Uncategorized

Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini

 

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

BOOK 2

Part (A)

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi

Lokacin da takobin Shumaira ta isa kirjin sarauniya larbisa sai ta dan soketa a kirji, tana kokarin danna takobin a cikin kirjin nata kafin larbisa tayi kara sai shumaira taji an daka mata tsawa daga baya bisa dole ta fasa dannan takobin izuwa cikin kirjin larbisa, ta mike tsaye daga kanta ta waigo tayi arba da wanda yayi mata tsawar, ba wani bane face mahaifinta mafarauci imshal.

.

Mafarauci Imshal ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai sai dai girma ya kamashi sosai domin shekarunsa zasu kai kusan arba in gaba daya gashin kansa sajensa da gemunsa duk farin gashine, yana rike da wata doguwar sanda a hannunsa ya rataya kwari da baka a bayansa rigarsa, wandonsa da takalminsa dake kafarsa duk anyi sune da fatar damisa.

.

Koda jaruma shumaira ta hango mahaifinta Imshal sai ta rugo izuwa gareshi ta dukar daki tana mai nuna girmamawa a gareshi, A wannan lokaci ne sarauniya larbisa ta mike tsaye tana mai dafe gefen kirjinta inda

shumaira ta soka mata takobi don har dan jini ya fito kawai sai sarauniya larbisa ta sunkuya cikin biyayya ta gaisheda tsoho Imshal. Imshal ya karbi gaisuwar yana mai kare mata kallo sama da kasa sannan ya karewa dakarunta kallo ya dubi shumaira yace akan wani dalili kike yaki da wannan mace mai daraja? Shin bakya ganin alamar cewa mai mulki ce.

.

Koda jin wannan tambaya sai shumaira ta dago kai ta dubi imshal ta ce yakai abbana kayi sani cewa haka kawai wannan sarauniya tare da dakarunta suka shigo cikin dajin nan suka dasawa dabbobinmu wawa, bisa wannan daliline na tarwatsa dakarun nata kuma na umarcesu da su fice daga cikin dajin nan tun kafin fishinmu ya tabbata a kansu amma saboda naci sai wannan sarauniya ta biyoni har cikin garken dabbobi, ni ina ganin cewa kawai ka kyaleni na gama da ita yanzu domin da ita da yaran nata su gane cewa ruwa ba sa an kwando bane kuma bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane.

.

koda jin wannan batu sai tsoho imshal ya bushe da dariya sannan ya hade fuska ya dubi shumaira yace ai ruwa baya tsami banza, shin a farkon bayaninta gareki bata gaya miki cewar tana da wata bukata ba a wajanki?

.

Cikin alamun sanyin jiki shumaira tace ta gaya mini cewar tana da wata bukata a wajena amma saina gaya mata cewar bata da abinda zata iya biyana da shi don haka babu abinda zan iya yi mata koda jin wannan batu sai imshal ya gyada kai yace yarinya kinyi hanzarin yanke hukunci shin bakya tunanin cewa bukatar da tazo mana da ita wata kila a sanadinta ne muma zamu fita bakin cikin da ya addabemu tsawon shekaru bakwai.. Shin kin manta ne cewar na gaya miki zamu iya nasarar samun abinda muke nema a cikin wannan shekara idan kin hadu da wadansu bakin jarumai guda uku?

.

Koda jin wannan batu sai jikin shumaira yayi sanyi ta sunkui da kanta kas ta kasa cewa komai daga can kuma sai ta dago kai da sauri ta dubi tsoho imshal tace amma ai wannan sarauniya ba ta da kama ko siffa irin ta mutane ukun dakayi mini bayani imshal yace hakane amma dai ki tsaya muji abinda ya kawota wajanmu babu mamaki a sanadin hakan a samu dacewa cikin nutsuwa tsoho Imshal ya dubi sarauniya Larbisa yace yake wannan sarauniya ma abociya kyawu da karjini wace bukata ce dake tasa har kikayi tattaki kikazo har wannan daji namu?

.

Kafin larbisa ta budi baki tace wani abu sai tsoho Imshal ya kara tarar numfashinta yace amma kafin kice komai ya kamata ku fara yiwa raunikan jikinku magani yana gama fadin hakan sai ya bude wata jaka dake rataye a bayansa ya dauko wani farin magani me maiko da kauri kamar daskararren nonon shanu ya mikawa yarsa shumaira yace ungo ki shafa a rauninki kuma ki shafawa bakuwar tamu cikin alamun damuwa shumaira ta karbi maganin ta fara shafawa kanta sannan taje ta zauna a gaban larbisa ta kama shafa mata fuskarta a daure babu annuri, su kuwa su sadauki Humaisu sai hankalinsu ya kwanta sukayi murna da ganin yadda tsoho Imshal ya karbesu hannu biyu, bayan shumaira ta gama sawa larbisa magani a rauninta sai tsoho Imshal ya dubi larbisa yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa ni yanzu na karbeku keda jama arki a matsayin bakina saboda haka yanzu zan kaiku zuwa gidana domin ku huta in yaso bayan kun nutsu saimu zauna mu tattauna mu dake idan har zamu iya taimakon juna zamu iya yarda da buqatarki, idan kuma ke

kadaice zaki amfana damu to sai dai muyi miki fatan samun nasara ki kara gaba, koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarauniya larbisa, ta dubi Tsoho Imshal cikin murmushi tace nayi farin ciki da wannan tayi da ka bani ya kai Abul Shumaira kuma zuciyata ta bani cewa nima zan iya baku taimako bisa taku bukatar.

.

Tsoho Imshal yayi murmushi yace sai an gwada Sannan ake sanin na kwarai yana gama fadin hakan sai ya kama hannun shumaira suka nufi bayan wani katon dutse yana mai yafito su larbisaa, Da hannu cikin hanzari larbisa taje ta kama dokinta ta hau tabi su.

.

Tsoho Huzallatul marwas ne ya fara bin bayanta sannan sadauki Humaisu da sauran Dakaru. Ana zagayawa bayan wannan katon dutse sai kowa ya cika da mamaki bisa ganin wani dankareren gida wanda aka ginashi da duwatsun wuta Gidan katone kuma anyi masa fasali na gidan sarauta dauke da bangare bangare, banbancinsu da gidan sarauta kawai shine babu bayi, dakaru da kuyangi mutum daya kacal suka gani a cikin wannan gida kuma ba wani bane face larisa mahaifiyar Jaruma shumaira

lokacin da larisa ta hango mijinta imshal da yarta shumaira tare da bakin mutane sai tsoro ya baibayeta domin wannan shine karon farko a iya zamansu a cikin wannan daji da ta ga sun zo mata da mutane har gida don haka bata yarda ta bude kofar gidan ba sun shigo har sai da suka matso kusa taga cewar babu wata alamar damuwa akan fuskar mijinta da ‘yarta Ita kanta larisa shekarunta sun kai hamsin da biyu koda uku amma saboda tsananin kyawun jikin da Allah ya bata mutum ba zai taba zaton ta kai hakan ba.

.

Da isowarsu tsoho Imshal ga larisa sai ya gabatar da sarauniya Larbisa a gareta sannan ya gaya mata cewa ita da jama arta bakine masu mahimmanci, cikin farin ciki larisa ta karbi sarauniya larbisa tana maiyi mata barka da zuwa, nan take aka kaisu sadauki Humaisu izuwa wani bangare daban na gidan ita kuma larbisa sai tabi jaruma shumaira izuwa dakinta.

.

Cikin hanzari shumaira ta dafa ruwan dumi ta kaiwa larbisa kewaye ta shiga wanka kafin larbisa ta fito daga wankan tuni shumaira ta shirya musu abinci. Larbisa na fitowa daga wankan sai itama shumaira ta shiga wankan sai da ta fito daga wankan sannan suka zauna tare bisa wasu kujeru dake karkashin wani tebur suka fara cin abincin, tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffab ba.

.

