Karfe A Wuta Chapter 4 By Ayshercool
“No Nabila, abun da ki ke yi is too risky, mutanen nan da gaske suke, they mean what they said, kar ki jefamu a matsala”Nabila ta ce”Karatunki ya tashi a banza kenan sumayya? Idonki har da hawaye saboda takaici. Wasu lokutan kin fiye sokwanci sumayya, da ni ce da tuni na ci buhun ubanta”.Sumayya ta ce “Ni ce sokuwa ko? na gode amma ni ba zan iya kasadar da ki ke yi ba, na rasa aikina, but wait mu je na rakaki in da aka aike ki mana”Nabila ta ce “Wa? Taɓ tuni na kira MD na bashi uzuri, dama barrister Habib ne ya aike ni, yadda wannan matar ta wurin aikinku take, lawashi ko lotion take, haka yake yi mini, ba ya ƙaunata””A’a, naki ya sha banban da nawa Nabila, shi taimakonki yake yi ai”Nabila ta kwaɓe fuska ta ce “Ke, idan fa kin ga ina zuƙewa a aikin nan, wanda za a kare ba shi da gaskiya ne, MD zan saka ya canza mini team daga na su Barrister Habib, na Barrister Bashir nake so, wata zazzafar shari’a za su kara, shari’ar manya ce, a kan kuɗi, zuwa zan yi na sha kallo, kuma an ce akwai yiwuwar na haɗu da masoyiyyata kwanan nan”Sunayya ta ce “Wa kenan?””Anty Naja’atu Bunkure mana, kin san am die hard fan of that woman, Barrister Naja’atu duniya ce, ga gayu malam, harshenta akwai turanci, kamar wadda aka haifa royal palace ɗin Elizabeth”Sumayya ta yi tsaki ta ce “Aikin banza ƴar wahala, ita ta zama abun da ta zama a harkar aiki, har tana burgeki, ke kuma kina zaune kina shashanci, wallahi ƙarshe ki koma ƴar ɗaukar jakarta”Nabila ta ce “Kan uba, degree holder in yi dakon jaka, Kin ci mutuncina fa, Sumayya ta girgiza kai, haryanzu Nabila shirirta da yarinta na damunta.Ko da Nabila ta je gida, tun a tsakar falo take tambayar magajiya, ina DSP.”Bai dawo daga aiki ba, na ji ɗazu yana cewa ko za su je ringin”Nabila ta ce “Aikuwa ya yi ya dawo, sun bayar da maza, in mun zauna ya yi ta cewa police ya fi lawyer, yau zai sha kunya idan ya ji me suka yi. Yau zazzafan debate ne tsakanina da shi, har lemo zan yi mana aji daɗin yin musu”Anty ta ce “Ka ji mashirirciya, musun da za ku yi za ki haɗawa lemo?”.”Eh mana, ɗan sanda sharri, lawyer kuma musu” tayi maganar tana dariya.Wani mugun kallo mama ta yi mata, yaran gidan nan har take suke yi wa Nasir da discipline master, saboda yadda suke jin tsoron sa, amma tsakaninsa da Nabila sam ba haka bane ba, suna good time sosai da Nasir, kuma duk gidan bayan Abba ba ta da abokin hira ko shawara sai shi.Nabila ta share mugun kallon da maman ke yi mata, ta tafi ɗaki.Misalin ƙarfe huɗu na yamma, Sumayya ta ga kiran lawisa, kawai ta basar ta cigaba da kallon tv, ta kira ya kai sau huɗu sannan ta ɗaga.”Ki na ji ina kiran waya ki ka ƙi ɗagawa?””A silent take, bacci nayi ne”.”Ki tura mini recodings ɗin nan, su murtala ba su sami wani samo rahotanni masu muhimmanci ba, kuma na ga su Mikiya radiyo duk sun wallafa labarin yaron nan, ki turo