Uncategorized

Zuciya da Kwanji Chapter 6 Hausa Novel

 

ZUCIYA DA KWANJI 

BOOK 1___6

Na Maimuna Idris Sani Beli

  Ranar da Sadiya ta karbi girki, washegari da safe ta jangwalo masa fitina yana shirin fita aiki, ya fita siyo wa Fatima karin kumallo, bayan ya hantse ke nan da girki sadiya, ya dawo da abincin ya kai wa fatima dakinta suka yi dan fadan nasu da ya zame masu jiki, ya nufi dakinsa ya kara kintsawa sai jin hayaniyar sadiya ya yi a bangaren Fatima.

  

   Haba da sauri ya fito sai yaga Fatima tsaye a barandar kofar dakinta sanye da hijab ga kuma Sadiya rike da zandameniyar tsintsiya tana hayaniya. Ya tsaya daga tasa barandar yana rike da jakar lap top dinsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, 

  “Me ya faru?”

  Zuciya a kule Sadiya ta hau koro masa jawabi.

  “Wai ita wannan ba aure ta zo gidan nan ba ne. Ni ban ga wani abu ɗaya da ta ke ko ake mata wanda zai sanya a kirata matar aure ba”.

  Bai ko motsa ba ya tari numfashin ta a dake “Oh wannan tambayar kika kira ta ki yi mata ke nana?”

 Cikin nufin tura haushi sadiya ta ce “Allah ya tsare, kai ma da kake kwanan kallon kwallon kafa a honey days dinta ba ka ga asarar bata bakinka ka yi mata wannan tambayar ba bare ni…. Maganar sharar tsakar gidan na nake mata, kasan nura ya je ƙauye, kwana ɗaiɗai muke ni da hindatu….. Ita kuma na ga kamar cin abinci kawai ta zo ci, to mu ba bayin ta ba ne, sai ta shigo anyi da ita.

  Ya dinga nazarin sadiya, idanunsa da fuskarsa na bayyan tarin bacin rai da suka riska, ya yi gyaran murya ya ce “Yau ne za ta fara sharar?” Cikin gadara ta gyada kai, shi kuma ya ajiye jakarsa ya nufo ta yana mika hannu.

 “Ba ni tsintsinyar duk ranar tata sharar a dinga tuna min ina sharewa.

  Ta kankame tsintsiyar tana kallonsa da yanayin takaici, ta ce, “Amman ai bai kamata ba”.

  Ya tsuke ido ya ce mata “Dama mun yi ajandar fadin ya kamata tsakanina da ke?” Ta yi saroro kunya ta rufe ta saboda ta san halin Abdullahi, babu ruwansa yanzu ya tsinkata gaban Fatiman da ta rungume hannu ta zuba musu ido, Sadiya ta yi dira dira ta ce. “Ka ga ni bana son bakar magana”.

  Nan ma ya tsare ta da ido ya ce, “Amma ai ke kika nema?” 

  Kamar zata saki kuka ta ce, “To, bayanta zaka bi ke nan?” Ya kada kafada alamar ko in kula ya ce, “Ke ce za ki fada, tunda watakila kin yi zaton naki bayan zan bi, sai kuma aka sami akasin haka….. Ba ni tsintsiyar na ce”.

   Ta mika masa tana shirin barin wajen ta ce, “Lallai aikin shara ya dawo hannunka domin kuwa ni ma bazan kara saka tsintsiya a tsakar gidan nan ba, kullum sai da ka dinga sharewa.

   Tana direwa ya amsa. “Ashe? Kema ba cin abinci kawai kika zo yi gidan ba, wanne za ki zaba ke nan? Idan kin zaba sai ki fada min kinga yau sai na yi kwannan kallon kwallo da safe na share miki gidan”.   

   Takaici ya lullube sadiya ta ma rasa da kalamar da zata amsa, kawai sai ta wuce ta barshi. Tana jinsa ya saukaka murya ya cewa Fatima. 

  “Yi hakuri don Allah ki shiga ciki. Ya nade riga ya share gidan tas inda ya tsallake barandar Sadiya da Hindatu, ya share ta Fatima sannan ya wanke hannu ya fice abinsa.

