Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 26 Complete Novel

 

🐅 MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of Tiger)

Written and story by
Asma’u Muhammad Auwal

( ASMEETAH NOVEL ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——->71 & 72 <——-

✈️✈️✈️ ƘASAR CALIFORNIA…

Sarki Raamud ne zaune akan kujerarsa ta mulki ya ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya yanata huci,
ga Mahaifiyar Ayush kuwa durƙushe a gabansa ya sata tayi kneeldown, tana kuka ga gumin dake yanko mata daga sumar kanta, tana faɗin “Shugaba kayi hakuri ka bar hukunta ni haka, nifa temako nayi….” kafin ta ƙarisa maganar ya daka mata wani irin gigitaccen tsawa “your very stupid, ni zaki munafurta? kin sace mun zoben Dish kin kaiwa Ɓingel kuna ganin shine hanyar da zaku bi ku magance matsalar ku, kin toshe mun kafar da zanga Ɓingel da kuma Junaidu! toh amma ina so ku sani cewa kafin ku aiwatar da aikin ku na rigada na tura Aljanin ƙudus yaje ya murɗe mun wuyan Junaidd….” Hahahaha ya kwashe da wani irin mahaukaciyar dariya..

tsabar tsoro da firgita sai da Bara’at ta faɗi zaune daga kneeldown ta dafe ƙirjin ta tana faɗin “shugaba ka kashe Junaid? Innalillahi wa inna ilaihi raju’un!” ta fashe da kuka “meyasa ka ɗauki wannan tsatstsauran hukunci? shikenam nima kuwa zaka rasani yanzu domin rayuwata batada wani amfani tinda har na gaza ceton Junaid.”

Da gudu ta tashi ta miƙi hanyar fita daga cikin falon masarautar kai tsaye ɗakinta ta nufa tana shiga ta danna key, zuwa tayi ta ɗauko poisen zata sha,
wani irin bugu akayi wa ɗaki ya buɗu, cafko hannun ta yayi sannan ya yi wurgi da ƙwalbar gubar ya zabga mata mari ya hankaɗata saman gado yana faɗin ” ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, idan kika kashe kanki kin mutu kafura…”
katse shi tayi da cewa “wanda yayi kisan kai kuma fa?? ya kamata kaji tsoron Allah Abul Mayush, ka sani fa wata rana zaka mutu, bawai kai kaɗai za’a bari a doron duniya ba,
Ka kashe Junaid ita kuma fa Ayush shin zata rayu ne? bakayi tunanin haka ba, ka yanke hukunci saboda ita to ka sani ko da ran Junaid ko ba ran Junaid Ayush zata mutu ne,
an zo wajen da bazata iya rayuwa ba tare da Junaid ba…..”
ta tinshire da dariya tana tafa hannayen ta biyu ta kuma cewa “shin baka san Junaid da Ayush jininsu ɗaya ba ne?
to ka ɓarar yanda ka kashe Junaid haka Ɓingel ɗinka ma mutuwa zata yi, bazata rayu ba……”

Ja da baya Sarki Raamud ya soma yi tabbas maganganun Bara’at sun juyar masa da kwakwalwarsa, zuciyarsa ne ta fara harbawa da ƙarfin gaske,
lokaci guda kuwa ya yi regret akan abunda ya aikata, “haƙiƙa Ayush itace mahaɗin Junaid, kuma jininsu ɗaya yanaso ya warware wannan al’amarin amma ya kasa…” haka ya tsaya cak yana maganar zuci, jikinsa ya sake baya jin daɗin jikinsa sosai, ga wani irin zazzaɓi da ya rufe shi..
lokaci guda kuwa ya zabura da sauri ya fice daga cikin room ɗin Bara’at wacce itama tsayawa tayi tana kallonsa cike da tsana da kuma mamaki ga hawayen da suke gangaro mata, kamar tasan abunda yake ransa ta furta cewa “yanzu haka nasan zai tafi ƙasar nigeria ne domin yaje ya dubo su Ayush….”
itama da gudu ta nufi waje, ta samu Sarkin har ya hau kan wani dokinsa mai ƙarfin gaske da kuma gudu, domin zai iya zuwa nigeria da wannan dokin ba tareda ya hau jirgi ba, domin yasan ta ko ina nemansa ake..
har ya fara tafi ta ƙwalla masa ƙira da ƙarfi tana faɗin ” *kasa a ranka cewa kana barin cikin masarautar nan shikenam ka barshi har abada, kuma ba kai ba mulki! ƙa’idojin dokar kenam, na tunatar dakai…*

