Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 19 Complete Hausa

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                               NINETEEN📍

      Ba karamin shock mama tashiga ba jin wani abu  banbarakwai namiji da suna hajara, abu daya tasani alhaji ko giyar wake yasha baze aureta ba mussamman yanda dansa mafi soyuwa ya mutu akanta, cike da gwarin gwiwa tace;

     “Ke karamar yar’iska bani da lokacinki! Ke ingaya miki dagani alhaji ya rufe kofa wallahi, in banda rashin kunya da rashin tarbiyya ina mutum ina tinanin auren uban saurayinsa”……..

Zama tayi akan 3 sitter tana dora kafa daya kan daya fuskarta dauke da dariyar rainin hankali tace;

        “In banda abinki hafsah ya kamata kisan abun kunya gaba na basa ba baya! Rashin tarbiyya ko da ita aka haifeni, ke in takaice miki nina tarbiyyantar da kaina kinga ko tarbiyya zero!”….. 

Saita fashe da dariya tana fadin;

      “Wallahi harna hango yanda salon kishinmu ze kasance, bari kijima mungama magana da mijinki a part dinnan zan zauna yanda abin namu zefi tafiya daidai!”….. 

Wani irin zuciya ne ya dibi mama dukda bata yarda da abinda tace ba, ta daga hannu da niyar kaiwa fatima zainab mari taji anyi saurin tare hannun an kuma ki sakin hannun, juyawa tayi a fusace sukayi ido hudu da daddy…. Sake hannu mama yayi da sauri jin fatima zainab ta fashe da wani mugun kuka, ya juyo da sauri yace;

       “Why’re you crying? Fadamin meta miki?”….

Kin magana tayi ta cigaba da kukanta kamar gaske…

Cikin rarrashi daddy yace; 

        “Talk to me dear, meta miki in rama miki!”….

          “Alhaji yanzu a gabana kake cewa wannan shaidaniyar dear?”…..

Be kulata jin fatima zainab na gunguni irin na wanda yasha kuka ya koshi alamun magana take sonyi…

       “Gaisheta fa nazoyi shine take ta zagina tana marina, harda cemin iyayena sunyi asarar haihuwata , wai ka taba fadamata ni shegiya ce banda uba!”……

 Ta fada tana fashewa da wani sabon kukan irin abun na tabata dinnan……

           “Wlh alhaji…..”

Bata karasa ba taji saukar lafiyayyen mari a kuncinta wanda bata tantama daddy ne ya mata,sannan cikin bacin rai yace;

        “Makircinki har ya kai kimin sharri hafsa Yaushe mukayi wannan zance da ke?”……

Cikin kokarin kare kai dukda marin ya shigeta sosai tace;

        “Alhaji wallahi yarinyar nan ce munafuka, harfa cemin tayi aurenta zakayi saboda tsabar abun kunya?”…..

        “Ni nasan bazata miki karya ba, nasan duk abinda ta fada kin fada din ne tinda halinki ne, Toh sai me inna aureta? Inma hada abinki kikayi dan nasan zaki iya toh bari in tabbatar miki aurenmu nida fatima zainab nan da sati daya, kuma a part dinnan ta zabi ku zauna tare”……

Wani kukan kura mama tayi ta chakumo wuyar alhaji, cikin fitar hayyaci tace;

      “Wallahi baka isa ba! Kayi kadan kamin kishiya da sa’ar ya’yana, ko zanyi yawo tsirara aurennan baze yiwu ba wallahi!”…..

Fincike hannunta daddy yayi yana hankadata kan kujera yace;

        “Ashe ko zakiyi yawo tsirara, dan ko khaleel be isa yasa in dakatar da aurennan ba!”…..

Dariya ce takecin fatima zainab sosai tadai daure ta cigaba da kukan munafurci zuciyarta cike da mamakin yanda daddy ya karbi auren hannu bibbiyu, anya kuwa? anya ba wata a kasa? Kai koma menene bazata hakura ba sai tafitar da mama daga gidan…… Tana cikin wannan tinani tajuyo muryar mama na iwun:

       “Wallahi bazata saku ba, duk wahalar danasha kafin na shawo kanka bazata tafi a banza ba wallahi, kasan ko nawa na kashe? Kai wallahi yau saidai ka zaba ko ni ko wannan tsinannan auren cin amanar da kuke shirin yi!”….

         “Au gurin mallamai dama kike kaini, yasa bana gane kaina wataran”?