   Kwana biyu da suka biyo baya bai share gida ba, amma yana ware barandar Fatima ya share, ba tare da ya damu da manya da kanana kalubalen da yake fuskanta daga Sadiya ba, kai har ma da Hindatu da a yanzu ta fara ganin kamar makancewarsa ta yi yawa, duk kuwa da iyakarsa ke nan da dare raba makwanci suke.

  Kai sai abin ma ya bar tsakar gida, kwananta biyar ya lura komai ya yi kura a falon Fatima, sam bai zarge ta da kazanta ba don yasan ba ta saba ba. Abin da ta sani kawai ta wanke goma ta tsoma biyar, don haka ranar lahadi da safe da ya je gaishe ta, sai da ya tabbatar ya goge komai tsab sannan ya yi mata kyakkyawar shara tana zaune tana kallonsa, sannan ya fice. Wannan dabi’ar tasa ta son bauta mata ba tare da neman raddi ba, wani lokacin ma yana yi suna fada, ta taimaka kwarai wajen zaftare fiye da rabin tsanarsa a zuciyar Fatima. Ta fara bude ido ta kalli kalarsa, kyakkyawan matashi mai akida, wanda ba ya taɓa sakaci ko sarayar da hakki ko damar sa ko a wajen da yake da kason kaskantar da kai. Sai fadan da suke yawan yi ya fara birgeta. Ta kuma fara nazartarsa a matsayin na sabo kawai, ba wanda ake yi a doron kiyayyar da ta ratsa zuciya ba, shi yasa hankalinta ya kwanta kamar tsumma a randa, ko yaushe suka yi waya da Alhaji ta kan tabbatar masa ai Abdullahi na aiki mai kyau, ya dauke ta kamar ‘yar uwarsa. Matsalarta daya su sadiya, wanda motsi kadan sai ta kwashi damin habaici da dalili ko babu, wannan ya kara mata tsanar su musamman sadiya, wadda ta lura kamar numfashinta ma neman masifa da gori ne.

   Dadinta daya idan Abdullahi na kusa wanda kan ari rigimar ya yafa ko da kuwa gorin zai fada kansa. Ranar lahadi girki ya zagayo kanta, a ranar ne kuma sam ba ta ji duriyar Abdullahi ba. Tun da ya yi mata gyaran falo ya fice bai shigo mata bankwana ba. har dare duk da ta ji shigowarsa gidan. Ga mamakin sai ta ji ciwon hakan ko saboda gorin sadiya, to mai gorin rashin kwanansu a dakin juna, ina kuma ya dauke mata kafa kwata kwata?    

   Da safe da ya shigo kawo mata karin kumallo bai gabatar mata uzuri ba, ita ma ba ta nema ba, duk da ba ta so hakan ba saboda neman tsira da mutumcin ta a idon sadiya a ragowar kwanakinta a gidan. Daga wannan rana kuma sai hakan ya zame masa dabi’a, illa dai yamma idan ya dawo ya kan shigo ya kawo mata abinci kusan kamar akan kaya sai ya fita, ko fadan ma ba ya saurararta su yi. Kwana sha biyu girki ya kuma waiwayarta, tana ta ɗokin dawowar Abdullahi saboda wunin da ta yi da yunwa sakamakon bakin kawayenta da suka zo. A ranar kuma ba ta da sha’awar wani abu da ya danganci gwangwani.

  Karfe biyar ta ji shigowar Abdullahi gidan, amma har shidda bai waiwayeta ba, cikin kuncin ta tashi  ta jona ruwa a kettle don ta sha tea. Tana tsaye tana jiran tafasar ruwan ne Abdullahi ya cimmata a kicin din cikin kannana kaya yanata zabga kamshin turare. Tana ganinsa ta ɓata fuska, ko sallamarsa a ciki ta amsa bai damu ba ya dora.

 Me kike yi?” 

 Ta share shi,

 Cikin zolaya ya ce, “Yauwa abinci za ki mana?” Kawai sai ta kashe butar ta zare cable ta nemi ficewa daga kicin din, shi kuma ya babbake kofar yana kokarin su hada ido. “To me ye na fushin don Allah? Ni ban ga laifin da na yi ba”. Ya fada da murya mai karancin sauti, wadda ake yiwa masoyi idan aka kadaice da shi, “Wata alfarma na zo nema”.

