonon uwa na gaske yake so ba madara ba. Ganin ya yi barci ne yasa ta zame tongue ɗinta a hankali, ta saɓa shi a saman shoulder ɗinta, can ƙasa ta ce. “Ina zan kwantar da shi?”….. Nan sister Zinta ta fara rarraba idanu, can ta hango gadon da yake empty, a nan ta gane ga wajensa, ta ce su kai shi wajen. A hankali sister Maya ta nufi wajen da shi. Kwantar da shi ta yi, suka zazzauna a gefen gadajen masu kula da babys ɗin, suna shirin fara yin magan kenan sai ga wata nurse ta shigo. Da ido suka bita, har katsa ta durkutsa ta gaishesu kafin ta faɗa masu ita ce wacce aka ce ta zo ta koya masu kula da babys for two days. Fuska ba yabo ba fallasa suka tarbeta tare da bata wajen zama, daga nan ta hau yi masu bayani, suka kasa kunne suna saurara, sai murna suke yi sun samu yara. ME KUKE TINANIN ZAI FARU JAMA’A?.A ɓangarensu 3D kuwa, wannan meeting room ɗin nasu suka shiga. A saman sofa suka zauna tare da kunna wannan makekiyar computer dake a gabansu, wasu lambobin Dr James ya shigar, take ya danna call. 3 times ya yi ringing sai duhu ya baibaye computer, after 3 seconds sai wasu mutane suka bayyana a gaban screen ɗin. Fararen mutane ne tas, suna sanye da rawani irin yadda larabawa ke sanyawa, kuma suna sanye da thobe a jikinsu, while sun naɗe fuskokinsu da rawanin wanda yasa idanunsu kawai ake iya gani, idanun nasu farare tas da shi.Mutane uku ne, kuma da alama manyan mutane ne sosai, dan tin daga kan yanayin shigarsu, yadda suke a natse, amma bayan su na zaka iya gano komai dake bayansu ba sai haske kamar kantarki.Ɗan gyaran murya Dr James ya yi kafin ya ce. “Hope Mark ya iso ku?”….. Ɗaya na tsakiyan ne ya amsa da. “Ya iso mu, mun karɓi saƙo kuma muna godiya matuƙa, kuma zaku ga saƙonku yanzu”. Jinjina kai Dr James ya yi. Da rufe bakinsu bai kai mintina biyu na sai computer ta yi ƙara. Yana zubawa alert ne ya shiga babban account ɗinsu na hospital ɗin wanda su dikka suke amfani da shi.Kimani dala miliyan 200 ne ya shiga cikin account ɗin. Hannu Dr James ya ɗaga ya jinjina masu alamar komai ya tafi daidai. Kai suma suka jinjina kafin na gefe ya ce. “A gaskiya waɗan nan kaya suna mana kaɗan, bamu ki kowani shekara mu dinga samun jarirai 500 ba, ku kara kokartawa”. Cikin harshen turanci suke magana.Kai kawai Dr James ya jinjina masu alamar ya ji, daga haka suka yanke kiran. Suna yankewa sai ga wata kira ta shigo. Ɗaukar kiran ya yi, wasu mutane ne suma su biyu zaune a saman kujera, amma suma baka iya ganin background ɗinsu, suma dai fuskokinsu a rufe yadda zasu san ba aikin ALLAH suke yi ba.Dr Kamal ne ya ce. “Meke da akwai?”…… Ɗaya daga cikin mutanen ne ya amsa da. “Kaya muke so kimanin 300 a wannan shekara”….. “Zan iya”. Shi ne abin da Dr James ya faɗa kawai kafin yasa hannu ya katse kiran nasu, sannan ya shigar da sunansu a list na masu son jarirai shekaran nan…… Ya rab, wai rai ne ake cikinsa yadda kuka san ana cinikin kayan sawa? Tambaya wai me ake yi da jariran ne? Uhm zan warware komai In Sha ALLAH.Yana katse kiran ya zauna tare da cewa Dr Kamal. “Yakamata ace izuwa yanzu dik shekara muna kyankyasan 1000, 150 zuwa 200 ya yi kaɗan, mu kanmu a nan muna da buƙatar guda 300 a kowani shekara, amma ka duba guda 55 kawai muka barwa kanmu, abin ya yi kaɗan”. Jinjina kai Dr Kamal ya yi game da cewa. “Haka ne, matsalar mahaifar ce, yakamata mu kara mayar da himma, idan ta kama mu kara masu kuɗi mu koma saya 100 million dan mu samu sosai, yanzu mahaifareda muke da shi a ƙasa dik bai wuci 200 ba fa”…… Shiru Dr James