Uncategorized

Matar Makaho Part 7 Complete Hausa Novel

MATAR MAKAHO

Chapter 7

By Rukayya Ibrahim

Keke napep na sayar ban kulasa ba

Hajiya Ina Zaki?Mai napep in ya tambaye Sumayya.

“MEGA restaurant” na basa Amsa

Ok hau muje

Sumayya restaurant Kuma?Koh dai banji daidai bane? Al’ameen ya tambaye ta

“Daidai kaji,yau agun zamuci abincin dare,banyi girki ba”

Sumayya ai akwai wajen Saida abinci Koh round about ana sai dawa basai munje restaurant ba.

“Nidai gun zamu Kuma sai kaje”   

Wai hajiya bazaku hau bane? Koh nayi tafiya tane? ,kun tsaidani Kuna Bata mini lokaci ga dare nayi  

“Yi Hakuri.

 yayan Khadija muje”  nace Ina Kama hannunsa muka shiga keken        

 A MEGA restaurant, Mai keke ya saukesu

Biyansa nayi kudinsa bayan mun sauka, Kama hannunsa nayi muka shiga ciki,

Al’ameen Kam binta kawai yake baida baki ,sai dai yaji sun shiga wani waje Mai mugun sanyi sai Kuma D’an motsen jama’a d’aid’ai ku

Har lokacin Ina rike da hannunsa,D’aya daga cikin kujerun dinning table dake wajen,na nufa ja Masa kujera nayi”ka zauna”nace Ina zama a nawa kujeran

Ok , yanzun cikin inda muke nan shine restaurant in? ya tambaye ta Yana zama

“Eh Mana Hala baka taba zuwa ba”?

Nasan restaurant Amma bana shiga.

“Toh yau ka shiga”

Waiter ne yazo, sannunku da zuwa mega restaurant,ga list nan ka duba abinda za’a kawo muku,yafada Yana mikawa Al’ameen Takardan hannunsa

“Yauwa bani Anan”nace Ina karban list in.

“Me za’a kawo maka”? 

Duk abinda kike so, Al’ameen ya Bata Amsa

“Tamabyar ka fa nayi”

Amsa na b’aki 

“Ok toh a kawo maka tuwo Koh shinkafa Koh doya”?

Aban doya 

Ok,mikawa waiter in nayi hade da basa amsa”ka kawo plate biyu D’aya na doya da miyar kaza,D’aya Kuma fried rice with chicken  yaji vegetable sosai,in Kuna da exotic a had’a mana da ruwa”

Ok ma, an gama,ya karbi takardan in ya wuce

Sosai mutanen restaurant in suka bisu da ido tun shigarsu kowa yake gulman su da ido wasu Kam har kasa hakuri sukaye sunayi da baki,abin mamaki ya Basu ganin matsiyacin MAKAHO Koh suturar arziki Babu a jikinsa,mace Kamar Sumayya tana rike da hannunsa Koh tantama Babu daga ka gansu kasan ma’aurata ne,Amma kallo D’aya zakama Sumayya kasan ba karamar classic bane 

Bayan an kawo Mana abincin,tura Masa nayi nasa a gabansa shukali na Mika Masa”ungo shukalinka abinci na gaban ka”

Abinci muka faraci a nitse idon mutane na Kan mu sosai har abin ya takurani

Sumayya!!

“Na’am”

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


Nikam wajen nan akwai mutane sosai ne?

“Eh akwai Amma ba sosai ba kasan yanzun dare ne”

Amma dai kallon mu suke koh?

Mamakine ya kamani Amma na maze, “ah ah ba Wanda ke kallon mu kowa harkar gabansa yake,Amma meyasa ka tambaya”

Jikina ya bani ana kallo nane tunda muka shigon nan

“Aiko ba Wanda ke kallon mu”,na basa amsa

Taima ke kike kallona.

“Akan me Zan kalleka Kuma”😒?

Waya sani Koh kyau na Miki,Kinga dogon hanci

“Ina abin yake bare a yabasa”

Abinci muke ci muna Hira har muka Gama Amma dukan mu bamu cinye duka ba,

list aka akawo mana,na duba kudin mu dubu 3,800 ne, bude Purse nayi nabiya kudin, ordern ice cream nayi aka Mana takeaway a laida

Mamakine ya Kama Al’ameen yanzun abincin da sukacin nan shine 3800 ,ai cefenen dubu uku da dari takwas zai musu wata ma suna dafawa.

Suna fitowa a restaurant in ganin titi ba napep yasa Sumayya duba wayar ta

Karfe 10:3 na dare ne,”asaifa mun jima a wajen nan 8 fa Muka bar gida”

Gaskiya Kam Kuma bana majin dirin machine sai mototi

“Ba machine Kam sai dai mu taka da kafa”na basa amsa Ina Kama hannunsa muna tafiya inda Allah ya somu ma tsakanin sintali da mega ba nisa sosai 

“Nikam azumi saura wata nawane”?

Saura sati nawa dai?ya Bata Amsa

“Satitika kenan baikai wata ba?Ashe shiyasa aketa aure aure”

Gaskiya Kam saura sati uku da kwana hudu

Lalle kam,”kasan yanzun haka gobe, za’a yi bud’an kan Amarya da yamma,sai ayi fitan Angonci duka,da dare Kuma dinner,Kuma nice duka Zan musu kwalliya, shiyasa nake son in Allah ya kaimu gobe sai ka nemo mini yaro yaje Mana kasuwa Ina son Gama girki da wure”

Yaro Kuma wani yaro.kike ga Zan iyya aika a unguwan mun nan har kasuwa ,sai dai naje kawai tunda khadija ba lfy.

“Toh Allah ya kaimu,ni chemist ma nakeson mu shiga nasai maganin gajiya,Amma dare yayi”

Ah ah Sumayya da kankantan shikarunki karki Bata shi dashan maganguna, don kina aikin gajiya,in Kika riga Kika saba,toh zai biki Koh yaushe kikaye aiki sai kinsha 

“Gaskiya ne Amma wallahih bayana ya tokare ni sosai,gashi yanzun ma sai tafiya muke da kafa”

Da kafa suka taka har sintali suna tafiya suna Hira,Dayake gidan Adara ba’a rufesa Koh karfe d’ayan dare ne yasa suka samu kofa a bude,

Shigan su, suka shige shashen su bakin su d’auke da sallama

Al’ameen ne ya bude d’akin 

Muna isa ruwa na iba duk yanda nake tsoron toilet in dare yayi Amma zafin da nakeji Bai barni naji tsoron ba,

band’akin na shiga na kwara ruwan na fito,

d’akin na shiga.

Al’ameen na zaune a Kan kujera Yana jiran Sumayya ta fito shima ya shiga Wanka don yaukam ba NEPA an d’auke

“Assalamu alaikum”nace Ina shigowa d’akin

Waalaikumu salam, gaskiya yau Kam Alhamdulillah akwai.zafi Kam

“Gaskiya ni a waje ma zanyi shimfid’a yanzun”

Ok.bara nayi wanka daidai kinyi shimfid’ar?yace Yana fita a d’akin ban d’aki ya shiga bayan ya ibi ruwan shima

Yayan khadija na fita na saka.kayana saboda zafin da ake have vest na saka ,da wandon bacci fankalele shara shara har kasa,kayan shinfid’a na fitar na shinfid’a mana darduma a baranda na shinfid’a zanin gado da filoluka, kwanciya nayi a gefe tsabar gajiya Koh hula ban saka ba,bayana sai damuna yake koh bacci na kasa.