Ya kuma fada yana kara kaskantar da murya. Ta yi baya rungume da hannu tana kallonsa duk ta.takura, kasancewar ba ta sanye da hijabi, don tun shigowarta gidan bai taba katarin ganinta haka ba, hasalima kanta ko kallabi babu sai kwantaccen bakin gashinta da ta makale da ribon. Shirunta ya ba shi damar karanto alfarmar.

  “Don girman Allah ki zo mu je gadanmu ki gaida su hajiya, ba ki ji fadan da malam ya yi min ba yau akan hakan, har yana ganin ko don babu ran mahaifiyata ne, shi ya sa na ki kai ki ki ga yan’uwa”. Har yau ta kasa dauke ido a kansa, fuskarta ba ta bayyana rashin kunya ba, illa ta bayyana damuwa kamar a raunane ta ce.

 “Wacce irin rigima ce wannan Abdul, bisa wacce fuskar zaka kwaso min fita da kai?” Ya kawar da kai, ya marariraice mata. “Ki yi hakuri, kin san sha’anin iyaye, sai ka kansance mai taka tsan-tsan a cikin lamarinsu don ka samu ku rabu kalau…. Kuma ya kamata mu yiwa malam uzuri tunda bai san me ye akwai a tsakaninmu ba… To banda abinki ma waye zai san mun fita taren? Idan Alhaji ne sai kar ki sanar da shi a waya alal akalla dai ba ki taimaka na ma mahaifina ba don ban taba yi miki irin abin da ya yi min wannan sakayyar ba”

 Ta dan yi rau-rau da ido, amma sai ta hada ta motsa ta ce, ” Ban hanya na wuce”.

  Ya ba ta hanyar, sai da ta jima a falo sanyaye ya bita jiki a sanyaye ya same ta sanye da hijabi ta rafka tagumi.

  Ya kara kan kan da murya ya ce, “Ki daure muje fadimatu”.

  Ta janye tagumin ta ce, “Zan je, amma kai ma ka yi kokari salin’alin jibi ka sallme ni na bar gidannan nan”.

  A takaice ya ce, “Toh”. Sannan ya dubi agogo ya dube ta. “Tea za ki sha? Bari na hada miki ki sha sai inyi wanka ki shirya da kyau, don Allah ki binne matsalarmu a zuci kar ki bari ko kadan a san babu jituwa a tsakaninmu kin ji? In kin yi hakan ma kin gama biyana”.

  Cikin mintuna kadan ya hada mata tea din tun a kicin ya hada komai kofi choculate guda biyu ya saka mata a cikin tea ɗin, ya ajiye a coffe table ya janyo mata har gabanta ya yi mata kyautar murmushi, sannan ya juya yana cewa. “Idan na dawo sallar isha sai mu tafi”. Kai tsaye masallaci ya wuce, har bayan isha. Yana dawowa ya cancaɗa ado kamar mai shirin zuwa zance ya baza turare sai kanshi ya ke, sannan ya rufo kofarsa ko su sadiya bai yiwa sallama ba ya nufi dakin Fatima.

  Ta gaji da nata kyan cikin riga da zanin dinkin atamfa super milk, kala mai ratsin purple da ruwan zuma. Idon Abdullahi sai dai iyakarsa ke nan ganin domin ko yabo ba shi da ikon ya yi balle abin da ya fi shi. Tana ganinsa ta yi saurin shigewa daki ta dauko mayafin da takalmi da jaka purse, ya yi saurin janye kallon da yake mata lokacin da ta karso kusa da shi. Suka jera suna tafiya cikin burgewa.

 Ko gezau ba ta yi ba, sai dai ta saci kallon kofar dakin, sannan ta mayar da hankali ga nazartar gidan. Ya kayatu kwarai, ya sha adon furanni ko’ina, ga shi makeken gaske saboda yanayi shirunsa kamar babu kowa a cikinsa, sai karar A.C ko’ina. Sai da suka bi wani korida sannan suka fita harabar gidan, tana binsa a baya har wajen motarsa ya bude mata kofa ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar suka fice waje, sannan ya tsaya ya fito ya rufe garkamemiyar kofar gidan da key. A sannu yake tafiya da motar bayan gilasai da ya rufe kirif, ya kunna A.C, ga kamshin airfreshner da ke motar ya gauraye da kamshin turarukan jikinsu ya hadu ya ya zama samfurin wani kamshin na daban. 

