Hausa novels

Fatalwar Delu Part 6

Fatalwar Delu Part 6

 

🤡 FATALWAR DELU 🤡

 

Part 6

 

Kingboy Isah 👑

 

Short story

 

 

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

 

 

 

Cike da kwarin gwiwa na bude dakin yayin da na dalla fitilar wayata na fara haskawa ina leka waje, da alamu dai karen baya nan, domin in da yana kofar da na ganshi. Ajiyar zuciya nayi a zahiri na ce, “Shege ai na so ace ka tsaya da na koya ma hankali”. Ko maganar ban karasa ba naji karan gudu a gefen damana, ai kuwa na haska fitila hade da gyara rikon kotar fartanya dake hannuna. Hasashena baiyi karya ba domin kuwa karen na gani yayo kaina a guje yana zaro harshe. Baya-baya na fara yi kamar zan sake fadawa daki kafin karen ya karaso gareni, domin kuwa lokacin da ya matso kusa sai naji tsoro ya kara ziyartata. Tabbas duk wanda ya ga wannan katon bakin kare yanayin girmansa da kuma yadda yake da muni, musamman idan yana bude baki yayin da yake zaro harshe hakoransa na bayyana dole ne mutum zai tsorata. To amma a tunanina shi kare sai kaje gidan mai shi yake yunkurin farmakarka shi kuwa wannan ina da tabbacin ba ma a unguwar nan yake ba, domin tun jiya da na zo banga alamar kare a layin ba.

 

 

Tunanina ya tsaya a lalai wannan azzalumin karene kasheshi ko illata shi ba karamin jahadi bane, da wannan na samu kwarin gwiwar fuskantarsa, yana zuwa gaf da ni kuwa yayi tsalle hade da bude katoton bakinsa da nufin kai min cezo a duk inda ya samu na jikina. Ni kuwa daga fartanya nayi na kwada masa a kai, wanda karfin dukan yasa sai da yaje kasa. Sai dai cikin hanzari ya sake mikewa ya yo kaina. A wannan karon ina ankare don tuni na mayar da wayata aljihu na rike fartanya da hannuwa biyu. Ba zan yarda ko kadan ya taba ni ba balle ya samu nasarar cizona, idan ma naga alamae ya fi karfina ba abun kunya bane in wullar da fartanyar in gudu daki. A karo na biyo na samu nasarar kai masa duka a wuya nan ma sai a ya fadi kasa yana wani irin kuka dake nuna alamun ya wahala, ya dan jima tukun ya tashi.

 

 

Amma wannan karon maimakon ya sake kawo min farmaki sai na ga ya tsaya a inda yake yana ta yi min haushin nan nashi marar dadin saurare, ni kuwa ganin haka yasa na nufeshi kamar zan kara buga masa fartanya, ai kuwa sai ya juya da masifaffen gudu ya bar wajen. Dariya nayi hade da cewa, “Ja’iri yau ka hadu da gamonka”. Daki na koma har na kwanta na fara jin zafi don haka na yanke shawarar fitowa waje, wannan karon tabarma na fiddo harda filo, na shimfida a waje, a hasashena karen nan ba zaiyi kuskuren dawowa ba. Amma sai na daukko fartanya na ajiye a gefena da nufin ko da ya dawo ma. Ina nan dai kwance bansan lokacin da bacci ya dauke ni ba.

 

Fatalwar Delu Part 6

 

Ganina kawai nayi a cikin daji daga ni sai fitilar hannu wanda nake haskawa, ni kaina bansan daga ina na fito ba haka zalika bansan inda zan dosa ba. Haske-haske kawai nake a cikin dajin mai cike da dogayen bishiyoyi. Nayi tafiya mai nisa a cikin dajin amma ba mutum ba ko kukan tsuntsu banji ba, wannan ya fara sa mun shakku da tsoro a cikin raina. Tambayoyin da ke yawo a cikin kaina, wannan dajin ina ne, me ya kawo ni cikinsa daga ina nake kuma ina zani? Gaba daya babu amsar da na sani. Daga can nesa na fara jiyo ihu da karan gudun mutum yayo inda nake muryar namiji ce tana fadin, “A taimake ni, zasu kashe ni Dan Allah ku taimake ni”. Jin hakan yasa na ruga da gudu na nufi inda nake jiyo muryar, duk da kasancewar ban san mai muryar ba kuma bansan su waye yake cewa zasu kashe shi ba. Amma a kalla dai nasan idan naje wajen zan ga mutane, watakil ma in samu abokin tafiya wanda ya san hanyar barin dajin nan.

 

 

Ba tare da tunanin komai ba na nufi wajen da na ke jin ihun a guje ina haska fitila. Ina cikin gudun na fara hasko mutumin da ke ihu wanda shima gudu yake ya nufo inda nake, irin gudun da ake kira na ceton rai. Daga inda nake hango shi na duba bayanshi amma banga wasu mutane ko muggan dabobbin dake biye da shi a baya ba, don haka na fara kwala masa kira da karfi ina tambaya suwa ke binsa. Ko da ya jiyo ni sai yayo inda nake gadan-gadan ba batare da ya ban amsa ba, yana kara matsowa na haska shi sai na ga ashe ba kowa bane Bukar ne, jikinsa duk rauni yayi zufa sosai da alamu yasha wuya kuma ya dade yana gudun. Kafin ya karaso wajena ya fadi kasa nayi saurin zuwa na kamashi ya tashi ina fadin, “Kai Bukar me ya faru da kai haka? Su wa ke binka yan ta’adda ne ko barayi”. Ya dago kai ya kalle ni kana a razane ya nuna baya da yatsarshi yana kokarin tashi ya ce, “Nura dan Allah mu gudu aljannu ne ke neman rayuwata idan suka zo zasu hada har da kai su kashe, don haka dan Allah tashi mu gudu”.

