Uncategorized

Yadda Za’a Magance Ciwon Sanyi (Infection) Da Tafarnuwa

Yadda Za’a Magance Ciwon Sanyi (Infection) Da Tafarnuwa:

Yar uwa shin kinsan amfani da maganin da tafarnuwa yake yi a jikin mace kuwa??

Duk ‘ya mace tana bukatar sanin wannan domin yana da mutukar amfani. Bincike ya nuna cewa mata dayawa suna fama da ciwon sanyi (infection), kaikayin gaba da kuma warin gaba. Shiyasa hakan yake hana su sukuni kuma suke neme nemen magunguna ko sabulai (vaginal wash) domin kawar da wannan ciwon ko warin gaban.

Meke Kawo Ciwon Sanyi Ga Mace Akwai dalilai masu yawa da ke kawo wa mace ciwon sanyi amma ga kadan daga cikinsu:

🧄 Mata masu biye biyen maza. Anfi yada ciwon ta hanyar jima’i don haka mace ko namiji zasu iya harbin wadanda bai dashi Cushe cushe da shafe shafen magunguna da mata sukeyi da sunan matsi ko karin ni’ima na iya kawo musu kurarraje (rashes), kaikayi (itches), da warin gaba wanda zai rikede ya zama ciwon sanyi.

Karanta>>> Mene ne Ciwon Sanyi 

Karanta>>> Amfanin Dabino Guda 50 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Karanta>>> Amfanin Zogale 20 A Jikin Dan Adam

Amfanin Tafarnuwa:


🧄 Tafarnuwa tana daga cikin tsirrai mafiya amfani wadanda duniya ta dade tana amfani dasu. Shiyasa larabawa suke yawan amfani da ita.

🧄 Yana kashe duk wani infections (toilet infections etc)..

🧄 Yana cire warin gaba.:

🧄 Yana maganin ciwuwwuka da dama.

🧄 Masu ciki na amfani dashi kafin cikin ya tsufa.

🧄 Yana qara ni’ima kuma babbar jagorace wajen samun karfin jima’i da dadewa.

 🧄. Zaki iya amfani dashi lokacin al’ada yayin da jini ya ke daukewa ko yanai miki wasa.

Ze yi protecting dinki against all kinds of infection.

Maganin ciwon sanyi da ke addabar mata (musamman me sanya warin gaba, fitar farin Ruwa da kurajen gaba)

Yadda Zaki Hada Maganin Ciwon Sanyi Da Tafarnuwa:

Ki samu tafarnuwa ki daka ta ki ciri ruwn jikinta ki zubar da tukan. sai ki dibi ruwan tafarnuwan kadan ki goga a jikin pad (abinda kike sawa in kina al’ada). Sai ki kawo man zaitun shima ki diga sai ki saka a jikinki ki cigaba da harkokinki.

Bayan kin saka zaki ji zafi amma ki bari kar ki cire. Anfi so kiyi idan za ki kwanta bacci da safe sai ki cire don yafi shiga jiki. Ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba, sai ya huce sai ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwanakin da zaki ji kin daina jin kaikayi ko hamamin warin gaban. Allah ya taimaka.

Back to top button