Zamantakewar Aure

Sako Mai Mahimmanci Ga Duk Wata Mace Da Kaddarar Rabuwar Aure Ya Auka Mata.

SAKO GA DUK WATA MACE DA KADDARAR RABUWAR AURE YA AUKA MATA.

Shi rabuwar aure kaddara ce, kuma ba karshen rayuwa ba kenan kuma, sau da dama abu zai faru da ɗan Adam yana mai kin wannan abin amma alkhairi ne a gare shi, don haka wannan ki ɗauke shi a jarrabawa.

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Kiji tsoron ALLAH a cikin dukkanin lamarin ki zai ba ki mafita ya azurta ki ta inda ba ki taɓa zato ba, kuma ya ba ki Kyakkyawar rayuwa bayan wannan da kuma miji mai NAGARTA.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Kada kiyi tunanin ba ki samun irin mijin da ya rabu da ke, a’a rahmar UBANGIJI mai yawa ne kuma babu mai cire rai daga rahmar UBANGIJI sai mara rabo, shi kwanciyar hankali aure ba’a yawan dukiya bane ko sarauta ko daukaka, a’a a kulawa ne da samun Hakkokin aure dai-dai gwargwado, kada don kin fita wata gida na alfarma kice sai irin mijin ko fiye da shi, a’a ki dubi nagarta, kuma kada ki ki wani mutumin kirki saboda ba yi da abin duniya matukar zai iya rike ki babu Wanda yasan menene gobe za ta haifar, kuma ba ki san hikimar UBANGIJI ba da ya turo shi gare ki.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Za ki fuskanci jarrabawa iri iri, wasu su miki isgili, wasu su raina ki, abinda yake karya da gaskiya duk a cakuɗa ayi ta yaɗawa, kiyi hakuri, hakuri domin ALLAH ki kauda kai, za ki ga canji a gurin mutane daban daban wanda kuma ba ki taɓa zato ba.

Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure

Kada sabo da zama da miji ya sanya ki soyayya da kananun yara wanda ba auren ki za su yi ba, kawai sai dai shiririta, kada saboda rashin tsayayye ki tsaida mutumin banza, ko ki auka soyayya da wa’enda kawai ba auren ki za su yi ba, sunji kawai ke bazawara ce bari su zo su yaudare ki, ayi ta soyayyar sabon ALLAH, kada ki biye musu matukar kina son samun miji na gari kuma da mafita a rayuwar ki, ki kame kanki daga lalata ballagazanci na karshe shine ki kinyi aure kin fita, kizo kina kwanciya da wasu samari ko wani namiji wannan tozarta kanki ne da ya’ya da dangi kuma saɓon ALLAH ne mai girma.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

Ki samu sana’a duk kankantar sa ki rike kina yi, kiji tsoron ALLAH kada ki zamo mai kwadayin abin duniya ki auka abinda wasu suka auka ana sana’a ana kuma bawa maza jiki, ki takaita a ribar sana’ar ki, kiyi hakuri kiyi jumriya, wasu sun maida ZAWARCI kawai hanya ce ta holewa da yin Arziki ta kowanne hali, sai suka auka sana’ar ƙaruwanci, kowanne NAMIJI yazo ba dai don aure ba sai don a hole kawai daga ƙarshe suka shiga da na sani a rayuwa wasu kuma suka ma kamu da cututtuka.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Ki rike ibada kina kuma rokon ALLAH ya tabbatar dake akan shiriya ya tsare ki da zamewa, ki kama kanki sosai da bakin ki, kada duk inda kika shiga ba da labarin auren ki ko zagin mijin ki da wasu da suka cutar dake, idan za ki iya yafewa ki yafe in baki iyawa ki bar lamarin ga ALLAH, ki riki azkhar da karatun Alqur’ani, ki daina sanya damuwa da shiga kunci saboda yana gadar da cututtuka, ki yi hakuri duk tsanani na tare da sauki watarana sai labari komi na tafiya ne abisa kaddara, in kika ji tsoron ALLAH zai sanya miki sauki cikin al’amuran ki kuma ya gafarta miki zunuban ki.

Karanta>>> Yadda Ake Mallake Miji Da Kalmomin Soyayya Da Kauna

Sai kuma ki dauki darussa da kuma gyara kura-kuranki na baya, da kuma sake inganta nagartar ki, kuma kada ki zamo mara neman ilmi ki samu yar islamiyya kina zuwa in ma AKWAI sarari ki samu makaranta, ki koma, kokuma ki nemi sana’a ki koya.

 

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

 

Rasheedah Bintul Islam

Back to top button