Abinda ya daurewa shumaira kai shine ganin yadda larbisa ta saki jiki take ta cin abincin Alhalin ba abinci ne mai dadi ba irin nasu na sarakai Abincine irin wanda kowane talaka zai iya ci musamman mazauna daji cikin matukar mamaki shumaira ta dubi sarauniya larbisa tace yake wannan sarauniya menene dalilin da yasa kika saki jiki kike ta cin irin wannan abinci namu na talakawa alhalin nasan a guzurinki akwai irin naki abincin da kika taho dashi?

.

Koda jin wannan tambaya sai sarauniya tayi murmushi tace ai dokar bakunta itace yin koyi da irin mutanen da ka riska, ni kaina nayi mamakin yadda akayi naji ina matukar jin dadin wannan abinci naku amma fa babu abinda ya bani mamaki a yanzu sama dake, koda jin haka sai shumaira ta dago kai da sauri ta dubi larbisa cikin mamaki tace ke kuma me nayi wanda ya baki mamaki? Larbisa ta ajiye cokalin da take cin abinci gami da yin ajiyar numfashi sannan tace gani nayi da farko baki karbeni da wata daraja ba har ma yakata kikayi kikauda batun matsayina na sarauta yanzu kuma sai gashi kina yin biyayya da hidima a gareni.

.

Yayin da shumaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai nima nayi amfani da maganar manya da suke cewa idan babba ya rike girmansa dole ne karami yayi masa biyayya. Lokacin da kika shigo cikin wannan daji namu ke da jama arki baki hanasu kokarin yi mana sata ba dalilin da ya sa na ki karbar bakuncinki kenan tun da farko amma yanzu dana gane cewar wata kila kina da mahimmanci ga rayuwata shi yasa nake yi miki ladabi da biyayya larbisa ta bushe da dariya sannan tace ai kowane mutum yana da rana komai kaskancinsa shin zaki iya gaya mini babban burinku na duniya keda mahaifinki wanda har kuke tunanin zan iya taimaka muku a kansa?

.

Sa adda shumaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace me kikeci

na baka na zuba ehm wato ( what are you eating na baka is falling down )

zakiji amsar wannan tambaya taki idan mukayi zama na musamman mu dake kuma a sannan ne muma zamuji taku bukatar a wajanmu, kodajin

wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace tabbas zancenki dutse ne, haka dai shumaira da larbisa suka ci gaba da hira har suka gama cin abincin kuma dare ya raba sannan suka kwanta sukayi barci, .

.

Kamar yadda aka karrama sarauniya larbisa hakama aka karrama sadauki humaisu da dukkan dakarunsa suka ci suka sha sukayi hani’an kuma suka kwanta a masauki mai kyau, Al amarin da yayi matukar daure musu kai kenan suka cika da tsananin mamakin yadda wadannan mafarauta suka tara arziki mai yawa haka.

+++±+++++++

Kashe gari da safe bayan sarauniya larbisa ta yi wanka ta kimtsa sai ta ga shumaira bata kawo musu abincin kalaci ba kawai ta zauna tana jiranta ta gama kimtsawa tana gama kimtsawa kuwa sai shumaira ta mike tsaye ta dubeta tace iyayena suna jiranmu acan turakarsu domin muyi mude baki tare dasu kuma mu sami damar tattaunawa akan abubuwan da muka sa a gaba koda jin haka sai sarauniya larbisa ta mike da sauri cikin murna ta bi shumaira a baya suka fice daga cikin dakin suka nufi hanyar da zata kaisu bangaren da iyayen shumaira suke, sai da sukayi yar tafiya mai dan tsawo kadan sannan suka iso wani babban falo mai dauke da Wani faffadan tebu A karkashin teburin kujerune guda biyar

tsoho Imshal tare da matarsa larisa na zaune akan kujeru biyu ga abinci nan wajen kala uku akan teburin dake gabansu, da isowar shumaira da larbisa sai tsoho imshal da larisa suka mike tsaye suna musu girmama sarauniya larbisa gami dayi mata barka da isowa nan take larbisa da shumaira suka janyo kujeru daga cikin karkashin teburin suka zauna aka fara cin abincin.

.

Tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffan ba daga can sai tsoho Imshal yayi gyaran murya yace yake wannan sarauniya mai daraja yanzu saiki gaya mana abin da ya kawoki garemu kafin muma mu

gaya miki bukatar da muke da ita a wajanki.

.

Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi sannan tayi gyaran murya tace ba wani abu bane ya sa na baro kasata ba mulkina da jama ata face don na riski kogon Kitabul sihir inda littafin TSATSUBA yake, littafin da shine kadai zai cika mini babban burina na duniya na samun damar yin aure gami da samun magaji kuma na mallaki komai da kowa dake cikin wannan duniya ba zan iya isa inda kogin yake ba face na ratsa ta cikin dazuzzuka guda uku;

.

Daji na farko shine ake kira da Shajarul Shaljuma wanda ke dauke da mugayen  dabbobi da mugayen tsuntsaye. Bokaye sun tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki wanda zai iya wucewa dani ta cikin wannan daji a raye face wannan ya taku shumaira daga nan ne zamu wuce izuwa dajin Ujurul Majnun bisa jagorancin Jaruma Larifat, daji na uku kuwa wanda ake kira darul maut zamu shigeshine bisa jagorancin jaruma Lubaina muna wuce wadannan dazuzzuka sai kuma mu tunkari dajin da kogon Kitabil sihir yake shi kuwa kogon babu mai iya yi mana jagora izuwa cikinsa face jarumi Ruhaisu dan sarki Zaiyanu na birnin kufa. A cikin kogon kitabul sihir ne zan iya dauko littafin TSATSUBA domin na lalata duk sihirin tsafin dake cikinsa don na sami damar yin aure na sami da ko yar da zata gajeni idan ban lalata sihirin dake cikin wannan littafi ba na tsatsuba har abada burina ba zai cikaba.

.

Koda sarauniya larbisa tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal ya tuntsire da dariya Al amarin da ya baiwa larbisa dasu shumaira mamaki kenan daga can kuma sai Tsoho Imshal ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa..

.

Nan fa sarauniya Larbisa ta kara cika da tsananin mamaki ta dubi tsoho Imshal tace yakai Abul Shumaira ina dalilin yin dariyarka gami da zubar hawayenka a bisa

abinda kaji na fada??…

.

Ni nima zan dakata ana sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ji abin da tsoho Imshal sai fada a huta lafiya.

TSATSUBA

BOOK 2

Part (B)

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.

Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa ba wani abu bane ya sakikaga na bushe da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa kanki gagarumin aikin da sai kinyi nadamar yinsa domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara a kansa, sannan kuma zaki iya shan bakar wahala da bata da misali kuma dake da duk abikan tafiyar taku zaku iya rasa rayuwarku ko lafiyarku. Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a taɓa samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye

ba don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce ta gaji da rayuwar duniya take neman mutuwa ruwa a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !!

.

Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine biwa wannan TAFARKI da kike son bine na rasa iyayena da kakannina domin suma sun bar gida sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin magance wata matsala data addabi gaba daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa amma dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin gaba namu mafarauci ne kuma takadarin boka ne tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai wannan

boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin gari shi da iyalinsa yaji kamar ana konashi da wuta. Matansa da ‘ya’yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji ya zamana cewa ba shiri suka hada nasu ‘i’ nasu suka koma cikin daji da zama bisa dole kakan namu ya hakura da sarautar sarkin daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan zuri armu sai suka tsani cikin gari daga wannan rana kawo iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu wanda ke rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya tsawon rabin sa a sai dai muyi siyayya a kasuwa mu fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman yadda zamu karya wannan sihiri amma abu ya gagara kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba zamu taba iya samun nasarar karya wannan sihiri ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta wata kalmar tsafi guda daya wadda ke shafin tsakiya, yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan iya barin yata shumaira tayi wannan tafiya ba tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude kenan tunda mu ne kadai mukayi saura kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu a lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi sani cewa ko ka barni ko ka hanani yin wannan tafiya watarana sai mutuwa ta daukeni shin ka manta cewar ka gaya mini cewa dukkan mai nema yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu abin tarihin da baza a taba mancewa dashi ba ka tuna cewa har yanzu sarautar sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka zarratu tunda mu mun kasa zama a cikin gari lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu na dawo mana da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin wannan gidan sarauta namu na sarkin daji wanda kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan dama ayi wannan tafiya dani da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara na kwato mana yancinmu.