Yana fitowa d’akin ya shiga 3quiter yasa Koh riga baisa ba ya rufe kofar, ya nufi inda yake kyautata zaton agun ta musu shimfid’a

Ina kwance Ina kallonsa harya matso inda nake kwance hannu yasa ya tattaba shimfid’ar sai Kuma ya fara laluben Kan shinfid’ar  bayan ya xauna.

Jin ya tabata yasashe Hawa Kan shinfidar kwanciya yayi a Gefen pillow n da ta d’aura kanta akai

“Bakaji pillow da na aje maka bane”

Naji Mana Amma a naki nakeson kwanciya

“Kaga ka rabu Dani jikina ciwo yake mini”

Hannu kawai naji yasa a bayana Yana mammatsa mini baya,naso hanasa amma Jin yanda message in ke kauda tsamin da bayana yake mini yasa nayi Shuru

Yana ta mamatse Mata baya da kafa duka har yaji tayi bacci, gyara Mata kwanciya yayi,daga kefuwarda tayi shima ya kwanta a Gefen ta bacci ya d’aukesa.

Misalin karfe biyu na dare ya farka Jin iska na kad’awa ga kamshin kasa na tashi bude ido yayi sosai, ya mike zaune hannu yasa ya taba Sumayya Aiko tana kwance Koh juyawa Bata sake ba tun gyarata da yayi, Sumayya!! Sumayya!!

“Ummmm menene”nace cikin magagin bacci don harga Allah yau dai baccin gajiya nake

Ana iska ga hadari,ki tashi mu shiga d’aki

“Da wani idon kaga hadarin ni wallahih ka barni nayi bacci”,na fada Ina gyara kwanciya

Sumayya ruwane fa da gaske

Shuru na Masa abina na koma bacci 

Jin Taki tashi yasa ya mike key ya d’auka ya bude d’akin, d’aukarta yayi a hannu a hankali yake tafiya Yana lalube harya shiga da ita d’akin,Kan gado ya haura ya kwantar da ita,Jin an Soma yayafi da sauri ya fitoh a d’akin shimfid’ar su ya tattara ya Kai d’aki randar robansu ya zubar da ruwan ya hada da bokataye ya jejjera a bakin baranda,daidai lokacin aka fara ruwa sosai Kamar me .

Alwala yayi ya shiga d’akin sallaya ya d’auka ya shimfid’a wa yayi ya Tada kabbara,lafilfilu yake har kusan karfe uku na dare kafun ya kwanta shima a gefenta 

 *Washe gari*

Kamar kullum yaukam da safe kudi na basa yasai Mana manya manyan gongomin Madara da bornviter  na sai suga Rabin kwano Lipton kwali d’aya na had’a da cornflakes,dashi muka karya ya fita

Al’ameen kam yasan baida abinda zaiyi haka ya fita yaje ya zauna a bakin titi ya rasa mafita Allah ya gani Yana iyya bakin kokarinsa wajen niman abinda zai rufawa kansa asiri,Amma abin yaki yasan kome na Allah ne Kuma Bai manta dashi ba a hakan ma yana kara godewa Allah tunda Sumayya nada rufin asiri da ace Bata sana’a a war yanzun da kayan abincin ta ya fara karewa baisan yanda zaiyi ba.

***********

Khadija ce ta shigo bayan sallan azahar lokacin Ina kanwa matan da suka zo make-up, Assalamu alaikum

“Waalaikumu salam” dukan mu muka amsa Mata

“Ah ah khadin Goggo idonki kenan”?nace Ina kallonta sanye take da atamfar dana Bata riga da zani sai gyle da takalmi harda jaka sai laida Mai tambarin asibiti a hannunta sosai tayi kyau fuskarta tayi fayau alamu dai batajin dadi,abinka da farin fata

Wallahih Aunty na fitoh asibitine nace bara dai nashigo yau Goggo takece mini kun shigo da dare Ina bacci.

“Eh wallahih mun shigo da yayanki nace abarki kawai kar a tasheki”

Allah sarki,tace tana gaida matan dake zazaune suna jiran na Gama wa Wanda

 nakema make-up 

“Khadija ki shiga d’aki Mana akwai NEPA ki jona kittle akwai kayan shayi asaman freezer”

Aunty bazan iyya shaba bakina ba dadi Sam shiyasa koh abincin dare ban iyya ciba Haka karyawa ma.

Ah ah khadija dadai kin daure kinsha shayin Daya fi Amma ace bakinki ba Dadi saiki kicin abinci,ai ko magani in ba abinci baya aiki,D’aya daga cikin customers nawa ta fad’a

“Gaskiya ne  khadija,ki shiga in kinsha saiki kwanta ki huta”

Toh Aunty tace tana shiga d’akin, kittle in ta d’auko ta zuba ruwa ta jona,shayi ta hada kad’an ta iyya Sha ta balle maganin Tasha  kwanciya taye  lokaci D’aya bacci ya d’auke ta

Sai kusan 4:30 na Kamala wa sauran kwalliyansu Daman Amarya tun 3 na yamma na Gama Mata saboda bud’an Kai,

Gaskiya yau  na damki rabona mutane kusan goma nama makeup heavy make-up

Simple make-up

Light make-up

Duk yau ba Wanda banyi ba sosai na samu kudi 50k yau na damka nan ma banyi na dinner ba kenan.

Misalin karfe biyar khadija ta mike zata wuce gida Aunty nikam Zan wuce sai gobe 

“Toh khadija Allah ya Kara lafiya ga wannan ki D’an samu abinda kike bukata ki Saya dashi” nace Ina Mika Mata 10k

 Aunty ki barshi kawai d’awainiyar tayi yawa jiyama fa Goggo tace mini kun kawo Mana 5k naje asibiti danaje in ma,Ina saurayin da nace Miki yazo guna?

“Eh na tuna har kikace bazaki fita ba”na Bata Amsa

Ashe Dr ne Ina zuwa na gansa shine ya sayo mini magani  kyauta,

“Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari”

Ameen Aunty

“Wancan yayan kine ya baki wannan Kuma nawane,ki karba khadija kid’an Saya Abubuwan da baki dasu”

Gaskiya Aunty nagode Allah ya saka da alkhari,tasa hannu ta karbi kudin

“Ameen khadija”

Yauwa aunty nace Koh Zaki aje mini tunda Naga azumi ya kusa Inna tashi zuwa kasuwa saina karba naje na sai kaya,samun na samu dinki da wure?

“Ah ah khadija insha Allah, Allah zai Bud’a Mana har yayanki ya sai Miki kayan Sallah, wannan dai ki sai Abubuwan bukata irinsu kananan Kaya da mayuka Turare pad omo sabulu ke dai irin Abubuwan bukatar Yan Mata haka”

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


Toh shikinan Aunty Daman bani da kananan Kaya sai na saya pant biyu Brz sai vest shima biyu Amma na gwanjo Zan Saya aunty sauran chanjen, Ina materials da ake yayi yanzun ana yankawa a dinka dogayen riguna dasu?