mini mu ga wanda za a iya tacewa a saka” Sumayya ta taɓe baki ta ce “To”Ta kashe wayar, ta ce “Allah ya ƙara, da mu muka fara sanar da labarin, kuma mu ka saka a internet, ai da ya fi, tun da ni ce ƴar jarida ta farko da ta fara zuwa wurin, amma ki ka ƙi”Ta lalubo lambar Nabila ta kirata, ta gaya mata abun da ya faru. Nabila ta ce “Amma baki da wayo sumy, ke yanzu sai ki tura mata, saboda ba ki da zuciya?””To yaya zan yi mata?””To amma kin san ko kin tura mata, sunanta za ta faɗa a mai rahoton ko wanda ya karanta ba ke ba ko?”Sumayya ta ɗan yi shiru ta ce “Kuma fa haka ne””To tun wuri ki ce mata kin goge kawai, gobe ba za ta ƙara yi miki wulaƙanci ba”.Sunayya ta ce “Haka za ayi, na gode sosai” cikin hanzari ta kira Lawisa, ta sanar mata da cewa ba ta ga recordings ɗin ba.Aikuwa ta hau ta da bala’i, Sumayya ta danna recording tana dariya ƙasa-ƙasa da niyyar ta turawa Nabila.Bayan sun gama wayar, ta turawa Nabila, suka din ga dariya, Nabila na ƙara bata ƙwarin gwiwar, kar ta sake ta ɗauki raini ko wulaƙanci daga wurin lawisa.Ta kuma cigaba da lallaɓa sumayya, a kan lallai ta koma asibiti, ta sake tattaunawa da mutumin nan, ko iya sunan mai laifin ta samo.Barrister Habib ne ya shiga office ɗin MD, ya zauna suka gaisa, cikin takaici Habib ya fara magana, “Barrister, ni fa na gaji da iskanci yarinyar nan, idan a team ɗi na za ta zauna, ta zauna, kuma dole ta yi biyayya ga abun da na sakata, idan wurin Bashir za ta koma, ta koma na gaji da iskanci da rashin mutuncin da take aikatawa, ba ta san aiki ba ko kaɗan”MD ya ce “Calm down Habib, na sani wallahi, na san ku na haƙuri da ita, wallahi nima nauyin mahaifinta nake ji ne, abun da yayi mini a rayuwa idan na kore ta ban yi wa kaina adalci ba, shi ma yana yawan bani haƙuri a kanta, marainiya ce kuma ba ta da cikakkiyar lafiya.””Mu ma duk marayun ne ai, waye yake iskancin da take yi? Ta zo lokacin da ta ga dama ta tafi lokacin da ta so, she’s not serious at all””Na sani, kuma nima ina gani, ka rabu da ita, duk wani abu da za ku yi ku daina sakata a ciki, ƙyaleta da bashir ɗin, shi ne daidai da ita, ku yi haƙuri dan Allah” MD ya din ga lallaɓa Habib, dan ba zai so rasa gogaggen lawyer kamar Habib a law firm ɗin sa ba, a kan Nabila da ba aikin ne a gabanta ba.Yau weekends ne, gaba ɗaya iyalan major na babbn falo, kowa ya ja nasa wuri yana karyawa, Nabila ce kawai babu a wurin.Tun yana jurewa ya kasa, yayi gyaran murya ya ce “Ina arfa ne?”Anty ta ce “Bacci take yi”Ya kalli walida ya ce “Tasota, ta fito ta karya, sai an cinye an bar ta, ta cikawa mutane kunne da kuka”Kusan mintuna goma da taso ta, sannan ta fito, kayan bacci ne a jikinta, dogon wando da rigarsa har gwiwa, kanta babu ɗan kwali.Nasir ya tsura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi.Abba ya ce “Ina kallabinki? Ki ka fito da wannan gashin ba kyan gani, kamar totuwar masara?”Ta