Uncategorized

Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 49 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                            FORTY-NINE📍

        Ze tura kofar ya karasa shiga ciki kenan wayarsa dake aljihunsa ta hau ringing, komawa yayi da sauri yana zaro wayar a aljihunsa duk a tinaninsa wanda yasa ya masa bincike akan wani abu ne yake kira, saidai me yana kallon screen din wayar yaga sunan sameer, tsaki yaja me karfi yana maida wayar aljihu da nufin komawa ciki, ze sake murda kofar kenan call din sameer ya sake shigowa, da sauri ya kuma dawowa ya daga wayar da niyar ciwa sameer mutunci, yana daga wayar sameer ya rigasa da fadin;

       “Dan Allah dan annabi deen ka saurareni”….

Tsaki yaja ya hada rai kamar sameer din na ganinsa yace;

      “Banace karka sake kirana ba? Kai wani irin dakiki ne?!”…..

Kwantar da murya sameer yayi yace;

    “Ko wani zagi zakamin zan dauka amma inaso kasani wallhi duk abinda nayi wasn’t intentional, I just felt betrayed amma wlh yanzu nagane gaskiya nayi nadama kuma, dan Allah amin afuwa boss”…

     “And who do you think you’re fooling again?”….

     “Wallahi ba fooling dinka zanyi ba smart, ka yarda dani nayi nadama sosai, naji ance kasa a rufe pman dina amma  banji haushi ba saboda kayi abinda ya dace kuma inataso in fadamaka wani abu kawai na rasa yanda zan fadamaka ne, dan Allah ka bani chance inzo in maka clearing wasu abubuwa daya kamata ka sani”…..

Dan jimm yayi yana reasoning wasu abubuwan, ko bayan wannan abun daya faru yana san ganin sameer dan akwai abubuwa dayawa da yakeso ya tambayesa, so zeyi using opportunity dinnan…

       “Kazo ka sameni a gidan mami gobe!”…. 

     “Gidan mami kuma boss? Kasan fa mami na nemana, tsoron haduwa nake da ita wallahi”….

     “Wannan kuma matsalarka ce! Idan ka isa kar kazo goben!”…..

Deen na fadin haka ya kashe wayarsa, ya bar sameer da tinanin ko be wuce ba har lokacin, kar yazo ya masa dukan da yace ze masa, ga mami da yake tsoron haduwa da ita itama, amma dole ya daure yazo inba haka ba yasan duk abinda Deen ya masa shi ya jawo……

       “Dan Allah kimin bayani sis, kukannan da kike yana dagamin hankali wallahi”…..

Mami ta fada yayinda hawaye ke taruwa a idonta itama….. 

Sakinta umm tayi ta fashe da dariya hawayen farin ciki na zuba a idonta tace;

      “Dan Allah kuka nake yaya?”…..

Dariyar itama mami tayi tace;

      “Gashi kuwa, au bakisan kina kukan ba kenan?”…..

Ruko hannun mami tayi har lokacin bata dena dariya da kuka at the same time ba tace;

     “Bansani ba, ni dariya nake ai”…..

Zaunar da ita mami tayi tana facing dinta tace;

      “Toh Alhamdulillah koma me kikeyi ni dai ki taimaka kimin bayani”…..

Sassanyar ajiyar zuciya umm ta sauke ta ruko hannunta tace;

      “Ko hannu ba’a taba sa mata ba, which of the favors of my lord will I deny?”….

Murmushin farin ciki mami tayi tace;

      “None! Allah abun godiya me kare kowa kuma me komai, shiyasa nace karki daga hankalinki because Allah does not burden a soul beyond that it can bear, koda hakan ya faru sai kiga Allah ya kawo mana mafita yanda bazamu damuba barema komai is intact, sai kije kiyi bacci me dadi ai”……

Dariya umm tayi tace;

      “Banga ta bacci ba mami, kwana zanyi a gaban Allah ina masa godiya!”…..

     “Gaskiya kam ai be kamata muyi bacci ba, yanzu baby tee din bacci take?”….

Mikewa da sauri umm tayi tace;

     “That reminds me nayi wata yar mantuwa wallahi, Allah ya sa mu kadaine, ina zuwa”….

