Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 37 Book 2 Complete Novel

  

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

                                                               

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

   Fitowa hafsat tayi hannunta janye da trolley ba komai bane aciki ba fa ce kayansu jahad, ɗayan hannun nata kuma na ruƙe da basket na breakfast dinsu data haɗo masu, 😥😥😥

  Tana isowa ta buɗe boot ɗin motar ta saka trolley ɗin sannan ta rufe, duk aunty babba na tsaye ruƙe da qugu tana sakin murmushi,

   Bude back seat ɗin hafsat tayi inda su jahad ke zaune ta miƙa musu basket ɗin, hannu na kerma jahad ta kar6a,

  Sannan ta rufe musu murfin motar, har tasa hannu zata buɗe gaban motar ta shiga ta juyo ta kalli aunty babba idonta jawur tace “Baki bani numbar mutumin ba, wanda kika ce zai kaisu Orphanage home ɗin,”

  cikin sauri aunty babba ta ɗago wayarta dake hannunta, tashiga contact numbar baba alamu ta lalubo, sannan ta shiga karanto ma hafsat ita kuma tana rubutawa a wayarta, bayan ta kammala sa numbar tashige cikin motar kafin ta rufo ƙopar ta aza idonta akan aunty babba tace “Ina fata kin ji daɗi mommy, yau hussana da jahad zasu bar miki gidanki, sai ki zuba ruwa a ƙasa kisha don murna,”

  tana faɗin hakan ta datse motar tare dayi mata key, ta juya sitiyarin motar tayi baya² da ita sannan ta karya kwana ta juyar da ita direct ta nufi gate ɗin gidan ta fuce da motar aguje, 

  Lumshe ido Aunty babba tayi afili tace “Alhamdulillah na kawar da wannan matsalar, yanzu abunda ya rage mun shine zuwa wurin boka domin gudanar da target ɗina na gaba,” tana faɗin hakan ta nufi cikin gidan fuskarta washe yau ta rabu da alaƙaƙai, 

sai da ta ɗan yi nisa da motar ta fito bakin titi sannan ta dakatar da driving ɗin, wayarta ta ɗauko dake ajiye agefe, Lambar baba alamu ta danna ma kira, bayan ya ɗaga ta sanar dashi kwatancen inda motarta take,

 bayan ta katse kiran ta ambaci sunan Jahad da Hussana, atare suka amsa mata da “Na’am,” juyo taɗanyi ta kallesu da idanunta waɗanda suka canza launi, cikin sanyin Murya tace”kun san inda za’a kai ku”?

  Har suna haɗa baki wurin cewa “A’a,”

  Shiru taɗanyi kafin taci gaba da cewa “Gidan marayu !!!!!!!’

 Zaro ido su kayi gaba ɗayansu hankali atashe suna kallonta, hussana da tagaza jurewa tuni ta soma kuka tana cewa “Yaya Omar fa? dan Allah kar akaimu can ku bari yaya Omar yazo ya ɗauke mu mana, ni bana son mu rabu dashi,” 

Murmushin takaici jahad ta saki tare da cewa “Aunty hafsat ba wai gidan marayun ke bama so ba, kawai ni so nake naji da sanin yaya Omar za’a kaimu can”?

  girgixa kai hafsat tayi tare da cewa “Jahad bada sanin shi ba, kuma nima ba da son raina ba na amince da hakan, amma ina so ku sani can shine zaifi muku zama cikin salama, saboda shi kan shi ya Omar ya manta daku tun da gashi ko kira a waya yadaina yi, babu tabbacin cewa ma yana ƙasar tunda dama banan yake zaune ba, don haka ku Cire tsammani da shi, kawai ku rungumi ƙaddara, kuyi haƙuri³,” har kusan sau uku tana maimaita masu kalmar suyi haƙuri,.