saka hular hannunta ta ce “Haba Abba, dan daga bacci na tashi ne fa””Tafi can ƙazama, kullum kai babu kitso, ba za a rasa kwarkwata a wannan gashin ba” dariya aka hau yi mata.Ko a jikinta, ta zauna kusa da Abba, ta kalli Nasir ta ce “DSP, yaushe ka dawo ba labari, ya hanya?”Ya jinjina kai ya ce “Alhamdilillah”Major da kansa, ya taya Nabila haɗa shayi, ga soyayyen dankali, ga bredin ta, amma tana buɗe bredin ta ce ba za ta ci ba, kwantai ne.Major ya miƙa mata nasa ya ce “Duba zaki iya cin wannan? Dankali kawai ba zai riƙe miki ciki ba” ta duba buredin Abban ta ce “Eh wannan sabo ne, Abba ka ƙara mini ƙwan, ni ba na son dankalin ma”Ya ce “To shikenan, ɗauki nawa da ma ni yanzu ƙwai bai dace da ni ba, a shekaruna”Idan da sabo, sun saba da ganin irin wannan fifikon da major yake nunawa, duk da mutum ne mai ƙaunar yaransa sosai da sosai, amma son da yake yi wa Nabila na musamman ne, amma fa hakan ba ya hana idan suka yi laifi, ya hukunta su kamar ba ƴaƴan cikin sa ba.Anty ta ce “Arfa ba zaki bari Major yayi ƙiba ba, kalli yadda ki ke tara mazaunai, saboda ci”Yayi murmushi ya ce “Tafi kowa girma a gidan nan”Nabila ta ce “Abba, Allah ya ƙara arziki, ka yi ta sayowa mu na ci””Amin arfan Abba”Nasir ma ya juye mata nasa ƙwan, ta tattare tana dariya, dan ta na son ƙwai sosai.Mama kuwa kamar za ta yi bindiga, saboda baƙin ciki.Bayan an kammala cin abinci, su walida ne suka kwashe kwanukan da aka ci, Nabila kuma ta hau labartawa Nasir, abun da ya faru da sumayya da ta je Asibiti.Fafur Nasir ya ce ƙarya take yi.Ta haɗe rai ta ce “Yaya, wai meyasa a duniya jami’an tsaro ba kwa yadda kun yi laifi, ko wani ne daga cikinku yayi, sai kun ƙaryata, kun kare mutum””Wa ya gaya miki hukuma tana laifi?””Ba mutane ne hukunar ba? Ai mutane na laifi, kuma hukuma ma suna yi, wallahi da gaske nake, ka bincika ka ji kuma, koma na kira maka sumayyan”Ya ce “A’a ai ƙarya ki ke yi, ni zaki zauna kawai dan ki ƙure”Duk yadda ta so, ta fahimtar da shi, amma ya ƙi fafur.Abba dai kallonsu kawai yake yi yana dariya, ganin ba zai yarda ba, ya sanya ta ƙyale shi, ta koma wurin Abba.”Abbana” tayi maganar tana ɗan murmushi.Abba ya ce “Kuɗi zaki tambaya kenan?”Ta girgiza kai ta ce “A’a Abba, abu zan tambaye ka””Ina jin ki””Abba dama, wata amarya ce, suka kira ni a waya, zan je gida na yi musu make up, ita da ƙannenta na biki, za su biyani, VIP ne har gida”Haɗe rai yayi sosai sannan ya ce “Me na gaya miki a kan wannan sheɗancin? Kin san na hana ki sabgar banzar nan, ban da kalen sheɗanu jikinku, me wannan shashancin zai amafana miki, na fuskanci kin fi fifita wannan kwalliyar a kan aikinki, to babu in da za ki je”.”Dan Allah Abba, wallahi zan samu kuɗi fiye da salaryna, dan Allah””Ba in da zaki, tun da babu abun da ki ka rasa a gidan ubanki, ba matar da zaki bi gida ki na shafawa hoda, idan ta matsu tayi da kanta mana, banda shashanci