Haihuwa Da Hanji Page 13 Hausa Novel
Sabo ne mai ƙarfi ya shiga tsakanin su ba na wasa ba ta sanadiyar wannan text message da suke yi wa juna, yana matuƙar wuya ta sanya shi a idanu amma baya yini ya kwana ba tare da sun ɗauki mintuna masu ɗan dama suna exchanging SMS ba, sai dai idan inda yake babu network, idan kuma tana aiki ne wayan na maƙale a kunnenta tana sauraron karatun alarammar Prof Isa Ali phantami wato sheikh Abba zari’a yana matuƙar yi mata daaɗi har ta roki Saleem da in zai zo ma ya taho mata da alqur’ani ta cigaba da koyo don yadda yake karatun daidai da ‘yan koyo.Yau ya kama Lahadi kusan duk iyalan gidan suna a gida in ka cire salim da rabon shi da gidan ma an kwana biyu, da zazzabi ta tashi tana jin sanyin hunturu dake busawa na Huda jikinta, kasancewar koyaushe hannunta na ruwa ne ko tana bakin pampo kuma sossai bazarar ya shiga hakan ya haifar mata da mura da ta ɗan kwana biyu dashi, a maimakon ya ragu ma na safiyar yau worst ga ciwon kai mai tsanani da take fama da shi ko idanunta bata iya buɗewa da kyau, a hankali kuma karo na ba adadi ta ɗago su da kyar ta kalli agogo kusan ƙarfe tara na safe ko shara bata yi ba gashi babu wanda ya leƙo ta bare a yi mata uzuri, lallaɓa wa tayi ta miƙe tsaye atishawa na ƙwace mata da ƙarfi ta ja hanci tana dafe kai haka ta sauƙa ta zari hijabai har biyu ta sanya saboda yadda a ɗaki ma sanyin ya isheta bare ta fita waje, a hankali take tafiya har ta isa main parlorn gidan daidai kofar kitchen ta hadu da Talatuwa.”A’a yanzu kenan zan tafi biɗar ki, na gama abin kari tuntuni ina son fitarwa kuma ba’a yi shara ba. Lafiya kam?”Ta ja hanci tana ɗan dafe kanta dake juyawa “Wallahi mura ne ke damu na sossai, kaina kaman an ɗora min dutse””Ashhaa! Sannu Allah ya baki lafiya, idan Hajiya ta fito ki gaya mata za ta baki magani. Yanzu ki je ki kwanta bari ni na yi sha….””Ta Yi mene? Kwanciya ta zo yi gidan ne da masu gida suna kwance itama tana kwance?”Sadiqa ta katse musu zancen da gadara.”Wai na ga bata jin daa…””Kinga Talatuwa ba dake nake ba, ki je ma ki fara shirin ɗorawa friends ɗina abinci za su shigo babu jimawa, ki tabbatar abin da za ki dafa zai ishi cin mutane shidda zuwa bakwai… Ke kuma”Ta juya ga Afeefah”Ki wuce ki je kiyi aikin ki, kuma ki tabbatar tana gamawa ba’a ajiye mana kwanuka a mawanki kudaje suyi ta bi ba”Kai Afeefah ta gyaɗa bata ce komai ba ta wuce ta ɗauko kayan sharar ta duƙa don fara wa, da ƙarfi ta runtse ido jin kanta kaman zai biyo ta ya faɗo haka ta cigaba da aikin cikin dauriya irin nata, Sadiqa dake tsaye tana danna waya rashin maganan yarinyar ke matukar bata haushi ta ja doguwar tsaki kan ta juya fuuu tayi ɗakinta.Afeefah ta gama sharan tana mopping kenan ta ji zuban kaya bisa saman kanta, baya baya tayi Allah ya taimaketa ta dafe jikin dining table, ta ɗago rinannun idanunta ta zubawa Samha da ta watso mata kayan…”Ni ki daina kallona, kurwata kurrr… Wa ma ya sani ko naman wanda ya fi ƙarfin ki kika ci ya tsaya miki a wuya. Ki gama abin da kike ki wanke min kayannan sameera ta aiki