       “Kwarai kuma ba abinda ka isa kayi dan na gama dakai, sai yanda nayi da kai, saboda haka ka janye aurennan kona bar maka gida!”….

        “Allah ya toni asirinki muguwa azzaluma, wannan auren kuma ba fashi, saiki tattara yanaki yanaki ki barmin gida, na tsinke igiya dayan daya rage a tsakaninmu, kije na sakeki! Na baki minti uku ki kwashi tarkacenki ki barmin gida, karki sake ki tafimin da ya’ya kuma”….

Wani mahaukacin ihu mama ta rusa da hatta megadi dake chan bakin gate saida ya jiyota,jin abun tayi kamar saukar aradu, ko a mafarki bata taba kawowa zasu kara rabuwa da daddy ba musamman yanda take tinanin aikin da mallaminta ya mata na cin shi sosai, a haukarta kuma in kayiwa mutum asiri zaka iya fadamasa tinda kariga ka gama dashi, sai gashi alhaji ya tsinke igiya dayan da take takama dashi abu kamar almara? ganin fa wankin hula na neman kaita dare yasata tsugunawa tana fadin;

       “Dan Allah dan Annabi alhaji ka fadamin mafarki nake baka sakeni ba, inka rabu dani ina zan nufa”…..

A hassale yace;

       “Ki nufa duk inda kikaso mana, in bakiji sosai ba bari in kara maimaita miki, na sakeki saki uku hafsah!!!”…

Sai ganin mama kawai sukayi a sume tsabar gigicewar datayi, sai a lokacin su husnah dake labe sunata kuka sukayo kanta da sauri suna jijjigata…..

Fatima zainab ko ganin ankashe boss yasata zamewa sadap sadap ta gudu daga part din, tabar gidan gabadaya, a ranta tana fadin ko banza kwalliya ta biya kudin sabulu, ko a iya haka aka tsaya anbiyata….

 Convoy din wasu zafaffan Louis Vuitton ne suka sharo a guje, duk inda sukabi sai an kallesu saboda kana gani kasan ba karamin mutum bane a ciki, basu tsaya a ko ina ba sai a unguwar Asokoro dayake cikin garin abuja, a gaban wani hadadden mansion sukayi parking suka shiga yin horn… Sun jima suna horn kafin wani security ya fito ya tambayesu visiting or appointment letter dinsu dame gidan, dukda yasan ba kananan mutane bane saidai doka ce me karfi baa shiga gidan without permission!, wani bodyguard ne yayiwa security din bayanin wanda yazo ganin me gidan, ce mishi yayi ya danyi holding on yana zuwa…

Juyawa yayi ya koma ciki, landline din daze sadasa da me gidan directly in tana kusa ya kira, saida yayi ringing sau uku sannan aka dauka, bayani ya mata tace ‘ok a barsu su shigo’…… 

Bude musu gate akayi suka shiga, duk yawan motocinsu saida parking space din ya daukesu harda sauran space banda tarin motocin dake jibge a gidan…. 

Dakatar da bodyguards dinsa yayi daya daga cikin securities din gidan yayi leading dinsa to guest part…

Yana zama wata maid tazo ta cika gabansa da kayan ciye ciye, dan haka tsarin gidan yake indai akwai bako ko baki a guest part zaayi cika gaban mutum da abubuwa, haka aka kai bodyguards dinsa garden suma aka cikasu da kayan ciyeciye, suka bararraje sunaci suna hirarsu abunsu….. 

Tinda aka kai Dad part guest part din mami yake bin parlourn da kallo yana mamakin yaushe ta bunkasa haka?, ashe dole rashin mutunci ya karu tinda tana cikin daula haka? Bawai befi karfin duk abinda yake parlourn bane saidai betaba expecting ze ganta a cikin mansion haka ba, address din gidanma saida yasha wahala kafin ya samu tsabar yanda ake tsare komai nata, wai a hakama dan shima wani ne…. 

Anfi minti talatin sannan ya hangota tana tafe cikin takunta me birgewa da gayunnan nata daya santa dashi haryanzu yananan, shi sai yaga kamar ma yarinta ta kara dan bazaka kalleta kace tanada da’ kamar Deen ba, dama familynsu haka suke sunada diri da kyan jiki,….

Tana karasowa yayi saurin dauke kansa jin wata tsanarta data sauko masa…..

Itama tana ganinshi tayi kicin kicin da fuska tana gyara zaman glasses din dake idonta tace;

        “Who gave you the permission to enter my house? How dare you!!”…. 