“Eh khadija”na gane su 

Yauwa yadi d’aya dari uku su Zan Saya kala biyar na dinka 

“Gaskiya khadija kinye tunani Mai kyau kema saiki samu na chanjawa kwana biyu”

Toh Aunty Zan tafi nagode Allah ya Karo customers

“Ameen khadija yanzun ma wasu na zuwa da dare maganar dinner aike alkhari ce tunda sanadin ki nake samun kudin”

Ah ah Aunty Allah ne ya tsaga da rabonki , shiyasa kike ci

“Hakane Kam khadija” nace Ina shiga kitchen da sauri nake na d’aura Mana abincin da zamuci

Bayan fitar khadija girki na Gama na juye Mana a kula,sai goshin mangari ba yayan Khadija ya dawo

Sumayya sannu da gida?

“Yauwa sannu yayan Khadija sai yanzun”

Eh wallahih ya aiki?

“Lafiya klau” nace Ina kallon sa ganin Kamar a cikin damuwa yake

D’azun Bashir wani makwancin mu ke tambaya ta Wai MATAR sace taji labarin Wai kina lalle ke kikama Asma’u na aure shine Wai yake tambaya ta zata samu lalle gobe,make-up jibi da Rana?

nace ya bari saina tambaye ki inyaso in mun hadu a masallaci anjima na fad’a Masa amsar ki.

“Lallen me za’a ma MATAR tasa”?

Suna ne haihuwa tayi jibi suna

“Gaskiya nifa bazanje home service ba,in mutum nason lalle Koh kwalliya yazo ya same ni a gidana”

Amfa Sumayya haihuwa ne ya za’a yi mace maijego tazo lalle gidanki?

“Wallahih yayan Khadija ni raini ne banaso a rayuwa na kar mutun yaga kaje Masa lalle ya Raina ka” 

Kai Sumayya ba wani raini ai sana’a ce ta kaiki ba maula ba,ki daure kije ki Mata kinji?

“Shikenan Allah ya kaimu goben Amma bansan gidansu ba da yamma ta tura yaro yazo ya kaini”

Sumayya har yamma?ya tambaye ta

“Eh man saina Gama aikina,Koh so kake na tafi da safene,jibine fa sunan”

Toh shikenan Allah ya kaimu yace Yana mikewa ,ruwa ya ibo a boket ya shiga bandaki

Muna idar da sallan mangariba Koh abinci bamu ciba Yan make-up na dinner suka zo su biyar ne dukansu harda Amarya heavy make-up suke so,Dole tasa na hakura dacin nawa zuba Masa nayi na d’auko Masa ruwa a freezer na jira Masa,a d’aki na fitoh waje,don ni bana saka baki a dakina Sam kowa ya zauna a waje kawai

Sai da yaye isha’i kafun ya shigo gidan, gaisawa sukaye da customers nawa,don na fahimci yanzun mutane na ganin kirmansa tunda kofarsa suka shigo

“Abincin ka na d’aki yayan Khadija”nace Masa ganin ya nufi d’akin kar yaje ya zubar da abincin tunda a kasa na jira.

Toh yace Mata Yana shiga d’akin

Make-up na Amarya na fara, Gamawa ta biyani akazo aka d’auketa saura hudun ma duk na Gama musu kafun 9:00,kudin da suka bani 25k Inna hada Dana d’azun kusan dubu saba’in na samu kenan Alhamdulillah yau kawai na tashi da kudi dubu sittin da biyar in aka cire 10k Dana bawa khadija

Wani tunanine ya fado mini akan kudin, murmushi kawai nayi na nufi d’akin

Ina bude labulin idona ya sauka Akan plate inda nasama yayan Khadija abinci nakai dubana garesa da mamaki ganinsa 

     

Al’ameen ne, Sumayya ta gani zaune ya zuba tagumi Koh abincin Bai d’and’ana ba.

Cikin mamaki ta karaso cikin dakin”yayan Khadija lafiya kuwa”? tace tana matsowa kusa dashi  

Firgigit ya dawo hayyacinsa,  Sumayya har kun Gama kwalliyar?

“Eh mun gama,Naga bakaci abincin kaba Allah dai yasa lfy Koh” ta Kara tambayar sa.  

Lafiya Sumayya jiranki nake  in kuka Gama saimuci”ya Bata Amsa

Da mamaki sumayya ke kallonsa”banace kaci ba”? 

Sumayya na kasaci ne, kece Kika nema Kika dafa Taya zanyi na rigaki ci bayan ke kina ta faman aiki.

“Karka Kara fad’amin irin wannan magana daga yau”

Don me?ya tambaye ta

“Saboda duk abinda na baka ni gani nake kamar kaika bani mukeci banason Kara Jin irin maganar nan,Ina zaune itdakai ne badon kome ba sai don Allah,rufin asirin ka nawa ne nawa nakane”ta fada tana kallonsa

Shikenan Sumayya nagode,

“Bana bukatar godiyan ka ka gode Allah”tace tana matsowa kusa da abincin budewa tayi tasa shukali”Bismillah muci”tace tana iba 

Toh yace Yana laluben nasa shukalin

Abinci sukaci Amma cikinsu Babu Mai magana kowa Yana cin abinci ne,bare Hajiya sumy 

Suna Gama cin abincin Al’ameen ne ya tattara Kwanukan yafita dasu waje 

Sumayya Kam wanka ta shiga,tana fita tayi Alwala,kayan bacci tasa ta kwanta 

Al’ameen Jin ta kwanta yasa shima fita wajen ruwa ya Iba yayi wanka.kamar yanda yazamo musu Al’ada wankan dare kafun su kwanta,Yana fitowa ban d’akin kofar shashen su ya rufe,ya shigo d’akin,rufewa yayi a hankali yake takawa Yana laluben gadon harya iso, Hawa gadon yayi ya kwanta a hankali,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 3 HAUSA NOVEL”


Sumayya Kam mamakine ya kamata ganin sa a hakan Sannan yahau gadon ma Bai Saba Mata yanda yake Mata ba, watoh son mannuwa kusa da ita.

A hankali ta mirgina kusa dashi hannu tasa ta Kama NASA hannun”yayan Khadija”

Cikin sanyin halinsan nan ya amsa mata, na’am.

“Menene yake damunka ne Wai” ?

Ba kome Sumayya me Kika gani?ya tambaye ta Yana Mai dagota ya d’aurata a jikinsa gabaki d’aya

“Ba kome, yauwa nace kanada National ID card ne”?

Sai dai voters card bani da National ID card

“Ok shima zaiyi Daman inason na bude account a bank ne kasan banzo da details nawa ba”

Toh shikenan Allah ya kaimu goben saina baki 

“Zaka rakani bank in? Koh naje da kaina”ta fada tana gyara kwanciyar ta akansa 

Duk yanda Kika gani goben ne Zaki bank in Koh yaushe?

“Sai na Gama lallen da akayi booking innan”

Toh shikenan Allah ya kaimu saina rakaki,in khadija taji sauki Kuma sai kuje tare kinsan me?ya tambaye Sumayya

“Ah ah”

Khadija na son zuwa bank Kamar me haka lokacin kudin covid 19 ta dameni Wai sai naje mun bude account muma,mun cika Koh zamu samu kudi,Amma da mukaje bank hanani Shiga sukayi security Wai ba’a bara a banki,Kuma su tsaya su saurare mu sunki Haka suka kuramu waje.

Sosai naji maganar ta tabamin rai”aiko Insha Allah da ita zani taga bank,Amma kaima fa Dole zamuje tare tunda account Kai za’a budewa ba niba.