 

 

A yadda yake maganar wai aljannu ne ke binsa, ba dan halin da na ganshi a ciki na firgici da jigata ba da zan iya daukar zancen nashi a shiririta. Amma yanzu ba yadda na iya illa in biye masa mu gudu din kamar yadda ya nema. Haka ya mike cikin juriya ya sake zafgawa a guje yayin da ni kuma na rufa masa baya. Mun dade muna gudu da ni har lokacin bansan dalilin yin gudun ba, dan banga abinda ke binmu din ba. Dan haka nayi saurin kama hannunsa na tsayar da shi ina fadin, “Kai ni fa wallahi na gaji da wannan gudu na banza da wofi, tun dazun kake fadin zasu kashemu amma har yanzu banga wanda zasu kashe mu din ba”. Ya daga baki zaiyi magana kenan muka fara jiyo wani iska mai karfi ya nufo inda muke ta bayanmu. Ai kuwa Bukar ya kara rikicewa kamar zaiyi kuka ya ce, “Shikenan gasu nan sun kamomu, shikenan zasu kashemu”. Ina shirin yi masa magana kenan naji wata iriyar dariya a sararin samaniya, dariyar macece amma amon sautinta na fita uku-uku. Ni tunda nake ban taba jin sauti mai ban tsoro irin wannan ba.

 

 

Ba’a dade ba sai gani mukayi kasa ta fara jijiga, nan take kasar ta fara tsagewa tamkar ana yaga paper, hannu ya bullo daga cikin kasar, sannan sai kan wani yaro baki mummuna ya bullo shima daga kasa yana dariya da jajayen hakoransa. Ai da ganin haka ba Bukar ba ni kaina tuni cikina ya duri ruwa, na tabbata ina gaf da sakin fitsari a wando, zuwa lokacin yaron ya gama fitowa nan take mu ka ga yayi tsaye a cikin iska yana sanye cikin doguwar farar riga ya daga kai sama yana dariya. Mikewa mukayi da dukkan sauran karfin da ya rage a jikinmu muka sheka da gudu, amma maimakon wannan yaron aljanin ya biyomu sai na lura yana nan tsaye inda yake sai dariya yake. Muna cikin gudu ba zato ba tsammani sai ga wani hayaki ya bayyana a gabanmu, da faruwar haka wata budurwa ta fito daga cikin hayakin ita kanta mummuna ce ta gaban kwatance wacce in ka kalleta sau daya ba zaka so ka sake karawa ba, saboda yanayin tsoro.

 

 

Wannan budurwa tayi nuni da hannuta masu zankala-zankalan farata zuwa ga Bukar, nan take wani iska da bamu san ko daga ina yake ba, ya kwashi Bukar sai gashi a gabanta a tsugunne. Ba shiri ya fara karkarwa yana ba wannan aljana hakuri, amma sai gani nayi ta daga kai sama tana wata irin mahaukaciyar dariya kafin daga bisani ta ce, “Kai fitsararre dama ka daina bata bakinka, domin kuwa yau kwanakinka a duniya sun kare, yau zan kasheka kamar yadda kuka hadu kuka kasheni a baya”. Ko da jin haka sai naji duk wani tsoro da firgici ya kaura daga zuciyata, nan take na dakawa wannan budurwar tsawa hade da cewa, “Ke azzalumar shedaniya, karki kuskura ki aikata abinda kike kudirin aiwatarwa in ba haka ba kuwa yanzu zan konaki da ayar Allah, maza ki sake shi”. Bisa mamaki sai naga wannan yarinya ta sake kyalkyalewa da dariya a karo na biyu, kana ta juyo gareni tana muzurai da idanunta masu kama da na damisa. Zata fara magana kenan mu ka ga wani walkiya mai haske, ko da hasken walkiyar ya washe, sai ga wata doguwar tsohuwa mai farin gashi, itama dai kamar yaro da budurwar, sanye take da doguwar farar riga. Ga kuma auduga a hancinta da na rasa ko ta uban miye.

 

 

Cikin murya marar dadin saurari naji tana fadin, “Ke Surayya me kike jira da shi, maza ki aikashi lahira yau ce ranar daukar fansa da muke jira”. Daga fadin haka na ga wannan budurwa ta mika hannunta cikin iska, nan take wata wuka ta bayyana sai walkiya take, Bukar kuwa tuni fuskarsa ta cika da hawaye jini da majina, ko da ya ga ta daga wannan wuka sai ya fara yunkurin tashi domin ya tsere. A wannan lokaci ita kuma budurwar ta daga wukar sama zata fille masa kai, ni kuwa bansan lokacin da na fara karanta ayatul kursiyyu ba. Da faruwar haka naji su duka ukun sun fasa ihu sun zama hayaki sun bi iska. A daidai lokacin ne na fara jin sauti ana yi mun sallama sama-sama. A zabure na farka ina kallon mai yi mun sallamar, tun a cikin baccin dai naji muryar macece sai dai ko da na bude idona ina iya gane macece a tsayi nesa kadan daga inda nake a kwance, amma bana iya ganin fuskarta. Hannu na sa na share zufar dake ta tsatsafo min a fuska, wanda nasan bai wuce mummunar mafarkin da nayi bane dalilin fitarta. Wayata na zaro daga aljihu domin da ita na kwanta, na haska domin ganin fuskar mai yi mun sallama bayan na amsa mata. Suman zaune nayi, ga dukkan alama a dai-dai lokacin jinin jikina ya tsaya ya daina aiki na ‘yan dakiku………

 

 

Zan cigaba

Back to top button