     “Me kika manta haka?”…

Mami ta tambaya da sauri amma ko kafin ta dire umm tabar dakin….

Iska Deen ya furzar  bayan ya kashe wayar sannan ya sake dora hannunshi akan kofar….

      “Hey! Hey! Me zakayi a ciki?”…

Ya juyo muryar umm a bayansa….

Fasa murda kofar yayi ya juyo ya kalleta yace;

      “I want to check on baby tee? Yau throughout banganta ba”….

Kallonshi daga sama har kasa umm tayi tace;

    “Baka ganta ba? Baka fadamin kana needing eye glasses ba aida namaka da kaina”…..

Sai a lokacin ya tina ko dazu daya fito daga dakin mami yaci karo dasu, amma meyasa yakejin kamar be ganta ba gabadaya ranar, kodan basuyi magana bane?… Shafa gemunsa yayi yace;

       “Oh hakane fah ashe naganta, I forgot”….

Hararasa tayi tace;

      “A’a kara tinawa dai”…..

Marairaice fuska yayi irin yanda yake mata a duk lokacin dayaga tanaso ta hanashi abu yace;

   “Umm dan Allah inaso in ganta yanzu, there’s something I want to discuss with her”…..

      “Ka bari gobe da safe saif, tayi bacci yanzu”…..

Umm ta fada a nitse…. 

        “Ai ba lallai sai nayi magana da ita ba, I just want to check her health as a doctor dan naga kamar bata jindadi”……

Mamaki ne ya kama umm yanda ya manta she’s also a doctor, tsattsareshi da ido tayi irin yanda take hukunta mutum idan tanaso ya gano laifinsa da kansa……

A take ya daburce ya hau kame kame, shi kwata kwata bayasan kallon nan da umm takeyi yiwa mutum dan duk abinka saika shiga hankalinka, cikin daburcewa yace;

     “Oh sorry Doctor umm”….

       “Saida safe!”…

Ta fada tana nuna mishi hanyar stairs da hannu…..

        “Umm dan Allah ki bari na shiga na ganta”….

Ya fada a hankali hoping zata barshi ya shiga, toh shi bema gane ba wai meyasa ta hanashi shigane bayan yasan normal Umm without second thought zatace ya shiga, kodai kodai? Koma menene shidai yanaso ya shiga ya ganta……..

Hanyar stairs ta nuna masa tana masa kallon datasan bayaso tace;

      “Before the count of three leave here, 1,2,…….”

Be bari ta karasa ba ya sauka da sauri yanajin haushin hanashi ganinta datayi…..

Fitilar parlourn ya kashe sannan yaje ya bude kofar ya rufe kamar ya fita, ya dawo ya samu guri ya zauna akan kujera…..

      Juyawa umm tayi tashiga daki tana sauke ajiyar zuciya, yau ita taga naci a gurin saif, mamaki ma yake bata dan batasan shi da naci ba kasancewarsa mutum me zuciya, da wasa idan akan hanasa abu sai yace wallahi bayaso…..  Tabe baki tayi tace;

     “Allah ya kyauta”…. 

Rufe kofar tayi ta Isa ga baby tee, maida mata da kayanta tayi sannan tayi  kissing forehead dinta ta mata addu’a ta shafa mata a ko ina sannan ta lullubeta…

Alwala ta dauro ta tada sallah kamar yanda tayi niya.

     Yana zaune a yanda yake tin bayan umm ta koreshi, babu abinda yakeyi banda tinaninta,da yayi kokarin kauda tinanin sai abun yasake dawo masa kamar wanda akewa dole.

    Kamar wanda ake tinzurashi wurin karfe daya yasake mikewa ya haura sama, a kofar bedroom din umm ya tsaya yana addu’ar Allah yasa bata rufe kofa ba ko yasamu yashiga ya ganta ya fito dan yasan yanzu dole umm tayi bacci,murda kofar yayi a hankali sai dai kash yajita a rufe,sai kawai ya tsilale ya zauna a bakin kofa, jingina da kofar yayi yanajin sanyi a ransa saboda kusancin da yake gani yasamu da ita ..