.

koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal da matarsa larisa suka kamu da tsananin tausayinta suka rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama saita tayasu kukan.

.

Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin wani ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane ya janyo hakan ba face  ganin matsalar ta tazo iri daya da tasu.

.

Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame da shumaira sannan imshan ya janye jikinsa daga cikin na shumaira ya dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake yata hakika kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba zan iya yanke hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya larbisa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin cewa tsoho Imshal ba zai yarda da wannan tafiya ba don haka duk shirinta ya rushe.

.

Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin falon duk su biyun jikinsu a sanyaye, lokacin da dare ya sakeyi sai shumaira da sarauniya larbisa suka kasa barci saboda zulumi da fargabar sakamakon shawarar da iyayen shumaira zasu yanke akan wannan tafiya suna cikin wannan hali ne shumaira ta mike zaune daga kan gadonta ta dubi larbisa tace ranki ya dade ni fa tunda ina cikin zulumin abinda zai biyo baya ba zan iya barci ba, ina mai tabbatar miki da cewar rayuwata gaba daya yanzu babu wani abu da ya shiga raina sama da yin wannan tafiya koda kuwa ina da yakinin zan mutu nafi son na mutu jaruma akan na mutu raguwa a cikin rashin yanke wannan bakin ciki na zuri armu saboda haka yanzu zanje na gana da mahaifina domin naji hukuncin da ya yanke koda gama fadin hakan sai shumaira ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ita kuwa sarauniya larbisa saita bita da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa, jikinta na tsuma zuciyarta na dukan uku uku tana fargabar abinda zaije ya dawo lokacin da shumaira ta isa falon mahaifinta saita iske mahaifiyarta zaune akan kujera tayi tagumi kanta a sunkuye tana zubar da hawaye shi kuwa tsoho Imshal yana tsaye yana kai kawo duk su biyun fuskokinsu na nuna alamun tsananin damuwa da fargaba.

.

Koda shumaira taga iyayenta a cikin wannan hali sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji kamar ba zata iya tunkararsu da maganar ba tunda su ma suna cikin irin halin da take ciki kawai sai shumaira ta juya da nufin ta koma izuwa dakinta.take tsoho Imshal ya kira sunanta shumaira , kada ki koma kizo mu tattauna wata muhimmiyar magana koda shumaira ta juyo tana mai amsa kiransa saita ga fuskar tsoho Imshal ta juye izuwa murmushi da annuri cikin mamaki shumaira ta tunkari mahaifin nata ta iso daf dashi yadda har suna iya jin numfashin juna tsoho Imshal ya dafa kafadar shumaira yace, yake yata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa ba zan iya hanaki yin wannan tafiya ba saboda ganin muhimmancinta.

.

Amma akwai sharadi guda daya da zamuyi dake wannan sharadi kuwa shine ba zamu yarda kiyi wannan tafiya ke kadai ba sai tare damu koda jin wannan sharadi sai idanun shumaira suka zazzaro hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubeshi tace haba yakai Abbana tayaya zanyi wannan tafiya tare daku alhalin girma ya kamaku baku da karfin jiki gami da jarumtaka irin tawa koda jin wannan batu sai tsoho Imshal ya sake yin

murmushi a karo na biyu yace Ashe kin manta da cewar nine na koya miki yadda ake farauta a cikin daji da yadda ake yin yaki a cikin dandazon mayaka??

.

To kiyi sani cewa ko giwa ta fadi tafi gaban a dasa mata wawa malami har abada malami ne akan dalibansa ina mai tabbatar miki da cewa ni da mahaifiyarki zamu baku gagarumar gudumawa a cikin wannan tafiya yadda zaku sha dumbin mamaki saboda haka ki koma dakinki ki gayawa sarauniya larbisa cewar ku fara shirin wannan tafiya tun a daren yau amma ina son ta turo mini babban abokin tafiyarta tsoho Huzallatul marwas yanzu take kuma ta gaya masa cewa ya taho tare da jakar sihirinsa shumaira ta juyo jikinta a sanyaye ta koma izuwa can turakarta zuciyarta cike da zulumi. Fargaba da tsananin damuwa lokacin da shumaira ta isar da wannan sakon mahaifinta izuwa ga sarauniya larbisa ta firgita kuma ta kamu da tsananin mamakin yadda akayi tsoho Imshal ya san da batun jakarsa ta sihiri alhalin bata gabatar dashi ba a wajansam nan take larbisa ta gano cewar lallai shi ma tsoho Imshal ya cika boka masanin abinda ke boye ba tare da boye komai ba sarauniya ta tashi ta tafi izuwa masaukinsu tsoho huzallatul marwas ta jashi izuwa gefe daya ta sanar dashi sakon tsoho Imshan, koda jin hakan sai huzallatul marwas ya bushe da dariya.

.

Al amarin da ya baiwa larbisa mamaki kenan kuma ranta ya baci ta dubeshi a fusace tace menene kuma abin dariya a cikin wannan Al amari?? 

.

Huzallatul marwas ya numfasa yace hakika mahaifim shumaira ya cika hatsabibin boka domin ban taba zaton zai gano da batuna ba a cikin wannan tawaga taki bare ma har ya san da batun jakar sihirinsa babu komai ki kwantar da hankalinki yanzu jamuje na riskeshi domin naji dalilin da yasa ya bukaci ganina, koda gama fadin hakan sai tsoho huzallatul marwas ya yunkura da nufin ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar tsoho Imshal yake. Tsulum sai suka ga aljani subauratu ya baiyana a sama daf da fuskarsa yana mai kyalkyala dariya lokaci guda kuma sai ya hade fuskarsa ya risina ga huzallatul marwas yace ya shugabana kayi sani cewa zuwanka kai kadai izuwa ga tsoho Imshal yana da hadari don haka duk yadda za ayi ka tafi tare da sarauniyarka komai rintsi da tsanani kada ka yadda kayi wata magana dashi sai sarauniya na kusa tana sauraronka, kafin tsoho Huzallatul marwas ya budi baki ya tambayi subauratu dalilin da yasa ya bashi wannan shawara tuni subauratu ya bace bat, sai jin motsinsa yayi a cikin jakarsa ta sihiri Huzallatul marwas ya dubi larbisa yace ranki ya dade menene abinyi?

.

 Larbisa tayi murmushi tace yadda Aljani subauratu ya fada haka za ayi, nan take suka dunguma su biyun suka koma can turakar tsoho Imshal inda suka iskeshi tare da yarsa shumaira da matarsa larisa a zaune koda Isham yaga larbisa ta biyo tsoho huzallatul marwas sun dawo tare sai ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi larbisa yace ai sai ku bamu wuri don ina son na gana da huzallatul marwasu koda jin haka sai huzallatul marwas ya matso gaban Isham ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace yana daga cikin sharaddan tafiyarmu nida sarauniya cewar komai tare da ita zanyi, ba zan boye mata komai ba koda jin wannan batu sai jikin tsoho Isham yayi sanyi kawai sai ya kyalkyale da dariya ya rungume huzallatul marwas yana mai cewa lale marhaban da babban aboki ma abocin hikima da hangen nesa shi kenan kuje ku kwanta domin ku dan rintsa kafin gari ya waye mu kama hanya dajin haka sai larbisa da tsoho Huzallatul marwas marwas suka dubi junansu suka yi murmushi nan take suka yiwa su tsoho isham sallama suka juya suka fice daga cikin falon, fitarsu keda wuya sai jaruma shumaira ta dubi isham fuskarta cike da alamun tsananin damuwa tace ya kai abbana yanzu ta yaya kenan zamu san shafin  da ya kamata mu karanta a cikin littafin tsatsuba domin kawai da wannan matsala tamu tunda gashi sarauniya larbisa taki yarda ta barka ka kebe da tsoho huzallatul marwas bare har kuyi wannan yarjejeniya damu ka tsara?

.