Ishaq kuma ina da bukatarsu babu jimawa”.Bata jira amsar Afeefah ba ta wuce zuwa ɗakin Sadiqa, dukkansu biyu suna zaune ne Samha ta isa tace.”Allah da gaskiyar ki Aunty sadiqa yarinyar nan ta samu wuri har wani iyayi take kaman ta Allah, muka cigaba da zuba mata ido babu wanda ya san me gaba za ta haifar kin ga har wani fresh tayi ta kara kyau”Sameera tace “Ni na fi tausayin Yaya Salim don daga ganin yarinyar nan wallahi green snake ce, bana tunanin idan da Mommy bata ɗauki matakin da ta ɗauka kanshi ba zai rayu har yau, gwara mu kasheta da aiki ta yadda zata gaji ta gudu”Sadiqa tace “Toh ai yanzu sai mu ci ɗamarar hakan don na ga mommy ta fara mance zancenta, kin ga idanunta kuwa? Wlh muddin yarinyar nan ta samu rana ba karamin shanya za ta yi ba”.Suka cigaba da tattaunawa akan Afeefah da idan an matse su ba za su iya faɗan laifinta guda a gare su ba amma da yake amfani da zancen mutane ya riga ya zama jinin ɗan Adam sai ya zamana kawai da gaske Mayya ce a gare su kuma idan bata bar gidan ba za ta iya raba ɗayan su da rayuwarshi, haka kuma duk wanda ya nuna mata tausayi to fa shi za ta fara lamushewa.Zaune yake cikin mota da alama abu yake dubawa don hankalinshi duka ya tattaru ne ga wayan hannunshi, sanye yake da wani grey trouser mai taushi ya haɗa ta da cream Color shirt da yafi yanayi da gashin mage tsabar taushinsa, high neck ce wuyan don idan da zai ja daga sama zai iya rufe har hancinshi da rigar, Dukda wani irin sanyi da hazo da ya cike sararin samaniya motar dake kunne cike take da sassanyar iskar Ac ya haɗu da ni’imtacciyar kamshin shi da ma flavours da yake amfani da su na motan suka ba da wani kamshi na musamman. A hankali sautin waƙan Alex Warren ta ordinary ke tashi, tsaki ya ja a karo na barkatai a ranshi yake shirin fara masifa don baya ƙaunar bata lokaci sai ga wayanshi ya shiga ƙira, Bluetooth na kunnenshi ya ɗan danna.”Allah Saleem zan yi tafiyata ka san na tsani ɓata lokaci”Duk da a hankali yayi maganan alamun muryarshi ya nuna ya hasala kuma tabbas zai iya tafiya ɗin don saleem ya shiga masa lokacinsa.”Afuwan mutumina wallahi sai yanzu na tuna inda papers ɗin nan suke, suna ɗakina kuma kyakyawar ɓoyo na musu babu wanda zai san inda suke ban zaci boss zai tambaya bane da na taho da su, please help me ka je ka dubo min”Shiru yayi saleem ya marairaice murya “Please help a soul ba ni da mai min sai kai, ka ji Autan Mammi?”Da magiya ya ƙarasa hakan ya sa Rayyan ɗan murmushi “Don dai kai ne…””Eh taimaka pls”Ko kan salim ya gama maganan ma ya ja motar cikin natsuwa yana sauraran kwatancen da saleem ɗin ke mishi na inda safe ɗin da ya ɓoye confidential files ɗin yake, Saleem ya bashi wahala don ya fi hour yana neman su a office nashi na nan head quater don mance inda ya ajiye yayi sai daga baya ya tuna da kyar. Daga waje Ryan ya ajiye motar shi ya sauka ya shiga cikin gidan da ƙafa cikin tafiyar shi mai cike da ɗumbin ƙasaita wane saraki hannayenshi duk zube a aljihu, waƙa still yake ji a Earpods ɗin kunnen nashi saidai sautin na fita ne da sanyi ba