Toh Allah ya nuna Mana yace Yana zura hannunsa a cikin rigan bacci dake jikinta

Jin hannunsa a riganta unexpected yasa ta zabura sai Kuma ta koma ta kwanta a hankali ta lumshe ido Jin abinda yake Mata da hannunsa a cikin riga”kasan me”?

Ah ah ya Bata Amsa

“Nikam Ina ga Zan Saida laptop Ina da waya”

Akan me Zaki saidasu toh?

“Saboda Banga amfanin suba inba kallo ba me nake dasu shiyasa Zan sayar”tace. Tana taimaka Masa ganin Yana kokarin zare rigar Tata

Umm umm Sumayya waike bazaki ringa d’aukar kwalliya kina sawa a media ba Koh Allah zaisa asamu location naki Kinga ai sai afi saninki sosai a Jala

“Kasan ba kowa keson  asa hotonsa a social media ba shiyasa ban fara posted ba,Nima nayi wannan tunanin”

Eh ai tambayan su zakinayi Zaki d’aura hotonsu kiyi Tallah Amma fa Yan Mata banda matan aure, insun Amince shikinan,tunda wasu da yawa in sunyi kwalliyar ma post suke.

“Gaskiya ne Amma waya fad’a maka ana d’aura kwalliya a online?

Kuma ya akayi kasan ana Post”?Sumayya ta tambaye sa tana kakkama Masa gashin kai Jin wani magic dake bin jikinta a sanadin abinda yake Mata

Uhmmm ai inaji ana Hira koma ni lokacin da na makance ma waya tayi araha a hannun kowa ba,Kamar yanzun

Washhhh toh,uhmm tace tana zillewa daga kansa ta sauka a gefe.

Jin ta zame yasa ya bita shima, tana kwanciya ya kwanta akanta rumfa ya Mata da kirjinsa,ya had’a fuskarsa da Tata fuskar yayi Yana tsintsinar bakinta,dake kamshi 

“Wayyo ka sauka nauye”tace tana mutsu mutsu tana damke damtsen hannunsa

Shagwaba Koh bafa nauyina na d’aura miki ba

“Nidai ka sauka,kawai tsoro nakeji”

Tsoron me?ko ni dodone?ya tambaye ta Yana Mai Kara matsota garesa

“Ka sauka”

Naki,yace Yana Kara Danna kansa akanta

“Nifa bacci nakeji kaji muye bacci”

Nikam banajin bacci

“Nikam ai inaji Koh”?

Sai kiye ai na hanaki ne?

“Amma ai ka tokareni”

Shuru ya Mata yaki kulata sai bidirinsa yake a kanta jifa jifa tana taimaka Masa 

Jin abin NASA ya fara yawa yasa ta fashe Masa da kuka

A tsorace ya mike a kanta sauka yayi gefe cikin tsoro,yake tambayar ta,ke Sumayya menene,Yana tattabata yaji Koh lfy

Saura kad’an dariya ya kubucewa Sumayya Jin yanda duk ya tsorata dagajin kukanta kawai,ta rasa ma wani irin namiji ne Mai shegen tsoro haka

“Toh ba Kaine ba nace maka inajin bacci sai matseni kake”ta fada da muryar kuka tana kallonsa tana Masa gwalo ganin yanda sai zazzare ido yake kamar kace kittt ya ruga

Shine abinda ya saki kuka?

“Eh Mana”

Toh Yi hakuri kwanta toh.

Dariyace ta subuce mata Jin abinda yace Yana kwanciya a gefenta baima mannu kusa da itaba

Cikin mamaki ya Tashi zaune Jin tana dariya, Sumayya Anya lfy kuwa daga kuka saiki koma dariya?

Shuru tayi gudun karya harbo jirginta”babu kawai ji nayi kamar jakulkule ake mini a ciki”

Shuru yayi baice kome ba illah rufe ido da yayi Yana nazarin Rayuwa yau Wai shine da Mata,Ashe haka zama da mace yakeda Dadi duk halinda kake ciki muddin ka samu mace na gari ka Gama samun Jin dadi,duk halinda namiji zai shiga mundin dare yayi zata ga tayi kokarin kauda damuwar tasa Koh Bata cireba,zatayi iyya bakin kokarin ta taga ta d’auke Masa hankali

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 4 HAUSA NOVEL”


Jin yanda Sumayya keta motse yasa shi kiranta, Sumayya!!

“Na’am”ta amsa tana gyara kwanciya

Bakiyi bacci ba?

“Umm banyi ba”

Saboda me?

“Haka kawai”

Jin Amsar da ta basa yasa a hankali ya matso gareta,lumshe ido tayi Jin yanda tsikar jikinta ke tashi,Jin gashin kirjinsa na goguwa da bayan ta

Hannu yasa a hankali ya Kama waist inta d’an zabura tayi kad’an,yasa hannu ya maidata,watoh kukan shugwaba Koh?

“Bawani shugwaba,Kuma ni ba shagwabebbiya bace atoh”

Shugwabebbiyace Mana ai duk lukutaye akwai shagwaba

“Waye lukutar”?ta tambaye sa tana juyowa suka fuskanci juna

Daga Sumayya har Al’ameen wani yanayi sukaji a tare da junan su sosai kusancin su yayi yawa akwance da suken nan

Kece Mana, lukuta kiga nan naki fa Kato,yace Yana Kama Mata bombs,

Hannu tasa ta buge Masa hannu”ai naka yafi nawa girma”

Zare ido yayi Kamar tana ganinsa,ai Dana shiga uku ai,sai wando Mai shape za’ana dinka min.

Hhhhh Sumayya ta Kama dariya “Wai wando Mai shape waya ganka kana tafiya kana murgud’asu a cikin jallabiya”ta karasa maganar da kamo hannunsa dake Kan kirjinta don wallahih kirjin zafi yake Mata 

Shi Karan kansa Al’ameen abin sai da ya basa dariya,Amma yakiye, murmushi kawai yayi,Jin ta Kama Masa hannu kafarsa ya daura Mata akan kafa.

Kokarin mikewa ta fara har lokacin hannunsa na rike a nata Wai don karya taba Mata inda bataso

Jin tana kokarin tashi yasa sa tambayar ta,Ina Zaki Kuma dare fa yayi.

“Rigata nake nema”

Kiye me dashi?

“Me ake da riga”

 Sawa, ya Bata Amsa

“Nima sawan zanyi”

Nikam gaskiya banso kawai mu k’wanta haka.

“Jikinka Koh nawa?wato mu k’wanta haka ka karasani ba”

Sorry zafi yake mikine?

“Eh Mana duk ka mammasa mini jiki”

Amma ai kinji Dadi

“Banjiba”ta basa amsa tana mikewa zaune

Ai da sauri yasa hannu ya rike Tata hannun,yana kwance  Bai tashi ba,kiyi hakuri mu k’wanta haka ba abinda Zan sake Miki.

“Ai kasan bakyau kwana ba Kaya”

Menene a jikinki Koh tsirara kike yanzun?

“Rigan fa”

Ai nace bazan miki kome ba yace Yana jawota jikinsa matseta yayi a hankali ya jawo blanket inda ke Kan kadon ya rufe jikinsu.

***********

Washe gari Kamar kullum bayan Al’ameen ya dawo sallan asuba, sunnah TV Sumayya ta kunna musu daga ita harshi in suna kwance suna sauraron wa’azi.

