Hausa novels

Halysaah Page 54 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 54…Wajen karfe shidda na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Ummanta tana yanka mata alaiyahu a cikin roba, stepsisters dinta Labeebah da Lamisah na can zaune su ma daga bakin kofar dakin Mama Shatu da kawayensu sai hira suke suna shewa duk sun cika tsakar gidan kai kace gidan biki ne, Mama Shatu da Mama Zubaida su ma suna tsakar gidan don da su ake hiran da kawayen ‘ya yan nasu, magana daya biyu sai su kwashe da dariya, yawanci kuma duk habaici suke jefa ma Umma da Khaleesat, ita dai Umma tana zaune gaban Coal pot tana kwashe tuwon masara da ta gama tukawa, Aunty Farida kuma ta tafi Hotoro tun bayan la’asar da su Noor, Nenne ce ta shigo gidan rataye da jakarta a kafada, lkci daya gidan yayi tsit, a takaice Nenne ta amsa gaisuwan da su Mama Zubaida da Lamisah da kawayensu ke yi mata ta nufi gun Umma tace “Zahra’u Alin ya dawo ko be dawo ba?” Umma ta gaida Nenne sannan tace “A’a bai dawo ba tukun Nenne, sannu da zuwa” Nenne tace “Kin gan ni nan daga Sheka nake daga can na tafi Ɗan Agundi, ni ce har Na’ibawa yau, tun safe na bar gida sai yanxu nake dawowa ‘yan adaidaita sahun kano dai sauransu yawo da bindiga kawai….” Murmushi kawai Umma tayi tana ci gaba da kwashe tuwon da take yi, Nenne ta jawo kujera ta zauna tace “Gidan Katime me Aya na tafi a Sheka, in gaya maki me Aya dai kafafuwanta sun mutu murus Zahra’u, ko tashi bata iya yi, babu yanda ban yi da matar nan ta rage cin nama ba amma taga kamar bakin ciki nake mata don mijina baya kawo min, to yau ni da ban ci nama ba gani da kafafuwana biyu rass, ita kuwa duk sun mutu, wai tana ganina ina taku dai dai na shigo gidan sai ta fashe da kuka, ni dai bata ban tausayi ba wallahi, sai kinga yanda take mana fafa da nama lokacin, kullum kya ji kamshin tafashen nama a gidanta, mu sai dai mu watsa er daddawa a miya” Umma na girgiza kai tace “To Allah Ubangiji ya bata lafiya” Nenne tace “Ba batun Allah ya bata lafiya ba, ai duk kafafuwan sun rube, da kyar in baza ace za a yanke mata su ba tunda ko motsa su bata iya yi ” Su Mama Zubaida gaba daya kunnuwansa na kan labarin da Nenne ke ba Umma, Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne ta juya tana kallonsa, can ta mike ta nufesa tace “Yanxu Ali baza ka hakura da fita kasuwar nan ba tun da ba wani abu kake yi a can ba sai zama cikin rana da iska? Ka dubi yanda duk kayi bakikirin kamar baka taɓa haske ba a rayuwarka Ali, tunda ba aikin fari gareka ba balle baƙi a kasuwar ka hakura da zuwa mana” Gaisheta kawai yayi ya dau buta zai debi ruwa ya fita waje ya zauna ya jira Magariba, Nenne ta tabe baki tace “To wajen kai da matar ka Zahra’u na xo” Umma ta juya tana kallon Nenne jin abinda tace, Shi ma ya tsaya yace “To lafiya dai ko?” Nenne tace “A ina lafiyar take, ba sai kun nemi zaman lafiyar za a zauna lafiya ba, labari na samu wai masu kare hakkin ‘yan Adam sun zo gidan nan sun ce za su ci gaba da daukar nauyin karatun Khaleesat a Amurka saboda tausayin abinda tsinannen mutumin nan Awdul yayi mata, to amma wai saboda kai da Zahra’u yan bakin ciki ne sai ku ka gwalesu ku ka koresu, da wanne ku ke son yarinyar ta ji fisabilillahi? Da mayar da ita bazawara da aka yi tana da karancin shekaru ko kuma da asaran karatun ta da kuke kokarin yi mata? In ita Zahra’u jahila ce bata yi karatun boko ba kai ma Jahili ne Ali? Ina ne ban shiga nayi aikatau ba don kayi karatu? To wallahi ko karshen bangon duniya ne sai Khaleesat ta koma ta karasa karatun ta tunda har aka ce za a dau nauyinta babu ko sisin ku, to ina ma ku ka ga ko sisin” Malam Ali dake ta kallon uwar tasa yace “A ina kika ji wannan zancen Nenne?” Nenne tace “Labarin duniya na buya ne dama? Ina zaune yan Mariri suka zo suka tsegunta min har unguwan da naje yau….” Mama Shatu ta kalli Mama Zubaida da ta saki baki tana sauraron Nenne, Mama Zubaida ta kasa daurewa ta gyara zama cikin kwantar da murya tace “Amma Nenne na farkon ma ba a wanye lafiya ba shi ne za a sake na biyu? Dama gashi duk garin nan kallon makwaita masu son abun duniya kawai ake mana, ko ina sai zaginmu ake tun da aka samu labarin sakin walakancin da aka yi ma Khaleesat, ana ta cewa ubanta ne ya ja mata, A rayuwar nan yanxu fa in ba iyayenka ne za su yi maka dawainiya ba duk wanda yace zai dau dawainiyar ka sama ta ka to da wani abu da yake hangen zai samu a gare ka ne, Khaleesat fa ‘ya mace take ba namiji ba Nenne, kuma ba komai ke rudar maza akanta ba sai kyanta da kalan fatar ta sun ga buzuwa, shi kenan saboda son abun duniya sai a zuba ido har sai yarinyar nan ta lalace tukunna, Abdul ya gama nasa ya samu abinda yake so ya sako mana ita sai kuma yanxu ace ga wani ma ya zo wai zai ci gaba da daukar nauyinta? Haba sam batun nan babu tsari a cikinta, shikenan ita kuma haka ta zama kamar Tasi….” Nenne ta kundumo wani zagi tace “Toh duk wanda ya fasa fadin abinda ke ransa akan Khaleesah Allah ya tsine masa albarka, kuma in de karatu ne kamar tayi ta gama sai dai bakin ciki ya kashe duk wani shege wallahi, ko ma ina za a kai ta a kai ta ni na amince ta je, ai ita tasan tarbiyyar da muka yi mata in ma ta gantalar da tarbiyar ita da Allah, kuma gobe gobe zan sa a kira min baƙar kawar tata ta zo in gaya mata uban Khaleesah ya amince koma waye zai dau nauyinta ya dauka, taje can ta ci gaba da karatun ta, ai gwara tayi nesa da mu ko bakin cikin dake damunta a rai zai ragu, mu kanmu in tana ganinmu takaici da bakin ciki take don ba mu da wani babanci da Awdul a wajenta tunda mu muka ja mata komai, gwara ta koma ta gama karatunta ta dawo da kwalinta don bazata tashi a tutar babu ba, shi kansa Awdul din yana samun labari an samu wanda ya maidata Amurka ta ci gaba da karatu sai bakin ciki ya kusa kashe shegen, a nan kuma zai san ba a banza Khaleesah take ba farin jininta ya shahara” Nenne na huci ta juya ta kalli Umma tace “Ke kuma Zahra’u halan tallan alalen ki ke da niyyar dora mata da kike mata bakin cikin komawa ta karasa karatun? To kamar yanda kike takama kina da iko da ita nima haka tunda ni na haifi ubanta, ban ga shegen da ya isa yace bazata koma ta karasa karatun ta ba” Ita dai Umma bata ce ma Nenne komai ba, Malam Ali dai na tsaye rike da buta a hannunsa yana kallon uwarsa, can dai yace “Amma dai Nenne sam babu tsari ace mun sake barin yarinyar nan ta bar kasar nan da sunan wani zai dau nauyinta bayan duk abinda ya faru, me kike son jama’an gari su ce a kaina? Sannan nace duk sanda na samu kudi zan nema mata Jami’ar garin nan tayi, ba wasu shekaru gareta ba balle ace lokaci zai kure mata” Nenne ta kallesa da sauri tace “A gidan uban wa zaka samu kudin? Mutanen garin in sun fasa fadin abinda za su fada a kanka Allah ya tsine masu albarka, kai bari kaji Ali bana bukatar ra’ayinka ko shawararka a yanxu saboda kai ma sanda ka bi ra’ayinka ka yarje ma Awdul ya kai ta kasar waje babu wanda ka saurara ko kaji shawaransa, don haka ni ma yanzu wallahi bazan saurare ka ba Amurka ne sai Khaleesat ta koma ta karasa abinda ta fara in sha Allahu, in kuma nuna ma duniya zaka yi ni er banza ce a gareka to Bismillah” Kofar gida kawai Malam Ali ya fita da butansa a hannu, Nenne ta kalli Khaleesat tace “Maza ki hada akwatinki ki tsaya cikin shiri, in sun biya maki kudin jirgin ki kama gabanki kije kiyi abinda zai taimaki