ya yi, nazari ya fara yi kan yadda zasu bi ko ta halin ƙaƙa su samo mahaifa, ya ci alwashin kyankyashe jarirai 1000 a wannan shekara mai zuwa..ALLAH sarki ƴan matan da ake cirewa kwai sun shiga uku, yanzu za’a haka takurawa eggs ɗinsu, zasu sake matsawa jikinsu da magunguna dan su dinga sakar masu kyau sasai, imagine ƴan mata guda 50 ne zasu bada eggs guda 1000, ya ALLAH waɗan nan yara sun shiga uku, wannan azzalumin Dr James ɗin yanzu zai yi ta danƙara masu allurai da magunguna, dole kowani wata jikinsu ya bada kwai sama da guda 10 zuwa 20, innalillahi wa inna ilaihir rajiun.Wlh da wannan shegiyar tiyatar da ake masu, a zura masu karfe a gaba a zuƙo kwayayyen ma ai kawai balai ne, bare magungunan da ake ɗirka masu, wannan tiyata ta fi komai wahalar da su, imagine karfe a gabanka, a zura har cikin cikinka, har wajen mahaifarka, a zuƙo ruwan eggs ɗinka, kai ya ALLAH ka tsaremu, ALLAH dik yadda zamani zata juya ALLAH ka taimaka mana ka barmu da imaninmu, kasa mu fi karfin suƙatanmu.Dr Kamal ne ya ce. “Bari ma in kira waɗan da muka bawa contracts na nemo mahaifar mu ji, shin guda nawa aka samo?”…… Jinjina kai kawai Dr James ya yi, tare da jingina da jikin sofar ya shiga tsara irin yadda zai takurawa jikin ƴan matan nan su bashi eggs guda 1000 a ƙasa da watanni biyu, innallilahi wa inna ilaihir rajiun.Jama’a zaku yi mamaki idan na ce maku wannan computer da ake hada-hada da shi, ake saye da sayarwa daga ƙasashe da dama ta cikinsa, zaku yi mamaki idan na ce maku lallai mallakin daddyn Lion ne, da wannan computer ake iya buɗe dik wasu mataƙan tsaron hospital ɗin nan, da wannan computer ake juya dik wasu abubuwa, komai a kanta yake, dik wasu bayanai da abokan cinikayya, dik wata ɓarn da komai, tana da mahaukatan matakan tsaro wan daddynsu Lion da kansa ya sanya mata, baka isa bibiyar na’urar ba, kuma baka isa iya buɗeta ba, da karfin tsiya suka kwaceta daga hannunsa bayan sun sacesa, suka ɗauko har da Computer!. Shi ma Dr Kamal bayan ya gama kiran dik waɗan da suka baiwa contracts kan samo mahaifar mata, ya ji guda nawa aka samu, sai ya sanar da su yanzu ba 80 million zasu saya mahaifar ba, sun ƙara ya zama 100, a nemo masu kawai, yana gama basu bayani shi ma ya jingina da jinin sofa ya hau tunanin yadda zai angwance da Maya.A can Avaris kuwa dik ya haukata likitoci suna ta faman sace mahaifar bayin ALLAHN da basu ji ba basu gani ba, sun ji karin kuɗi, gari ya fara rikiciwa, kowacce mace ta zo asibiti ace mahaifarta ya lalace sai cirewa, wasu masu ciki ace ba zasu iya haihuwa da kansu ba sai aiki, daga yi masu aiki a sace mahaifa.Yanzu ta kowani asibiti a faɗin Avaris halin da ake ciki kenan, magana har ta fara yawa, dan har IRON FIST sun fara jin kishin-kishin ɗin maganar, amma da yake akwai wani babban aiki a gabansu sai basu mayar da hankali a kan wancan batu sosai ba. CRYSTAL PALACE.🔥Lokacin da Aryan ya koma sai ya isko Lion cikin wata shiga ta alfarma, wani irin tsadaddun tail coat fari tas yasa mai kwalliyar zubin na sarauta, tin daga kan cover shoe dake kafarsa zaku san waje na musamman zai je. Ya cire bandejin dake forehead ɗinsa, amma bai cire na hannunsa ba, saboda ya fi jin ciwo a hannun nasa, na kai kaɗan ne.Sai tashin fitinannen kamshi yake yi. Cikin zolaya Aryan ya ce. “Yau mai girma granny zata yi babban bako kenan?”…….. Guru dake zaune yana dannar waya ne ya amsa da. “Zaka bisa ne?”