Sai wajen 7:3pm Sumayya ta mike shara tayi yayan Khadija ya Mata wanke wanke, ruwan zafi ta jona abuta,Yana tafasa ta juye a boker tasawa yayan Khadija nasa, ta shiga ban dakin

 tana fita yayan Khadija ma wanka ya Shiga.

Vayan sun Gama shiryawa kudi ta mika masa 1k”ka sai Mana egg’s guda biyar sai bread na 500 Mai kyau ka hada Mana da butter “

Karban kudin yayi,ya fita.

Bayan ya sayo k’wai da bread, soya k’wai in Sumayya tayi ta hada musu cornflakes ga tie,jira musu tayi a kasan cafet,kamo hannunsa tayi suka zauna a kasa, bubude abincin tayi”karbi shukalinka”

Toh yace Ya karba shukalin ,tattaba plates in yayi Jin plate biyu ne ga bowl d’aya ga cups biyu,wannene abincin nawa Naga Kwanukan da yawa?

Duka zakaci d’ayan soyayyen k’wai ne d’ayan bread ne da butter a jikinsa sai Kuma bowl na cornflakes,sai cups na tie”nace Ina tura Masa plate in k’wai a gabansa”kaci kwai sai kana Had’awa da tie ga bread”

Shikam Al’ameen ya kasa magana Wai karyawane da abinci Kala uku shi Al’ameen,ganin Al’ameen bai fara ci ba ita har tayi Rabin cup na tie inta yasa ta aje kofin,hannu tasa a cikin k’wai in ta yagi babba ta tura Masa a baki

Shikam Jin abinci a bakinsa da Kuma yatsarta sai faman tura Masa take yasa sa cizon yasan kad’an,

Ai Kara ta sake hade da yarfa hannun nata”wayyo yatsana jini jini yake na bunu tace tana duba hannun”.

Da mamaki Al’ameen yace jinii ma Sumayya?

“Eh gashi shikinan ya gusuramin yatsa”

Mu gani

“Bazaka gani ba sai kace idone da kai”

Toh muji.

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 5 HAUSA NOVEL”


Bazakaji ba din,tace tana daukar kofin shayen ta

Jin tayi Shuru yasa sa gutsurar bread Mai butter,Wai zai Bata itama d’ayar hannun nasa yasa ya lalubo fuskarta,Jin fuskar Tata yasa ya fara lalubar bakinta da hannunsa

“Kasan Allah Inka samin hannun hagunka a bakina ba”tace ganin Yana ta tattaba Mata baki da hannun nasa

Kayya abinci Zan baki,yafada Yana Mika Mata gutsuren bread inda ke hannun damansa a baki,

Rufe bakin tayi Taki budewa.

Shikam sai goga Mata bread in yake a lebe gashi duk butter ya Bata Mata fuska

“Kanata Bata mini fuska da butter”tace bayan ta rike hannunsa

Toh ba kinki bude bakin ba sai kokari nake,

Kaga kaci abincin kan, ka barni naci nawa,tace Masa tana goge fuskar ta 

Toh ki bare na baki wanann kawai kinji

Ganin yanda ya nace Mata yasa ta bude bakin Yana saka Mata bread in da sauri ta datse hakorin ta,Wai don ta cije yatsarsa shima abin mamaki da sauri taga ya cire hannunsa kafun ma hakorinta ya Sauka akan yatsar,Yana dariya

Ai Daman nasan saikince Zaki Rama shiyasa Nima nayi taka tsamtsam da yatsana.

Shuru ta Masa Bata tanka masa ba.

Haushi ya shigane bakutuwa?

Kara ta sake tayi kansa “nice bakutuwa”

Jin ta hafto, yasashi Kare kansa, hannu yasa ya tare fuskarsa.

Ganin haka sai abin yayi mugun Bata dariya waishi harga Allah tunani yake wani abin zata Masa haryana tare fuska.

Jin shuru baiji tayi Masa kome ba yasashi fara laluben ta Aiko ya jita a kusa dashi,da sauri ya rikota, sorry kinji

“Ni……shuru tayi Bata karasa ba Jin sallama a kofarsu amsawa tayi ta mike kaci abincin kafun na dawo”

Toh yace Yana saka hannunsa ya d’auki cup inda ta aje masa…

Sumayya tana fita taga wata budurwa irin classic innan zata Kai kusan sa’ar ta kyakkyawace Amma baka Tasha kwalliya tana rataye da school back “sannuki da zuwa”tace Mata tana shimfid’a musu darduma”Bismillah ki zauna”

Yauwa Ina kwana?bakuwar tace tana zama akan sallayar

“Lafiya ykk ya gida”?

Lafiya Alhamdulillah,ya aiki?

Lafiya klau,Ina zuwa Sumayya tace tana mikewa d’akin ta shiga ta hada cornflakes da ruwa  Daya a fijrij ta hada a tire ta kawowa bakuwarBismillalahih ka  abin Kari ba nauye Kam”tace tana ajemata a gaba

La d’awainiyane haka Allah dakin barsa yanzun na fitoh gida zanje school ne ma nace bara na biyu dai ta gidanki

“Allah sarki Amma dai ki saka Koh albarkane yafi dai kikici bazanji Dadi ba”

Shikenan bara dai NASA albarkan tunda kin Masa tace tana iban cornflakes in da shukali uku tayi tace Alhamdulillah

“Badai harkin koshi ba”?

Alhamdulillah wallahih ya isheni,suna na kamila Ina zaune a unguwan gadi,Daman nazone wajen ki in Babu damuwa inason zan fara Training in make-up,Naga wanda kika ma kanwata a auren Asma’u shine nace tamin kwatancen gidanki  inyaso sai nazo inji.

“Toh gaskiya ni bana koyarda make-up saboda bani da shago sai gidana Kinga Kuma Ina da ayyuka yau da gobe”tace Mata tana tunanin ta yarda ne Koh karna yarda

Ba damuwa sister Nima Ina zuwa school Kinga saiki bani time inda zanna zuwa Koh ki ban number ki duk lokacin da kike free sai ki kirani Koh Kika samu Yan make-up.

“Shikenan yanzun dai ki bare Inna ma mijina magaa in ya Amince xakiji daga gareni”

Ok ba damuwa saiki bani contact naki Koh in ba damuwa sannan nawane kudin da Zan biyaki Kinga Inna koma Koh yaushe Kika kirani saina tawo dasu

Toh, make-up dai kashi kashine sanann yanayin kwakwalwar mutum wata a wata D’aya zata koye make-up wata biyu wata fiye da uku ma Bata iyya ba so ni bansan ya yanayin d’aukar kwalliyarki ba Amma dai inso samune wata uku kina koya”

Ok yanzun wata ukun nawa ne kudina

“50k Koh wani wata kudinki na wata uku 150k kenan”

Wai habba sister kudin nan yayi yawa Mana dubu dari da hamsin,

Gaskiya kenan Kinga a cikin kudin Zan Saya make-up kit sabo duka,saboda bazaiyu Ina baki na aikina kina koya dashi ba, sanan infa kika iyya a kwana uku Zaki iyya samun sama da kudinda Kika biya na koyo”

Hakane Kam Amma dai ki duba ki rage mini kinsan baban mu yace in zaiyu nida kanwata zai biyawa.