  Hussana dae bata dakata da kukan da takeyi ba sai ma sautin da ta ƙara, jahad ta jinjina kai idonta acikin na hafsat tace “Shikenan Aunty hafsat, kada ki sa damuwa aranki, mu kan mu bamu ta6a tunanin zamu kawo wannan lokacin araye ba, amma gashi mun kawo da ran mu da lafiyar mu, wannan alama ce dake nuni da cewa Allah yana sane damu !!! Kuma shine zai kare mu aduk inda muka kasance a faɗin duniyar nan! mun gode sosai da kulawar da kika nuna mana,” daga haka jahad tayi shiru idonta na zubar da hawaye hussana kawai take kallo wadda ke ta faman shessheƙar kuka,

  Jikin hafsat ya gama yin sanyi sam tagaza yin kwakkwaran motsi, suna cikin wannan Yanayin Motar baba Alamu ta ƙaraso dab da tasu, wata tsohuwar jeep ce ta ragwaggwa6e ta fita hayyacinta, kai wannan motar ko kyauta aka bani ita wlh na kwammace inci gaba da yawona da ƙafafuwana saboda muninta, gaba ɗaya fa glass ɗin motar ya faffashe kana hangen cikin motar, babban abunda zai ɗaure maka kai shine yadda yakeyi wurin tayar da motar domin kuwa babu wurin zura mukulli atada mota, sai dae wasu wayoyi gasunan birjik su yake haɗawa sannan ya tashi motar,

hankaɗa murfin motar yayi sannan ya fito, wani irin Matsolan mutun ne ramamme sai uban ƙasusuwa gashi baƙi wulik kana ganinsa kaga cikakken ɗan duniya, fuskarsa yana da wasu irin tsaguna waɗanda zasu tabbatar maka da cewa Magobiri ne, yadda kasan kwarya haka tsagunan fuskarsa suke, yana da kwalakwalan idanuwa kuma jawur dasu, ga wani irin fankacecan hanci harya so yafi ƙarfin fuskarshi, haƙoran bakinsa kuwa sunyi jawur dasu saboda Cin goro, a shekaru zai iya zarce shekara hamsin, jikinsa na sanye da wani tsohon yadi wanda yausha rabon da yaji dutsen guga ajikinsa tun 1960 😔 

  fitowa hafsat tayi ita kanta da ta ga mutumin sai da gabanta ya faɗi saboda muninsa, shi kuwa washe baki ya shiga yi yana cewa “Yarinya ta girma ! komai yaji dai² nasan baki sanni ba, amma ita jatumarki kullum tana bani labarinki,” 

  ɗaure fuska hafsat tayi zuciyarta har wani tashi take yi, hannunta na kerma ta buɗe masu hussana motar, fito wa Su kayi atare da jahad duk jikinsu ya gama mutuwa, musamman da su kayi arba da baba alamu, sai duk suka firgita jiki na kerma Hussana ta ƙanƙame jahad saboda tsoro,

  Buɗe boot ɗin motar hafsat tayi tare da curo masu trolley ɗin kayansu ta miƙa ma jahad ta kar6a, sannan ta ɗauko masu food basket ɗinsu da suka manta, ta miƙa ma hussana daker ta kar6a,

  Cikin kuka Hussana ke cewa “Aunty hafsat dan Allah kada ki tafi kibarmu a hannun wannan mutumin !!” 

rigima sosai hussana ta sanya, hafsat kuwa tsananin tausayinsu duk ya kamata, purse ɗinta ta ɗauko cikin motar, sannan ta ƙirgo kuɗi kusan dubu 30 ta miƙa ma Jahad tace “Ki ruƙe wannan a wurinki nasan za suyi maki amfani, ni zan wuce,”

  Bin ta da kallo kawai jahad ke yi idonta na zubar da hawaye duk yadda hussana ke faman rusa kuka tana rurruƙe mayafin jikin hafsat amma hakan bai hanata tafiya ba, cikin sauri ta shige motarta, taja ta da gudun gaske tabar wurin,

 Mayar da idonsu su kayi kan Baba alamu wanda ke ta faman bin jikinsu da kallo yana sakin wani irin shu’umin murmushi,

  hannu yasa ya buɗe masu motar yace “Maza ku shiga ciki,” 

   Amsar trolley ɗin yayi ya bude boot ɗin motar ya wurgar dashi ciki sannan ya datse shi, shiga ciki su kayi gabansu na faɗuwa zuciyarsu nayin wani irin bugu mai sauti,

dawowa yayi ya shige gidan gaba sannan ya jona wayoyin nan take motar tayi wata irin ƙara ƙirrrrrrrr bakin hayaƙi ya soma fita ta baya, sannan yaja motar da gudun gaske ya miƙi hanya dasu,