Sarki da jin hakan ya tsayar da dokinsa, gabansa na yankewa, idanuwansa
kuwa har sunyi jawur, fuskarsa ya nuna alamar damuwa ajiyar zuciya yaja sannan ya kanne idanuwansa sosai, yana so yayi kuka amma ba hali domin zubda hawayensa shima wani makaryin asiri ne a jikinsa…

Ba yanda ya iya haka ya juyo da dokinsa saboda mulkinsa shine babban abun tasirinsa kuma shine tushen sa na iyaye da kakanu…
Haka ya sauƙo yana tangaɗi hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfin bala’i, tabbas shima yasan idan babu Ayush shikenam tashi tazo ƙarshe,
saida yazo daf da Bara’at ya tsaya yana kallonta cike da tausayawa kansa, bazai iya control hawayensa ba haka ya durƙusa da gwiwowinsa sannan ya fashe da wani irin matsanancin kuka kansa a sunkuye….

zaro ido Bara’at tayi tace “Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, nashiga uku *SHUGABA* tinda uwata ta haifeni ban taɓa ganin damuwa a fuskar ka ba balle hawaye uwa uba har da rera kuka, abun babba ne, shikenam ka korar da ALJANUNKA sunga hawaye a idonka….”

Aljanun da suke cikin masarautar sa kuwa haka suka rinƙa ɓacewa,
duk wani abun tsafi sai ɓacewa suke,
duk abubuwan tsoro dake cikin dajin maƙarƙashe duk sun ɓace daman shi ya ƙirƙire su da yarjejeniyar bazasu ga hawaye a idonsa ba har abada…
gashi kuwa yanzu komai ya rushe masa ata sanadiyar Ayushert!
Haka masarautar nan ta dawo babu komai na tsafi a ciki, daga shi sai matarsa Bara’at sai kuma DAMUSAR JUNAID wanda shi kuma makaryin tsafinsa yana jikin zoben cibiyar Ayush,
Shima Sarki Raamud akwai sauran tsafi a jikinsa wanda shima makaryinsa yana a tattare da wannan zoben cibiyar Ayush,

suna tsaye a harabar masarautar sai ga wasu tsuntsaye suna shirin shugowa, da gudu Sarki ya miƙi hanyar babban gate wanda ya buɗe yaje ya rufe ya danna ƙwaɗo
haka tsuntsayen suka juya ba halin shugowa domin akwai hayaƙin da suna shugowa zasu ƙone…

ita kuwa Bara’at jikinta ne yayi sanyi domin za’a iya kawo musu hari a koda yaushe idan aka fiskanci babu masu kula da masarautar nan, tana cikin wannan tunanin taji ya riƙo hannunta suka shiga cikin falon masarautar, gaban Damusa yaje ya durƙusa yana shafarsa
murya na kakkarwa yake magana da Damusar “kai kaɗai ne ka rage mun a halin yanzu daga kai sai matata, itama Allah yasa kar ta gujeni, ga shi na rasa ɗiyata tilo, nasan Ɓingel mutuwa zata yi! banaso na rasa masarautar nan saboda amanar mahaifina ne..”
Hmmm! ajiyar zuciya yayi sannan yakai idonsa kan Bara’at wacce take tsaye kanta a sunkuye, ya taso yazo gabanta ya riƙe hannayenta yana faɗin “idan bakya son zama dani akwai sauran tsafi a jikina zan mayar dake nigeria a yanzu, sai dai amma gurin zama zai gagare ki…”