“Shikenan Zan rage dubu goma”

ok shikenan an gode saina jiki

Shikenan bara na baki number,daidai lokacin Al’ameen ya fito d’akin hannunsa rike da cup inda yasha shaye

What?? wa nake ganin nan Kamar  Muhammad Al’ameen Yusuf bakuwar tace tana zare ido

A matukar razane har bakin sa na rawa yace kamilaaaaa…

Kamila kice Koh dai Mai irin muryar tane, Al’ameen yace cikin d’unbin mamaki

Ikon Allah Ashe da rabon za’a sake ganin juna Muhammad,kamila tace tana me Kara kallon Al’ameen

Wallahih fa kamila yace Yana isowa kusa dasu sumayyar

Oh duniya Muhammad Daman a unguwan nan kake?

Anan nake kamila,ya bayan rabuwa ya maigidan ki da yara?

Jiki a sanyaye kamila tace,hmm muhammad mijikam aure ya kare, yara Kuma Allah Bai kawo ba tukum.

Allah ya kawo masu albarka

Ameen Muhammad,Amma nayi mamaki wallahih wannan ce matar ka,ta fad’a jikinta na Kara sanyi tunawa da abinda ya faru a shikarun baya da suka wuce

Eh kamila matatace sunanta Sumayya

Masha Allah gaskiya matakam tabar kalla Masha Allah wallahih gata kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa,tace tana kallon Sumayya har lokacin

Haka Allah yake abinsa sai ya baka abinda baka taba tunani Koh tsammani ba, shiyasa duk abinda bawa ya samu a rayuwa rabonsa ne ba Mai hanasa muddin Allah ya basa

Gaskiya ne muhammad,Aiko shikenan Daman kwalliya nazo tambaya Allah dai yasa madam in zaka barta ta koya mini,tace tana Mai Al’ajabin Rayuwa

su kamila kenan yaushe Kika dawo Jala ne?

Shap aini na jima a Jala, Amma Dad nawa transfer mun dawo nan

Allah sarki toh ya gidan naku da aiki?

Gida Alhamdulillah aiki Kam Babu sai karatu.

Karatu Kuma,kamila?

Eh Mana ai kasan bayan rabuwar mu aure nayi sai karatun ya tsaya sai yanzun na samu na Shiga TSU 

Gaskiya ne Allah ya bada sa’a..

Ameen, muhammad Kai ya lbrn karatun?

Kai kamila wani karatu Kuma makaho talaka zaiyi ba kudi ba ido ya fad’a Mata maganar cikin murmushi

Sosai taji wani abu ya Tukare Mata makoshi Jin kalaman da ya fad’a ya tuna Mata da kuskuren da ta tafka a rayuwar ta tabbas Al’ameen Mai hakuri ne da wanine haduwarsu yanzun bazai ma saurare taba

Cikin sanyin jiki tace,toh nikam Zan tafi Sumayya saina jiki Koh,ta fad’a tana kallon Sumayya dake zaune a Kan darduma

Sumayya Kam ba karamin haushi taji ba Kamar ta tashi ta Basu waje, Amma saita maze gudun karta bada kanta agun kamila,”yauwa”kawai tace tana kallon kamila dake Shirin fita a kofar

Sumayya! Al’ameen ya Kira sunan ta

Kin amsawa tayi Tamar kunnen uwar shegu

Sumayya Koh kin tashi a wajen ne?

Nan ma Sumayya kin amsa Masa tayi.

D’aki ya shiga a zatonsa ta koma d’akin ne Amma ya Gama laluben ta bai jita ba

Sumayya Kam na zaune duk haushi ya Gama kasheta Jin yanda Al’ameen ke wani sake baki Yana Hira da Yar banzar bazawaran (Kai Sumayya harda zagi)

Ji kawai tayi Al’ameen ya rungume ta a zaune da take

“Menene”tace tana zame jikinta a nasa

“Me yasa kika ki amsa mini bayan kinji Ina kiranki,yace Yana Kara lafewa a bayanta

“Oho Kuma ka sakeni”

Meye Kuma nayi Miki haka hajiya

“Bansani ba nika sakeni nace maka”

Habba bakutuwa

“Ka sakeni fa”

Green sum……

Sumayya Bata bari ya karasa ba kawai ta dasa Masa hakoranta a hannunsa D’aya zagayo dashi Kan kirjinta

Washhhh Allah na yatsata,yace Yana yarfa yatsar don harga Allah da gaske Sumayya ta cijesa,ni Kika ciza?

“Eh din kuma,ka sakeni nikam”

Wai menene Kam?

“Bansani ba”

Karki sani Kuma kamila zata fara zuwa make-up gobe nace Mata na, Amince kamar yanda Kika Bata umurni,yace ya na son gane dalilin fushin nata Koh saboda kamilane, don shidai lfy suka rabu kafun ta fitoh waje

“Bazan Yi ba ai ba’a dole karta kuskura tazo mini gida don kurinta zanyi”

Kishi kike da ita?

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 6 HAUSA NOVEL”


“Akan me zanyi kishi da ita kuma” samayya tace tana Jin bugun zuciyarta na karuwa

Akan mijinki,Mana

“Ina mijin yake”

Au bakisan inda yake ba?

“Eh ban sani ba saika sanar dani”

Jin abinda Sumayya tace yasa Al’ameen zabura da karfi ya fizgota jikinsa ya juyarda ita suna fuskantar juna,kikace in sanar dake Ina mijin yake? Sumayya ni kike fadawa wannan magana saboda Ina miskini Kuma kina ciyar dani,ya fada ransa a matukar bace

Sosai Sumayya ta razana harga Allah batasan maganar ta fita ba Sam ita Karan kanta bazatace ga abinda ya harzukata ba yanzun yanzun nan

Tambayar ki nake Sumayya saboda kina ciyardani? Koh saboda bana gani shine kike wulakantamin aure?

Sosai ta Shiga rud’ani Bata d’auka Al’ameen da ta sani yanada irin wannan fuskar ba”Kayi hakuri”tace tana zame damtsen ta a hannunsa D’aya damke

Kala baice ba mikewa kawai yayi ya d’auke sandarsa da ciny’ayyen takalmin sa yafita

Bayan fitar Al’ameen sosai Sumayya ta Shiga Dana sani,tabbas magana zarar budu inta fitoh Bata komawa,da tasan haka zai Bata Masa Rai da Bata fara ba

Mikewa tayi ta Shiga d’aki ta kwanta sosai zuciyarta ke Mata zafi 

Bangaren Al’ameen Kam bayan fitarsa gida Tashan kayan marmari ya nufa, duk yanda yaso ya samu bashin Kaya abin ya gagara haka yayita yawo Amma shuru Bai samu kome ba ,tabbas irin wannan yake gudu Sam bayason mace  ace ita ke ciyar da miji,Sam maganar Sumayya Ada Baya Masa ciwo Amma yanzun yaji wani irin ciwo akan maganar sosai,sanann ya Mata hakan ne don ta kiyaye gaba in zata Masa magana ta ringa taunawa,ya fahimci kishine kawai ke d’awainiya da ita 

Jin ana Kiran azahar yasa Sumayya mikewa sallah tayi ta d’aura shinkafa da wake,zubawa tayi a flasks don itakam Sam bazata iyyacin kome ba yanda take Jin tsananin damuwan nan,gashi batasan Ina Al’ameen ya Shiga ba,har yanzun Bai dawo ba 

Har yamma Al’ameen shuru Bai dawo ba duk inda hankali Sumayya yake ya Tashi sosai ta Shiga damuwa matar Bashir data ma alkawarin lalle day uku tana Aiko yaro karshe ma Sumayya tace yaron yace Mata bazata samu zuwa ba