……. Da sauri Aryan ya girgiza kai yana faɗin. “Tab! Zuwa RING OF POWER ai sai shi ɗin! Mutanen da in sun gammu tamkar su zare mana ranmu, dan dai kawai ba yadda suka iya damu ne”. Ya kai karshe tare da wucewa ciki, saboda ya tina baya, da alamar sosuwar rai a kan fuskansa.Guru ne ya ce. “Let me see him”….. Lion dai bai ce komai ba, ya ɗauki wayansa ya fito waje. Kai tsaye sama ya haye, sai wajen sauƙar private jet ɗinsu, sai tashin kamshi yake yi, yau fuskansa ta banbanta da kowacce rana, yana ɗaure tamau tamkar hadari, idanunsa sun nuna alamar yau babu mutunci.Jiga-jigan guards 8 ne a saman wajen su ke kewaye da jet ɗin, dikkansu cikin bakaken suit masu balain tsada, babu alamar wasa a kan fuskan kowannensu. A tsakiyar wajen ya tsaya, sai kuma ya juyo baya. Yana juyowa guru da Aryan suka zo suka yi hugging ɗinsa, rungumesu shi ma ya yi, still bai yi magana ba, babu ma alamar zai motsa kyawawan laɓɓan nasa. Sun ɗauki 5 mins a haka kafin ya sakesu ya nufi cikin jet ɗin nasu. Cikin zafin jini guards ɗin suka take mashi baya izuwa cikin jirgin, sai da ya shiga ya zauna sannan guards biyar suka shiga tare da shi. Kansa a ƙasa yana kallon wayarsa, amma a zahiri su Aryan yake kallo, yana mugun son mutane biyun nan, a duniya a yanzu dai wlh daga Leo ɗinsa sai su yake so, kai baya ma iya banbanta su ya fi so ko Leo.Idan baku manta ba a farkon littafin nan na faɗa maku Leo yana da kaka, amma kakan nasu basa tare da su? To suna da kakanni mace da namiji, amma da mutum ɗaya suke magana, basa yi wa ɗayan magana, hasalima basa zuwa in da ɗayan yake saboda laifin babansu da ya shafesu. Amma mu bi Lion zaku gani!.jirginsu na ɗagawa basu dira a koina ba sai a birnin ELDORIA cinin ƙasar AVARIS. Ya ilahi, kunga wani irin mahaukacin cikar da international airport na ƙasar ta yi da dubban jama’a da motoci kuwa? Ƴan jaridu ta ko’ina, jama’a manya-manyan a ƙasar dik sun ziyarci wannan airport ɗin, Prime Minister na Avaris da kansa ya dira a wannan Airport ɗin domin tarbar Lion da ya zo masu a matsayin Prince ɗinsa. Jerin comboi na motoci dankara-dankara kawai sai da aka jera motoci guda hamsin ciff waɗan da suka zo ɗaukarsa, sojoji, ƴan sanda, da dik wasu kaki sai da suka dira a wannan airport ɗin, jiniya tamkar filin yaki zasu tafi, motocin sojoji 10 ciff suka zo dan takewa motocinsa baya.The only Prince of RING OF POWER kenan…….. Tin da ya sako kafarsa a step na jirgin nan ta koina aka fara kashe mashi pic. Manyan mutane dake tare gefe guda suna jiransa ne suka fara gyara tsayuwa dan ya fito su gaisa. Sai dai tin da ya fito kansa a ƙasa, bai ɗago ba, yana wani irin taku cikin zafin jini, guards biyar ɗinsa suka take mashi baya suma cikin tsananin jarumta, kai tsaye wajen tsadadden motar dake fara tas a cikin jerin bakaken motocin dake fake dan shi ya nufa, gabaɗaya numbobin motar an rubuta PRINCE OF RING OF POWER a jiki, da alama mallakinsa ne kawai motocin, shi kaɗai akewa comboi. A jikin motar ya tsaya tare da juyowa, har lokacin kansa a ƙasa, Prime Minister ne ya fara nufosa cike tsaro da girma, guards ɗinsa suna take mashi baya shi ma. A gaban Lion ya tsaya, hannu Lion ya bashi suka yi musabaha, sannan ya juya ya shiga motarsa, bayan Prime Minister bai sake gaisawa da kowa ba, kuma akwai manya sosai da suka halacci wajen saboda shi, ko meyasa yaki amsa masu?.A jere motocin suka tashi, kai tsaye sai katafaren MASARAUTAR BARTHARUN wacce suke kira da RING OF POWER. Masarauta ce mai ɗimbin tarihi wacce ita ke juya Avaris a yau, su da saurata suke mulki ba siyasa kai tsaye ba. Kamar England, kunga suma da sarauta suke mulkar