Uncategorized

Babu So Chapter 2 By Billyn Abdull

 

Typing📲

      ❤‍🔥BABU SO….!!❤‍🔥

                 (Miya kawo kishi?)

              Bilyn Abdull ce🤙🏻


*_02_*

………Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu. 

Karanta>>>> Sanadin Labarinah Chapter 2 By Hafsat Rano


      Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.

     Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.

     Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba’ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi, dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.

     Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da  matarsa mai suna Asiya haihuwarsu ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba sai fatan shiriya yake musu. 

      Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar saudia sunje aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa ragamar rayuwar ƙannensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da Mimi. A wannan gaɓar ƴan uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daɗi har cikin ransa.

       Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai ɗan Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ƴan uwansa rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ƙanwarsa Mimi dake fama da ƙaramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ƴan uwan nasa dan kuwa su ko auran Mimi duk da ya basu hakkinsu ƙin zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta’aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane su manta kawai.

        Ɗan shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk iyalansu, dan kuwa a baya basu taɓa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin ƴaƴansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila ɗiyar ƙanwar gwaggo nada yara huɗu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna kiransa da *_Shareff_*. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ƙaramin ciki da take kan laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta mugun tsanarsa saboda huɗubar Gwaggo, ƙinsa take tamkar itace ƴan uban nasa ba mijinta ba. a gefe tana matuƙar jin kishin yana rayuwa a ƙasar waje a ganinta kodai yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matuƙar takaicin ganin su Muhammad sun fara sakkowa akan ƙin ɗan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke ɗaurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai son jama’a da haƙuri, duk da ƙiyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin kishiya ta zama mai haƙuri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daɗin iyayen mijin nata takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai ɗiyar ƴar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haɗata fitinar da aka dingayi da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk maza. sai dai tana da ciki ɗan watanni biyar. Umar dai yaƙi aure, hasalima ya zama fanɗararre a cikinsu sai addu’a. Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba’a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.

Karanta>>>> Farhatal Qalb Chapter 2 By Nana Hafsat

     Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba’a faɗaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.

     Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.

      Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri’arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al’amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya ɗauka yaƙi. 

     Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.

         A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa….

Karanta>>>> Inayah Chapter 2 By Mamuhgee

        Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.

       A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su’ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma. 

       Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace. Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama. Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi. Yarinya taci sunan *_Juwairiyya_*, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da *_Anam (Blessings of GOD)._*

         Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana maƙale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami’a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na’a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.

       A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.

     Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai…..

      A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.

Karanta>>>> Gurbin Ido Chapter 2 By Safiyya Huguma


     Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko’a mafarki bata fatar haɗa zuri’arta dasu Abie a duniya…..

       Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa’aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna’a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da *_MM Shareff_* a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya Shareff bai yarda ya ɗauka ma’aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma’aikatansa damar yin wasan kuma.

     Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo. 

        To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba………✍

_Ko yaya wasan zai kasance🤔? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO…! MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taɓa zuwa muku da kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taɓo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki a yanzu da rawar da tarbiyyar ƴaƴanmu ke takawa a social media batare da saninmu ba ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da zafinsu suke😉🥰🥰😘🚶🏻._

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏🏻

GA TSARIN YADDA FARASHIN SU SUKE;

ZAFAFA GUDA BIYAR 1  PAGE 1 NA KOWANNE BOOK A KODA YAUSHE INSHA ALLAH . KAMAR KO WANI YI. FARASHIN NA NAN AKAN NERA DUBU DAYA

ZAFAFA BIYAR

Littafi daya 300

Littafi biyu 400

Littafi uku 500

Littafi hudu 700

Littafi biyar 1k

GURBIN IDO

SAFIYA HUGUMA

SANADIN LABARINA

HAFSAT RANO

INAYAH

MAMUHGEE

FARHATAL QALB

NANA HAFSAT

(Miss Xoxo)

BABU SO

BILLYN ABDUL

ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES!! WANNAN SASHI NE NA BANGAREN YAN ZAFAFA NA MUSANMAN DA KE SON KARANTA SHAFUKAN LITTAFAN ZAFAFAN SAMA DA DAYA. TO KU SHA KURUMIN KU. KUDIN VVIIP NA ZAFAFA NERA DUBU BIYAR NE KACAL NA DUKKANIN BOOKS DIN BIYAR. A KALLA A RANA ZAKU DINGA SAMUN SHAFUKA 10 KOWANNE BOOK SHAFUKA 2 KENAN.

PAY 5K FOR ZAFAFA BIYAR VVIP SUITE SECTION. MAXIMUM OF 10 PAGES DAILY, 2-2 PAGES OF EACH BOOK. MAKING 10 PAGES IN WHOLE. LITERALLY

SANNAN AKWAI TSARIN VVIP NA BOOK DAYA GA MASU RAAYIN VVIP NA BOOK DAYA KO BIYU KO UKU KO HUDU GA KUDIN SU KAMAR HAKA;

BOOKS HUDU 4500

BOOKS UKU: 3500

BOOKS BIYU: 2500

BOOK DAYA: 1500

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500

3 BOOKS : 3500

2 BOOKS : 2500

1 BOOK: 1500

MUNA TALLATA HAJOJIN KU CIKIN FARASHI MAI RAHUSA

TALLA SAMAN SHAFI

DAYA NA BOOK DAYA :1000

TSAKIYA 800

KARSHEN SHAFI 500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

BANK NAME: ZENITH BANK

ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR

ACCOUNT NUMBER: 2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA DA SHEDAR A TARE:

09134848107

Back to top button