  Motar ta yi dif! Kowa zuciyarsa na na zarin, hakurin Abdullahi dai ya fara zarce awon da ya mallaka, kusancinsa da fatima ya dinga buga masa zuciya yana kuma kore masa duk wani tashin hankali da zai iya samun kansa a ciki. Ya dinga satar kallonta yana kallon titi. A karshe sai ya mika hannu ya latsa sautin D.bany a wakarsa ta Fall in love. Fatima ta kara yin dif! Ko motsin kirki ba ta son yi. Zuciyarta ta kasa nutsuwa don ta tabbatar Abdullahi na nufin wasu abubuwa masu tsauri a kanta, abin da yake ba za ataba kiransa plan na gaske ba, kuma ba yau ya soma ba tunda ya tsiro da aure to amma da wanne KWANJIN zata kalubalance mutun mai fuska biyu irin sa?

   Sai kawai ta zabi yin bakam ta manne jikin kofar motar, tare da alkawarin anyi na farko anyi na karshe. Har suka je salon wakokin da yake sa wa ke nan, daga fall in love ya fada, no one like u, ya zarce I’m in love, duk ta shanye ta yi banza da shi. Da ya tsayar da motar kofar gidan ma sai ya ki bude mata kofar ta ja mabudin ta saki ta dube shi, lokacin da ya kife kai a sitiyarin, a kufule ta ce, “To ka bude ni mana!”

 “Ya dago a gajiye ya dube ta ya ce “Oh ba zaki barni na nutsu ba kenan?” Sai ta kasa magana, tsawon fiye da mintuna goma sannan ya gaji ya dago ya dube ta “Ki yi kokari don Allah ki toshe duk wata barakar da zata nuna ba kya sona fatima, ina so su ganki a mace mai ilmi da tasan abin da ta ke, ki daure ki yi mani wannan alfarmar domin ubangijin da ya halicceki”.

  Kai tsaye ta amsa mas. “Na ji, amma sauti idan ba haka ba wallahi babu wata alfarmar da zaka kuma neman a wajena na yi maka, ko da kuwa zata shafe ni”

  Ya hadiye dariyarsa ya ce, “Don dai in tsargu ne, amma ni ba ke na sa wa ba, bari na bude miki kofar”. Ya balle kofar sannan ya fito ya bude mata, ta fito ya rufe kofar sannan ya yafuceta suka zagaya ta wata hanyar daban saboda cikar da kofar gidan nasu ya yi da masu daukar karatu.

   Iyakar karamcin yau Fatima ta je gidansa, babba da yaro kowa na farin ciki da zuwanta. Waje waje Abdullahi ya dinga kai ta yana gabatar da ita. Matan malam Uku, Hajiya Zainab, Hajiya Anisa da Haj umma, ko wacce ta karrama su kwarai, turamen atamfa da turaruka. Haka ya kai ta wajen matan yayyensa wadanda ke nasa bangare su ma suka dinga karram ta. A nan ne ya shiga kiran kannensa yana gabatar mata da su ita kuma tana yabawa da

matukar karamcinsu gareta. Ita kuma babu ta inda ta bude kofar sai suka dinga yi mata kallon mace mai kirki matuƙa da son mutane. Kai har dakin da ya yi samartakarsa sai da ya nuna mata, sannan ya nuna mata dakin mahaifiyarsa wanda yanzu kannensa mata suka gaje ya ce. “Kin ga dakin Innata, shekararta biyu da rasuwa”.

  Har cikin zuciyarta ta tausaya masa yayin da kalamanta na alhini suka shiga cikin kwakwalwar sa, “Allah sarki, Allah ya ji kanta, ya sada ta da annabin rahma”.

  Idonsa kwal-kwal ya amsa mata, “Amin”.