Haderai yayi shima sosai yace;

       “Bana bukatar wani permission din shigowa wannan cage din naki da befi a saka kaji aciki ba!”….

          “Get out of my house now! Or I sue you for bulging into my space without my permission!”..

 Dariya yayi sosai dan bayajin ze biyemata yau, dan yanada dalili me karfi daya kawoshi….. 

               “Relax Justice Fatima, niba wannan shirmen bane ya kawoni, nazo muyi magana akan Deen ne, I can’t see my only son stranded for the crime he hasn’t committed, ni nasan bashi yayi kisan ba”……

         “Wannan kuma chan ta matse maka mallam! Who tell you you’re invited? Ba kace ba ruwanka ba? Muje chan mu karata, toh yanzu ma ba ruwanka!”..

       “Kema fa kinsan I don’t mean that, tayaya zan zuba ido abu ya samu beloved son dina?”….

        “Son din dana lalata maka tarbiyarsa ne ya zama beloved? Ko kunya bakaji?”…..

         “Enough of all this Justice Fatima, ki nutsu muyi abunda ya kamata kinga Deen is in danger, and there’s something I want to tell you nasan ze kara baki highlight akan binciken da kikeyi”….

          “Kayi kadan ka bani information din dazanyi amfani dashi wallahi mallam, so kake kacemin kaine kayi kidnapping dinsa in the first place? To koma bakai bane ka saurari yanda bincike ze hau kanka, so hold your information to yourself, idan nasa aka kama min kai ze maka amfani gurin bayani, now out!!!”…..

           “Wai ke meyake damun foolish brain dinki ne da bazaki tsaya ki saurari abinda ake fada miki ba? Me kike takama dashi ne? Nawane net worth din naki duka? Da har kike tinanin zaki iya cin galaba akaina da matsayinki a kotu?”…..

Batace komai ba ta danna wani abu, in a blink of an eye securities guda ashirin suka zagaye dad kowannensu dauke da bindigu a hannu, kana kallonsu kuma kasan ba karamin karfi sukeji dashi ba……

    “Before I count five leave this parlor or they get you out! 1……. 2…… 3……..”

Dad ya fita da sauri badan baze iya tsayawa yaga abinda zasuyi ba tinda shima yana tafe da nasa bodyguards din, yasan kuma ba karamin hargitsa gidan zasuyi ba, sai a kashe wani garin haka ma, saidan sulhu yake nema a gurinta, so yake su hada hannu akan case din amma taurin kanta ya hanata ta nitsu suyi magana….

Tsaki taja ta koma main part dinta, working room dinta ta nufa straightly tashiga typing termination letter, saida ta duba cctv taga duka securities din dake bakin gate din a lokacin da dad ya shigo sannan ta saka sunayensu duka a letter din, bayan ta gama tayi printing out ta fito dauke da letter din a hannu..

Karo suka kusayi da Umm daketa nemanta har letter din ya subuce a hannunta, da sauri Umm ta tsuguna ta dauko mata, har zata mika mata sai kuma taga heading din, fasa mika mata tayi ta shiga karanta content din mami na tsaye tana jiranta ta gama ta bata, saida Umm ta gama karantawa tsap sannan tace;

         “Why’re you firing them?”….

         “They let an idiot into my house!”

     “Ikon Allah, waye idiot kuma?”

    “Waye banda so called father din Saifuddeen!”….

Dariya Umm tayi tace;

      “Au shine idiot din, lallai ma mami, to ai nina basu permission din shigo dashi, kinsan muryarmu daya they probably thought kece,kinga wannan firing letter din bari na yageta ni ya kamata a kora basu ba”…….

Harara mami ta aika mata tana fadin;

        “Sunci sa’a wallahi, ke kuma saiki bari mutum ya shigo baki tambayeni ba?”…..

       “Ya zanyi in tambayeki kamar wani wanda bansani bane ze shigo, kudai haryanzu kun kasa dena ga macijinnan naku ko?”….

Bata kulata ba tace;

       “Next time karki sakemin haka pls!”..

      “Yes ma’am, yanzu ya kukayi dashi toh?”…

      ” I sent him away! Tsabar renin hankali wai yazo mu hada hannu akan case din bayan yagama cewa insan yanda zanyi a station”…..

     “Toh Allah ya kyauta, I already have two suspects according to my investigation!”….

      “Wow! weldone barrister, Who are they?”….

      “I’ll let you know tomorrow, there’s something I’m compiling for now”…

      “No issues”….