Koda jin wannan batu sai tsoho isham ya bushe da dariya yace ai maso abinka ya fika dabara kuma masu iya magana sunce samu yafi iyawam idan har muka mallaki littafin tsatsuba a hannunmu munyi mai wuyar da sannu zamu gano duk wani sirri dake cikinsa da jin wannan batu sai hankalin jaruma shumaira ya kwanta zuciyarta ta cika makil da farin ciki amma da ta tuno irin mugun hadarin dake cikin tafiyar da zasuyi kuma gashi tare da iyayen nata za ayi wannan tafiya sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda yake yi mata dadi haka dai ta yiwa iyayen nata sallama cikin sanyin jiki ta tafi izuwa turakarta kashegari kuwa tun kafin Alfijir ya keto kowa ya gama shirin tafiya nan take aka hau dawakai aka kama hanya aka nausa cikin daji tsoho huzallatul marwas, sarauniya larbisa da sadauki humaisu ne akan gaba jaruma shumaira da iyayenta kuwa sune a karshe domin dakarun larbisa ma suna gabanta bayan an shafe sa a guda ana tafiya sai tsoho huzallatul marwas ya dubi sarauniya larbisa a lokacin da suke tafiya kafada da kafada bisa dawakansu yace ya shugabata kiyi sani cewa ruwa baya tsami banza lallai akwai wata hujja mai karfi wacce tasa iyayen shumaira suka siyar da rayuwarsu wajen biyomu a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske. Yayinda sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a jeba

.

Kamar yadda sannu sannu ba zata hana AlQuyraemey xan ci gaba da rubuta muku wannan littafi saidai a jima ba ajeba..A nan nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe dominmjin Yadda zata kaya a cikin wannan Littafi Na tsatsuba

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

BOOK 2C

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.

Yayin da sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul marwas ya gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka dosa ne?

.

Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda abinki ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni kaina ina bin jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan nake bi damu. Amma ai idan baki manta ba zamuje neman jaruma larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin daji na biyu wanda shine dajin Ujurul majnun ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba zamu dauki wani dogon lokaci ba muna tafiyar zamu riske ta bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa.

.

Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara cewa komai ba haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango face gajiya ko yunwa da kishirwa, har tsawon kwana uku sannan suka iso wani babban birni mai kyau gaske wanda aka kawatashi da gine gine masu kyau da kawa ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma tana cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi hakama abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za a taba samun birnin da

yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya amma sai gashi tun kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba haka

bane.

.

Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka hango tawagar sarauniya larbisa sukaga alamar cewar manyan mutane ne masu daraja sai suka bude musu kofada sauri har daya daga cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma shumaira ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai shin mu yanzu menene yashigo damu cikin wannan gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma ga yadda aka bayar da labarinta ba zata yi rayuwa ba a cikin gari sai dai a daji?

.

Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace ai da dan gari akanci gari, yanzu idan muka ce zamu tafi neman jaruma larifat bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda take wata kilama mu sami karin haske akan yadda zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci wata matsala ba. koda shumaira taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba…

.

Fada ce kasaitacciya abar kwatance domin lokacin da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin fadar sai gaba dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar yan kauye saboda ganin irin kyan fadar da kawatuwarta.

.

A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta Ita dai a iya saninta a can nahiyoyin dake bangarenta babu wata kasa mai girma da karfin Arziki kamar kasarta don haka sai ta fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a taba samun kamarta ba amma a yanzu da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da wannan bakuwar fada sai ta karyata kanta, wani kyakkyawan saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin wannan fada  ya yi babbar shiga ta alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka gawurta ne kadai ke iya yinta domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da kwagirin dake hannunsa na lu’u lu’u ne a yatsun hannayensa na hagu da dama akwai zobuna guda shida kuma duk na zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin dake kansa da falmaran din dake jikinsa da zaren zinare a aka dinkasu.

.

Koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da kwarjininsa ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da tsananin sonsa. Hakika babu wata ‘ya mace da zata ga wannan sarki bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda baiwar da allah yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne koda shigowar su sarauniya larbisa cikin fadar sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska kuma babu annuri akan fuskar tasa, Al amarin da ya dugunzuma hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu bare kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin sanyin jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi cirki cirko caraf sai tsoho isham ya zube kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya larbisa da jaruma shumaira ya kara da cewa yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba wani abu bane ya kawomu birninka ba face neman jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa saboda muna son tayi mana rakiya izuwa dajin ujurul majnun domin biyan wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa.

.

Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa cike da annuri ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye

ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su sarauniya larbisa ma sai  yasa aka basu kujeru na alfarma suka zauna sannan aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka kama kimtsa cikinsu suna masu murna da mamakin yadda akayi nan da nan ra’ayin sarkin ya sauya bisa jin abindake tafe dasu sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa sosai, sannan kyakkyawan sarkin ya dubi tsoho isham yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau shekara bakwai kenan ina fama da tsananin so da begen wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata taba kallona ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau bakwai sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma bata taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba yi mini magana ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa wannan gidan sarauta ba.

.

Lokacin da na dameta da aika manzanni da kyaututtuka iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda nake bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini dasu gami da wasika.

.

A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina bata lokaci na da tunanina a kanta domin ta daukarwa kanta alkawari cewar ba zata taba yin aure ba ko soyayya har sai tayi gagarumin abin gwanintar da wani bai taba yi ba a duniya lokacin da naji wannan batu sai na kamu da tsananin bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici domin banga ranar da larifat zata cika wannan buri ba daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a wuri mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni har izuwa karshen rayuwata face a ranar da naji cewar ta sami damar da zata cika burinta.

.

A tsawon shekaru bakwai da suka gabata wannan dama bata samu ba sai yanzu naji kunzo mini da wannan batun na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba yake sai naji a jikina cewar lokacin samun yardar larifat yayi a gareni

domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har abada ba za a mance da ita ba a duniya, ko shakka babu na san cewa larifat zata karbi wannan tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani abu mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu wanda zaku iya biyanta da shi domin ta wuce daku ta cikin dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta burin ba wani abu da yake burge jaruma larifat a cikin wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan uwanta da dukkan danginta bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin mutane ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta karasa sauran rayuwarta gaba daya yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku masauki ku huta washe gari da safe ni da kaina zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat take domin ku gana da ita, ku sanar da ita bukatar dakuka zo da ita a gareta. Amma ina neman wata alfarma guda daya a wajanku? Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku rakiya a cikin wannan tafiya domin idan kuka tafi kuka barni fargaba tunani da begen halin da larifat ke ciki zai iya jefani cikin wani mugun hali.

.

Koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa sai kowa ya cika da mamaki musamman sarauniya larbisa da shumaira. Sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin mamaki tace yakai wannan sarki mai daraja kayi duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi girman kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka sani cewa akwai mata da yawa masu kyau a sassan duniya wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka da mulkinka saboda me yanzu zaka siyar da rayuwarka don baiwarka?

.

Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan tambaya daga bakin sarauniya larbisa sai ya bushe da dariya kamar ba zai daina ba daga bisani kuma sai ya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a cikinta kawai sai aka ga idanun sarki ayubul hasnu sun ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki ayubul hasnu ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya babu wani abu wanda yafi soyayya karfi da hadari masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan tafarkin mallakar masoyansu ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar da babu masoyi dai dai take da zama a cikin kurkukun daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma shumaira duk kun kasance kyawawan matan da babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da nahiyarmu amma kuma baku kama farcen kafar jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan a yanzu babu wata ya mace da zata iya maye gurbin larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren jarumta kuwa ina mai tabbatar muku da cewa in daku biyun nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba samun galaba a kanta ba koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka bushe da dariya domin su a ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul hasnu yake fadi shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda masana da masu bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin damtsensa da sa arsa idan muka hada karfi nida larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma larifat wacce ta kasance ‘ya mace kamarmu yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai shi kenan inda babu kasa nan ake gardama Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku duk abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI. Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi sarki Ayubul hasnu tace wanene kuma sadauki Hulkas mai hular lamsara?

.

Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon numfashi sannan yace labari ne mai tsawon gaske sai dai nayi iya kokarina na gani ko zan iya gajarce muku shi…

.

SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN JARUMAN DUNIYA GUDA UKU wadanda akayi musu lakabi da MAZAN JIYA jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba kuma ba za ayi ba a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin da ba za a taba mancewa dasu ba sai dai kash! Duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a tafarkin soyayya. Yanzu dai saiku saurara da kyau kuji wannan labari domin akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki AYUBUL HASNU ya shiga basu labari kamar haka……

.

Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan gadan a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai Hulkas mai hular lamsara kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya saboda haka sai ku gyara zamanku Amma fa sai gobe idan Allah mai kowa da komai ya kaimu.

TSATSUBA

BOOK 2

PART (D)

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.

Nan take sarki Ayubul Hasnu ya shiga basu labari kamar haka ”kimanin shekaru Ashirin da hudu da suka shude a birnin Romaniya anyi wani azzalumin sarki mai suna SHARDAS IBN KAUMIL sarki shardas ya kasance gawurtaccen jarumin sadauki mai tarwatsa maza a filin daga yana da tsananin karfin damtse na Allah ya isa don ance ko giwa ya yiwa naushi daya saita fadi kasa kisan kai kwace da cin zali kuwa bai maidasu komai ba.

.

A cikin wata daya yakan shirya dakarun sumame su kai mamayar bazato izuwa ga ayarin fatake ko izuwa ga manyan garuruwan da suke da karfin arziki cikin bad da kama su kwato bayi da dukiya da mata ba tare da an shaida ko su waye ba, a bisa wannan halaiya ne ya addabi gaba dayan kasashen dake nahiyar gaba daya kuma gashi an kasa gano mutanen dake yin wannan barna, babu irin matakin da sarakuna basu dauka ba kuma babu irin binciken da bokaye basuyi ba don gano rundunar dakarun dake wannan mummunar barna amma abu ya gagara babban abin bakin cikin ma shine sarki shardas ya tara dukiya mai tsananin yawan da jikokinsa ma da tattabakunnansa ma ba zasu iya cinyeta ba amma duk da haka bai daina yin wannan fashi da kwace ba.

.

Masana da masu bincike na wannan zamani sun tabbatar da cewar duk duniya babu wani sarki da ya kai sarki shardas tarin dukiya kuma babu wani gidan sarautar da yakai nashi girma da kawatuwa, duk bayin da ya kamo da mata ana boye sune a gidajen gonarsa da wani bangaren daban na gidan sarautar inda har abada ba za a sake ganinsu ba bare ma wani ya shaida dayansu asirinsa ya tonu a gane cewa shine dan fashin da ya addabi Mutane a nahiyar.

.

Tunda yake kamo Bayi da mata ba ataba samun wanda ya taba guduwa ba daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa face sarki shardas yasa anbi bayansa an kasheshi saboda tsananin tsoron da ake yiwa dakarun sarki shardas ne yasa aka musu lakabi da suna DAKARUN AJALI.

.

Wata rana sarki shardas tare dakarunsa kimanin mutum dubu uku sun fito mamayar bazato izuwa wani babban kauye da ke gefen wata makociyar kasa da ake kira salmas sai suka kai hari izuwa ga ayarin wadansu matafiya masu yawan gaske wadanda suka yada zango a gefen kauyennwanda ake kira Malgur.

.

Su dai wadannan matafiya suna da tarin shanu tumaki da raguna masu yawan gaske kuma Allah ya albarkacesu da kyawawan mata ababan kwatance ga kuma tarin zuri’a.

.

Al amarin ya faru ne da yammaci sakaliya daf da faduwar rana shugaban wannan ayari saurayi ne ma aboci kyau kwarjini da jarumtaka ana kiransa da suna Hailur, a wannan rana ne hailur yayi aurensa na farko a duniya kuma matar da ya aura budurwace yar shekara goma sha takwas a duniya wacce babu mai kyawunta a duk cikin zuri ar ayarin gaba daya.

.

A wannan lokaci wannan ayari sun shagala a cikin bikin auren hailu ana ta kade kade da raye raye saboda murna kowa da kowa ya zage yana ta rawa maza da mata yara da manya gaba daya dakarun ayarin dake tabbatar da tsaro sun ajiye makamansu sun shiga cikin taron ‘yan rawa suna cashewa kwatsam ba zato ba tsammani sai gani akayi dakarun Ajali sun bullo daga kowace kusurwa gabas da yamma kudu da arewa bisa dawakai aguje kuma sun zare makamai suna ihu da kururuwa nan fa taron biki ya watse mata, yara da tsofaffi suka kama ihu da guje.guje suna neman maboya, a dai dai wannan lokaci ango Hailur na tare da amaryarsa shadila a cikin tantinsa suna more amarcinsu kwatsam sai suka jiyo iface iface da guje gujen jama arsu a rude ango Hailur da amarya shadila suka mike tsaye zumbur daga kan shimfidarsu suka suri suturarsu suka sanya hailur yayi waje ya dauko takobinsa da garkuwarsa ya dubi shadila yace komai wuya komai rintsi kada ki fito daga cikin wannan tanti indai kika kiyaye wannan umarni nawa ni dake duk zamu tsira daga sharrin wadannan yan harin bazati kada ki kuskura kiyi ihu ko maganar da wani zai jiyoki shadila ta kada kai cikin alamun tsananin damuwa tace lallai zan kiyaye wannan umarni naka nan take hailur ya sumbaci goshin shadila sannan ya juya zai fice daga cikin tantin sai tayi wuf ta ruko hannunsa ta rungume shi tana mai fashewa da kuka ba komai ne ya sa tayi hakan ba face taji a jikinta cewar abune mawuyaci su sake ganin juna, ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba face ta dan leka wajan tantin daga tsananin yawan dakarun sumamen da suka kawo musu hari tasan cewa tabbas an shammaci nasu dakarun ba zasu iya kare kansu ba.

.

Cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin nata ya sake dubanta cikin yanayi mai nuna yarda dakai yace ki barni kamar yadda kika saba ni nasan dabarar da zanyi na kubutar da rayuwarki da tawa, shin kin manta ne da cewar irin wannan ta taba faruwa shekaru uku baya sa adda wata rundunar yan fashi suka ritsamu a daji mu biyu rak nidake muna kiwo?

.

Ko dajin wannan batu sai Shadila ta gyada kai cikin murmushin karfin hali tace haba ya masoyina ai ba zan taba mancewa da wannan gagarumar jarumtaka da kayi ba, koda jin haka sai fuskar hailur ta fadada da murmushi yace to wannan karon ma abinda zai faru kenan baya ga wannan ina mai yi miki wani babban albishir cikin matukar mamaki da zakuwa shadila ta zaro idanu tace wane irin albishir kuma zakayi mini yanzu?

.

Hailur yace boka zaifur ya gaya mini cewa a ranar farko dana sadu dake juna biyu zai shiga don haka yanzu ina mai tabbatar miki da cewa kina dauke da cikin dana kona mutu a wannan yaki bani da nadama ko takaici na san cewa na bar wanda zai kula dake.

.

