Hausa novels

Halysaah Page 186 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 186…..Jay ya daga kai yana kallon Mami da ta fito daga cikin ward din ya mike yana kallonta ganin tana goge hawayen da yaki tsaya mata, da kyar tace “Na gansa Jawwad har ya tashi” Sai da Jay yaji gabansa ya fadi da Mami tace Ajay ya tashi, zai shiga dakin sai ga likitan ya fito, Jay yace “Pls zan iya shiga in gansa Dr?” Likitan ya girgiza kai yace “He needs rest, kaga Mama ma cewa muka yi ta fito, in sha Allah zuwa nan da wani lokaci zaka iya shiga wajensa don he is gradually progressing, ba mu son a damesa ne da yawa, thanks for understanding” Daga haka likitan ya kullo kofar ward din bayan nurse din ta fito…. Mami na ta zaune ita kadai a corridor din ward din har wajen karfe goma na dare, ba da dadewa ba Jay ya fita waje don tare suke zaune all this while a corridor din Ward din, farin ciki yasa Mami ko gajiyar hanyar da ta biyo ma bata ji balle yunwa, she is just full of excitement, not long after Jay ya dawo ya zauna kusa da ita yana kallonta a hankali yace “Mami i paid for a hotel room for you, ki je ki huta, hotel din babunisa daga nan, i even got you some food….” Mami tace “A’a kai dai ya kamata kaje ka huta Jawwad ni ka bar ni a nan, naga you are stressed, kawai ka samo min bottle water ya isheni, bazan ci komai ba….” Jay yayi shiru yana kallonta, sai kuma ya mike a hankali ya bar wajen, Mami ta sauke ajiyar zuciya tana kara hamdala a ranta, farin cikin da take ciki yau kam bazai ma misaltu ba, ko minti biyar Jay bai yi da barin wajen ba sai ga shi ya dawo with surprise written over his face, ya nufo Mami yana kallonta yace “Mami Mai martaba is here” Da mamaki Mami tace “Mai martaba? Dama akwai jirgi ne daga Bauchi zuwa nan?” Jay ya girgiza kai yace “Sai dai ko Corporate Jet…” Mami ta mike bayan ta hango sarki /with 3 of his trusted kinsmen tare da likitocin asibitin da suka rakosu, sai Dsp Bilyamin da wasu yan sanda biyu dake biye da su a baya, Mami taji tausayin Mai martaba har cikin ranta, duk zaton ta gobe da safe za su gansa a asibitin tunda dare yayi ashe tuni ya kamo hanya, shi kansa Jay was expecting him to be at Makurdi tomorrow morning, Mai martaba na kallon Mami murya can kasa yace “Fulani” Mami ta sauke idonta ta kasa ce masa komai lokaci daya hawaye suka kawo idonta ta fara gogewa, Mai martaba ya juya ya kalli Jay that was beginning to get emotional too, Dafa sa Sarki yayi amma ya kasa ce masa komai, daya daga Doctors din ya bude kofar ward din da Ajay yake, Mai martaba sai kallon kan gadon da Ajay ke kwance yake yi, ya kasa shiga ciki har sai da likitan yace “Bismillah ranka shi dade” Mai martaba ya sauke idonsa ya karasa cikin ward din walking slowly ya isa har inda Ajay ke kwance ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, dukawa yayi ya kamo hannunsa cikin nasa, Ajay ya bude ido a hankali, yana hada ido da Mai martaba ya rike hannunsa gam yana kallonsa, da kyar ya mike zaune har sannan bai sake hannun Mai martaba ba ya daura kansa a jikinsa, Mai martaba ya rungumosa a hankali, cike da karfın hali yace “Ahmad” Ajay ya kasa cewa komai hawayensa na zuba jikin Mai martaba yana kara kwantawa jikinsa, sosai Sarki ya kai zuciyarsa nesa, ya dinga shafa gashin kan Ajay a hankali ya kasa cewa komai, they were like that for almost 5 mins sarki ya bai sakesa ba, both the Doctors and