******************

  tun jahad tana ganin gine-gine da gifcin mutane har ta soma ganin  dajijjika, hakan yasa hankalin jahad ya tashi ganin ya fidda su cikin gari bayan cewa Hafsat tayi zai kai su gidan marayu, zazzare ido jahad ta soma yi gabanta na wani irin bugu, juyawa tayi don taga wane hali hussana ke ciki, abun mamaki saita samu hussana sai bacci take shara hannunta ƙanƙame da kwandon abincin su,

  Kai tsaye baba alamu ya kutsa dasu cikin dajin mai uban bishiyoyi da ciyayi ba gifcin mutun acikinsa sai dabbobi dake shawagi,

  Murya na rawa jahad tace “Bawan Allah ina zaka kaimu ne !? Ba gidan marayu akace zaka kaimu ba,”? Ta tambaya idonta cike taf da hawaye cikin tsananin tsoro,

 fashewa da dariya baba alamu yayi sannan yace “A sanin ku ba, amma ni ba gidan marayu nayi da ita hajiyar zan kaiku ba, ce mun tayi in zubar mata daku acikin daji,”

  Cikin kuka jahad tace “Dan Allah kada ka cutar damu , ka sauke mu kawai anan,”

 Baba alamu yace “Yarinya kenan ki daina wannan tunanin, ae tunda idanuwa na suka yi arba da surar jikinku na kwaɗaitu da son kasancewa tare daku, don haka zan kai ku gidan gonata dake acikin dajin nan don na runƙa rage zafi daku,” ya ƙarasa maganar da wata irin shaƙiyar dariya,

  Jahad kuwa neman hanyar fita take yi daga cikin motar amma ta gaza buɗe murfin motar saboda ya datse shi sosai, duk wannan tashin hankalin da ake ciki hussana bata sani ba, saboda baccin da takeyi,

  jahad bata haƙura da ƴunƙurin buɗe motar ba sai da ta sanya iya ƙarfinta na ƙarshe ta tunkuɗe murfin motar ya buɗe aikuwa nan take baba alamu ya girgiza motar da mugunta, nan take jahad ta faɗo ƙasa timmmmm ! ta gangara Ta bugi wani dutsi  nan take goshinta ya fashe, 

Shi kuma yaja motar da gudu ya tafi da hussana acikinta, hankali a matuƙar tashe jahad ta ɗago daga jikin dutsen jini na zuba a goshinta, miƙewa tayi da gudun gaske tabi motar tana kuka tana ambaton sunan HUSSANA, muryarta har wani shaƙewa take yi saboda yadda take kwala mata kira ga uban gudun da takeyi don ta taddo motar, amma ina tuni yayi mata nisa ga tafin ƙafarta da ƙayoyi suka sossoke ta duk ƙafar ta fashe jini nata faman gangarowa a ƙarshe data gaji da bin motar jiri na kwasarta nan take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya acikin korayen ciyayin dake a wurin, 😭

 Kiran ƙarshe da jahad ta kwalama hussana kafin ta sume har cikin zuciyarta taji shi tuni ta soma ƙoƙarin buɗe idanunta wanda ke cike da bacci, a lokacin har baba alamu yashiga da ita gidan gonarsa ƙopar katako ce ke gare sa tamkar ɗan gate, bayan ya shigar da motar ya fito ya rufe ƙopar gidan gonar da kwaɗon dake ajiki,

  Sannan ya koma tare da buɗe murfin motar inda hussana ke zaune tana faman lullumshe ido alamar bacci bai isheta, so take ta buɗe Idonta taga ina jahad take amma sam bacci ya hana Ta,

  hannu baba alamu ya zura tare da ɗauko hussana ya sa6ata a ƙafaɗarsa ya miki hanyar wata ƙopa inda ya dosa ya buɗe ta ya shige da ita ciki sannan ya sauke ta ƙasa har tana yin tangyaɗi zata faɗi, sai da baba alamu ya datse ƙopar ɗakin gam yadda bamai shigowa sannan ya juyo yana kallon hussana tare da washe waɗannan haƙoran nasa marasa saiti,

