Zamantakewar Aure

Magungunan Da Yin Amfani Dasu Ke Lalata Juna Biyu

Da dama mata za su ji ana fadin cewa ba a shan wasu magunguna idan da juna biyu don kada su sa wa jariri matsala ko su jawo bari.

Wannan doka an sa ta ce tun kusan shekara 60 da suka wuce a kasashen Turai lokacin da aka yi haihuwar jarirai marasa hannaye ko kafafuwa.

Da aka tsananta binciken haihuwar wadannan jarirai sai aka gano cewa iyayensu duk sun sha wata kwayar magani ne da ake kira thalidomide mai tsayar da laulayin aman da masu juna biyu ke yi.

Akwai sauran wasu magungunan da bai kamata masu juna biyu su sha su ba, saboda gudun illa ga jariri. Lokutan da magungunan suke wannan illa su ne watanni uku na farkon cikin.

 

Karanta>>> Yadda Garin kurkum da na Citta suke Maganin kusan cututtuka 20

 

Ga jerin magungunan na asibiti kamar haka:

1. Magungunan hawan jini irin su Aspirin da Lisinopril. Idan mace mai hawan jini ta samu juna biyu kuma tana shan daya daga cikin wadannan sai ta je an canza mata su.

2. Magungunan farfadiya irin su carbamazepine da sodium balproate. Mace mai farfadiya da take shan wadannan magunguna idan ta samu juna biyu sai an canza mata

 

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

 

3. Magungunan kurajen fuska irin su Isotretinoin ko kwayoyin Bitamin A.

4. Magungunan ciwon kwakwalwa da na sa barci ma idan mace na shan su ta samu juna biyu sai an canza mata.

 

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

 

5. Magungunan ciwon olsa ma idan mace na shan su ta samu juna biyu sai ta je an canza mata

6. Magungunan kashe kwayoyin cuta irin su Doxycycline da Tetracycline su ma suna da illa ga hakora da kasusuwan jariri.

 

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Nonuwanki Lokacin Da Kike Shayarwa 

 

Akwai ma wasu magunguna na gida wadanda su ma za su iya sa illa ga dan tayi idan mace mai juna biyu tana shan su.

Misalan wadannan magunguna su ne tagargaje da dogonyaro da ganyen idon zakara da sauransu. Wato su ma ke nan magungunan gida sai an shawarci masana harkar kafin a sha idan akwai juna biyu.

Da fatan mata za’a kiyaye sosai da irin magungunan da ya dace a rika yin amfani dasu a yayin da aka samu juna biyu.

Karanta>>> Matsi Biyu marasa illar ga mata kuma Masu saukin hadawa 

Back to top button