mai hayaniya ba, kamar ko yaushe a murtuke fuskar nan sai kace wanda aka zagi iyayenshi har ya shige, bai nufi ma main parlorn ba ta kofar baya ya zagaya ya haura stairs da zai sada shi da ɗakin salim, a jikin kofan ya tsaya ya duba inda suke ajiye key ya ɗauka ya buɗe ya sanya kanshi ciki don duk sun san inda ɗayansu ke barin spare key incase of emergency, dulum ɗakin don komai a kashe ya kunna wuta ya wuce uwar daka direct wardrobe da ya mishi kwatance ya je ya buɗe, kaya ne a jikin hangers ɗin ya ware bangon ya bayyana gefe wani keypad ne da ba zaka ce akwai wani abu da zai iya buɗuwa ba ko da an danna.Wasu numbobi ya saka sai ga wardrobe ɗin ya dare, ya turo wani box waje nan ma ya saka wasu lambobin sai ya budu bai tsaya ma duba me ke ciki ba ya zaro files ɗin ya buɗe don tabbatar da shi ne ko ba shi ba, su ɗin ne kuwa yana ƙoƙarin scanning dilim nepa suka ɗauke. Ɗakin ne yayi duhu sossai ba zai iya scanning haka ba sai ya nufi balcony door yana dan tsaki ya buɗe ya tsaya daga saman ya fara scanning yana forwarding to salim dake online yana jira har ya gama, yana ƙoƙarin mayar da wayan aljihu ya ɗan ɗago sai idanunshi suka faɗa kan ta, har ya juya ya ɗan dakata ya sake waigo wa ya kalli ƙasan ba fuskarta yake kallo ba irin aikin da take yi a sanyin yake gani a ranshi yana raya’Mutane are heartless’Ya dai san babu ɗiya mace mai gata da zata zauna a wannan uban sanyin tana wanki ga tarin wanke-wanke dake jira a gefe, bai ga dacewar a ce kowa na ɗaki a ɓoye ita ɗin tana ƙasan pampo ba, bai gama tunanin ba ta saki atishawa har huɗu a jere ta ja hanci tare da ɗora goshinta a kan gwiwarta, wani iri yaji sai yaji yana son kallon fuskarta, hakan ne ya hana shi tafiya har ta ci seconds kan ta ɗago ya ɗan ƙurawa face ɗin idanu.Kawar da idanun yayi ya mayar hannunta dake wani irin rawar ɗari duk kakkarwa suke, sun sandare saboda sanyi ga hijaban da ta lafta rabi a jiƙe shakaf. Tunanin inda ya san fuskan yake sai dai ya kasa ya ɗan sake kallon gashin idanunta da suka yi fari fat ya ja tsaki tare da barin wurin gabaɗaya, mayar da takardun yayi ya fice daga sashen ya nufi harabar gidan don tafiya sabgar gabanshi sai ga Sadiqa ta fito taryar Ƙawayenta da Shigowar su kenan kowacce na ƙoƙarin sauƙa a motar ta, ganin shi ya sa ta wani zaro idanu shi kam kallo ɗaya tak yayiwa gefen da suke ya ɗauke kanshi ya cigaba da tafiyarshi with steez bai ma san su waye ba bare ya tantance mutane ne ko aljanu.”Ya Ryan”Ta ƙira sunan a hankali sanin baya son ihu ko hayaniya, in ka cika ko magana da ƙarfi ne sai Ranshi ya ɓaci kuma muddin nashi ya ɓaci kaima sai naka ya ɓaci haka yake, ya ɗan ɗago ya kalleta a kan rigar sanyi jibgege dake jikinta ya soma sauƙe ido kan ya ɗan ja tsaki matsalar shi kenan, da wuya ya ga abin da ke cutar da wani ya iya ɗauke kai, baya son zalunci sam a rayuwarshi Dukda ana yi mishi kallon miskilin mai murɗaɗɗiyar hali sai dai yana da tsananin tausayi, ‘yan aikin gidansu sun shaidi hakan don shi mutum ne dake so ya ga an baiwa ɗan Adam haƙƙinsa na mutum cikakke