  Har karfe goma suna gidan, sam Abdullahi ya tsani a tafi saboda ya sami damar mu’amala da Fatima da kare mata kallo, bai kuma taɓa sanin tana da fara’a kamar haka ba. Muryarta sassanya mai dadin sauraro, kalamanta a takaice masu azanci da sanyaya rai, ga ta da karrama mutum ta hanyar ambaton sunansa a duk maganar da zata fada masa, shi kansa ba ta sanya shi a kwandon shara ba, idan magana ta biyo ta kansa ta kan ce, “Abdull kaza-kaza.

  Karfe goma da kwata suna dakin kannensa mata ana hira ta dube shi ta ce, “Abdul mu tafi dare ya yi”.  

  Ba shi da wani zabi duk da ransa bai so hakan ba, suka yi sallama da kowa, wani jikan gidan Adamu ya rako su da kayan Fatima har mota. Sun fara tafiya kamar dazu sai dai yanzu babu D.bank, tunda ta yi hani da wannan. Da kanta ta kawar da shirun da ke tsakaninsu ta hanyar wani raddi da ta ke fatan ranar samuwarsa. “Abdul kulliyar jama’ar gidanku suna da kirki da son farantawa dan Adam ba kamar kai ba”.   

   Ya dauke wuta kamar bai ji ba, sai can ya muskuta ba tare da ya dubeta ba ya ce, “Yarinya ni na rufe shafin rigima da ke” Kamar ba zata tanka ba, sai kuma ta tanka din. “Haka ne, gara mu yi rabuwar

arziki, mu sami kafar zumunci ko?” 

   Tana kallonsa kai tsaye shi kuma nasa kallon a titi, bai tanka ba amma kuncinsa cike da murmushi. Ya dinga tukin cikin matukar kasala kamar masu tafiya a keken da babu birki, can ya kira sunanta a kasalce, ta yi dif, takaici na isarta.

 “Fadima wallahi ba ni da lafiya”. Ya fito fili ya fada mata, ta kuma share shi, sai ya kuma shagwabewa. “Da gaske nake fadimatu, kirjina bugawa yake, taba ki ji”.

   Cikin tsuke ido ta fuskance shi, “Abdul ka mayar da ahankalinka, babu irin wannan a tsakaninmu sai ka bari mu isa gida akwai wadanda zasu iya daukar alhakinsa.” Bai sami damar bata amsa ba wayarta ta shiga ruri, sai ya bata damar ta amsa alhalin dukkan hankalinsa na kanta don yana tsammanin kiran Alhaji ne.

  Ilai kuwa ita ma ta amsa ba tare da wata shakka ba, suka yi gaisuwa irinta masoya, sannan yace mata ina kika shigane ina ta faman kiran wayarki baki daga ba, ta danja fasali sannan ta amsa ina falo ne wayar na cikin daki”

   Yace mata “Wlh har nashiga damuwa fati, nayi tsammanin ko kun hada kai da Abdul. Kinsan kuwa dazu mun gamu da abdullahi a gidan mai ya shareni? sai yayi kamar bai ganni ba alhalin mun hada ido, ya ja fasali Sannan ya ci gaba da cewa Fatimah ko kin bashi dama ne ya shigo dakinki har yasan wacece ke?”

   Da sauri ta dubi Abdul, wanda ta ke da yakinin zai iya jin abin da Alhajin ke fada, ta danna maɓallin rage sauti, sannan ta canja wayar zuwa kunneta na dama murya na rawa tace.. “Kai haba, kila dai bai ganka bane kawai, amma har yau bai saba dangantakar da ke tsakannmu ba, nakanyi kwana biyu ma ban sa shi a ido ba”.

Also Read:

 

   Alhajin ya saki ajiyar zuciya yace, “To allah yasa ya dore nidai na karaya ko jiya doctor ya tabbatar min B.P dina ya kai 160”.

   Cikin tausayawa matuka ta ce “Ayya Alhaji ka kwantar da hankalinka, inshaa Allah nan da kwana biyu mun fara lissafin rayuwa tare”

  Ya ji dadin kalamanta don haka ya kyalkyale da dariya yace “Inshaa Allah, bari na barki ki huta sai da safe”

 Ta sauke waya a nutse kuma tayi fuska, har sukaje gida babu wanda ya tanka ma wani, fuskar Abdul ta murde kamar wanda aka aikowa sakon mutuwa, sai huci kawai yake, hakan bai hanashi rakata dakinta da kyaututtukan da ta samo ba, sai dai baice mata kala ba ya fice. Ya yinda tabi shi da kallo tana mamakin wannan sauyawar tasa cikin ƙanƙanin lokaci.