ƙasa, sarauta ce mai power a ƙasar. To haka Avaris ma, RING OF POWER ita ke da karfi a ƙasar fiye da politics. Masarauta ce da dik wani jarumi ko mai mulki da ya fara mulkan Avaris daga cikinta ya fito, masarauta ce da ita ta kafa Avaris da kewayenta, masarauta ce da ita ta jagoranci mahaukatan mayakanta da basu ɗauki rai a bakin komai ba suka yi faɗa suka kwatowa Avaris ƴanci a hannun turawar mulkin mallaka, shiyasa masarautar take da karfi sosai, ita ta sama masu ƴanci.Kakan Lion namiji shi ya jagoranci mayakansa suka yi fito na fito da Burtaniya a lokacin yana matashi, shiyasa dik wanda ya fito daga wannan masarauta mutanen Avaris mugun girmama shi suke, ana ji da shi, to Lion shi ne the only magajin da masarautar take da shi, shi ne yarima mai jiran gado, Nirash bai san da su a duniya ba, kazalika suma basu san da shi ba, Lion dai shi ne yasan komai, kuma kunga na faɗa maku ya ki faɗawa Leo tarihin iyayensu.Masarautar tana da balain girma, tana da fuskoki biyu da fadoji uku, tana da tarihin mayaka da dawakai, sune suka zo na biyu a duniya a masarautar dake da yawan dawakai da mayaka, su in zasu yi yaki a kan dawakai suke yi, suna da karfin masifa tamkar dawakan nasu, kakansu Lion har yanzu shi yake mulkar masarautar, kuma babansu Lion da Hussaininsa su biyu ya haifa a duniya, amma dik ya rasasu, tin suna raye ma suka bar masarautar.Daddyn Lion zuciyar balai ne da shi, akwai saurin fushin masifa, baya ɗaukar nonsense, baku ji shiyasa su Dr James suka ce sun ci bakar wahala kafin su samu damar kama shi ba? Mutun ne mai haɗari, ya gaji jarumta daga mahaifinsa. Saboda wannan zafin zuciya da ɗan banzan girman kai nasa ya ɗebesa suka yi faɗa da mahaifinsa, shi kuma mahaifin nasa ya yi amfani da power ɗinsa na mulki ya hukuntasa, ya jefasa a kurkukun masarautar tamkar ba ɗan sarki ba, ya ce sai daddyn Lion ya durkusa ƙasa a gabansa ya bashi hakuri, shi kuma daddyn Lion ɗin ya ce da ya bashi hakuri gwara ya sanya takobi ya datse wuyansa ko kuma ya rataye kansa.Kafiyar bala’i daddyn Lion yake da shi, ga shegen zafin kai, aikuwa Iron Sovereign watau King ya ce shi kuma sai daddyn Lion ya ce mashi sorry, ya ɗauki tsawon wata ana ganawa daddyn Lion ɗin azaba, amma taurin zuciyarsa da taurin kansa tasa ya ce sai dai ya mutu a azaba amma ba zai bada hakuri ba. Da mahaifinsa ya ga haka yana tsoron rasa ɗansa sai ya fito da shi, ya ce ya koresa ya bar mashi masarauta cike da sa ran daddyn Lion zai bashi hakuri komai ya wuce.A maimakon ya bada hakurin, sai ya ce tafi nono fari! Wlh yaki bada hakuri, ya gwammaci ya bar family da gatansa ya tafi saboda furta kalmar sorry kawai, ya ce ba’a mahaifi wanda zai bawa hakuri ba! Aka ce ɗan nagada ya fi ɗan na koya, shi ma kakansu Lion ɗin fa haka yake, a lokacin yakin kwato ƴanci da turawa da turawan suka kama shi, a kan ya basu hakuri ne ya gwammaci dik azaban da suka gana mashi, daga karshe duka datse mashi yatsun kafafu, amma dik da haka yaki bada hakuri, yasan halinsa kuma yake ƙoƙarin tursasa mahaifin su Lion da ya basa hakuri.In takaici maku labarin dalilin kenan da yasa daddyn Lion ya komawa US da zama, daga bayan Husaininsa ya ji ba zai iya zama ba, ya rufa mashi baya, dan kamar chewing gum suke! Mahaifiyarsu ta yi ta baiwa Iron Sovereign hakuri kan wai ta bada hakuri madadin ɗan nata, ya yafe mashi, amma sai ya ce yana son ɗansa da bakinsa ya furta wanda kuma shi kansa yasan abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba.Har daddyn Lion ya koma ga ALLAH bai