“ya Allah ka dawo mini dashi lfy”tace tana zabga tagumi

Sai bayan Isha’i Daya idar da Sallah Aljuhunsa ba kome yanda ya fita haka ya dawo Koh abinci Bai Karaci ba bayan na karyawa,da sallama ya shigo d’aki

Sumayya dake cikin dogon tunani tana zaune akan sallaya Koh hijab Bata cireba , da sauri ta amsa”waalaikumu salam yayan khadija lfy kuwa baka dawo ba sai yanzun”tace tana isowa garesa

Uhmm sai yanzun, kawai yace Mata Yana k’wabe rigansa,jallabiya ya d’auko a cikin kayansa ya fitoh waje Bai Kara Mata magana ba

Baki a sake Sumayya ta Bisa da kallon mamaki harya fita,ta koma ta zube a jikin kujera hawaye na cika Mata ido,ta Shiga uku sauran hope natan Daya saura shine shima yake kokarin juya Mata baya Wai meke faruwa da itane me yasa duk Wanda zai sota daga baya sai ya kaurace Mata,kuka kawai ta sake “nikam na Shiga uku”tace tana cigaba da kukanta, Al’ameen Bai taba fushi da itaba sai yau menene Bata Masa ba Abaya Bai taba fushi ba sai yau daya ga kamila.

Al’ameen Kam wanka ya Shiga Yana fita yaji muryar Sumayya kasa kasa tana kuka da sauri ya aje kayanda ya cire,Wanda yaso wankewa Amma baida omo.

D’akin ya shiga Amma saiya maze ya kwanta akan kujera Bai kulata ba 

Sumayya Kam Jin yanda Koh damuwa baiyi da kukan da yaji take ba yasa a hankali cikin muryar kuka tace”yayan khadija ga abincin ka”ta fada tana mikewa ta dauko a saman freezer

Na gode Amma bazanci ba yace, ba tare da ya Koh motsa a inda yake ba

Kuka kawai Sumayya ta sake kamar ana yankata”nikam na shiga uku tunfa safe banci kome ba bayan karyawa saboda Ina jiranka ka dawo Amma shine ka dawo kace bazaka ci ba”

Na hanaki cine ai ban hanaki ba kici Mana ni indai nace bazanci ba

“Wayyo Allah na ni Sumayya Yaya zanyi da Raina ne”

Da na Miki me?

“Kaci abincin toh kaji”

Ah ah naci ai 

“Waya baka kudi ka saya”

Ai Ina da sana’a Koh?

“Nidai don Allah Kayi hakuri kaci kaji”

A matsayina nawa Kika damu da sai naci abincin ki?ya tambaye ta

“A matsayinka na”……

Sai Kuma tayi shuru tana kallonsa

Uhmm ,kawai yace Yana lumshe idanunsa so yake ya kitsema wannan baiwar Allah Koh Amafarkine Yana son kallonta, tunda ya makance Bai tanajin yanason kallo ba irin haduwarsa da Sumayya sosai yakeson ganinta da idanunsa 

“Wa…..i mi…jin..a..”tace cikin eeii eiiina

Waine ma kenan?

“Mi..ji…na”

Sumayya!ya Kira sunanta

“Na’am”

Meya Bata Miki Rai d’azun?

“Babu”

Akwai Kam?

“Babu”tace hawaye nabin kumatunta

Nine Koh kamila?ya Kara tambayarta

“Koh D’aya”

Ki fadamin gaskiya wannan shine kad’ai zaisa na hakuri.

“Kaine”

Me nayi Miki har zakina fad’amin magana irin Wannan

“Toh ba Kaine ba”

Nine me?

Kaketa Mata dariya harda wani…..sai kuma tayi shuru Jin subutar baki da tayi

Shikam murmushi ne ya subuce Masa hade da wani irin farin ciki tunda Sumayya na kishinsa,Kuma duk inda akwai kishi akwai alamun so,

sai Kuma akace ki gaggaya min magana?

“Kaye hakuri don Allah”tace tana mikewa a hankali ta matso garesa fadawa tayi kansa da karfi ta sake kuka

Rumtsa idanunsa yayi Jin saukan hawayen ta a kirjinsa tamkar ruwan guduma haka yajisu, Sumayya!ya Kira sunan ta Yana Mai Kara matseta a jikinsa

“Na’am”ta amsa Masa hade da cusa kanta a kirjinsa ji take Kamar numfashin ta zai d’auke

Sumayya na hakura Amma karki sake mini Wasa da aure kinji banaso.

“Wallahih bazan sake ba”

Allah yasa,yace Yana shafa rigan jikinta

Sumayya wannan ba kayanda kikasa da safe ba?

“Shine” Ta basa Amsa

Miya hanaki wanka? sai tsami kike ma,ya fada hade da shafa Mata baya

“Damuwa ne ya hanani,Kuma ni bana tsami”

Bagashi  ba sai tsami kike, yace Yan sunsunar wuyanta,dake tsananin kamshin Turaren ta

“Zakaci abincin na baka”?ta tambaye sa cikin damuwa

A koshe nake ki bare sai da safe sai naci.

“Nidai ban yarda ba wallahih Koh kaci saikaci nawa”

Toh zanci,kije kiye wanka ki wanke tsami kisa Kaya 

“Bayan na Gama sai muyi me”?

Saina karbi hakkina,ya Bata Amsa shima

“Niii….. niii.. Babu ruwana,abinci nake nufi”

Ai kema abinci ne,ya Bata Amsa

“Wacece kamila”?

Uhmmm abinda ya hanaki sukuni kenan?

“Nidai ka fad’amin kawai malam”

Toh malama bakutuwa kije kiyi wanka sai kizo kici abinci sai mu k’wanta da safe saina fad’a miki,.

“Har gobe kuma”tace tana hada fuska

Eh na gaji bacci nakeji yanzun yace Yana cire Mata riga

“Bacci Kuma kake kwabeni”?

wanka zakiy i,ya Bata Amsa hade da karasa cire Mata rigan

 

Wanka Sumayya ta Shiga tana fitowa lokacin karfe 8:00 dai dai, shiga d’akin tayi Kaya tasa,tana Gamawa ta jawo abincin “yayan khadija muci abinci”

Sumayya kici nikam na koshi saiki  dumamin da safe.

“Ni wallahih ban yarda ba,toh bakace ka hakura ba Koh baka hakuran bane” tace tana hawaye

Tabbas ko yaki Koh yaso Sumayya ce rufin asirin sa inba itaba bashida wajen da zaici abinci tunda ba kudi Koh sana’a bane dashi,sauka yayi ya matso Yana lalube ya zauna shukali Sumayya ta Mika masa,ya karba suka faracin abincin

Koh minutes uku basuyi ba sukaji sallaman yaro a kofarsu,

“Kai wallahih nifa na gaji habba matan nan bazata samu lallen nan ba”

Wace Mata Sumayya kardai kice min matar Bashir baki je kin Mata lallen ba?da mamaki yake tambayar ta

“Nikam banje ba”

Saboda me?

“Saboda baka dawo ba,Kuma ni yanzun dare yayi”

Amma sumy gobe nefa sunan Kuma baki je kin Mata ba,sannan yanzun Kuma kice kin fasa,baxataji d’adi ba in Kama mutum Alkawari Yana da kyau ka cika Kinga na riga nace wa Bashir zakizo kima matar sa lalle bazaiji Dadi ba in Kika ke zuwa Kuma gobe suna.