Yayinda shadila taji wannan batu sai hawaye ya zubo mata tace lallai ina son ta kowanne hali ka rayu a wannan yaki kuma mu tsira tare domin babu abinda na tsana a wannan duniya sama da dana ya taso maraya. hailur yayi murmushi yace nayi miki alkawari cewar danki ba zai taso a maraicin rashin uba ba yana gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice da gudu daga cikin tantin. Ai kuwa yana fitowa yaga yadda ake ragargazar jama arsu ana saransu da sukarsu suna ihu jini na tsartuwa fallatsi da malala suna zama gawa sai ya fusata ainun ya kwarara uban ihu ya zare takobinsa daga cikin kufenta ya afkawa dakarun sumamen ya hausu da sara da suka ya zame musu guguwar annoba a wannan lokaci hankalin sarki shardas yana kan bayi mata da ake ta kamawa da kuma dukiyar da ake diba amma ko da yaji ihun dakarunsa ya yawaita a wani bangare daban sai ya juyo da sauri izuwa wajan take ya hango jarumi Hailur yanata ragargazar dakarunsa duk inda hailur yasa gabansa sai dai kaga maza na Zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona Al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan dimin tunda yake fita sumame da yaki bai taba ganin jarumi mai irin zafin naman hailur ba gami da tsagwaron jarumtakarsa duk da cewar a wannan lokaci dakarun sarki shardas sun kashe kaso takwas daga cikin kaso goma na jama ar jarumi hailur sai da ran sarki shardas ya baci ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fishi sarki shardas ya takarkare ya kwarara wani uban ihu wanda ya firgita komai da kowa dake cikin dajin aka daina yakin aka tsaya cak tamkar babu abu mai rai a wajen a lokacin da amon ihun sarki shardas ke tayin amsa kuwa a dajin gaba daya shi kansa jarumi hilairu sai da ya firgita bisa jin wannan kururuwa ya kura idanu izuwa sashin da kuwar ta fito da yake a sannan ne kurar yakin take lafawa sai da yan dakiku suka shude sannan ya hango sarki shardas ya tunkaroshi daga can nesa kadan take zuciyar jarumi hailur ta buga da karfi ya ji tsoro ya darsu a cikin ransa a karon farko a duk gwagwarmayar da yakeyi da mazaje a rayuwarsa bakomai ne ya haddasa hakan ba face a iya rayuwar jarumi hailur bai taba ganin mutum mai kirar sadaukai da kwarjininsa ba kamar sarki Shardas duk da cewar fuskar sarki shardas a rufe take cikin rawani sai da jarumi hailur ya gane cewa lallai wannan sadaukiba saurayi bane shekarunsa sun kai arba in da ‘ya’ya kuma idanunsa ya kalla kawai ya gane hakan abinka da jarumi mai dakakkiyar zuciya kuma wanda baya fidda rai ga samun sa a da rabo sai hailur ya gyara tsayuwarsa ya rike takobinsa da garkuwarsa da kyau koda ganin haka sai sarki shardas yayi murmushin mugunta kawai sai shima ya zare takobinsa daga cikin kufenta wata irin  takobi ce mai tsawo da kaifi kuma anyita ne da wani irin karfe na musamman wanda sai kwararren makeri ne zai iya gano hakan take sarki shardas ya falfalo da gudun tsiya izuwa kan jarumi hailu duk sa adda sawun kafafun sa suka taba kasa sai kaji kamar takun giwa ne saboda nauyinsu.

.

Koda jarumi Hailur ya hango sarki shardas ya rugo izuwa kansa cikin mugun nufi haka sai shima ya ruga izuwa gareshi duk su biyun suna ihu da karaji yayin da ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakai wawan hari sarki shardas ya kaiwa hailur sara a wuya da nufin ya cire masa kai hailur ya kare saran da garkuwarsa take garkuwar ta rabe gida biyu tamkar an yanka tsakiyar tufa da wuka cikin zafin nama hailur ya kaiwa shardas suka da takobinsa a ciki shardas yasa garkuwarsa don tare sukan amma duk da haka sai da takobin ta huda rigarsa ta tsargeta in ba don ma ya kare harin ba cikin zafin nama dasai takobin ta huda cikinsa koda suka duro kasa sai kowannansu ya cika da mamaki shi dai sarki shardas bai taba karo da jarumin da ya taba samun nasarar ko da lakutar rigar jikinsa ba amma yau gashi ya hadu da wanda ma ya tsargeta da takobi shi kuwa jarumi hailur firgita yayi ainun bisa ganin yadda takobin sarki shardas ta tsarge garkuwarsa gida biyu don haka ya tabbatar da cewar duk sa adda takobin shardas ta sami jikinsa ba karamar illa zata yi masa ba, nan fa Hailur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya iya kare kansa koda ya dubi garkuwar dake hannun sarki shardas sai yaga anyi tane da irin karfen da akayi Takobin, cikin sauri hailur ya dubi kaifin takobinsa sai yaga she har ta dan dakushe a wajen tsininta sakamakon haduwa da tayi da garkuwar sarki Shardas.

.

Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin hailur kenan ya tabbatar da cewar babu wata hanya da zai iya kare kansa a wajen sarki shardas face ya kwaci garkuwar dake hannunsa yin hakan kuwa yasan cewa ba karamar sa a bace da nasara.

.

A wannan lokaci gaba dayan dakarun sarki shardas da tsirarun dakarun su hailur da sukayi saura a wajan sun zuba idanunsu a kansu kawai kowa so yake yaga yadda karshen wannan gumurzu zai kasance tamkar dacan ba yaki ake ba a wajan su kuwa matan da aka kama amatsayin bayi aka daddauresu tuni sun fara kuka tare da ya yansu kananan yara wadanda kusan su duka an kashe iyayansu maza an mai dasu marayu sai da kimanin dakiku dari da arba in suka shede ana kallon kallo tsakanin sarki shardas da jarumi hailur kowannansu tunanin dabarar da zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa yake sannan suka sake rugawa izuwa kan juna a karo na biyu suna haduwa asama sai sarki shardas ya kawowa hailur sara a cinya shi kuma yakai masa sara a ka kowannansu

yayi iya kokarinsa wajan kaucewa harin cikin zafin nama amma sai da takobin sarki shardas ta yanki hailu ta dara naman cinyar jini yayi tsartuwa hailur ya kwala uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji shi kuwa sarki shardas bai ankara ba sai gani yayi hailur ya tuje rawanin dake kansa ya fado kasa sai ga fuskarsa ta baiyana a fili karara kafin su duro kasa gaba daya tuni hailur ya doki hannun sarki shardas mai dauke da garkuwa garkuwar ta subuto kasa cikin bakin zafin nama hailur ya fada kan garkuwar ya sureta kuma yayi ‘yardungure sau uku izuwa can gaba yana mikewa tsaye yayi sauri ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin cinyar tasa don tsaida jini.

.

Shi kuwa sarki shardas ko da yaga tsirarun dakarun su hailur sunyi arba da fuskarshi kuma sun shaida ko shi wanene sai ya dakawa dakarunsa tsawa yace su karasasu gaba daya take dakarun suka hau tsirarun dakarun da sara da suka suka karkashesu a cikin ‘yan dakiku kadan koda ganin abinda ya faru sai jarumi hailur ya kurma uban ihu ya ruga izuwa kan sarki shardas har dakaru sun yunkura zasu tareshi sai sarki shardas ya tsaidasu yace ai wannan nawa ne ba naku ba kuma abin kunya ne a ce nidaku munyi masa rubdugu ku zuba ido kamar yadda kukayi da farko kuga yadda zamuyi dashi koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya tari jarumi hailur suka ci gaba da kaiwa juna mugayen hare hare wannan karon dai sarki shardas yana kaiwa

hailur sara da suka ne da dukkan karfinsa cikin azababben zafin nama na gaban kwatance.

.

Kaico mai karfi sai Allah ya isa kuma na gaba yayi gaba na baya sai labari duk da irin tsananin juriya da jarumtaka irin ta hailur wannan karon sai da ya raina kansa domin bambancin a baiyane yake kuma sarki shardas ya shammaceshi wajan sauya salon fadan, a lokaci guda ya hada da kai masa naushi da bugu da hannu da kafa sai gashi nan da nan ya hadawa hailur jini da majina yana bal dashi kamar tamola…

.

Tab ganin wannan yanayi da hailur ya shiga ya sa ni tsaya wa cak! Da typing ɗin da nake, kuyi haƙuri bisa jin shiru na wasu kwanaki da kuka jini InSha Allahu zamu ci gaba a gobe idan Allah ya kafin 

TSATSUBA

BOOK 2

PART (E)

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.

.