Bara’at tana kuka tace “ba yanda zanje ina tare da kai, gurin wacce zanje a nigeria nasan ta mutu, ina zanje to? sai dai mu mutu tare….” ta ƙarasa maganar tana kuka ta rungumi Sarki,
shima hawayen yake zubar wa yana mamakin ta yanda al’amarin nan ya afko masa lokaci guda,
Abubuwa sun taɓarɓare masa, lokaci ɗaya ya zamo kalar tausayi,
kamar ba shi bane *SARKI RAAMUD, SARKIN MATSAFAN DUNIYA*….

(( *Yaaa Salam!*
*ku duba abunda ya faru da Mahaifin Ayush lokaci ɗaya,*
*ba’a jayayya da ikon Allah, duk abunda Allah ya tsara ba makawa sai ya faru kafin ƙiftawar ido,*
*Allah shine mai komai a hannu kuma shine mai mulki shine mai yin abunda yaso, duk tsafin mutum, duk izzar mutum, duk ƙarfin ikon mutum, duk zalincin mutum a lokaci ɗaya Allah zai gama da shi,*
*ya Allah kasa mufi ƙarfin zuciyar mu 🙏🙏* ))

******

Doctor Hasheem ne ya fito falo yana zaune akan sofa idonsa akan plasman,
Muryar Laila ya jiyo tana faɗin “Bros kai kaɗai ne a falon?..”
Juyawa yayi zai mayar mata da amsa kwatsam eyes ball ɗinsa suka sauƙa akan Maimoon wacce tasha doguwar riga da gyalensa iri ɗaya tasha makeup ba ƙaramin kyau tayi ba,
ta ƙaraso gaban Dr Hasheem ta durƙusa gwiwowinta ƙasi sannan ta kamo hannayensa tana zubda ƙwalla tace “Yaya Hasheem! bansan laifin mai nayi maka ba, kasan ina matuƙar ƙaunarka, bazan iya juran rashin ganinka ba, bazan iya juran rashin jin muryarka ba, amma meyasa ka daina zuwa gidan mu? ka daina ƙirana a waya ko da saƙo ne,
why my Doctor! why!! why!!!….”

Laila ce tayo kan Maimoon tana faɗin “dan Allah Besty ki tashi ba girmanki bane, Aji down wallahi..”

Maimoon katse ta tayi da cewa “Laila ko cewa yayi na kwanta ya takani ya wuce da gudu zan kwanta indai zamu dawo da soyayyar mu,
Soyayyar yarinta har zuwa girman mu ai ba wasa bane, cikin zuciyata tafarfasa take”

Doctor Hasheem kuwa yana jin raɗaɗi a cikin zuciyarsa baya son jin kukan Maimoon tin tana ƙarama ma!
eyes ɗinsa na kan plasman yana kallo kunnuwansa suka fara jiyo masa kukan Ayush, da sauri ya kalli Maimoon sai yaga fuskar Maimoon ta koma ta Ayush tana kuka tana riƙe da hannayensa,

Da sauri Doctor shima ya durƙusa ƙasi ya riƙe hannayen ta yana faɗin “Ayush! Ayushert meya sameki kike kuka, bazan iya juran ganin hawayen ki ba…”
yana share mata hawayen kan fuskar ta.

zaro ido Maimoon tayi leɓɓen bakin ta na kakkarwa tace “wacece Ayush?..”
itama Laila ta girgiza ganin yanda Yaya Hasheem yake kiran Maimoon a matsayin Ayush, cikin firgici Laila ta dafa kafaɗar Doctor tace “Yaya baka gani ne? Maimoon ce fa a gabanka ba Ayush ba” ta ƙarasa magana itama tana zubda hawaye,
domin ta tsani taga Maimoon tana kuka wani irin takaici take ji….

Doctor Hasheem ƙamewa yayi a wajen ya zuba wa Maimoon ido sai a lokacin ya lura ashe Maimoon ce ba Ayush ba,
Ayush gizo take masa….