everyone suka bar masu ward din, that was when the king shed the tears he was avoiding yana kara rungume dan nasa yana jin kamar mafarki yake…. A daren ranan Mai martaba yace za a fara processing din fita da Ajay America for treatment, ya kuma yi requesting asibitin su sallamesu su koma Bauchi gobe da safe, sai a ci gaba da kula da Ajay a can kafin a gama processing fitar su Amurka, the Doctors Agreed to that ganin Ajay is stable enough za a iya tafiya da shi…. Wajen karfe sha biyun dare Mami na zaune kusa da Ajay bayan Jay da Dsp Bilyamin da officers din dake tare da Dsp din sai local ruler din Makurdi sun tafi yi ma Sarki da kinsmen dinsa rakiya zuwa hotel din da aka yi booking masu, cup din shayi ne a hannun Mami wanda Ajay ya sha ya rage ya mika mata, Mami dai sai kallonsa take babu ko gajiya, he looks fresh alamar he was doing well a duk inda ma yake, kawai dai rama ce da yayi, tambayoyi da yawa ne ke yawo a zuciyar Mami at this point amma this is not the right time na yi masa ko wani tambaya, infact babu wanda yayi masa wani tambaya tun bayan da aka yi admitting dinsa a asibitin ana basa enough time to rest, shi kansa Mai martaba har yanxu bai masa ko wani tambaya ba, a hankali Mami tace “Baka tambayi Halysaah ba Junaid” Ajay da yayi nisa cikin tunanin da yake ya daga kai da sauri ya kalli Mami don tunanin da yake kenan tayi masa wannan tambayar, ya zata Khaleesat will be among the first person he will set his eyes on, but may be there is a reason why she is not here, a hankali ya sauke idonsa ya kasa cewa komai, lokaci daya yaji zuciyarsa ya fara bugawa bayan wani tunani ya fado masa a rai, bude kofar ward din aka yi, Jay ya shigo ward din suka hada ido da Ajay, Jay na tafiya slowly ya karasa har kusa da gadon yana kallonsa babu ko kiftawa kamar yanda Ajay ma ke kallonsa, a hankali Ajay yace “Jawwad….” Jay ya rungumesa ya runtse ido yana patting bayansa, da kyar yayi gathering courage din cewa “I missed you each and every day Junaid, I…..” Jay ya kasa ci gaba ya dora goshinsa a kan Ajay yana sauke numfashi a hankali, after some seconds cike da karfin hali yace “Having you back is the greatest thing that have happened to me Bruh, I will now appreciate every second with you in life” Mami dai kallonsu kawai take a sanyaye tana jin wani farin ciki a ranta, Khaleesat ce ta fado mata, tayi murmushi tare da sauke ajiyar zuciya. Washegari da sassafe Khaleesat ta samu Ammi a parlonta, tun jiya da daddare aka kai Inteesar gidanta tunda babu wani occasion da aka yi na bikin da ya wuce daurin aure sai Walima, bayan Khaleesat gaida Ammi tana wasa da hijab din jikinta tace “Ammi kano nake son zan tafi, Kanwar Ummata jiya aka daura aurenta ita ma” Ammi na murmushi tace “Hajiya Aseeyah ta gaya min Mai martaba ya daura aure da kanwar mahaifiyarki, na kuma yi farin ciki sosai, har na ma Ummanki Allah ya sanya alkhairi ta waya….” Khaleesat ta dinga kallon Ammi babu ko kiftawa, a ranta ta fara tunanin Mai martaba as in how? she became so confuse, ta zauna da kyau tace “Ammi Me martaba kuma?” Ammi tace “Au wai da baki sani ba Khaleesat?” Khaleesat ta girgiza mata kai still in shock, Ammi na murmushi tace “To Kanwar Ummanki ta zama matar Mai martaba yanxu, fatan dai Allah ya basu zaman lafiya, nayi farin ciki da wannan aure sosai, zumunci me kwari ya kullu har abada dake da gidan sarki in sha Allah, bari