Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 125 Complete Novel

Father of soldiers

🔥TAKUN ƘARSHE🔥

 

Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags

Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃

 

Remain few pages 😢

 

 

Bayan tafiyar Jahan,Amal ta sanarwa Amani abunda yace ta koya mata,tasha ruwan mamaki,amma ta wani 6angaren ba ƙaramin taimakonta yayi ba,tunda gashi Ya tuna mata abunda ta manta bata koyar da Amal din ba don tasan tana bukatar hakan,

A taƙaice cikin ƴan kwanakin nan,wata irin shaƙuwace a tsakanin Sgr da Sehrish,Soyayyarsu gwanin ban sha’awa,wani irin so suke yiwa junansu,a koda yaushe yana manne da ita idan har ba lokacin sallah bane tunda aikinshi na Nigeria Ya qare,jikinta yayi sauƙi sosai,tana samun kyakkyawar kulawa a wurinshi,komai atare suke yinshi,Cin abinci,bacci,da sauransu,Yanzu kowa na gidan hatta su Ammi sun gane cewa Sehrish da Sgr sun sasanta tsakaninsu,wannan yasa ammi bata ƙara neman Sehrish da su zauna akan maganar kar6ar takardarta ba,dama abunda suke fata kenan,

A 6angaren Omar da Hosana,abun sai son barka,hajiya azeema ta gyara mashi ita sosai,yanzu ta rage wannan soki burutsun nata,duk da akwai sauranta,Amma an samu cigaba,

Idan muka dawo 6angaren Romeo da Juliet,ko ban faɗa ba kunsani,Masoyane na gaske,duk da rashin jin Junaid haka Jahad ke son abunta,kamar yadda shima yake sonta,basu gajiya da bama furannin soyayyarsu ruwa,wata irin shaƙuwace a tsakaninsu,hakan yasa koda yaushe suke manne da juna,

A 6angaren Kanal Yusuf da Amrish kuwa,tuni ya bayyana mata soyayyarshi,kuma da Maganar aure ya fara zuwan mata,don baya buƙatar su 6ata lokaci wurin yin soyayya a waje tunda sun aminta da juna,abu ne kana so ana sonka,no need to waste time,hatta Abbansu yasan da maganarsu,

Saboda tafiyar Sgr da Omar U.s,Yasa aka shirya yin bikinsu a cikin ƙurarren Lokaci,gagarumin bikine aka shirya yinshi cikin sati guda,Wanda tuni an fara sanarwar ɗaurin Auransu wanda za’ayi ranar Juma’a,gaba ɗaya Social media ta ɗauka,gidajen talabijin dana radio,Ko’ina zancen auran Ƴa’ƴan Abban sojoji ake yi,Labarin ya karaɗe Duniya,wato bikine na zaratan samarin gidan wanda sukayi shura a duniyar nan tamu,daga cikin waɗanda za’a daura auransu,Akwai Omar da Hosana,Junaid da Jahad,Jahan da Amal,Yusuf da Amrish,Osman da Khadija,Adam da Nafeesat,Fawan da Yusra ɗiyar abokin Abbansu Tafeeda,dama sun jima atare tun lokacin da yake tashen rashin jinshi atare suke da ita,kafin Allah ya shiryi kowannansu,Ayaan da Yuhana ƴar wurin ƙawar Mommynsu Dr Harriet,wanda Mommynsu ta haɗa shi da ita,Don ayi auransu atare da Jahan,saboda ya nuna cewa in dai baza’a ɗaura Auransu da Ayaan ba sai dai shima a fasa nashi,wannan dalilinne yasa Mommynsu ta haɗa Ayaan da Yuhana kuma cikin sa’a,A rana ta farko da Ayaan ya haɗu da ita yaji ta kwanta mashi aranshi,ita ma kuma haka,sun amince da junansu batare da sunsha wahala ba,bayansu kuma sai Uban gayya,Babban ɗa a wurin Abban sojoji,General Ishaq tare da Amaryarshi Hajjaju,Sai daga baya Abbansu yaji labarin rabuwarshi da Laila,Yasha faɗa a wurinshi duk da yayi mashi bayanin dalilin rabuwar aurannasu,daƙyar ya samu Abba Ya haƙura da maganar,
Abusufyan ma yana ɗaya daga cikin wanda zasu Angwance,Shida Uwar ya’yanshi Zainabu Abu,