Driving take a nitse tsabar yanda take cikin nishadi, inta tuna dramar daddy da mama sai taji wani mugun dariya ya kamata, kida ta kunna dan ta kara jin dadin moment din, sai kuma tashiga tinanin yanda zatayi da wannan aure tinda gashi burinta ya cika kafin akai ga yi, yanzu kuma in tace ta fasa daddy ze zargi wani abun, kodai ta bari a daura tace sai ya saketa a ranar?…. Rasa abun kamawa tayi kawai saita banzatar da zancen ta cigaba da nishadinta……. 

Hanyar school ta dauka tana ayyana irin tests din  datayi missing dan ta dade bata shiga school ba, har tabi normal way sai taga mutane sun danyi yawa a hanyar hakan yasan tabi hanyar da baa samun mutane sosai sai jifa jifa…..

Saura kadan suyi karo da wata mota data sharo a guje tayi saurin kaucewa, inda Allah ya taimaketa ba gudu takeyi ba, ganin me motar yayi parking yasata fitowa daga tata motar da sauri da niyar ta zazzagawe meshi balaki dan shine ya biyo one way..

Fitowa wanda ke cikin motar yayi fuskarsa dauke da mask yana nufota gadan gadan…… 

Bata damu da mask din dayasa ba cikin isa tace;

        “Kai wani irin mahaukaci ne da baka kallon gabanka sai kace……”

Bata karasa ba taji numfashinta na sama sama, batasan meya shaka mata ba saiji tayi komai na jikinta ya tsaya chak lokaci daya….. 

Cikin sauri ya turata cikin motar gudin kar wani yazo ya gansa, mutane uku dake bayan motar yama alamu dasu fita su shiga tata motar, fita sukayi da sauri shikuma yaja motar a guje……

Saida yayi tafiyar kusan minti talatin kafin yayi parking a gaban wani mini apartment da suke kira da ‘base’….. 

Daukarta ya kuma ya shiga da ita ciki, be direta a ko ina ba sai a daya daga cikin bedrooms din dake parlour…. 

Kallon kyakkyawar fuskarta me daukan hankali yayi yana fadawa kanshi ‘she’s mine’ kome ze faru dole ya sameta, toh mema ze faru when he have her all to himself now? Ai sai abinda yaga damar yi da ita… Koda baze sameta ba gwara ya dana ya rage zafi ballema yanaji a jikinsa saidai khaleel ya hakura ya bar masa kawai idan yagama da ita…. 

Hand gloves dinta ya cire ya shiga shafa zarazaran yatsunta masu azabar kyau, da palms dinta me laushin gaske, sosai yaji ya fara shiga wani yanayi, wai iya hannu kenan ma? Kokarin cire hijab dinta ya shigayi sai wani tinanin ya fadomasa, ‘shit’ ya fada yana lalubar wayarsa a cikin aljihu…. Yamanta duk wannan plan din Deen be saniba, kuma ya kamata ace yasani tinda shi yake basa shawara, shi sameer sam bega baiken abinda yayi ba, ganin yake kamar yayi abinda ya dace ne……. Sai ya shiga kiran number Deen….

Deen na zaune abin duniya ya ishesa ga guilty conscience din da yake damunsa tun bayan yayi barin zance a gaban Umm da mami, kuma har yau basu kara zuwa ba… Gashi an kara masa damuwa akan damuwa na dauketa daga asibiti da akayi, da yana tinanin ya saci hanya yaje ya ganta a hospital yanzu kuma batanan gabadaya, ya kuma rasa wanda ze fadawa damuwarsa yaji dadi, shi haka Allah yayisa da mugun zurfin ciki babu wanda yakejin cikinsa saidai friends dinsa su kawo nasu ya basu shawara koya taimaka musu ayi abinda ya dace, shiyasa kullum suke masa kallon wanda bashi da damuwa basusan na ciki na ciki ba……. 

Kamar kullum ana kawo masa wayarsa na yan mintina yayi amfani da ita haka yauma ta kasance, saidai ko an kawo baya komai da ita, mami ce kadai ke kiransa dan ita kadai tasan da waya a hannunsa dama kuma ba business line dinsa bane so few mutane ne suka sansa da line din……

A irin wannan lokacin yaji wayarsa na ringing, dauko wayar yayi yana tinanin mami ce sai yaga sunan sameer na yawo akan screen din, dauka yayi yana karawa a kunnensa….. 

Daga daya barin sameer yace;

      “Boss baka da kirki wallahi, kai in baa neme kaba baka neman mutane”…..