taɓa furtawa wani kalmar sorry ba, kuma tin da ya bar masarautar bai sake waiwayarsu ba saboda bala’in zuciya, sai wani lokaci da mahaifiyarsa bata da lafiya, a lokacin Lion yana da 5 years a duniya, shi ne ya ɗauko shi suka zo, bai je in da Iron Sovereign yake ba, ya duba mamarsa kawai ya bar masarautar abinsa. KUN JI TARIHIN DADDYN LION A TAƘAICE KO?.To Lion ya zo masarautar sau uku bayan babansa ya bar duniya, ɗaya tare da su Aryan ya zo, biyun shi kaɗai, kuma dik yana zuwa ne saboda kakarsa da ita kaɗai ta taimaki mahaifinsa, lokacin da mahaifin Lion ya bar masarautar granny ɗin tasu ce kawai ta ɗebi gwala-gwalai ɗinta ta bashi, ta ce ya je ya saidasu ya rayu cikin farinciki da walwala, shiyasa dik abin da Lion yake yi idan granny ta yi kira zai amsa, yanzu ma ita ta kirasa kan ya zo. And mahaifinsa kafin ya rasu ya faɗa mashi ya kula mashi da mahaifiyarsa, kullum maganarta kawai yake yi, ita kaɗai ta tsaya mashi, ita ɗin uwa ce da kowa zai yi burin samun irinta, so shiyasa Lion yake tare da ita. Abin da yasa baya zuwa wajen kakansa namiji kuma, kakan nasa ya ce ba zai karɓi Lion a matsayin magaji ba har sai ya zo ya durkusa a gabansa ya bashi hakuri, watau ya yi abin da babansa bai yi ba kenan, idan ya yi haka zai karɓesa a matsayin magaji.Shi kuwa Lion ya fuskanci kakan nasa ido da ido ya ce waye ya ce mashi shi Zayra’an yana neman a karɓesa a matsayin magaji? Baya da buƙatar sarauta a rayuwarsa, kai family ma kanta baya buƙata bare wata sarauta, wlh shi Zayra’an da ya bada hakuri, da ya furta kalmar sorry gwara ya kashe kansa. Babbar magana, King ya ga wanda ya fi daddyn Lion izza da isa, watau dik da yasan kashe kai ba kyau amma da ya bada hakuri gwara ya kashe kan nasa.To shi ne suka raba jaha da Iron Sovereign ɗin, saboda ya ce ba zai bada hakuri ba, shiyasa kuma kuka ga Lion ya tsani kalmar sorry, ya ce ba zai taɓa furtawa ba! Kuma waɗan da suke tare da shi ma ba zasu furta ba, yanzu ko kashe Leo zaku yi ba zai taɓa ce maku sorry ba, sun ce da zu furta wannan kalma gara a kashesu! Tin da a kan kalmar aka kori babansu daga dangi, to ba zasu furta ba!……… E to akwai kura, mah people me kuke tinani ne wai?.Tin da suka danno hancin motocinsu cikin katafaren gate na farko na masarautar na fara ganin wasu irin kyawawan mutane masu cikar kyau da haiba, sai dai fa mutanen suna da abin al’ajabi, dik wanda zaku kallah a cikin masarautar yana sanye ne da wata iriyar shiga ta ban mamaki, wasu irin king tail coat suke sanya da. Kuma abin mamaki mazan masarautar su suke yin kitso, mata kuma sai su ɗaure gashin kansu gida biyu su sako jelar ta saman kafaɗa.Ashe ga daga in da su Lion suka gado kitso a kai, daga wajen daddynsu suka gada, shi kuma daddyn nasu kunga daga nan Masarautar ya girma da shi kenan, al’adarsu ce, dole maza suna kitso mai shegen kyau, sai su ɗaure jelar gashin su yi tuntu da shi. Wasu kuma kitso baya wuce dogaye kwara uku suke yi, sai su yi amfani da kitson su ɗaure gashinsu da shi su yi tuntu, style na kitso dai kala-kala, kuma da yake gashinsu yana da tsantsi da kyau, baki da sheki ba karamin kyau kitso yake yi masu ba!A kaf masarautar babu mai golden hair sai Lion, kada ku manta shi ma a wajen mom ɗinsu da ta fito daga kabilar Pamira ya gado golden hair ba daga wajen daddynsu ba. So shi kaɗai ne mai kalar wannan gashi, shiyasa ya kara fita daban a cikin daban na mutanen masarautar. Yana da causin dayawa, da sauran ƴaƴan ƴan uwan Iron Sovereign, amma dai shi kaɗai ne magaji.