in ma Umar magana ya siya maki available ticket zuwa kanon, ita ma Hajiya Aseeyah ta kirani jiya wai zata je wani waje emergency, na ma kirata wajen karfe tara na dare jiya ban sameta a waya ba, zuwa anjima zan sake kiranta inji ko yau zata dawo” Khaleesat dai tayi shiru don har sannan she was shock da news din da Ammi ta mata breaking wai Mai martaba ya auri Aunty Farida, flight din karfe goma na safe Umar yayi ma Khaleesat booking zuwa Kano, har ta kagu ta ganta a Kano bayan wannan labarin da ta ji. Karfe tara na safe masarauta ta rikice bayan Mai martaba sun dawo daga Benue tare da Ajay, abun ya zo ma kowa kamar al’mara, dama tun basu taso ba Sarki ya kira yasa aje gidan Hajja a daukota zai yi magana da ita, ko da suka iso Hajja na gidan, ga kuma likitoci har uku na jiran isowarsu to attend to Ajay, irin shock da rudanin da aka shiga a masarautar ganin Ajay ba a cewa komai, sosai Mami taji dadi ganin yanda kowa ke farin ciki wholeheartedly har da koke koke, tsabar shock Hajja ko kukan ma ta kasa sai kallon Ajay kawai take tana ganin abun kamar mafarki, sai shi ne ya isa har gabanta ya zauna yana kallonta, ta jawosa jikinta ta fashe da kuka sosai tace “Ahmad…” a cikin commotion din happiness din nan Mami ta ciro wayarta ta tafı kiran Ammi, Ajay ya daura kansa jikin Hajja duk jikinsa a sanyaye ganin bai ga Khaleesat ba balle babies dinsa da yake ta zaton zai gani idan suka shigo Emirate din, kuma babu wanda yace komai akan both his wife and babies, everyone is just happy to see him, sai ya fara tunanin ko Khaleesat tana gidansu ne, har cikin rai kowa ke murna a parlon Hajja, suna ta kiraye kirayen yan uwa da abokan arziki ana sanar masu ga Junaid ya dawo, su Hajiya Sumayya da Gimbiya Firdausi tuni suka kamo hanyar gidan sarki a rikice… Hadiyah was so shock bayan Ummi ta kirata ta sanar mata dawowan Ajay, ita ma gashi har tayi booking ticket zuwa Kano sannan ta biyo wani jirgin da zai karaso da ita Bauchi, Hadiyah tafi minti biyu ta kasa motsi a inda take zaune, ko minti biyar bata yi da fitowa daga dakin da suka sauka ba ta bar Khaleesat na shiri Umar zai kai ta Airport, da kyar ta mike hawaye cike idonta tana jan kafa ta fito daga dakin da take, a corridor ta ci karo da Ammi ita ma ta fito tana share hawaye, Hadiyah na kallonta ta fashe da kuka tace “Ammi an kira ki kema ko?” Hawaye na zuba idon Ammi tace “Yanxu Hajiya Aseeyah ta kirani Hadiyah, ina Khaleesat din?” Cikin kuka Hadiyah tace “Tana daki” Ammi tace “To ki kyaleta kar ki ce mata komai, Umar zai mana booking jirgi yanxu zuwa Bauchin, tafi ki shirya kawai, ita ma ki sa ta shirya” Hadiyah da ta kasa dena kuka ta gyada ma Ammi kai kawai. Khaleesat tayi mamaki da Ammi tace mata Bauchi za su tafi, nan taji hankalinta ya tashi sosai duk tunaninta ko wani abu ne ya samu Mami, nan da nan hawaye suka ciko idonta muryarta na rawa tace “Ammi me ya faru?” Ammi tayi murmushi tace “Babu komai Khaleesat, ba nace maki an daura auren Sarki da Kanwar Mamanki ba, shi yasa za mu je ai” Khaleesat taji hankalinta ya kwanta don sai da ta sauke ajiyar zuciya, Ammi bata sanar ma Inteesar da aka kai gidan mijinta abinda ke faruwa ba sanin sai ta iya birkicewa tace zata Bauchi ita ma, karfe hudu saura Khaleesat suka isa Masarauta da Ammi da Hadiyah don basu samu jirgi direct ba, nan Khaleesat taga gidan cike da mutane, tun da suka shiga babban parlor