Dariya Deen yayi yace;

          “Kai bazaka gane bane, wani dan chasu nashiga”

     “Chasu kuma? Meya faru?”…

Cewar sameer yana mamaki dan be tabajin Deen yayi magana makamancin haka ba”…

         “Kai nothing serious fa share kawai, ya ake ciki ne?”….

Cikin farin ciki sameer yace;

        “Guess what?” I know you’re very good at guessing”

       “Wannan farin ciki da kakeyi nasan baze wuce akan babe din khaleel ba? Kayi wuff da ita kenan”.

Ya fada yana shekewa da dariya…..

Dariyar shima sameer yayi sannan yace;

      “Ba abanza muke ce maka smart ba, kamar kasani nayi wuff da ita wallahi, saceta nayi, kaganta nan a kwance, a sume na kawota dama”

Gyara zama Deen yayi strictly yace;

       “You must be joking! Me hadinka da kidnapping yarinya?”….

      “Toh ya zanyi yarinyar tafiya ji da kanta sosai! Ba gwara in saceta inyi abinda zanyi da ita ba sannan…..”

     “Enough sameer! Wani kalan stupidity ne wannan? Haka mukayi dakai? Waya baka wannan gurguwar shawarar? I hope baka taba mutuncin yarinyar mutane ba ko?”…

Deen ya fada a tsawace dan haka kawai yaji brain dinsa baze dau wannan shashancin ba…

Cikin kwantar da murya sameer yace;

     “Relax man! Ko tabata banyi ba, kiranka nayi dama ka bani shawara”…

Sai a lokacin yaji nitsuwa ta saukar masa, a nitse yace;

     “Good, yanzu ina ka kaita?”..

       “Base na kawota”…

    “I hope babu wanda ya ganka?”

     “Ba wanda ya ganni”…

“Okay, In zakabi shawarata zan taimaka maka kasamu abinda kakeso”…

Cikin jindadi da yadda da Deen sameer yace;

     “Smart namu!!, ina jinka, yadda kace haka zaayi boss”…

Gyara zama deen yayi yana kallon kofa yace;

     “Aure zamuje a daura muku kaida ita ko tanaso ko bataso!”…

 Wani uban tsalle sameer ya daka cikin ihu yace:

     “Kayi a rayuwa wallahi, shiyasa nake yinka over”..

    “Ah toh ya daifi ka keta mata mutuncinta, kasan duk rashin jin da mutum zeyi nafisan yayisa in halal way, sai kasan me zaka gayawa tsohon ka daga baya”..

     “Kar kaji komai zansan yanda zanyi handling wannan”…

    “Ita kuma yarinyar kome zatayi karka saketa, ka barta tagama haukarta harta hakura ta zauna dakai”.

    “Yanda kace haka zaayi, Allah ya barmin kai dan gaban goshin mami”…

    “Zan zageka wallahi”…

Cewar Deen yana dan murmusawa 

   “Ni ai ko dukana kayi bazance komai ba”…

     “Uhm, yanzu ina yarinyar take, kace a sume take ko?”

   “Yes, gatanan a kwance”…

   “Ok karka tabata ka barta a sumen dan zata iya bata maka plan idan idonta biyu”…

     “Ok Doctor, yanzu in jiraka kazo ko?”..

Cikin kasa da murya Deen yace;

       “Yes, yanzu abinda zaayi tinda Allah yasa kana base ka dauko artificial face dinnan daka tabamin?”

      “Nagane, sai ayi yaya?”…

   “Saika dauko dayan dakayi creating na black American dinnan, kasamo wani sharp person ku tawo tare”..

Cikin rashin fahimta sameer yace;

     “Bangane ba, ina zamuzo?”…

Sake kasa da murya Deen yayi yace;

      “Oh forgot to tell you, ina cell dinnan da aka taba kawoni, so nake kuzo a matsayin visiting kuka kawomin, sai mu rena musu hankali mu saka wani a matsayin ni, sai nasa dayan mask din chan yanda bazaa gane ni ba mu gudu”….

Haka kawai yakeji yana bukatar taimakon sameer akan abun, sannan zeyi using opportunity din ya fita ya nemeta ko Allah zesa ya ganta… 

     “Shege mutumina, tantirancinka har tsoro yake bane”…

   “Kyalesu in sun san wata basu san wata ba!”….

      “Ka bani nan da 20mins komai ze zama ready, kazama cikin shiri kawai!!!”….

Akwai show gobe😂

~Unique Barakancy~

Back to top button