Waɗanda aka sanyama biki kuma,Hafsat da Ya mu’allim,bayan dagar da suka sha dashi,da farko taƙi amincewa da auranshi saboda malamine,Amma daga baya ta amince da auran nashi,gaba ɗaya sauran matasan gidan,tun daga kan Captain Najeeb,Jabeer,khaleed,da Talal,kowannansu An sanya ranar auranshi,

Murna awurin Family dinsu ba’a magana,musamman Abbansu yafi kowa farin ciki,burinshi na qarshe da ya rage mashi a duniyar nan shine yaga auran ƴa’ƴanshi,kodan yaga ƴan jikokinshi

Ba ƙaramin ƙoƙari Hajiya azeema tayi ba,tare da Mommy da Oummansu Sehrish,domin kuwa sune suka yi tattaki har zuwa Dubai wurin haɗa masu lefensu,jigunannun kaya haɗaɗɗun gaske,An kashe kuɗi kamar ba’asan wahalar nemansu ba,musamman a lefen Sehrish da Hosana da Jahad,shi Junaid ko sisi bai kashe ba,Komai da aka kashe ma Jahad Sgr ne ya ɗauki nauyin komai,hatta sadakin Junaid,Sgr ne ya biya shi gaba da baya auran gata za’ai mashi,Daga Hosana har Jahad sadakinsu da Gold aka biyashi irin na Sehrish,sauranne aka biya sadakinsu kowacce dubu ɗari uku uku,Amrish ta samu kyauta sosai a wurin Sgr da Abbansu,saboda sune suka biya kuɗin komai na kayan daki,da duk wani abu da zata buƙata,

Special Gift Sgr ya shirya ma Sehrish,Amma yace Sai sun koma California zai bata kyautarta ta musamman,Saboda ta bashi abu mafi daraja the most greatest gift,wanda kowani miji yake burin ya samu a wurin matarshi a rana ta farko daya kusanceta,tunkafin ma wannan kyautar acikin akwatinan lefenta hada na kayan adon mata,zallar Diamond ne acikinshi,

Ba ƙaramin gyaran jiki Amaren suke sha ba,masu gyaransu har daga kasashen ketare,koda yaushe cikin gyarasu akeyi,tun cikin satin da za’a ɗaura Auren,gaba daya amaren suka hallara a gidan,saboda programes da aka shirya,gidan yasha gyara sosai,An ƙawata shi,idan ka shiga cikinshi kamar ka bar Nigeria ne saboda tsabar haɗuwar da yayi,Naira tasha kashi,an ɗaukko masu aikin cikin gida,manya manya chefs waɗanda zasu gudanar da abincin bikin,da kuma Event planners wanda zasu tsara shagulgulan da za’ayi na bikin,
Anyi shagulgulan biki na kece raini,An yi shiga ta alfarma,Anci ansha An godema Allah,kuma kowa ya nishaɗantu,

A ranar Juma’a,dubban Jama’a suka shaida ɗaurin Auran zaratan Samarin gidan Abban Sojoji A Abuja central Mosque,Masallacin ya cika maƙil da Mutane,ba masaka tsinke duk wani wanda ya amsa sunansa a Nigeria ya hallaci daurin auren,Bayan kammaluwar ɗaurin auran,A daren Ranar aka kawo duka amaren wanda acikin gidan Abba zasu zauna,don tuni an fara gine gine na wasu 6angarori da za’a ƙara,Amma kafin nan,kowaccensu zata tare a ɗakin Mijinta ne na wani lokaci,dama burin Abbane kowannansu in yayi Aure yafi son ya zauna a gidan tare da matarshi,saboda baison suyi nesa dashi,

