Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 6 Complete Novel

Matar Damisa Complete Document

🐅MATAR DAMISA🐅

(The Wife Of Tiger)

MALLAKIN

ASMEETAH ✍️✍️

The writers of…

1️⃣ Ikram ko Kausar.
2️⃣ Rayuwar Siyama.
3️⃣ Baby Ogah.
4️⃣ Yayana Zan Aura.
At now
5️⃣ *MATAR* *DAMUSA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️17 to 18

Ayush tsayawa tayi a bakin gadon da Junaid yaketa sharar baccinsa ya rufe fuskar da pillow, tana tunanin ta tashe shi ne ko kuma ta kyale shi kawai tayi tafiyarta
Lokaci guda ta yanke shawarar tashin shi yaci abinci kada yayi sanyi, cikin ‘karfin hali ta haye saman gadon tana rarrafawa a hankali cike da fargaba saida tazo saitinsa ta tsaya cak ta kasa tashin shi.
Shi kuwa adai dai lokacin ya fara wani irin mafarki mai tsoratarwa, A cikin baccin yaga wata ba’kar Damusa mai jajayen idanuwa ta tsaya daf dashi tana shirin Kai masa hari! A gigice Junaid ya Kai mata naushi da iya ‘karfinsa
Wayyo a madadin ya naushi Damusan ashe a Ayush ya kaiwa wannan naushin a saman Nononta ta 6angaren dama, wani irin ‘Kara tayi ta wantsilo ‘kasi sai datayi dungure sau uku ta tsinci kanta a bakin ‘kofa, hankali a tashe ta mi’ke tana tangal tangal kamar wacce tasha kayan maye! a haka ta fice daga d’akin…
Shi kuwa cigaba da baccinsa yayi hankali kwance.

Mommy tana shirya musu kayan abinci a dinning
Ta jiyo kukan Ayush da sauri ta waiwaya bayanta domin ganin abunda take ji,
Ayush bata tsaya wata-wata ba sai yaraf ta fad’i ‘kasi tana ta faman juye-juye da shanbe-shanbe “wayyo Allah Zan mutu, kirjina ya fashe ciwoo”. Ta Kama Nononta da hannunta domin ba ‘karamin zogi yake yi mata ba
Duk ta rasa Ina zata saka kanta, idanunta duk sun kad’a sunyi ja tsabar azaba ga wani gumin da yake yarfo mata..
“Ayush lafiyanki kuwa? Ke da waye? Meya sameki” haka mommy taita jero mata tambayoyinda bazata iya amsa su ba a yanzu,
Ganin yanda taketa juyi a gurin yasa mommy tsorita da sauri ta kamo Ayush tana fad’in muje mu d’aki kiyi hakuri”
Ayush KO mi’kewa bata iya yinsa kamar Wanda wuta yake ci akan Nonon haka take jin rad’ad’in nan.
Zaunar da ita tayi a bakin gado, tana fad’in “sannu ko, wai meya faru ne Ayush?”
A lokacin Ayush ta d’an dawo hayyacinta duk da zafin da gurin yake yimata da ‘kyar ta bud’i baki tace “buguwa nayi” bakinta na kakkarwa kamar maijin sanyi,
“A’a Ayush ki gaya mun gaskiya, shin da mai kika bugu?
Kamar bazata yi magana ba can tace “na bugu da ‘kofar d’aki ne” murya sanyi sanyi take magana.
Mommy tace “kin tabbata?”
Kai Ayush ta d’aga mata alamar eh.
Mom tace “to muga gurin da kika ji ciwon” ta ‘karasa maganar tana faman cire rigar Ayush!
“A’a Aunty ki Bari kawai ba wani ciwo sosai bane” a cewar Ayush wacce kanta ke kallon ‘kasi alamar kunya.
Mommy kallon ta take cike da mamaki tace “to banda abunki nifa mace ce er uwarki sannan in baki manta ba ni Doctor ce, dubaki zanyi naga wani kalar magani ya dace ki sha” da kyar Ayush ta yadda ta zame rigarta daga sama sannan a hankali ta zame breziyar ta Mommy tana ganin yanda Breast d’inta d’aya ya kumbura suntum ga yayi jawurr abunka da farar mace
“Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, Ayush duk wannan ciwon a buguwar ‘kofa yake? Ki duba kiga?”.
Banda zubda hawaye ba abunda Ayush take, ita kad’ai tasan irin rad’ad’in da take ji!
Da sauri Mommy ta tashi tana fad’in “wannan bana zama bane kina bu’katar treatment”
Ta fice daga d’akin gaba d’aya ta susuce a ranta tana tunanin Junaid ne yayi mata wannan d’anyen aiki daman ya nuna baya son zamanta a gidan.
Ayush kuwa tashi tayi ta nufi toilet tsayawa tayi a gaban mirrow tana fad’in “wannan bawan Allah ba ‘karamin mungu bane, azzulumi daga tashin sa a bacci yaci abinci shine zaiyi mun wannan hukunci, Allah zai saka mun” ta ‘karasa maganar tana zubda zafafan hawaye, ga Nono d’aya kuwa yayi timm kamar Wanda ya Tara ruwa.
Tana cikin sambatun ta tajiyo bud’an ‘kofar d’aki.
Mommy ce ta shugo hannun ta ri’ke da boxes na pharmacy, ta ‘kara ficewa ta dawo da kulolin abinci ta ajiye a saman table, zama tayi a bakin gado tana jiran fitowar Ayush, ba jumawa Ayush ta fito da d’aurin towel a kirjinta tayi using da hot water domin jikin ta ya samu ‘kwari.
“Ayush en mata anyi wanka kenam, Bari na za6a miki ‘karamar riga wanda zakifi jin dad’in zama da ita”
Ta bata doguwar riga sleeping dress mai short hand marar kauri ta Sanya a jikinta bayan pant babu komai a jikin ta sai wannan longer shirt, zama tayi kusa da mommy wacce ta d’auko magunguna tana ‘ko’karin bud’e mata su ta bata lokaci guda ta Kora su, daga baya Mom ta d’auko Allura tana ‘ko’karin yi mata, tabb d’in Ayush taga makiyarta wato Allura da gudun gaske ta nufi toilet ta danna sakata tana fad’in “wallahi baza’a mun Allura ba, Dan Allah Aunty kiyi hakuri ki ban ko wani irin magani amma banda Allura”
Mommy sake baki tayi tana kallon ikon Allah kwashewa da dariya tayi tana fad’in “Ayush da girman ki kike tsoron Allura? Nake ga Allurar zaifi miki amfani cikin gaggawa KO!”
Ba yanda mommy bata yi da Ayush ba akan ta fito amma furr Ayush ta’ki Allura sai hakura tayi tace “toh shikenam ganan Abinci kizo kici tinda kin’ki Allura”
Momy cikin fushi tabar d’akin ba wai saboda Ayush ta’ki Allura bane, tana so taje ta samu Junaid ne akan Abunda yayiwa Ayush, Sam bai kyauta mata ba,