(Kun san me? Mutanen Ring Of Power nan sun tuna mun da mutane Birnin Black World na littafina na RAWANI ZALINCI! Mutane Big Bro Black Tiger namu, su kuma irin shigar Annabi Isa suke yi, amma su basa kitso a kai, su kuma wannan masarauta maza da kitso ita ce al’ada, mata kuma da tara gashin a ɗaure! Wlh sun tuna mun Black Tiger ɗinmu na amana!.)One thing about mutanen Ring Of Power rana suke bautawa ba ALLAH ba, so ba musulmai bane, harta kakan Lion ba musulmi bane, yanzu haka basu san Lion Musulmi bane da abin ya tsananta, shi daddyn Lion ALLAH ne ma ya tsaga da rabon musuluntarsa, ALLAH ya tsaga bai da rabon wahala, da ya bar masarautar ne ya samu damar musulunta ta dalilin mom ɗin su Lion ɗin, kun san ba zai auri musulma yana matsayin mai bautar rana ba ko? To dalilinsa kenan na musulunta a farko, ita ta koya mashi komai na addini kafin addinin ta tsara shi ya shiga neman ilimi gadan-gadan, dan haka family ɗin Lion masu bautawa rana ne, kuma basu san shi musulmi bane! Bama su san daddynsa ma ya musulunta ba, and Lion bai taɓa zuwa masarautar ya kwana ba, idan ya yi wuta ne ya yi awa biyu a ciki ya koma, da sun san Musulmi ne ai da bala’in sai ya fi haka, rikicin ba zata kare ba!.Tin da motocinsu suka shigo dik wani mai rai ya natsu tsit, kowa ya shiga taitayinsa, dan ba’a taɓa wanda ya taɓa fuskantar Iron Sovereign ya faɗa mashi magana kai tsaye ba sai Lion, ko daddynsa a lokacin da ya yi taurin kai wlh baya fuskantar baban nasa gaba da gaba ya faɗi magana, sai dai ya faɗa a bayansa a mayar mashi.Amma shi Lion ido cikin ido ya dubesa ya ce. “Da in durkusa in baka hakuri gwara na kashe kaina! Kuma ni ban ce maka ina da buƙatar a karɓeni a matsayin magaji ba! Bani da buƙatar sarauta a rayuwata, haka kuma bani da buƙatar family!”. Wannan magana ta yi matuƙar gigita Iron Sovereign, domin babu wanda ya taɓa kallon cikin idanunsa ya bashi martani, Lion ne na farko, kuma daga kansa baa sake samun wanda ya yi hakan ba! To wannan dalilin yasa kowa yake shakkar Lion, idan ya zo waje dik wani halitta mai rai natsuwa yake yi. Suna parking na motocin aka buɗe mashi kofa, take busa ya karaɗe ko’ina a cikin masarautar, The Crown Sentinel ya iso, ta ko’ina taken girma ake mashi, dik wasu bayi da kuyangu zubewa ƙasa suke yi a in da suke suna bashi hanya har sai ya wuce.Wlh The Iron Sovereign yana mugun son Lion, kawai ɗan banzan girman kansu na gado ne yasa yake ganin ba zai iya janye batun sai Lion ya bashi hakuri zai karɓesa matsayin Crown Sentinel ba, amma da ya ji ya zo ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da leƙasa ta view ɗin ɗakinsa saboda yana cikin room ɗinsa can saman bene mafi tsawo a masarautar.Kai tsaye babban sashen masarautar Lion ya nufa, in da uwar gida kuma amarya take kenan, kuma ita kaɗai ce matar sarkin, dan su a al’adarsu mace ɗaya suke aure, shiyasa yake da ita kaɗai.Tin daga nesa ake zube gwiwowi a kasa ake kwasar gaisuwa, idan sun durkusa ma sai sun kifa kansu a ƙasa, al’ada ce haka suke yi wa Iron Sovereign ɗin nasu, so shi ma Lion kamar haka suke girmama shi. Kai tsaye cikin katafaren ginin ya shiga. Dik masu gadi a wajen sai da suka zube ƙasa, tare da guards ɗinsa suka shige, sai da ya zo kofar babban parlonsu ya ɗagawa guards ɗin hannu alamar su tsaya. Tsayawa suka yi shikuma ya wuce ciki.Yana shigowa wasu mata suka fara buɗe shi da hayaki wai na addu’ar da aka yo daga rana, Lion zai yi albarka. Ai yana ɗago idanu gabaɗaya matan suka dare suka bashi hanya, wasu har da faɗuwa a garin