A lokacin Hosana ta dawo cikin hayyacinta baccin yabar jikinta, bin wurin tayi da kallo ɗakine mai faɗin gaske babu komai aciki sai jarkokin ruwa da bulo bulo, da wani ajiyayen genarator tsoho, sai sauran tarkace, wurga idonta tayi akan baba alamu dake tsaye agabanta yana washe mata baki, nan take ta buga uban tsalle taja da baya tana faɗin “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un nashiga uku, Ina jahad take! Wayyo Allah na Me zaka yi mun meyasa ka kawo ni nan ! tayi maganar tana ja dabaya a tsorace

  Baba alamu ya kashe mata ido ɗaya tare da cewa “daɗi zan baki, kiyi shiru da bakin ki kada wani yaji mu, indai kina son ganin ƴar uwarki to ki bani haɗin kai muyi mu gama cikin salama,’

  Yayi maganar tare da kai hannu zai shafa fuskarta a firgice taja baya tana girgiza masa kai atsorace take cewa “Dan Allah kada ka cutar dani, ka ƙyale ni bani da lafiya, idan ka ta6ani mutuwa zanyi,” ta faɗi tana faman zazzare ido, ga wata irin zufa dake wanko mata dakyar take haɗiyar numfashi,

“Ba zaki mutu ba, bada zafi zan miki ba kaɗan kaɗan, in dai baki bani haɗin kai ba zan ƙwata ta ƙarfi kuma naƙi nuna miki inda ƴar uwarki take,” 

Cikin kuka hussana tace “a’a nidai kada ka cutar dani  bana so, kadaina matsowa kusa dani, wlh Allah bazai barka ba kuma yaya Omar ma bazai ƙyale ka ba sai ya kashe ka,”

  fashewa da dariya Baba alamu yayi tare da gwalo ido yana mata gwalo yace “Wanene wani Omar kuma? babu kowa anan daga ni sai ke ! Kuma yanzun nan zan kawar da sha’awata tare dake,” yayi maganar tare da yin kwakkwaran taku ya fusgo mayafin jikin husana nan take ya zame ƙasa, watsa wa tayi da gudu ciki tana kuka cikin rashin sa’a tayi tuntu6e da bulo ƙafarta ta harɗe ta kife ƙasa gaba ɗaya…………………….

dariyar mugunta baba alamu ya saki ganin abun yazo mashi cikin sauƙi, nan take ya shiga kwance zariyar wandonsa, 

   daker hussana take jan numfashi saboda buguwar da tayi wani irin ciwon kai yafar mata lokaci guda, jin motsinsa dab da ƙafafunta yasa ta dumbuzar ƙasa a hannunta, ta daddage ta tashi zaune tare da watsa mashi ita a fuska, nan take yashiga yin tsalle yana faɗin “kai ! Kai!! Kai !! Don ubanki ni kika watsa ma ƙasa a ido! aiko bazan ƙyale ki ba, saina wulaƙanta rayuwarki,

 Jin hakan yasa hussana zabura tare da miƙewa tsaye zata gudu batayi wani aune ba taji yaja rigar jikinta nan take ta soma yage wa, juyowa tayi tare dasa hakoranta ta gartsa mashi Cizo, azaba da raɗaɗi suka sa shi sakin ihu, kuma hakan ya ƙara fusata shi, a fusace yabi ta tare da damƙo gashin kanta ya janyo shi da ƙarfi ta dinga sakin ihu tana kuka tana kiran Sunan Jahad,

 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Matse ta yayi ajikinsa tare da sa hannun shi biyu ya ƙarasa yage rigar jikin hussana gaba ɗaya, hankali a matuƙar tashe husana ta watsa mashi miyau afuskarsa biji-bijin daya daya fara gani ne yasa shi ɗan dakatawa, hannunta ta sanya tare da ingije shi da ƙarfin gaske gaba ɗaya baba alamu yayi taga² zai faɗi ƙasa,