Sai gashi nan da nan ya haɗa mashi jini da majina yana bal dashi kamar tamola, ashe duk wannan abu dake faruwa shadila ta leko ta cikin tantin da take tana ganin abin dake faruwa cikin tsananin fargaba da tashin hankali kwatsam sai sarki shardas ya sami nasarar saran kafadar hailur ta hagu hailur ya kurma ihu a lokacin da jini yayi tsartuwa a kafadar tasa amma sai yayi sauri ya rike takobin ta Sarki shardas a lokacin da shi sarki shardas ke son ya danna takobin ta nutse a cikin kafadar koda shadila ta hango abinda ya faru ga mijinta saita kurma ihu bata san sa adda ta fito  da gudu daga cikin tantin da take boye ta rugo izuwa inda suke jiyo ihunta da gudun tane yasa sarki shardas ya waigo yayi arba da ita koda yaga irin tsananin kyawunta sai ya dimauce ya juya da sauri ya doke kirjin hailur da karfin gaske saboda karfin dukan saida hailur yayi tsalle sama da baya kamar an janyeshi da majajjawa ashe bayan nasa wani rami ne mai tsananin zurfin tsiya wanda karshensa kwazazzabo ne da magudanar ruwan wata korama koda hailur yaji ya fada cikin wannan rami sai ya kwarara uban ihu irin na wanda ya saddakar mutuwa zaiyi ita kuwa shadila tana ganin abinda ya faru ga mijinta sai ta sulale kasa sumammiya.

.

Sarki shardas ya bushe da dariyar farin ciki ya ruga da baya izuwa inda shadila ke kwance ya dauketa ya azata akan dokinsa nan take dakarunsa suka kwashe gaba dayan dukiyar wannan ayari nasu hailur suka ingiza keyar bayin da suka kama akayi gaba ana tunkarar birnin Romaniya.

.

Ana fara tafiya sai sarki shardas ya sake rufe fuskarsa da bakin rawani kuma ya shakawa shadila banju barcinta ya sake nauyi don haka bata farka ba har aka isa birnin romaniya da tsakiyar dare lokacin da shadila ta farka daga barci sai ta tsinci kan wani luntsumemen gado na alfarma a cikin wani kasaitaccen daki na sarauta cikin razana ta mike tsaye da sauri ta sauko daga kan gadon, ta kama kallon kowacce kusurwa koda tagama ganin kayan kawar dake cikin dakin sai tunanin mijinta da sauran jama arsu ya fado mata ta tuno da duk abinda ya faru a sansaninsu sa adda aka kawo musu sumame na mamayar bazato nan take shadila ta dafe kunnuwanta da hannayanta biyu ta kurma uban ihu tana mai fashewa da matsanancin kuka faruwar hakan keda wuya sai taji an bude kofar turakar ba wani bane ya shigo cikin turakar face sarki shardas a cikin wata irin kyakkyawar shiga ta sarakai fuskarsa cike da annnuri ya durfafeta.

.

Koda tayi arba dashi sai ta razana ainun taja da baya tana mai nunashi da yatsa a lokacin da hawaye ya zubo mata tace ka cuceni ka kashe mini miji kuma ka kashe dukkan mazajen ayarinmu ina sauran yan uwana mata?

.

Me kake nufi dani ka kawoni nan ni kadai kawai ka kasheni na huta da kunci da bakincikin rayuwa tunda ka rabani da masoyina da dukkan zuri ata koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubeta yace yake wannan ma abociyar kyawu da cikar zati kiyi sani cewa kece mafi sa a bisa dacewa da zama matar sarkin birnin Romaniya a yanzu duk wata rayuwa da kikayi a baya ki manta da ita ki manta da komai da kowa ki fuskanci sabuwar rayuwar da tazo miki wacce zaki tsinci kanki a cikin daular da baki taba ji da gani ba koda jin wannan batu sai zuciyar shadila ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fishi taji ta tsani sarki shardas fiye da komai a doron kasa koda idanunta suka kai kan wata wukar dake kan wani faranti babba mai dauke da tuffa masu yawa sai tayi zumbur ta suri wukar ta ritsa sarki shardas da ita tace kada ka kusanceni idan ka matso kusa dani zan kasheka.

.

Sarki shardas ya bushe da mahaukaciyar dariya ya durfafeta kai tsaye ai kuwa yana kusantarta sai ta caka maza wukar a kirji take wukar ta balle gida biyu taji kamar akan dutse ta bugata kawai sai sarki shardas ya hankadata ta fada kan gadon dake bayanta sannan ya bita izuwa kan gadon bai rabu da ita ba har sai da bukatarsa ta biya tana ta faman rusa ihu da kukan bakin ciki daga wannan rana shadila ta zama matar sarki shardas da karfin tsiya ya zamana cewa kullum a cikin daula take babu abinda takeyi da hannunta sai dai kuyangi da barori suyi mata duk da cewar ta tsinci kanta a cikin daula irin wacce bata taba ji da gani ba sai ya zamana cewa kullum a cikin kuka da bakinciki take musamman

idan ta tuno da tsohon masoyinta kuma sabon angonta hailur da kuma sauran danginta da zuri arta lokacin da shadila ta matsawa sarki shardas akan sai taga inda aka kai sauran +yan uwanta mata wadanda aka kama a matsayin bayi sai yayi mata jagora izuwa wani bangare daban na gidan sarautar wannan ranace ta farko wacce shadila ta sami damar fita daga bangaren  da turakarta take koda taga yadda girman gidan sarautar yake da yawan dakarun dake tsaro a ko ina sai hankalinta ya dugunzuma ainun domin take burinta na son guduwa ya yanke, haka dai sarki

shardas yaci gaba da yiwa shadila jagora suna ta ratsawa ta cikin lunguna da sakuna har sai da sukayi tafiya mai nisa duk inda suka ratsa sai dai kaga bayi barorim hadimai da dakaru suna risinawa suna gaishesu har suka iso wani katon gida wanda ke cike da bayi mata.

.

Koda shadila tayi arba da yan uwanta mata yan zuri arsu suna ta yin ayyuka na bauta iri iri sai ta ruga garesu tana mai kiran sunayansu daya bayan daya tana zubar da hawaye take suma bayin suka rugo gareta suka rungumeta suna kuka.bayan ta dan jima a kankame dasu sai ta janye jikinta daga cikin nasu ta juyo ta dubi sarki shardas tace ina neman alfarmar ka yanta wadannan yan uwa nawa daga matsayin bayi masu aikin bauta zuwa ga kuyangina.

.

Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi shiru yana mai sunkui da kai ya dubi shadila cikin murmushi yace yake matata kiyi sani cewa babu wani abu da zaki nema a wajena ki rasa saboda tsananin irin son da nake yi miki don haka zanyi miki wannan alfarma bisa sharadi guda shardin kuwa shine wadannan bayi idan suka koma can wajanki ba zasu taba fita ba daga cikin harabar gidanki duk wacce aka kama da laifin hakan hukuncin kisane a kanta.

.

Koda jin haka sai farinciki ya lullube bayin suka fara rungume shadila sunayi mata godiya ita kuwa shadila sai ta dubi Sarki shardas tace na amince da wannan sharadi naka nan take sarki shardas ya sa dakarun dake kula da wadannan bayi suka kwankwance musu sarkokin dake wuyansu da hannayensu sannan aka tafi dasu izuwa can bangaren gidan shadila a nan ne aka basu suturu masu kyau sukaje sukayi wanka suka sanya suturu

.

Tun da aka kawo shadila wannan gidan sarauta na birnin romaniya bata taba yin farin ciki ba sai a wannan rana da aka ‘yanta wadannan bayi kuma bata taba yiwa Sarki Shardas murmushi ba sai a yau din nan.

.

Hakika shadila ta tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma inda tana da ikon kasheshi ko guduwa daga gidan sarautar da tuni ta aikata haka dai dai da rana daya shadila bata taba mancewa da mijinta ba Hailur kusan kullum sai tayi mafarkinshi

sau tari a mafarkin nata ana nuna mata cewar hailur yana nan a raye bai mutu ba amma idan ta tuno da tsananin zurfin ramin da ya fada sai taga cewar mafarkin nata ba zai taba zama gaskiya ba babban abinda take yin nadamar aikatashi shine karya sharadin da tayi a lokacin da hailur ya gaya mata cewa komai tsanani kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take amma sai ta mance da sharadin ta fito da gudu bisa dimaucewar da tayi a lokacin da taga sarki shardas ya sareshi da takobi a kafada ta kwalla ihu ta fito da gudu ta baiyana kanta.

.