Hakane kam, Sumayya tace tana fitowa waje

Ina wuni Aunty?yaron ke gaida Sumayya

“Lafiya ya mamarka”?

Lafiya aunty Wai inji mamana inzo in fada Miki Wai don Allah kiye hakuri kizo ki Mata lalle ta nemi me lalle Bata samu ba

Toh shikenan bara na d’auko hijabina, Sumayya tace tana shiga d’akin

“Yayan khadija zanje lallen saina dawo ga abincin ka karasa ci”tace tana d’aukar hijab nata da jakan lalle   purse ta bude 50k ta d’auka,zata fita a d’akin

Toh baki karasa cin abincin ba?

“Ah Ah Alhamdulillah kaci kaikam nikam sai nadawo”

Sumayya muje na rakaki kinji?yace Yana mikewa

“Ah ah ga yaro zamu tafi tare,sai dai kazo ka d’auke ni anjima”

Kamar karfe nawa?

“Kana da agogone”?

Oho,nikam ki fad’amin.

“Yanzun 8:12 zuwa 10:00 sai kazo ka d’auke ni”

Toh shikenan yace Yana zama,d’aukar abincin yayi ya cigaba da ci

Sumayya Kam fita tayi da yaron,sai da sukazo kusa da titin first bank taga shagunan a bude kamar Rana ga wuta ako ina,”tsaya Kai mu Shiga shagon nan”  tace ma yaron tana Kama hannunsa suka tsallaka titi,shagon ta shiga”excuse me”tace ganin Mai shagon inyamurine

Yes ma barka da zuwa shigo ciki customer ki duba Kaya

Da mamaki sumayya ke kallonsa Ashe ya iyya hausa,yauwa “sannunka,Kaya nake so”

Ok wani iri?

“Jallabiyoyi”

Ok ki shigo gasunan kizo ki zaba Wanda ya miki,yace Yana zazzaro Mata jallabiyoyi sunfi kala goma

Guda uku sumayyaa ta zaba masu masifan kyau fari da baki Mai maiko sosai da hula sai Kuma Mai aiki ruwan sararen samaniya,takalmi ta sai Masa Mai kyau na tambarin Adidas silifas ne,sai t-shirt da 3quiter sai Jean’s,sosai Sumayya Tama Al’ameen sayayya harda Turare na maza ta sai Masa da abin haske Kai da gemu,sai kusan 9:26 suka je gidan Matan da zatama lalle 

Lalle Sumayya ta Mata baki da ja, Al’ameen tun 10 yazo Amma Basu Gama ba,ya zauna Yana jiranta a kofar gidan

Suna Gama lallen Sumayya ta karbi kudinta laidan da ta aje a kulle a gefe na kayan da ta saima Al’ameen ta saba,waje ta nufa

Tana fita taga yayan khadija a zaune

“Yayan khadija mu tafi Koh”tace Masa

Kun gama?

“Eh mun Gama”

Ok yace Yana mikewa tafiya suke shuru,can dai Al’ameen ya kasa hakuri Jin yanda yakejin motsen laida a hannun Sumayya

Sumayya nikam laidan menene a hannunki Kato haka don nasan dai laida kananu basa Kara haka?

“Abu na saya”ta basa amsa

Kala baice ba suka cigaba da tafiya har suka Isa gida,Dayake sunyi wanka dazun yasa Kaya kawai suka chanja 

Yauma kwanciya sukayi tare bayan Al’ameen ya Gama kwsan rabonsa

Washe gari da safe bayan Al’ameen ya tafi masallaci, Ghana must go nasa ta bude Daman jiya ta kirga kayan jallabiya ukune sai wando da riga D’aya sai 3quiter D’aya sai armless D’aya sai gajeren wando biyu vest D’aya, kwasosu tayi ta juye a basket na dattin kayanta,sabbin kayanda ta suyo jiya ta mayar cikin bakkon ta shirye Kamar yanda kayan suke a kirge sauran Kuma ta aje sai Randa ya wanke kayansa biyu masu dattin saita musanya Masa,

 Vaseline insa da ya kusa karewa ta juye a laida daukar manda ta siyo Masa tayi ta diga a cikin gongomin kamar yanda baseline insa yake, Haka ma tamasa da sabulu

Sai 6:30 Al’ameen ya shigo gidan

Sumayya Kam ganin ya shigo d’akin da sauri ta d’auki takalmin sa ciny’ayyen ta saka Masa sabo,ta dawo d’akin,kudi  ta basa 2k yasai musu dankalin turawa boket D’aya sai k’wai guda biyar,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 7 HAUSA NOVEL”


Fita yayi a d’akin bayan ya karbi kudin yazo ya zura takalminsa,sai Kuma ya cire da sauri,ya ringa laluben bakin dakalin Amma wayam baiji takalminsa ba

Sumayya!!ya k’wala Mata Kira

“Na’am”Sumayya ta amsa tana fita a d’akin itama

Sumayya Banga takalmina ba pls ki duba mini Mana?

“Ba gashinan a gefenka ba” tace tana kallonsa

Wannan ba nawa bane

“Nawa kenan?kadaisan banda takalmi irin wannan soson”?

Amma ni sai inaji Kamar ba nawa bane,nawa fa da laushi sosai ya kode

“Toh wannan in fa”,ta tambaye sa tana mamakin fahimta irin nasa

Kamar sabo sabo,

“Hhhh lalle zaka tafi da kafa kenan tunda dai ga takalminka kace Wai ba naka ba”

Sumayya bafa Wasa nake ba Wannan ba takalmina bane 

“Nidai naka na gani atoh”tace tana komawa d’akin

Al’ameen Kam ba yanda ya iya Haka ya saka takalmin Amma har ransa yanaji ba nasa bane.

Bayan fitar Al’ameen Sumayya aikace aikacen ta na gida ta Gama ta d’aura ruwan zafi a kittle.

Al’ameen Kam bakin kasuwa  yaje ya musu sayaya ya kamo hanyar gida

Bayan Al’ameen ya dawo Sumayya ta soya dankali da k’wai sai ta hada musu tie, rufewa tayi ganin Al’ameen ya Shiga wanka

Al’ameen aban d’aki mamakine ya kamasa Jin sabulunsa na kamshi ,Amma baiyi magana ba bayan ya fitoh, d’aki ya Shiga a hankali ya bude bakkon sa jallabiya D’aya ya zare a ciki ya zaro gajeren wando da vest.

Sumayya na zaune akan kujeran tana kallonsa saka wando yayi da vest sai Kuma taga ya tsaya Yana tattaba vest in,Amma baiyi magana ba ya d’auki jallabiyar yasa,sai Kuma ya juye kayan bakkon duka a cafet Yana tattabasu.

 Sumayya!ya kirata

“Na’am”tace tana kallonsa

Sumayya wa’innan ba Kayana bane?

“Akan me zakace haka”

Sumayya wa’innan Sabine kijifa kayan kamshin sabbin Kaya suke bama Turare ba kiji da karfi fa kayan ba masu laushi irin nawa  bane?

“Nidai naka na gani”

Sumayya me Kika sayo jiya da naji laida na kayo kayo a hannunki?

“Ina ruwanka”ta basa Amsa

Indai baki fad’amin gaskiya ba toh bazan fad’a Miki wacece kamila, menene hadin mu da ita ba

Tabe fuska Sumayya tayi “Gaskiya n…………….

Back to top button