  Cikin sauri hussana ta tattare rigarta ta kare kirjinta da ita, hanyar fita daga ɗakin ta nufa da gudun gaske tana kuka burinta kawai ta isa kopar ta buɗe ta fuce

   tana cikin gudun nan baba alamu ya taso a matuƙar zuciye ya nufe ta da sauri yakai hannunsa tare da jan rigarta data rufe jikinta da ita, gaba ɗaya ya 6an6are rigar daga jikinta ya cire ta gaba ɗaya ya ruƙe a hannunsa,

  Wani irin kuka hussana ta saki mai matuƙar cin rai ganin yarda ya cire mata rigarta, gashi ko brazier bata sanya ba, ƙirjinta gaba ɗaya sun fito, hannunta ta sanya ta tarbesu tana kuka kuma hakan baisa ta daina tunkarar ƙopar ba,

  Bin ta baba alamu yayi da gudun gaske saboda ya ruƙo ta jikinsa don ya idasa nufinsa,

 Sai dae ina kafin yayi wani kwakkwan yunƙuri tuni anyi ma ƙopar ɗakin wani irin kwakkwaran Naushi nan take katakon jikinta ya farfashe gaba ɗaya ta buɗe,

  A tsorace baba alamu ya dakata yana faman zazzare ido don son ganin wanene wannan ya faɗo masa cikin gidan gonarsa !!!!!!!!!!!!

Ita kanta hussana ta firgita tsayawa tayi jikinta na wani irin kerma ga zazza6i daya lullu6e ta, har lokacin hannunta na tarbe da ƙirjinta,

     Duro ƙafarsa yayi cikin ɗakin tamkar damusa wani irin kakkarfa ne mai ban tsoro, jikinsa na sanye da Jacket baƙa daga ciki kuma farar t*shirt ce wadda ta bayyana ƙirar ƙarfinsa, Sai dogon wando baƙi,

 bai bamu damar muga fuskarsa ba domin kuwa tana sanye cikin face mask baƙi, idonsa kuma na sanye da baƙin glass,

    gaban hussana ba ƙaramin faɗuwa yayi ba duk ta gama tsorata, baba alamu kuwa murya na rawa yashiga cewa “kai…Wai Wanene kai ! daga ina kake? Mai ya kawoka gidan gonata ! ya tambaya yana tada jijiyoyin wuya,

Har lokacin bai da alamar yin magana, a hankali ya sanya hannunsa tare da ruƙo jaket ɗin dake ajikinsa ya cire ta gaba ɗaya yayi wurgi da ita, sannan ya mayar da hannun nasa ya tu6e t-shirt ɗin dake ajikinsa ya rage babu riga ajikinsa,

   Hankalin baba alamu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin irin damtsen hannunsa a murmuɗe ga ƙirjinsa dake motsi abun gwanin ban tsoro,

   tuni zuciyar hussana tayi wani irin bugu nan take ta tafi zata sulale ƙasa, da Hanzari ya tarbota jikinsa gaba ɗaya tafaɗa a faffaɗan ƙirjinsa,

   hakan ya bashi damar zura mata t-shirt ɗinsa ajikinta donya rufe mata jikinta, bayan ya kammala sanya mata rigar, 

ya buɗe bakinsa ta cikin face mask ɗin yayi fito mai sautin gaske har saida baba alamu ya firgita yana faman kwalala ido, 

Da gudun gaske wani Saurayi ya shigo ya tunkare sa, batare da yace komi ba ya miƙe masa Hussana, cikin sauri yasa hannu ya ɗauketa tare da azata a kafaɗarsa ya fuce da ita,

    sai lokacin Yasa hannu ya cire glass ɗin fuskarsa tare da yin wurgi dashi, Azazafe ya sanya kyawawan idanuwansa waɗanda suka Canza Launi izuwa ja saboda tsananin 6acin rai, gadan gadan ya tunkari Baba alamu wanda ke shirin guduwa, hannunsa yakai tare da damƙar wuyan rigarsa ya ɗaga shi sama, ya dawo dashi ƙasa ya buga kansa jikin bulo nan take haƙora biyu daga bakin sa suka fito Jaga-jaga da Jini, saboda tsananin azaba da raɗaɗi ya sanya Baba alamun sakin futsari a wando yana cewa “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un na bani na 6atare na lalace nashiga uku, Dan Allah ka ƙyale ni wlh nabi Allah nabi manzonsa .,………..