Shirye shiryen tafiya U.s Ya kankama,tun ana saura kwana ukku ya rage jirginsu ya ɗaga,Sehrish ta lalla6a Sgr don ya kaita Gidan Yari taga Aunty azmee,Dayake yanzu farin cikinta yakeso,Baiyi mata musu ba,da kanshi yakaita prison,Lokacin da taga Azmee tasha kuka sosai kamar ranta zai fita,Azmee ta rame ta ƙanjame,idanuwanta daƙyar take buɗesu,Sun rungume juna sosai,koda Sehrish ta sanar da ita cewa zata sanya a sassauta hukuncin da aka yanke masu,sai cewa tayi ita batason fita daga gidan yarin saboda gudun ta ƙara faɗawa halaka,tafi son zama anan saboda tafi samun natsuwa wurin yin ibadarta da neman yafiya wurin Ubangiji,kuma ta nemi yafiyar Sehrish akan Laifin da tayi mata,tun daga kan juya mata da tunaninta da tayi,lokacin da ta manta dasu Hosana,tace ita tayi hakanne saboda halin da tashiga na yawan damuwa shiyasa ta mantar mata dasu,da kuma lalurar da ta ɗaura mata na yin gane gane,duk sai da ta nemi yafiyarta,ta kuma sanar da ita cewa itace take kiran Sgr a waya tana raira mashi kuka saboda Son da take yi mashi,Komai sai da Azmee ta sanarma Sehrish,A ƙarshe ta sanar da ita cewa Suyi ƙoƙari su nemo Haroon domin kuwa Haroon Jinin Salahuddeen ne,mahaifinshi Jabeer ɗane ga Aminullah,wanda ya kasance Ƙanin salahuddeen ne uwa ɗaya Uba ɗaya,Saboda ƙiyayyar da ke tsakanin duka 6angarorin guda biyu suka sanya dokar da zarar anga Jinin Salahuddeen A kashe shi,Suma kuma su Salahuddeen ɗin suka sanya dokar daga zarar anga Jinin Ubaid da Uba a kashe su,A sanadin tafiyar da Aminullah yayi tare da matarshi da dansu ƙarami wanda bai mallaki hankalinshi ba wato Jabeer,Akan hanyarsu ta dawowa gida,Ubaid ya sanya ƴan ta’adda suka farmakeshi,gaba ɗaya suka kashe shi tare da matarshi,Shi kuma Jabeer suka barshi yana ta gararanba a cikin garinsu,har Allah yasa wani malamin makarantar Allo ya ɗaukeshi,A wurin shi Malamin Jabeer ya taso,kunji yadda akai haroon ya kasance Jinin Salahuddeen,A wurin Saratu matar ya sayyadi Azmee ta samu labarin nan,Saboda ita kanta batasan wanene Jabeer ba,Ashe Danginsu sunsan komai game da Shi ita kaɗai aka 6oye mawa,sai daga baya take ji a wurinta,ta bata labarinne acikin ɗakin da aka kaisu dayake su biyune aka kulle acikinsa,kuma ta tabbatar mata da cewa Haroon ɗan Jabeer ne,domin kuwa Hamma Ghali baya haihuwa,shi kanshi ya san da hakan,Amma don baƙin zalunci ya 6oye mata komai akanshi,

Lokacin da Azmee ta kammala bata labarin nan,tasha kuka kamar kamar me,Ashe Haroon ɗan uwansu ne,abun ya ɗaure mata kai sosai,iya cuta dai sun cutar da rayuwarshi,sun kuma sanya ƙiyayyarshi acikin zuciyoyin ƴan uwanshi,bawan Allah,ko a wani hali haroon yake ciki ayanzu?