Tabbas inda bata fito ba da sai hailur ya kubuta daga sharrinsa kuma da sai sun gudu tare lokacin da shadila ta sami wata uku a cikin gidan sarautar sarki shardas sai alamun juna biyu suka baiyana a gareta ya zamana cewa tana fama da tashin zuciya, kumallo da zazzafi da ciwon kai ko da sarki shardas yaga shadila bata da lafiya sai hankalinsa ya dugunzuma nan take ya tura aka

kirawo wata likita tazo ta dubata cikin murmushi likitar ta dubi sarki shardas tayi masa bushara cewar matarsa ta sami juna biyu

Koda jin haka sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki amma da ya tuno da wani al amari sai hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama kyarma bai san sa adda yasa hannu ya zabgawa shadila mari ba, saboda karfin marin saida ta fadi kasa bakinta ya fashe jini yazubo sarki shardas ya sunkuya ya kamo kafadunta yana mai daka mata tsawa yace wanene yayi miki ciki ban sani ba a cikin gidan sarautata kiyi sani cewa yau shekara ashirin kenan ina neman haihuwa ban samu ba kuma matana na aure guda goma sha shida ne a cikin gidannan bokana ya tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa.ba har sai na mallaki wata hular sihiri wacce ake kira LAMSARA.

.

Lallai wannan ciki da kike dauke dashi ba nawa bane maza ki hanzarta sanar dani maishi kona shakeki ki mutu yanzu.

.

Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai shadila ta bushe da dariya al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan kuma jikinsa yayi sanyi ya mike tsaye yana mai kura mata idanu, shadila ta yunkura ta mike tsaye ta dubi sarki shardas a fusace tace shin kana tunanin ina tsoron mutuwa ne? To ka sani cewa duk wannan daula da nake ciki a wannan gidan sarauta daidai yake da kurkuku a wajena, gaba daya rayuwar duniya ta fita daga raina tun daga ranar da ka wargaza rayuwata ka rabani da babban masoyina hailur kuma ka tarwatsa ayarinmu, ka sani cewa wannan hari da kuka kai mana an kashe uwata da ubana da dukkan dangina a yanzu bani da sauran masoyi a doron kasa face masoyina hailur wanda har yanzu xuciyata ke wasu wasin cewar yana nan a raye bai mutu ba idan har yana raye ina tabbatar maka da cewa sai yazo har nan gidan sarautar ya daukeni mun tafi domin wannan juna biyu da nake dauke dashi nasa Ne bana wani ba, kafin shadila ta gama rufe bakinta ya sake zabga mata mari ta baje a kasa sumammiya nan take kuyangi suka rugo izuwa kanta suka shiga ceto rayuwarta.

.

Koda ganin haka sai sarki shardas ya rude yayi nadamar abinda ya aikata saboda tsananin son da yake yiwa shadila don haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba har kwallar takaici ta zo masa.

.

A fusace ya baro turakar shadila ya aika aje a kirawo masa babban bokan birnin wanda ake kira da Barwas ibn Mus ab Lokacin da ya isa wajan boka barwas sai ya labarta masa duk abinda yake faruwa nan take bokan yake shaida masa abubuwan

matakin da ya kamata ya dauka yake cewa akan wannan juna biyu data samu ya kasance mai nuna mata kauna kulawa da soyayya irin wacce ma baka taba nuna mata ba ka zamo mai tarairayarta kada ka bari koda kuda ya taba lafiyarta kuyi renon cikin tare kai da ita har izuwa sa adda zata haihu lafiya kuma har izuwa sa adda yaron zai cika shekara bakwai a wannan lokaci kun shaku ainun da yaron kawai saika tsiri tafiya wannan tafiya kuwa nine zanyi maka jagora a cikinta kuma ba zamu dawo ba har sai mun sami nasarar mallakar hular lamsara ina mai tabbatar maka da cewar da zarar mun mallaki hular lamsara tamkar mun dora duniyar nan ne dukanta a tafin hannunka komai da kowa sai ya dawo karkashin ikonka kuma babu wani makiyinka da zai iya samun nasara a kanka

.

Anan zan dakata haka amma kafinnan nake cewa mu kwana lafiya.

Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki bai san sa adda ya rungume boka barwas ba yana mai kyalkyala dariya daga can kuma sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace tabbas yanzu na sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo zaka ga abin da zai biyo baya, koda jin haka sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga can kuma saiya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun tsananin damuwa yace ya shugabana yaya batun alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya bushe da dariya yace ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai kankareshi face rashin biyan bukatata, daga wannan rana Sarki shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya zamana cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa

.

Al’amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce taga ashe zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda fuskarsa da zuciyarsa ke nunawa face tsananin soyayya da kulawa Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal sai gashi shadila ta fara sakin jiki da sarki shardas duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu kamarsa a cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa a cikin zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan gaba a ranta ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce nan fa zuciyarta taci gaba da raya mata cewar ya kamata ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci

sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a cikinta kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta.

.

Wata rana shadila na zaune ita kadai a cikin turakarta bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin ta sarakai a wannan lokaci tana sanye da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce ke nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi cikinta taga ya dan fara girma sai ta shiga shafa cikin tana murmushi ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face tunowa da babban masoyinta wato mahaifin abinda zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi tun farkon soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas suka kawo harin sumame ga sansaninsu lokacin da yake gaya mata cewar kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take ciki.

.

Koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya sareshi da takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne sarki shardas ya jiyo a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin firgici da razana sarki shardas ya rugo da gudu izuwa cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa ganin cewar babu kowa a cikin turakar face shadila ita kadai

a zaune hawaye na zuba daki daki a kan kyawawan kumatunta cikin sanyin jiki sarki shardas yaje ya zauna akan kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune ya kama hannayanta biyu ya

rike suka kurawa juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai taushi da sanyi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla a cikin idanun sarki shardas tun da aka kawo ta gidan sarautar Sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar a duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma kika daukeshi babban makiyinki sama dani saboda na kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan na rabaki da duk zuri’arki na kawoki kasata da karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe dake matata ta dole har abada babu abinda zan yi na goge wannan tabo nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare harna sami gafararki ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk da nasan bakya kaunata dai dai da tsawon dakika daya ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki haifa ta kasance a cikin farin ciki, alfarma daya nake so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na yiwa mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan gaba a sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana ganin zai iya daukar fansa a kaina sai ya dauka , kin san cewar ni ba zan taba haihuwa ba face  na mallaki Hular lamsara kamar yadda na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan mijinki hailur a matsayin dan cikina, wannan zai kawai mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi miki alkawarin cewar daga nan har izuwa tawon shekaru bakwan ba zan taba cutar  dashi ba amma fa ki sani cewar a ranar da ya cika shekara bakwai zanyi shiri na bar kasar nan don tafiya neman hular lamsara bokana ya tabbatar mini da cewa shima wannan da naki idan ya zama saurayi zai tafi neman hular lamsara to a sannan ne nake son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa domin daga wannan rana mun zama ABOKAN GABA na sani cewa a wannan lokaci bana gida don boka barwas ya tabbatar mini da cewar sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu gano inda hular Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san kamannin danki ba shima bai san nawa ba don haka ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu shaida juna ba zamu iya abokai kuma ko kuma abokan gaba idan kuwa na rigashi mallakar hular lamsara tofa duk inda muka hadu saina gane cewa shine dan hailur kuma nan take zan kasheshi. Sai kiyi tunani bisa wannan alfarma dana nema a wajanki kuma ki tuna cewar kin taba neman alfarma a wajena kuma nayi miki tun da kinsa na ‘yanta matan zuri arku daga matsayin bayi sun koma kuyanginki idan har kikayi mini wannan alfarma guda daya dana nema a wajanki babu mamaki ungulu ta Koma gidan ta na tsamiya.

A lokacin da Nikuma AlQuyraemey Zankoma Inda nafi Wayau wato Neman na Aure,,,

..

Anan ne Littafin TSATSUBA NA BIYU YAZO KARSHE marubucin Littafin yace.

.

SHIN SHADILA ZATA IYA YIWA SARKI SHARDAS ALFARMAR DA YA NEMA A WAJANTA?

.

SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?

.

WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR? SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA

.

Don jin Cigaban wannan labari na Tsatsuba Littafi na 3 sai ku danna bulun rubutun nan

Back to top button