   Da safe ma karfe takwas haka ya shigo mata babu walwala sam a fuskarsa da leda riƙe a hannu. Ta bude masa kofa bai ko dubi inda take ba ya wuce ya jona ruwa a kettle ya fasa kwai guda uku, ya soya ya rufe a faranti, sannan ya juye ruwan zafi a fulas ya jero mata a dogon faranti cup da sauran kayan tea ɗin, ya dora bread sannan ya ajiye kan center table. Muryarsa a cushe yace, breakfast is ready, bai jira cewarta ba ya kada kai ya fice, tabi shi da kallo cike da tunanunnuka iri iri, gabaɗaya zuciyarta ta jagule, me yayi zafi haka?

  Haka ta wuni zuciyarta sam babu dadi, gashi ranar ko kare bai shigo mata ba bare ya dauke mata kewa, wannan damuwar ta sabbaba mata dokin ganin jibi domin ta sami barin wannan gidan da ma’abotansa suke daga masiffafu, sarakan gori sai shugabansu tufkar hagu.

 Sai dai duk da haka aranta bata so suyi rabuwar tsiya da Abdul domin ta fara sabo da shi, kuma ta yarda da batun mahaifinsa yana da kirki da tausayi ga diya mace da son ya kyuatata mata.To ita ma zata dorar da wannan duk da rashin matsayinta a gurinsa hakan bai sa ya kware mata baya ba. Tana mamakin yadda damuwar yau ta ke saurin sanyata kuka, Dazarar ta zurfafa atunani kawai sai taji hawaye. Da la’asar sakaliya tana kwance dakin baccinta tana ƙananan hawaye, ta jiyo abin da aka saba, wato Hindatu da bakuwarta suna gulmarta. Tun da tazo gidan Hindatu bata taɓa tararta gaba da gaba da wata magana mai daci ba, amma sau uku kenan tana zuwa mata jikin windo da baki suna gulmarta, yau ma cikin gulma bakuwar tace “kwata-kwata wannan amaryar taki ba a ganinta ne?” 

   Hindatu ta maƙale murya ta ce, “ina za ki ganta? bata fitowa sai dai rako baki, duk da jiya dai ya kwasheta sunje gadon ƙaya, ina jin iyayenta suka kai ma malam kara, a ka yi kiransu a ka yi musu fada, ko kaca kaca Malam yayi masa oho! Don yau a wani hagunce ya tashi, daga magana ya hau surfa min balai wai na barshi yaji da abin dake gabansa” 

  Cike da son jin tsegumin bakuwar ta ce, “Oh me yayi zafi haka? Hindatu na dariya ta amsa Huum in kika ji labarin sai mamaki ya dame, kinga matar ne? Wanke hannu ka taba ce wallahi, kyakkywar mace iyakar saninki. Amma Abu Turab shakulatin bangaro yake da ita, kallo ma

ba ta ishe shi ba, ko girki fa ba ta yi, kullum safiya ranar girkin ta wajena yake cin abinci, da dare kuma shi yasan inda yake ci. Ita kuma ya fita waje ya siyo mata saboda tsabar daurewa karya gindi….”

  Bakuwar ta ce “Allah mai iko, to amman yaya suka kaya sadiya?” 

  Tab kinga yadda ta yaƙune kuwa? Duk da nasan  lamarin matar nan ke ramar da ita, donba abinda ta rasa, ga kudin ga kyau, ga kuma tsabar mulki. Kisan kuma sadiya da bakin kishi, yau da safe ai a kanta ya sauke fushin bayan ni na kama kaina. Tana fa ganinsa a birkicen nan ta hau tuhumarsa, wai jiya ya fita da amarayarsa bai fada mana ba. Kin san Abu Turab da bakar magana, kawai sai ya nemi guri ya zauna rai a bace ya yanko mai zafi ya ce, “To kinga sadiya tun da ke kika auro ni, kike kuma daukar nauyina zo ki kafa min padlock kar na dinga fita da ita, har sai na nemi izininki, saboda duk ke kike ciyar da mu….”

