Sologamy, wanda bikin aure ne wanda mutum zai auri kansa da kansa, lamari ne da aka rinƙa tattaunawa a ƙasashen Yamma a ‘yan shekarun da suka gabata. Wannan lamari a yanzu ya shiga India.
Kshama Bindu, 24, na shirin yin biki na Hindu, wanda za a gudanar a daren 11 ga watan Yunin a wani wurin bauta a birnin Vadodara da ke yammacin Jihar Gujarat.
Tana sanye da kayan amarcinta inda aka yi mata lalle a hannu, amaryar za ta zagaye wuta sau bakwai kamar yadda al’adarsu ta tanada, kamar yadda ta shaida mani ta waya daga gida.
Bukukuwan Hindu kamar su Haldi inda ake zuba wa amarya tumatir da mai, inda ake mata kiɗa da rawa. Bayan bikin za ta kai ziyara Goa domin hutun amarci na mako biyu.
Abin da aka rasa a wurin bikin kawai shi ne ango. Hakan ya faru ne sakamakon Ms Bindu ta yi niyyar ta auri kanta ne wanda shi ne auren kai na farko da ake kyautata zaton an gudanar a India.
Ms Bindu ta bayyana cewa idan ta auri kanta, za ta sadaukar da rayuwarta ga kanta.
“Auren kai wan abu ne na mutum ya dogara da kansa shi kaɗai, inda mutum zai zaɓi irin rayuwarsa da zai yi mai armashi da kyau da jin daɗi.
“Wannan hanya ce da ke nuna cewa na yarda da wasu sassan jikina, musamman sassan jikina da na yi ƙoƙarin na rabu da su.
A gare ni, aure wani abu ne mai muhimmanci kuma mai zurfi. Abin da nake nufi shi ne na yarda da kaina – gaba ɗaya kaina, har da sassan jikina waɗanda nake gani ba su yi mani kyau.
Batun iyalinta, Ms Bindu ta shaida mani cewa tuni suka saka mata albarka kuma za su halarci bikinta tare da abokansu.
“Mahaifiyata ta ce, Oh, kina so ki kawo wani abu sabo. ‘Amma iyayena waɗanda ba su da ɓoye-ɓoye sun amince da lamarin. Sun ce “muddin wannan lamari zai sa ki ji daɗi ba mu da matsala.”
Batun mutum ya auri kansa da kansa ya zama labari kusan shekara 20 da suka gabata a lokacin da Carrie Bradshaw wanda jarumi ne a wani shirin fim na Amurka ya soma magana kan batun. Sai dai lamarin wasan barkwanci ne.
Tun bayan lokacin, rahotanni sun ce an samu aurarraki irin waɗannan kusan 100 aksari waɗanda ‘yan mata suka yi.
Amaren kan saka kayan aure ɗauke da fulawa a wani lokacin ma ‘yan uwa da abokan arzikinsu suna musu murna.
A wani lamari ma da ba a saba gani ba, wata ‘yar ƙasar Brazil mai shekara 33 ta saki kanta watanni uku bayan aurenta.
‘Yan kasuwa da dama a faɗin duniya na ta biye wa wannan lamari, inda suke bayar da gudunmawa na kayan aure ciki har da zobuna da katunan aure.
Sai dai sakamakon irin waɗannan labarun ba a cika jinsu a India ba, batun auren Ms Bindu ya zama abin tattauanawa a ƙasar.
Wani likitan ƙwaƙwalwa da na yi wa magana kan wannan lamarin ya sha mamaki kan wannan lamari.
“A gare ni, wannan wani sabon abu ne,” in ji Dakta Savita Malhotra, wanda tsohon shugaban sashen lafiyar ƙwaƙwalwa ne a asibitin PGIMER da ke birnin Chandigarh.
Wannan labarin ya jawo an soma tafka muhawara a shafukan sada zumunta, wasu na ta yabonta kan cewa za ta zama abin koyi ga jama’a dama, sai dai ga wasu da dama kuma sun yi Allah-wadai da wannan lamarin.
Wata mata a Twitter ta yi ta tunanin cewa mene ne amfanin yin aure idan mutum ba wani zai aura ba. Wata kuma cewa ta yi da alama Ms Bindu kawai na so ne ta guje wa ɗawainiyyar iyali.
Ga waɗanda suke caccakar ta, Ms Bindu abu ɗaya ta ce a gare su kawai inda ta ce: “Zaɓina ne na auri wanda nake so – ko mace ko namiji ko kuma kaina.
Kuma ta hanyar auren kaina, ina so na mayar da auren kai wani abin daidai. Ina so na shaida wa mutane cewa mutum shi kaɗai ake haifa, kuma shi kaɗai zai mutu.
Wa zai so ka sama da kai? Idan ka faɗi, kai ne da kanka za ka ɗauki kanka,” in ji ta.