      Umm na cikin sallah taji an murda kofa,sai datayi sallama sannan ta tashi ta bude duk a tunaninta mami ce tazo ta duba taga ko tayi bacci dan tasan mami tana kan sallaya itama yanzu, bude kofar tayi deen dake zaune a bakin kofar ya mike da sauri yana sunkuyar da kai….

Da mamaki sosai tace;

      “dama baka tafi ba?”….

Kasa yasakeyi da kansa yace;

       “Eh”….

Da damuwa a fuskarta tace;

     “Meke damunka saif?”….

      “ba komai”….

Yabata amsa yana susa keyarsa…

Dago habarsa tayi tace;

     “do you still wanna see her?”…

Kin hada ido da ita yayi yana yaki da zuciyarsa akan tabashi hadin kai yace a’a saidai inaa taki bashi hadin kai,dole haka ya daga mata kai yanajin nauyi a ransa, hakanan yau yake ganinta kamar ba umm din da baya iya boyemata komai ba,sai yakejin dauyinta fiye da mami yau….

      “Come in”…

 Tafada tana basa hanya ya shigo, shigowa yayi yana kin yarda suhada ido……

Bata kuma bi takansa ba takoma ta cigaba da sallolinta, wannan karan sai ta mayar da addu’o’inta gaba daya a kansa dan tasan ko be fadaba yana cikin damuwa….

  Akan bedside drawer dake kusa da kan baby tee ya zauna, kallon yanda take sauke numfashi a hankali yayi ya zubawa kyakyawar fuskarta ido kamar wanda yake neman wani abu a fuskarta, a hankali yaji zuciyarsa nayin sanyi duk wani takaici daya kwasa a ranar yaji yana gushewa daga kallon fuskarta kawai daya keyi, mayar da idonsa kan umm yayi yaga ta juya musu baya tana sallah, juyowa yayi ya sauke idonsa daidai kan small red lips dinta dake dauke da natural dark brown lip liner daya kawata kyawun bakin, lashe lips dinsa yayi yana tuno ranar daya fara kissing dinta, har bayasan tina abinda yaji a ranar saboda kwana yake craving for more, index finger dinsa ya dora akan lips dinta ya shiga shafa shi a hankali yana jin yanda tsigar jikinsa ke tashi, kamar wanda aka tsikara ya janye hannunsa daga kan lips din nata yana kallon saitin da umm take, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah da umm bata ganshi ba da ya shiga uku dan besan da wani ido ze kalleta ya mata bayanin abinda yake aikatawa ba…

Dauke idonsa daga kan fuskarta yayi ya maidashi kan jikinta, sanye take da lallausan kayan bacci me dan kauri, a lullube take tin daga kirjinta zuwa kafafuwanta banda gashinta daya kwanta ta bayan bargon kasancewar zamewa da hularta tayi kuma dama ba wani rufe kan hular tayi ba…. 

Kallon gashin yayi ya tabe baki yana dan wani tinani aransa, fuskarta ya cigaba da kallo yanajin wani nishadi aransa…….

     Sai karfe biyu umm ta sakeyin sallama, juyowa tayi ta ganshi a zaune ya kure baby tee da ido, ita duk a tinaninta ma ya fita…..

     “Saifuddeen!”….

Yaji ta kira cikekken sunansa which is not common a bakinta…..

Da sauri ya dauke idonsa daga kan baby tee murya chan kasa yace;

      “Na’am umm na”….

      “Baka tafi ka kwanta ba dama?”….

     “Banajin bacci umm”…

Ya bata amsa a raunane….. 

Girgiza kai tayi ta mike ta dawo ta zauna kusa da baby tee tana facing dinshi tace;

      “Na dauka ko zaka boyewa kowa damuwarka ni bazaka boyemin ba ashe I was mistaken!”….

A hankali yace;

    “Ba haka bane umm, dama inaso inzo in gaya miki abinda yake damuna”.….

      “Menene? Share with your umm”….

Yanayin fuskarsa ne ya chanja yace;

      “Umm ashe mami bata bar maganar zainab take ko wa ba?”…..

     “Eesha?”….