rayuwarki, zama gidan nan kadai ya ishi mutum ya fada cikin mummunan damuwa, gida kamar na ‘yan sansanin gudun hijira, ga lafta laftan mata suna yawo suna doyi a cikinsa, ai ko mutum matsiyaci ne ya kasance dai yana da tsaftarsa dai dai gwargwado, amma gidan nan ga talauci ga kazanta, ina bawa zai iya rayuwa a nan idan ba dole ba” Nenne na kai wa nan ta kama hanya tayi tafiyarta, Khaleesat ta daga kai ta kalli Umma da ta bi Nenne da kallo, Mama Shatu ta mike tana kallon Umma tace “Muddin kika ce baza ki bude baki kiyi magana ba to kina ji kina gani za a mayar maki da er ki karuwa Zahra’u, wata birkitacciyar tsohuwa can kamar Nenne ce zata yanke ma er da kika haifa hukuncin abinda ya shafi rayuwarta? Ita ta tsugunna ta haifar maki er? Mu meyasa ba a mana iko akan namu yaran ba? Saboda an san baza mu dauka ba mu ba yan iska bane, to kuwa wallahi Nenne na dab da kai ki ta baro ki, mata me tabin ƙwaƙwalwa zaki yarda ta yanke hukunci akan ‘er ki? ai in ita Khaleesar ta bude baki tace bazata je ba babu uban da zai tilastata ta je wallahi, waye bai san Nenne da kwadayi da son abun duniya ba kamar tayi sata?” Muryar Nenne suka ji ashe tana makale bata tafi ba tana jiran jin abinda za a ce, Nenne ta dinga kwalo ma Malam Ali kira, sai gashi ya shigo da sauri yana kallonta yace “Lafiya Nenne? Ai magana ta wuce yanda kika ce haka za ayi” Mama Shatu tayi wuri wuri da ido daga inda take tsaye, Mama Zubaida ta mike ta lallaba ta dau kwandon kwanon wanke wankenta ta shige daki ta sako labule, Nenne ta rushe da matsanancin kuka tana kallon Malam Ali tace “Ali yau sai dai ka zaba ko ni ko Shatu a gidan nan, kawai ka zaba ko ni ko ita, ni Shatu zata kalla ta kira me tabin ƙwaƙwalwa wato mahaukaciya er macukule? Ni zata ce ma me kwadayi da son abun duniya? Tunda nake me na taɓa zuwa gun almajirin ubanta dake bara a bakin danja nace ya bani? Me na taɓa rokon uwarta me shanyayyen kafa? Bata san ina labe ban tafi ba duk ina jin abinda take cewa, cin mutunci da zagi sai wanda ta manta ne bata min ba Ali, har tana gaya ma Zahra’u ni na haifar mata er da zan yanke mata hukunci akan ta? Me nayi ma Shatu da har zata yi mugayen kalamai haka a kai na? Naga dai kullum ci gabanka da na iyalan ka shi ne burina, fadi tashi babu wanda bana yi akan kai da iyalinka, amma daga karshe sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, tsofe tsofe da ni Shatu tace min me son abun duniya?” Kuka sosai Nenne take tana share idonta da gyalen jikinta, Malam Ali na kallon Mama Shatu da tayi tsuru tsuru yace “Shatu ki tafi gida, sai na neme ki” Mama Shatu ta gwalo ido tace “Ban gane in tafi gida ba Malam, wani gidan zan tafi?” Malam Ali yace “Gidan iyayenki, ki je na sake ki” Mama Shatu ta zabura tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ka sake ni fa kace Malam, na shiga uku na lalace” Labibah ta mike tana huci tace “Gaskiya Baba sai dai mu bi Baabarmu mu ma” Nenne tace “Shegiya ku bi ta mana, yunwar cikin ku kadai ma ya isheku ai” Malam Ali na kallon Mama Shatu dake rusa kuka yace “Kar in dawo in sameki a gidan nan” Daga haka ya fice daga gidan, Nenne ta bi bayansa tana goge idonta ita ma ta fita, sai a sannan Mama Zubaida ta fito tana salati tana kallon Mama Shatu dake kuka wiwi, Umma tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta ma kasa cewa komai daga inda take zaune, Mama Zubaida na kallon Umma tace “Ke kam kinyi asara wallahi Zahra’u, ko wani bala’i ta dalilin ke da tsinannun ‘ya yan ki yake faruwa a gidan nan, gashi yau saboda ke da er ki an saki Shatu, sam babu alkhairi a tare dake da zuri’ar ki Zahra’u” Umma ta juya tana kallon Mama Zubaida sai dai bata ce komai ba, Khaleesat