Khaleesat taga su Kilishi na murmushi suna kallonta, sosai tayi mamakin ganin har Mami a parlon ta zauna ta gaishesu gaba daya tana mamakin why is everyone looking so happy, ko duk saboda auren Mai martaba da Aunty Farida ne suke murna haka, Hadiyah dama parlon Mai martaba ta nufa direct, a can second parlor dinsa taga Ajay zaune da Jay a gefensa, ga abinci iri iri a gabansa, ta sake handbag din hannunta ta tafi da gudu ta fada kansa ta rungumosa cikin kuka tace “Ya Junaid…” Ajay dai kallonta kawai yake, a hankali yace “Hadiyah” Kuka kawai take ta kasa cewa komai, Jay dai kansa na kasa, cikin rawan murya Hadiyah tace “We all missed you so much ya Junaid, don Allah kar ka sake barin mu” Ajay dai na rungume da ita bai iya yace komai ba, abincin da ta gani gabansa ta fara zuba masa a plate, sai ga Ammi ta shigo parlon tare da Gimbiya Firdausi da tayi mata rakiya, Ammi ta kasa daurewa ta fashe da kuka tana tsaye bakin kofa, Ajay ya mike tsaye a hankali yana kallon Ammi. Mami na kallon Khaleesat that was looking tired tace “Ya hanya Halysaah?” Khaleesat tace “Lafiya lau Mami” Mami tace “Kin sha magungunan ki na yau kuwa?” Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, Mami tace “To mu je bangaren ki” Mikewa tayi tana biye da Mami taga duk mutanen dake parlon sun bi ta da kallo, a haka suka koma part dinta da Mami, it was sparkling clean as usual, Mami tace “Jirgin ķarfe nawa ku ka biyo?” Khaleesat tace “Karfe daya da rabi” Mayafin jikinta ta cire tace “Zan yi sallah Mami” Mami tace “To shiga kiyi alwala….” Ta nufi Bedroom din Ajay ta shiga bandaki, Mami kuma ta bar part din tana murmushi. Khaleesat na zaune kan darduma bayan ta idar da sallah tayi nisa tunanin da take Kilishi ta shigo dakin da sallama tace “Har kin idar da sallahn Halysaah?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Na idar Aunty” Kilishi tace “To taso ku gaisa da baki a parlor” Mikewa Khaleesat tayi ta bi bayanta tana tafiya a hankali suka fita daga dakin har zuwa Main parlor, dai dai sanda Jay ya bude kofar parlon ya shigo Ajay na biye da shi a baya, Khaleesat bata kai ga karasowa cikin parlon ba tayi ido hudu da Ajay, ta tsaya tana kallonsa babu ko kiftawa, su Hajiya A’isha da Mami da Gimbiya Firdausi na zaune parlon ko wanne da murmushi a fuskarsa, a hankali take tafiya tana jan kafa ta nufesa har lokacin bata daina kallonsa ba, Jay ya koma gefe ya rungume hannunsa yana murmushi yana kallonta feeling so happy he brought back her husband to her, sai da ta kusa dab da Ajay ta sulale tun kan ta kai kasa yayi saurin rikota ta fada jikinsa a sume, Mami ta sauke idonta hawaye na zubo mata, Kilishi kanta dake tsaye parlon kuka take, Jay ya sauke idonsa ya karasa ya duka kusa da su sanin Ajay ba shi da strength din yi mata komai a lokacin, ya amsheta daga hannunsa…. karfe sha daya na dare Khaleesat ta bude idonta a hankali tana bin ko ina da kallo, Ajay dake zaune gefenta ya duka dab da ita ya kamo hannunta yana kallonta amma ya kasa cewa komai, hannuwanta tayi wrapping a wuyansa ta rungumosa har sai da ya fado kanta, muryarta baya fita sosai tace “Me yasa ka tafi ka bar ni” Tana fadin haka hawaye suka fara gangarowa gefen idonta tana kallonsa, muryarsa na rawa yace “Jeeddah….” Saukan hawayensa taji a jikinta, ta fashe da kuka a hankali tana kara rungumesa gam a jikinta kamar za a kwace mata shi…..

Back to top button