     “Eh ita! Ni yanzu kamar ni sai ayiwa auren dole? Nace banaso amma ace saina aureta”……

Numfasawa tayi tace;

     “It was your fault saif! Chances nawa aka baka ka fito da wacce kakeso amma kaki, yanzu kuma dad dinka yace aure ze maka dagaske, so sukayi sukai komai harda sadaki, nace bazeyiwu ba saidai a tambayo a baka dama ku daidaita”……

      “Nifa ba wani daidaitawa da zamuyi da ita, umm ki taimakeni a janye maganarnan”….

Ya karashe maganar kamar zeyi kuka….

 Murmushi tayi tace;

      “Kayita addu’a saif sai kaga in anyi auren kasota ma”….

Zeyi magana kenan tace;

     “Shhhh kar kace komai, kawai ka dage da addu’a”…..

Har zata mike deen ya kalli baby tee yace;

      “Umm kina ganin tasa attachment bazaki mata magana ba?”…..

    “Wa kenan?”….

Ta tambaya cikin rashin fahimta….

    “Baby tee mana!”…..

Dariya tayi tace;

         “Gaskiya a gaisheka saif, kai yanzu kana nufin baka taba ganin gashi ba duk zuwanka maiduguri?”…

Zaro ido yayi yace;

     “Kai umm gaskiya ba haka gashinsu yake ba, ni ban taba kallonsu ba”……

      “Ikon Allah toh ko nawa da kake jagwalgwalawa da fah?”…..

     “Umm naki be kai haka ba”….

     “Yes nata yafi nawa tsaho sosai saboda gado biyu da tayi, kaga muna da gashi suma su abby fulani ne masu gashi sosai”……

      “Oh! Yanzu kina nufin all this while da nake ganinta gashinta ne?”….

      “Eh mana! Kaidai Allah ya shiryeka saif bansani ba ko gabuntar fari ke damunka? Tashi ka tafi ka kwanta”….

Bata fuska yayi yace;

      “Ni bawani gabunta dake damuna umm, bana jin bacci kuma”….

       “Toh tafi kaje kayi sallah, nima sallah zan cigaba”…..

     “Dan Allah nima inyi anan? Bansan inyi nesa dake umm”…..

Dariya ma ya bata tace;

     “Ah lallai bismillah toh”…..

Alwalan ya dauro ta mishi alama daya tafi praying spot din dake dakin yayi sallah yanda bazena hango baby tee ba, gurin ya shiga ya ta tada sallah suka raba dare suna ibada shi da umm har akayi sallar asuba…… 

   

   “Ina kwana umm”

Deen ya fada yana dukawa har kasa bayan ya idar da sallahr asuba…..

     “Lafiya lau son, ya ibada?”….

      “Alhamdullilah, baby tee bata sallah ne?”….

     “Tanayi, na mata allura jiya shiyasa ban tashe ta ba, so nake ta tashi da kanta yanda zataji kwarin jikinta”…..

     “Okay, sai anjima”…. 

Har ya kai bakin kofa yaji tana addu’ar tashi daga bacci, dawowa ciki yayi ko kafin ya dawo ta tashi ta zauna, kallon yanda gashinta yabi kafadarta ya kwanta gwanin sha’awa yayi yace;

     “Meet me downstairs when you’re done praying, ki tawo da al-qur’ani kuma”….. 

Yi tayi kamar batajiba, saida umm tace bakiji ana magana bane sannan tace toh…. 

Tana idar da sallah ta dauki Qur’anin kamar gaske, harta nufi bakin kofa umm ta kirata, dawowa tayi ta tsuguna a gabanta…..

      “Baki iya gaisuwa bane? Haka ake sallah a wuce ba’a gaida mutane ba?”…..

     “I’m sorry, ina kwana”…..

     “Feel comfortable banasan nuku nukunnan da kikeyi, kin tashi lafiya?”……

    “Alhamdullilah umm” ……

    “Tashi kije, amma ki fara zuwa ki gaida mami and make sure kin gaida saif shima”…..

     “Okay”….

Ta fada tana mikewa …

Kamar yanda umm ta umarceta tana fita tashiga dakin mami…. 

Akan sallaya itama ta sameta, dukawa har kasa tayi tace;

      “Ina kwana mami”….

Murmushi mami tayi tana jawota kusa da ita tace;

     “Lafiya lau daughter, ya karfin jiki?”….