  tsawa mutumin ya daka masa tare da cewa “Kasan da Allah kake ƙoƙarin aikata ma ƙaramar yarinya faɗe tsofe tsofe dakai!! mutun mara imani da tausayi  irinka wanda baisan darajar ƴa’ mace ba Sam bai cancanta daya cigaba da rayuwa ba,’

   ɗagowa baba alamu yayi yana ja da baya da baya idonsa jawur, jini na kwaranyowa daga bakinsa yana cewa “Dan Allah kada ka kashe ni ! Kabarni a haka naji jiki sosai, ina da ƴa’ƴa da mata in ka kashe ni zasu shiga wani hali…..’ bai bari ya ƙarasa maganar ba, yakai masa wata irin mahangul6a da hanunsa nan take yasake fasa ihu,

   “Karka kuskura ka sake buɗe wannan ƙazamin bakin naka da sunan zakayi mun bayani ! Bani da lokacin sauraron jawabin Ka, har kana da bakin da zakace mun kana da ƴa’ƴa da mata, don ubanka su yaran daka ɗauko donka lalata ma rayuwa daga sama suka faɗo? Ko su basu da dangi ne da zasuyi kuka in sun rasa su? Idan ka lalata masu rayuwa kana da tabbacin zasu ƙara numfashi ne ko baza suyi ba ? Ka yi tunanin hakan? ! idan wani ya lalata rayuwar ƴarka yaya zaka ji? Ka ƙiyasta yaya raɗaɗin yake azuciya…………yana faɗin hakan yasa hannu ya rarumesa tare da wujijjiga shi ya sake buga kanshi ajikin bulo ɗin nan take kansa ya fashe jini ya soma kwaranya, ko shurawa baiyi ba nan take ya mutu a mace…………

 (Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar? Ka mutu kana aikata irin wannan mummunan zunubin batare da ka shiryu ba? Shin mai zaka ce ma Ubangiji? mutum baison lokacin mutuwarsa ba, shiyasa ake so koda yaushe mutun ya kansance cikin shiri kuma ya kasance yana aikata abun kirkiri, sam baba alamu baisan cewa yau wa’adinsa zai cika ba, Ga yarda ƙarshem shi takasance Ya Allah kasa muyi kyakkyawan ƙarshe, kuma ka kare mu daga aikata aikin dana sani 🙏😥

  duk da ya mutu amma hakan bai masa ba saboda raɗaɗin da yake ji azuciyarsa, hannu yasa ya rarumi ƙaton dutsin dake ajiye a ƙasan wurin zai rotsa masa kai, cikin sauri matashin nan daya fita da husana ya faɗo ɗakin ya tunkaresa tare da hanzarin ruƙo hannunsa yana cewa “Yalla6ai kabarshi haka mana, ya riga daya mutu,” fisge hannunsa yayi yayin da idonsa ke cike tab da hawaye da wani irin huci yake cewa “Kabarni kawai na tarwatsa kansa ko zuciyata ta samu salama, kasan yarda nake ji acikin zuciyata kuwa, tamkar ana rura garwashin wuta acikinta saboda tsantsar baƙin cikin da nake ji, WANNAN MUTUMIN YA SHIGA HURUMINA !!!!!!!!!!!!!!!!!!!! ⁉❗‼❗❓❓❓❓❓❓

 *SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN DAYA FARMAKI BABA ALAMU ACIKIN GIDAN GONARSA AYAYIN DA YAKE ƘOƘARIN KETA HADDIN HUSANA*❓⁉

   *WANENE SHI*❓❓

Amsar tana a wurin hafsat Bature muhammad Boss Lady domin son sanin wanene wannan sai ku antaya kuɗinku naira 300 kacal Vip kuma 700 a wannan acct number ɗin 3196407426 first bank Bature hafsat Muhammad ku tura shaidar biya ta wannan layin da kuma masu tura recharge card 08103884440 kada ku bari abaku labari 👍👏*

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Alhamdulillah finally na kammala free pages

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

Back to top button