ma ta daga kai tana kallonta, Mama Shatu na kuka sosai tace “Kuma in sha Allahu asirin da kike yi zai kare maki a gidan nan Zahra’u, yanda kika yi sanadiyyar tsinkewar igiyar aurena daya ke da er ki wallahi sai nayi sanadin naki igiyar kema, ko tsirara zan yi yawo kuwa, Ni saki daya aka min ke ukun gaba daya za a maki, kuma kamar Ali ya maida ni ne don yanxu na fara auren sa wallahi” Don mamaki Umma ta ma rasa abun ce masu ganin yanda suka juya zancen lokaci daya, yau ga fadan karfin hali tana gani kiri kiri, biyesu ma bata lokaci ne kawai a wajenta ga makota na jin su, tsam ta mike tayi shigewarta daki, Khaleesat ta mike ta bi bayanta. Washegari da sassafe Umma da Aunty Farida suka fito tsakar gida suka tarar da Mama Zubaida da Mama Shatu a tsaye suna jiran fitowarsu za a je ba Nenne hakuri, ko wanne da Hijab dinsa har kasa don sanyi ake sosai, duk abinda suka yi ma Umma jiya hakan bai sa tace bazata bi su zuwa gidan Nenne ba, Su ma din sun san ta dalilin Umman sai Nenne ta iya hakura ta sa Malam Ali ya maida Mama Shatu shi yasa Mama Zubaida da kanta ta samu Umma ko kunya babu tayi mata magana wajen karfe biyar din asuba, Mama Shatu dama a makota ta kwana ranan don sae da Nenne ta dawo ta korata har da watsi da en tsummokaran ta, sae kusan hudun asuba Shatu ta dawo gidan daga inda ta kwana, a haka duk suka kama hanya zuwa gidan Nenne da asuban. Ranan Thursday da safe Khaleesat na zaune dakin Umma tana kallon Aunty Farida dake ta jera mata kayanta da aka amso wajen guga a cikin akwati, ita dai Khaleesat har sannan ta rasa gane me take ji a ranta, farin ciki take ko akasin haka duk ta kasa ganewa, babban damuwarta yanxu bata san da idon da zata kalli Housemate dinta ba idan ta koma America, sannan gani take kamar babban burden kawai zata zame masa a can din tunda ita ba komai gare iyayenta da za su tallafa mata da shi ba idan ta koma, ɗan kudin dake account dinta ba wani kudin kirki bane kuma da shi ta siya sabon waya with new sim card, sai few abubuwan da tasan zata bukata a can kasar, sauran kudin dake account dinta ko dubu dari da hamsin bai karasa ba, duk wannan tunanin yasa take damuwa sosai a ranta, Aunty Farida ta daga kai tana kallonta kafin ta rufe zip din jakar tace “Baki manta komai ba dai ko?” Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Aunty Farida tace “A Airport din za ku hadu da Safiyyah goben?” A hankali Khaleesat tace “Eh” Aunty Farida ta kulle zip din tace “Gwara ki saki ranki kiyi abinda ke gaban ki Khaleesat, ki cire duk wani damuwar dake ranki kar ki je ki samu matsala a karatun ki, shi kuma Jawwad Allah ya saka masa da mafificin alkhairi….” Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, Aunty Farida ta mike ta dauko daya akwatin don hada few foodstuffs din da suka siyo mata da Umma wanda zata iya shiga Amurka da shi, a hankali Khaleesat tace “Toh Aunty ta yaya za a maida masa kudinsa dake account dina?” Aunty Farida ta daga kai ta kalleta, can tace “Kudin wa? Ko Abdul?” Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida ta saki baki, can tace “Wai dama har yanxu kudaden nan nasa na account din ki?” Khaleesat ta gyada mata kai, shiru Aunty Farida tayi kamar me nazari, after a while tace “Ki ci gaba da ajiye kudin kawai Khaleesat, duk sanda ya dawo ya bukaci kayansa sai a basa, ko Umma kar kiyi ma maganar kudin for now, bana son a samu delay a tafiyarki don yanxu sai su iya cewa sai an maida masa kudadensa, kuma hakan zai iya ja maki delay….” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta ci gaba da hada foodstuff din da take a akwati.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_

Back to top button