Uncategorized

Maryam Booth tana son Mercedes Benz CLA 250 a matsayin kyautar ranar haihuwa

 Maryam Booth tana son Mercedes Benz CLA 250 a matsayin kyautar ranar haihuwa

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Booth, ta ce tana son mota kirar Mercedes Benz CLA 250 a matsayin kyautar ranar haihuwa.

 Jarumar ta bayyana bukatar ta a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Litinin.

 “Bikin ranar haihuwa na yana kusantowa dan haka inason wani ya saya min wannan motar maras tsada,” ta rubuta.

 Jarumar haifaffiyar Kano da aka fi sani da rawar da ta taka a The Milkmaid ta kuma wakilci Najeriya a fannin wasan kwaikwayo na kasa da kasa a gasar Academy Awards.

 Ta kuma lashe mafi kyawun rukunin ƴan wasan kwaikwayo saboda rawar da ta taka a matsayin Zainab a cikin The Milkmaid da aka dauka a 2020 na African Movie Academy Awards (AMAA).

 Maryam Booth zata cika shekara 28 a ranar 28 ga Oktoba nan da muke ciki.

Ta samu mabanbanta ra’ayiyyika akan wannan posting din da ta yi, shin kaima meye ra’ayin ka akan wannan posting na Maryam Booth, kana ganin a matsayin ta na musulmai kuma bahaushiya hakan da tayi yayi daidai kuwa?

Back to top button