kaman yadda Allah ma ya karrama dan Adam ya kuma ba shi daraja.Yanzu dubeta killace cikin shigar da ba zai bar iskar bazarar cutar da ita ba amma ‘yar aiki zaune ƙasan pampo hannayenta da kafafunta duk cikin ruwa cikin halin rashin lafiya don a matsayinshi na likita kallo daya tak yayi mata ya san bata da cikakken lafiya hakan sai ya sake ɓata Ranshi amma sam fuskanshi na nan a yadda take bata sauya ba “Ina kwana? Ashe ka shigo?”Kai ya gyaɗa kawai ya zagaye ta ya wuce abin shi, da kallo ta bishi tana murmushi a fili ta furta “Miskili ka fi mahaukaci ban haushi””Waye shi?”Ɗaya daga cikin Ƙawayenta da duk suka bi shi da ido yuuu tayi tambayar.”Ryan Khamis kike ji da gani, sojan da ko a cikin sojoji ake ji dashi, likitan da ko a cikin likitoci babu kamarsa… Ga sanyi ga zafi, ganin dariyar shi ko murmushinshi sai ka yanki tikiti””Wow shi ne Surgeon General Ryan Khamis? Da gaske don Allah? Dama yana zuwa gidanku haka a bati?”Sadiqa ta saki murmushi “Abokin yayana ne, yana zuwa sossai ma musamman idan suka samu saukin aiki saleem na gida don ba’a raba su, mahaifiyarshi ma na zuwa har gidan nan, shine dai Ryan Khamis”No 1 matashi ne da ake ji dashi mata suke rububinshi don duk inda ya shiga akwai masu kyasawa amma fa shi duk basa gabanshi, yana flatforms sai dai babu wanda ya san handle nashi don akwai handles dayawa da sunayenshi na ƙarya ana yaudarar ‘yan mata, shi dai kam kaman dutse yake mace bayan mahaifiyarshi duk a maza Ƴan uwanshi ya ɗauke su.Da zancen shi suka shiga parlor nan aka baje ana cigaba da hiranshi kala kala da kyar suka saki suka kama wata.Shi kam Rayyan yana tada motar shi ya danna ƙiran Salim “Don iskanci ko godiya ba za ka min ba ko?””Afuwan Ryan ka san ina gani printing kawai nayi na tafi presenting don ana jirana, yanzu kenan fitowa ta ko wayan ban fitar ba na ji ƙiran ka”Driving yake slowly duk zantukan Salim ɗin bai tanka ba sai ya daka tsalle ya kama wani zancen da ya kasa bari a ranshi sai yake jin kaman shima Allah zai kamashi da laifin wulakanta dan Adam tunda ya gani bai yi magana ba “I saw someone familiar kaman na san fuskan but i cant recall”Salim ya ɗan tafi nazari kan ya ce “A gidan mu kuma?”Kai Ryan ya gyaɗa sai kuma ya tuna voice call ne suke yi a hankali yace “Yeah, choculate tall young lady haka””Afeefah ka gani?”Salim yayi saurin katse shi, a ranshi ya maimaita sunan ‘Afeefah’ ba tare da yayi magana ba, Salim ya cigaba da magana”Ka santa mana Rayyan, yarinyar da ka ceta wacce ta taɓa shan poison a Anchau?”Sai lokacin ya tuna inda ya san fuskar but Meyasa take aikatau gidan su salim? Ina iyayenta da family ɗinta? Kaman salim ya shiga Ranshi wai aka ce sanin hali ya fi sanin kama bai wuce magana ne a bakinshi ya kasa fitarwa ba don haka ya shiga bashi labarin yadda ya mayar da ita da irin wulakancin da suka sha yadda ta bashi labarinta daga farko har karshe sai da ya gama tsaf Ryan dake parking tsakar gidansu ya ce “Hmmm”Ya ƙarasa yana dan taɓe jajazir ɗin laɓɓanshi ba tare da ya ce komai ba bayan nan, har salim ya zaci ya katse kiran sai ya ji Ryan ɗin ya watsa mishi tambayar “Then taimakonta kenan ka yi to be lowly house help?””No! No!! Wallahi ba hakan bane a raina Rayyan na rasa yadda zan yi ne, mommy ta katange min duk wata ƙofa da zan iya inganta rayuwarta, abin is hurting me badly… Ka kuwa san akwai Allah ya isa a kaina muddin na yi magana da ita na fatar baki na sama da minti ɗaya?”