gudu, ƴan hayakin ƙaniya, ashe wargima waje yake samu, har da wani munafikin fure a kan tiren hayakin da wani munafikin tiraren wuta na tsinke. Dama sai da matan suka ce su suna tsoron yi mashi wannan hayaki, amma granny ta kafe lallai su yi mashi ai ita ta ce. Wai tana jin kamar ba zata sake ganinsa bane, shiyasa tasa a nema mashi rahama daga rana, ai mashi addu’a, dan tana ganin kamar ganin karshe zata yi mashi.Ta tsufa sosai da sosai, komai yi mata ake yi, zata kai 65 years a duniya, to tana jin kamar lokacin tashin ruhinta sama izuwa wajen hasken ranar da suke bautawa ya kusa, dan su basu yarda da akwai mutuwa ba, sun ce tashi sama ruhunsu yake yi, ya shiga cikin hasken rana ya zauna, to kunga wanda ya mutu baya dawowa bare ya dawo ya basu labarin ba haka abin yake ba sun canza salo da dabara, and su a nan gawa konawa ake yi, hasa binnewa, idan ruhu ya tashi sama ya shiga hasken rana, sai shi kuma gawa a konesa a hure tokar ta tabi iska.Kafin Lion ya yi magana ko mutum ɗaya bata rage a cikin room ɗin ba, dik sun fice da gudu. Takowa ya yi izuwa gaban gadon da granny ɗin nasu take kwance. A gefe ya zauna tare da yin ƙasa da kai. Da sauri dik kuyangun dake hidimta mata a cikin ɗakin suka nufi waje, dattijuwar tana ƙudundune cikin bargo kato na alfarma, ga king bed ɗin nata ya yi wani irin masifaffen haɗuwa. Ɗakin haske tankar tamkar tsakiyar rana suke saboda kwayayyen chandeliers na alfarma dake haske ko’ina. Shiru bai iya yin magana ba, yana dai duke da kai, umarnin daddynsa kawai yake bi, ba dan haka ba shi ba zai zo wannan masarauta ba, ba zai sake zuwa kusa da mace ba, amma daddynsa ya ce ya ɗauki granny a matsayin shi ne, idan ya saɓa mata tamkar shi ya saɓawa. Amma fa dik da wanna wasiya baya wani bi, yanzu haka sai da tai mashi kira ya fi sau goma, yaki ɗagawa ma bare ya ji menene, sai da ta sanya aka rubuta mashi saƙon tana gadon jinya, sannan ne ya yi reply da yana zuwa, tin last month aka yi hakan sai yau yaga damar zuwa ɗan duniya.Jin shirun ya yi yawa ne yasa ta ce. “Edward Harrison ba zaka mun magana bane yau ma?”….. Da kyar maganarta yake fita. Edward Harrison shi ne sunansa da suna sanya mashi, Harrison sunan babansa ne, basu san ya koma Muhammad ba. Lion da iskanci yake, akwai wata shekara da ya taɓa zuwa, tin da ya zo har ya ɗauki awa ɗaya a zaune ya koma bai yi wa kowa magana ba har dattijuwan, kuma tin daga wannan zuwa bai sake ba sai yau, shi ne take tambayar ko yau ma ba zata samu damar yai mata magana bane. Shiru babu alamar zai amsa mata, ganin haka yasa ta sake cewa. “Edward ina ganin kamar lokacin ɗaukakata izuwa sama ya yi, shi ne yasa na ce a kira mun kai”. Ta dakata saboda yanayin jikin bata iya magana mai tsawo. Babu alamar Lion zai tanka mata bawan ALLAHN nan, ko motsi bai yi ba.”Idan ruhunana ya ɗaukaka zuwa sama Edward kai nike son ka zo ka ƙona gangar jikina, ka sheke tokata mai daraja”. Ta sake yin shiru cike da sa ran zata ji muryansa, amma ina bai motsa ba. “Edward iyayenka Harrison da Robertson kawai dudu (ranan da suke bautawa suke kira da dudu) ya bani, yanzu kuma kai kaɗai suka bar mun, Edward ka yi magana mana in ji daɗi, ina jin kamar Harrison ne yake magana idan ka yi, ka bani kalamanka na karshe”.”Zan tafi”. Shi ne kawai abin da ya furta tare da miƙewa tsaye…… “Edward please ka fuskanci kakanka ku sasanta, ka mashi abin da…..”