Bayan fitar Mommy daga cikin d’akin Ayush ce ta bud’e ‘kofar toilet a hankali ta lalla6o ta d’auki Alluran da mommy ta ajiye saman table tasa a cikin boxes ta rufe, sannan ta d’auki flask din abincin ta zuba a plate paten doya ne da wake, sai ta tsiyayi ruwan tea a cup tana ci tana Kora tea, daman ba ‘karamin yunwa take ji ba, tinda ta shugo gidan nan take had’uwa da ‘kaddarorinta bata samu tasa komai a cikita ba, Ayush fah ansamu eating kamar ba gobe, tana ci tana yarfa hannaye tsabar zogin da Nononta yake yi mata kawai dai jurewa take……..

Mommy
Kamar zata dungura haka take hawa upstair nan tana zuwa ta bangaje ‘kofar d’akin tana shirin yin masifa, abunda ta gani ne yasa ta tsaya cakk ta zaro ido waje bakinta na kakkarwa take fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, JUNAIDDD”
wani irin gigitaccen ihu tayi ta fad’i ‘kasi sumammiya….

Ikon Allah mai Mommy ta gani haka???

Duk yanda akayi taga abunda yafi ‘karfin tunaninta ne!.

*TO* *BE* *CONTINUE* *INSHA* *ALLAH*

Sorry en uwa ina ganin complain d’inku akan rashin poster littafina da wuri, Dan Allah ayi mun uzuri Ina busy ne shiyasa, ga rashin wutar NEPA!
Please my fans pardon me 🙏🙏🙏

 

Click Here To Read Matar Damisa Book 1 Chapter 7 Complete

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

MATAR DAMUSA 🐅🐅🐅 Littafi kyauta domin nishad’i 💃💃💃
Qirqirarren labari from me 👇👇👇👇

ASMEETAH CE ✍️✍️✍️

Back to top button