        “Alhamdullilah”….

      “Masha Allah, ina zaki haka da al-qur’ani?”…..

       “Saif ne yace inzo dashi”……

Ruko hannunta tayi tace;

      “Maza jeki, ayi karatu da kyau kinji ko?”….

       “Insha Allah mami”….

Sannan ta tashi ta fita, sauka kasa tayi ta samu guri ta zauna a parlourn kamar bata ganshi ba…. 

      “Ke zonan!”…..

Ya fada ba wasa a fuskarsa…. 

Yi tayi kamar bataji ba tana yi dashi aranta wai yace mata ke…..

Daka mata tsawa yayi yace;

     “Ba dake nake ba! Kika bari na taso sai na babballaki a gurinnan fitsararriya kawai!”……

Ba shiri ta mike dan ba karamin shigarta tsawar tayi ba, guri ya nuna mata akan carpet ta zauna tana bata fuska sannan shima ya sakko ya zauna yana facing dinta…… 

Kwafa yayi yace;

     “Saboda nace kizo muyi karatu kikeso kimin rashin kunya?”…..

Marairaicewa tayi tace;

     “Toh ni bacci nakeji!”…. 

Sassauta murya yayi yace;

     “You can say that respectfully ai, yanzu kinaso in barki kije kiyi baccin?”…..

Gyada masa kai tayi tace;

      “Eh!”…..

Saida ya kalli ko ina na parlourn ya tabbatar da babu me jinsu sannan yayi kasa da murya yace;

     “Then answer my questions!”…..

        “Ina ji”…..

Sake kasa yayi da murya yace;

       “An daura muku aure keda wanchan so called boyfriend din naki?”…..

Girgiza masa kai tayi tace;

       “A’a”….

    “Has he ever touch you?”….

Nanma girgiza masa kai….

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani farin ciki aransa yace;

    “Can you please do me a favor dan Allah badan halina ba?”….

Ya fada a sanyaye …

Dagowa tayi ta kalleshi tana mamakin yanda yake mata magana yanzu, ita batasan ma ya iya kwantar da murya haka ba, cikin halin ko in kula tace;

       “What favor?”…..

A nitse yace;

     “Kice an daura muku aure da khaleel kuma ya sakeki! Sannan babu aure a tsakaninku again, idan kikamin wannan na miki alkawari kome kikeso a duniyarnan zan miki and na dena miki masifa da komai ma”…. 

Mamaki ne ya kamata dan bataga dalilin yin karya ba tace;

      “Why?”….

Kai tsaye yace;

     “Saboda banasan tarayyarku dashi, kinga mahaifinsa is a cultist too, idan kika aureshi dole ya’yanki zasuji labarin abinda kakansu yayiwa mamansu and it will hunt them for life”…..

     “Okay”…

Ta fada blankly….

     “Kin amince kome za’ayi zakice ba’a daura auren ba a gaban kowa?”….

Ya tambaya yana tsoron tace bata amince ba….

      “Eh na amince!”..

Besan sanda yayi hugging dinta ba yanaji kamar yafi kowa farin ciki a duniya, murmushi daya dade beyiba yayi yana fadin;

     “Thank you so much baby girl, ki gayamin kome kikeso a duniya wallahi zan miki”….

Zamewa daga jikinshi tayi tace;

      “Ba sai kamin komai ba, can I go and sleep now?”….

     “Yes sure, but ki tashi ki shirya da wuri nasan da wuri za’a hadu….

     “Okay”…

Ta fada tana mikewa….. 

    Da misalin karfe sha daya na safe kowa ya hallara a parlourn harda khaleel da akace ya dawo gobe, sai abby da dad da sukazo da safe suma…..

Dad ne ya bude musu taro da addu’a, gamawarsa keda wuya sameer da sukayi da deen ze zo da safe ya shigo, guri deen ya nuna masa ya zauna….. 

Saida kowa ya nistu sannan abby ya kalli baby tee yace;

      “Fatima yau mun taru ne saboda munaso ki warware mana wani abu, kuma munaso ki fadi tsakaninki da Allah abinda ya faru, shin an daura muku aure da khaleel a dubai?”…..

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button