A nan Sehrish take sanar da ita game da aurarrakin da aka daura ciki harda na Amrish da Yaya Yusuf,ba karamin farinciki Azmee tayi ba ta kuma kara yin danasanin abunda ta aikata masu don Mutane ne su masu matukar hallaci,Bayan Sehrish tabar prison ɗin,Ta kwashe komai ta sanar da Sgr,Sam bai yarda da maganarta ba,har sai da ya tambayi Abbansu game da Labarin kawunshi Aminullah,Anan Abba ya kwashe komai ya sanar dashi har labarin mutuwar da su kayi shida matarshi,labarin yazo ɗaya da wanda Azmee taba Sehrish,kuma Abba ya sanar dashi cewa Bayan mutuwar Aminullah da matarshi,An tsinci gawawwakinsu Amma ba’a samu gawar ɗansu ba ƙarami da suka tafi dashi,wato Jabeer,tunda Sgr yaji hakan,nan take ya yarda cewa dagaske dai Haroon jininsu ne,Abun Ya ɗaure mashi kai,ya kuma ji tausayin yadda rayuwar Haroon ta kasance,bashi kaɗai ba,Kowa na gidan da yaji labarin Wanene Haroon,wasu har kwalla suka zubar mashi,Kuma yanzu ashirye suke dasu nemo shi,don su dawo dashi acikinsu,yaci gaba da rayuwarshi kamar kowa,

An sassauta hukuncin da aka yankewa Azmee da Saratu,An fito dasu daga ɗakin duhun sannan An rage masu shekarun da zasu yi a kurkukun,daga shekara 20 zuwa shekara 10 cuf,ba kowane yayi masu wannan ƙoƙarin ba fa ce Sehrish,ita ta nemi wannan alfarmar a wurin Sgr,Ya kuma amsa mata,

A 6angaren Aunty babba kuwa,Tuni an sallameta daga asibiti,ta koma gidansu kano,lokacin da ta samu labarin Auran General Ishaq da aminiyarta Hajjaju,Tasha kuka tayi danasanin rayuwarta fiye da tunanin me tunani,taji raɗaɗi da ƙunci acikin zuciyarta,Har abada bazata ta6a manta Asarar da tayi a rayuwarta ba,duk don saboda abun duniya,yanzu gashi ta tashi a tutar babu,da ita da zero basu da bambanci,

Daga cikin waɗanda zasu tafi U.s,Hada Junaid tare da Jahad,Ba don Abbansu Yaso ba,Saboda shaƙuwar da yayi dashi,Ya amince ne kawai saboda Sgr ya nemi daya bar mashi Junaid ya zauna a wurinshi tare da Jahad har ya kammala karatunshi acan,Kuma hada ƙarin Idan aka tafi da Sehrish da Hosana,Jahad bazata ji daɗi ba,tasaba da ƴan uwanta sosai,Abba baidamu ba saboda Allah ya hore mashi,idan yaso duk weekend zai iya hawa jirgi don yaje can ya ganshi,wannan abu ne mai sauƙi a wurinshi,tafiya dai ta kankama,Yau ta kasance rana ta ƙarshe da ta rage masu a Nigeria,Washe gari zasu tafi tunda Asuba,duk wani shirye shirye daya kamata suyi sun kammala shi,tafiyarce kawai ta rage masu,Gobe in Allah ya kaimu da Rai da Lafiya.

*Ayi hakuri da wannan Yau sai ahankali,da babu kwara ba daɗi,Amma in sha Allah zanyi kokarin yin long pages na Ƙarshe,ina sa ran Sunday in Allah Ya yarda littafin abban Sojoji zaiyo maku bakwana,Lahadi kenan😢waɗanda ke buƙatar karanta Littafin daga farko zuwa na uku Suyi mun magana ta whatsapp 08103884440*

Back to top button