Da gudu Maimoon ta tashi ta nufi hanyar waje direct hanyar gate ta nufa.
Laila ma biyo bayanta tayi tana ƙiran ta “Aunty Maimoon! Aunty Maimoon!! ki tsaya mana dan Allah, Besty!!!” Ganin har ta buɗe gate ta fice yasa Laila ta koma ciki tana faɗin “haba Yaya mekayi ne haka, shin meyasa bazaka iya ɓoye soyayyar Ayush ba, gashi yanzu soyayyar da kuka yi shekara da shekaru kuna ginata lokaci guda ka rushe ta…”

buɗe baki yayi a hankali yace “please Auta don’t disturb me, am not feeling better”

“toh ka tashi Yaya kaje ka mayarta gida dan Allah, kaji Bros” tana bubbugan kafaɗunsa “Yaya ka ƙona mata rai sosai, ka ƙuntata mata akan wata banza Ayush…..”

kafin ta rufe baki Doctor Hasheem ya kwashe Laila da wani irin gigitaccen mari har sai da taga taurari,
ya miƙe tsaye yana faɗin “are you mad? kinsan abunda kike faɗa kuwa Laila, get out from my side…” ya ƙarisa maganar yana nuna mata yatsa,
da gudu Laila ta bar wajen tana kuka hannunta kuwa na riƙe da kuncin ta…
shi kuma ba abunda yake sai huci yana faɗin “sorry my Ayush, forgive me my Ayush ba wanda zai zage ki na kyale shi a gabana…”

******

Gab da mangrib Mommy ta shawo kwana da motar ta, ganin gate a buɗe abun ya bata mamaki ita dai kawai shigewa cikin gidan tayi a bakin gate ta tsayar da motar ta fito tana kiran “Baba mai gadi! Baba mai gadi!!” har cikin ɗakinsa ta leƙa amma bata ganshi ba, rufe gate tayi sannan ta shige motarta ta miƙe hanyar da zai sadata da harabar gidan, tayi parking motar ta hankalin ta a tashe bata ga Baba maigadi ba,
ganin motar Junaid yasa tajaa ajiyar zuciya, ganin motarsa yasa hankalinta ya kwanta,

falo ta shugo bakinta ɗauke da sallama, ga falo wayam babu kowa direct ɗakinta ta nufa taje tayi wanka ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar riga Bubaa!
ta ƙara fitowa ta nufi kitchen gani tayi anyi girki an saka a flask, fried rice ne ga naman kaji a saman food flask,
Murmushi Mommy tayi tare da faɗin “Allah yayi muku Albarka yarana, gashi Mommyn ku ta dawo da yunwa..”

sai data cika plate kafin ta dawo falo ta zauna akan 1 seater tana cin abincin ta cikin nutsuwa, bayan ta kammala ta ɗauko milk a cikin frig mai sanyi ta kora da shi….

ta miƙi hanyar ɗakin su Junaid tana faɗin “bari na dubo yaran nan a ɗakunan su ko kuma suna manne da juna sai Allah..”

ta haura upstairs tana taka matakala a hankali..
Ɗakin Junaid ta fara shiga ta duba bata ganshi ba

Murmushi tasau tana girgiza kai tace “nasan kuna tare ai daman…”
Ɗakinsa har yayi ƙura ta gyara masa komai har da wankin toilet, daman tin kafin Ayush ma ita take gyara masa room ɗinsa,
ta feffeshe ɗakin da turare…

Daga nan ta fito ta miƙi ɗakin Ayush, tsayawa Mommy tayi a bakin ƙofa ta fara knocking,
kar ta kutsa musu ɗaki tazo taga abunda zaisa taji kunya domin su ba wani kunya suka sani ba especially JUNAID…

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

*MASHA ALLAH*
Na gaji da typing wollah bacci nake ji, sai da safe zaku ga new update kuma du…

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

Back to top button