. Kasa karisawa ta yi saboda ɗago idanun da ya yi a kanta, kara ɗaure fuska tamau ya yi, bai sake yin magana ba ya juya ya fita abinsa. Bai sake bi ta kan kowa ba, ya wuce ya shiga mota dan komawa, Iron Sovereign yana ta faman leƙansa ta view, yana gani Lion ya koma sannu bata haɗasu ba. Ko yaushe wannan gaba zata zo karshe kuma? Kowa sai ji da girman kai da zafin rai game da taurin zuciya. Wannan kenan a ɓangaren Lion, to mu leƙa ɓangarensu Seraphina.Har cikin gida Rimsha da Faryan suka ni Seraphina, sai murna take yi, ta kaisu wajen Madam suka gaisa, Faryan ya zauna a parlo yana ta bin Seraphina da ido, dik in ta gifta sai ya ganta, while ita kuwa sun shige ɗaki da Rimsha, sai kai komo take yi tana ɗaukiwa Rimsha kayan cima.Yau wunin farinciki suka karisa, sai ana kiran mangrib Faryan ya ce Rimsha ta zo su wuce gida, tamkar zata yi kuka ta ce. “Uncle yaushe zamu sake zuwa?”. Shi ma da yake ya ga abin da zuciya ke so sai ya ce. “Ai bamu da nisa, dan haka zan dinga kawoki”. Haba take ta fara murna. Dik abin da suke yi Aryan yana zaune gaban computer yana kallonsu, dik kalle mashi baby Cherry Bloom da Faryan yake yana ganinsa, kishi ya gama tsumasa, jikinsa har wani tsuma yi, ga shi ba wani dressing na suturta jiki sosai take yi ba, ya dinga kiran wayarta dan ya faɗa mata ta sanya wasu kayan, amma tana can an samu Rimsha wayar ma bata san in da yake ba.Bai tashi shiga damuwa ba sai da ya ji Rimsha ta ce da Seraphina su je cikin toilet su yi wanka, a boarding school haka suke yi, tare suke wanka. Wannan abin ya yi matuƙar tayar mashi da hankali, jikinsa har wani tsuma yake yi, haka yana ji yana gani suka shiga toilet, babban abin da ya kara kiɗima shi ma yadda suka cire kaya a tsakar ɗakin, kuma ko kunyar juna basu ba, tambayar kansa ya fara yi menene amfanin boarding school ne ma a rayuwar ɗiya mace? Amsar da ya rasa kenan, amsar da ni kaina na rasa kenan, a zamanin yanzun nan menene amfanin boarding ga ɗiya mace, yadda zamani ta lalace, hmmm!.Kifa kansa a jikin table ya yi yana sauraran hirarsu har suka shiga toilet, basu aikata komai ba, wanka kawai suka yi suka fito, dik hirarsu yana ji, har suka gama suka shirya, Rimsha tasa abayar da suka sayo a shopping, Seraphina ma ta sanya abayar da ta ɗauka cikin sayayyar Rimsha. Daga nan suka dawo parlo suka hau hira da Faryan, suka bar wayoyinsu a ɗaki.Ai Aryan yana ganin su Rimsha sun tafi ya miƙe ya yi wanka, ya ɗauro alwala suka wuce masallaci, bayan sun yi sallar magrib da ishai suka fito shi sai ya wuce wajenta, guru na tsokanarsa bai tanka ba, saboda burinsa kawai ya je wajenta ya faɗa mata kada ta sake yin wanka da kowa. Zuciyarsa ta kara ninka tsanar Rimsha sosai, saboda ita ta ce su yi wanka a tare, sai ya ji yarinyar gabaɗaya ta fita ransa over.Bai san ba laifinta bane, ko bata ce ba Seraphina zata ce, saboda wannan ɗabiar ƴan boarding ne cire kaya gaban juna da wanka a tare, basu ɗaukesa a wani abu ba.A bakin door ya tsaya yana kallon yadda ta yi balain kyau cikin abayar, tana rike da waya suna chat da Rimsha, tana faɗa mata uncle Faryan sai yabon kyanta yake yi, sai zuba murmushi take yi an yaba kyanta. Unexpected ta ji ya kwace wayar.Da sauri ta ɗago kai, tana ganin shi ne ta saki ƙayataccen murmushi game da cewa. “Daddy shi ne ɗazun ka gudu ka barni ko?”………. A gefenta ya zauna tare da zuba mata ido bai ce komai ba. Gyarawa ta yi ta kwanto da kanta a saman laps ɗinta, ta juyo tana kallon kyakkyawan face ɗinsa da ya yi masifar yi mata kyau yau, yana ɗan ciza lips ɗinsa yana kallonta. “Daddy ka yi kyau sosai yau”. Ta faɗa tana riko hannunsa. Nisawa ya ɗan yi tare da cewa.