Ɗan zare shanyayyun idanunshi Rayyan yayi”Wow! Why?””Saboda kawai sun yarda da champin mutane da ƙagen da ake yi mata” nan ya shiga bashi labarin gumurzun da suka sha da mommy a kanta kan ma aka barta a house help ɗin.Rayyan ya ɗan lumshe idanu ya buɗe a ranshi mamakin mutane yake yi, Sai ji salim yayi yana cewa “Idan bata kashe ku ba ku ai kun ɗauki hanyar kasheta!”Yana kai nan ya yanke wayar don ya gaji da magana, ɓalle murfin motar yayi ya nufi cikin gidan cikin natsuwa da takunshi na ƙasaita haɗe da izza.Kasake salim yayi rike da wayan a hannu yana juyawa, jikinshi ne ke bashi ba haka kawai Rayyan yayi maganar Afeefah ba, ya kuma san a yanzu ko ya sake kiranshi ba lallai ya bi ta kan zancen Afeefah ba kuma bare yayi mishi bayanin me yake nufi da za su kasheta? Hankalinshi ne ya ji yana neman tashi. Allah ya sani daga lokacin da tausayinta ya yi tsanani a ranshi ya juye ya zama mishi so ba tare da ya farga ba, har ranshi sonta yake kuma so yake ya aureta saboda ƙaunar da yake mata not out of pity, ko da ya ajiye ta kaman yadda mommy ta umurta yayi iya kokarinshi wurin ganin ya manta da rayuwarta ya bar wa mommy ɗin sai dai hakan ya gagara mishi dole ta sa ya waiwayeta ya dawo ya kawo mata waya don ya dinga jin lafiyarta da bukatun ta, layinta ya lalubo ya zubawa idanu sama da mintuna uku kan ya danna mata ƙira sai da ya jera sama da 10missed calls bata ɗaga ba sai hankalinshi ya fi na da tashi ya tura mata text message sama da biyar ba reply.A lokacin tana ƙoƙarin tattara kwanukan da ta gama wankewa ta kai bakin kitchen, jikinta babu inda ba ya rawa har hakwaranta na haɗuwa, bayan ta ajiye ta koma inda ta tashi ta ɗauki wayan da karatun ma yau bata samu ta iya kunnawa ba ta nufi ɗakin tana tafiya da kyar, hijaban kawai ta zare ta zubar a wurin ta shige bargo tana hawayen tausayin kanta, jin kaman vibration na wayan nata ya sa ko ido bata buɗe ba tayi picking tare da maƙalawa a kunnenta, Sheshekarta ne ya fara shiga mishi kunne yaji wani abu ya sauka mishi har cikin zuciyarshi hakan ya rikita masa lissafin kwakwalwa…”Afeefah menene? Me ya sameki?”Shiru sai kuka da itama jin muryarshi ya sa ta ƙara karfin kukan, kaman shi ma zai fashe da kukan cikin sanyi ya shiga cewa “Don Allah ki yi min magana Afeefah, hankalina tashi yake da kukan nan naki talk to me please, menene?”Sauƙe wayan yayi ya kalli time saura seconds goma “Help me Afeefah ko ta text ne ki rubuta min Meke damun ki? Kar ki yi kisan kai ki taimaka”Yana kai nan ya sauƙe wayan ya kashe tare da jingina kanshi jikin motarshi, ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi Kaduna sautin Muryar kukanta ke ta amsa kuwwa cikin kanshi…