  Kin santa ita ma da dacin rai, sai kawai ta ara ta yafa ta ce, ‘Kamar gaske, idan kana sonta me yasa ka mayar da ita ‘yar gadin a cikin gidan nan.

   Babu shiri Fatima ta fice daga dakin baccinta zuwa falo don ta gaji da wadannan bakaken maganganun kar ta ji abin da zai balla mata zucita, ashe kallon da suke mata, wulakancinsa har ya kai haka?

   Cikin wannan radadin zuciyar ta yi wanka ta kasance cikin pink din kananan kaya, siket ɗin iyakar gwiwa da riga matsattsiya ko cibiya ba ta rufe mata ba. Ta kishingida a kujeru tana kallo, duk da hankalinta ba ya tare da abin da ta ke kallo.

  Biyar da kwata ta ji dirin motar Abdullahi, ta dubi agogo

gabanta na faduwa saboda tunanin yadda suka kwashe yau da safe. Sam ba ta yi tsammanin shigowarsa a wannan lokacin ba, don haka ba ta damu da kayan da ke jikinta ba, amma kwatsam sai ga shi tsinkayoshi yana kallonta tamkar ya sami majigin duk da fuskarsa babu walwala. Ta kawar da kai tana faman jan siket ɗinta sama, sannan ta ja riga, a karshe ta dube shi a turbune ta ce.

   “Haba malam, mene ne haka babu nemi izini?” 

   Ya dage mata gira ba tare da yace mata komai ba. Amman Sai ya share wannan batun, ya nemi guri ya zauna karo na farko ke nan da ya zauna a dakin tunda ta zo gidan, komeye ya kawo shi iyakarsa tsayuwa. Muryar a saukake ya ce.

   “Ba ni da kudi sosai ne zan shiga kicin, me kike so na girki miki?” Har zata gwale shi, sai ta tuno shaguɓen da Hindatu ta gama yi mata dazu, kawai sai ta kawar da kai, ta ce “Ni ‘yar cirani ko me ka bani ai godiya zan yi in karba, yau da gobe ne kawai, jibi ya zama tarihi”.

   Ya hadiye duk takaicin da maganarta ta sabbaba masa, ya ce “To za ki ci dan wake? Sai ki hada da fruit salad”.   Duk da ba ta san ya ya dan waken yake ba sai ta kada kai ta ce, “Zan ci”

  Ya ce, “To bari na dan huta”. 

  Ya kara share guri ya zauna, idonsa akan talabijin amma a saukake ita yake more wa kallo, ta gama sakwarkwatar zuciyarsa, da yi masa fami a soyayyarsa wadda yake ji a ransa ba ta shafi kyau ko iya wankanta ba. Cikin dabara ta silale daki, sai ga ta ta fito sanye da after dress suka dubi idanunwan juna kai tsaye ya tura mata wani sako, ta karba amma sai ta zubar har da tare gira, sai ya fito kai tsaye ya faɗa mata. 

  “Da ɗazun da yanzu ba ki canja a idona ba”.

  Ta kara bata rai ta ce, “Wasa ka ke, amma ni dai nasan na canja tunda ga shi har bakinka ya bude….”

  Tana rufe baki, ya magantu. “Zan yi tambaya. Ganin da na yi miki babu wannan after dress da matsala ko babu? Wai idan muka kalli hakan ta fuskar addini da kuma al’adar bahaushe”.

  Ta jima tana jan fasali sannan ta ce, “Ni ba diyar malamai ba ce, kuma ban karanci Hausa da al’adu ba” 

  Ya kada kai, ya ce, “Ni na ji a raina a duk bangarorin biyu, wato addinin da al’adarta babu matsala. Abin da kuma azancina ya kasa fassarawa shi ne, banji kin canja a idona da zuciyata ba, a ganin da na yi miki dazu da na yanzu da ma duk wanda na sha yi miki a baya tun kafin aurenmu, ko ke za ki iya fassarawa?” Kai tsaye ta amsa masa

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Also Read:

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.

Back to top button