ace mace ta zauna sai an bita gida shafa mata hoda da gazar””Abba!””Shut up” yayi mata tsawa, hakan ya tilasata mata yin shiru.Walida kuwa faɗan Abban dariya ya bata, wai idan sun matsu su yi da kansu, ba wadda za aje gida shafawa hoda.Nabila ta din ga jin ko a ɓoye sai ta je, tana son sana’arta ta kwalliya, Abba kuma ba ya so, wai shashanci ne da fatan aljanu, ita kanta idan tayi a fuskarta wasu lokutan, ya din ga faɗa kenan.Akwai ranar da za ta je biki, ta yi kwalliya ta saka eyelashes, ya kirata dan ya ga meya samu idonta, gashin idonta yayi tsawo haka, tun da ta ce masa sawa tayi, ba ta ankara ba, ya saka hannu, ya fige shi sai da ya haɗa da gashin idonta, ya ce ya kuma ganinta da shi sai ya zaneta.Har a gaban saurayi, ya taɓa korata gida, wai ta je ta wanke fuskarta, ba za ta cuci ɗan mutane ba, duk ta damalmala fuska da hauka, ta zama kamar wata bebin roba.Ta rasa meyasa Abba yake adawa da sana’ar nan tata.Nabila tun a weekend, take cigaba da zuzutawa Sumayya trial ɗin da za su je, kotu ranar laraba, farincikin ta ya kasa ɓoyuwa, wanda hakan ya samo asali ne, da yadda ta ga Barrister Habib ya ƙyale ta, ta koma team ɗin Bashir, kuma ta samu labarin barrister Naja’atu ma tana da shari’a ranar a kotun, dan haka za ta haɗu da ita. Nabila uniform ɗin ta, tamkar su yi magana, saboda ɗaukar guga, ita kanta a bar kallo ce a cikin kayan, ba fara ce tas ba, amma haskenta mai kyau ne da ɗaukar hankali, domin kuwa jikinta kamar ƙwai, dan tana kashewa Jikinta kuɗi ba kaɗan ba, ba ta da wata damuwa, ba abun da take yi da kuɗi, ban da sayen kayan gyaran jiki, ta samu kuɗi a aikinta, major ya bata, Nasir ma ya bata, ga wanda take tatsar samari, ga ƴan sana’ointa, dan haka kuɗi sam ba matsalarta bane ba.Barrister Naja’atu Bunkure matashiyar lawyer, mai dakawa maza gumba a hannu, karo da ita sai lawyern da yake jin kansa ya isa, dan abu ne mawuyaci case ya shiga hannunta ba ta yi wining ba. Ana yawan sanar da ayyukan alkhairin ta, a gidajen rediyo na taimako da tsayawa marasa galihu a kan shario’i daban-daban.Bakin Nabila ya ƙi rufuwa, ganin yau ga ta ga Barrister Naja bunkure, wata ƴar gayu da ita, yadda ta gabatarwa da kotu kanta kawai, ya isa ka tabattar da ta san me take yi, ga yaren nasara a harshenta wato turanci.Gaba ɗaya hankalin Nabila ba ya kan shari’ar, yana kan bunkure, da yadda take magana.Murna kamar nabila ta taka rawa, yau ga ta ga mentor ɗin ta.Sumayya ta samu damar editing news yau da kanta, kasancewar MD yana ta mitar, ta daina ware kanta, ta din ga shiga ana aiki da ita a haka za ta goge.Kiran Nabila ta gani, dan haka ta ɗaga ta ce “Kiran me ki ke yi mini ina aiki?”Sama-sama ta din ga jiyo numfashin Nabila, muryarta ƙasa-ƙasa ta ce “Kin tashi daga aiki ne?””A’a menene meyafaru?”A galabaice ta ce “Na dawo chamber ne, na ɗauki kayana, ina hanyar komawa gida, ji nake kamar ciwona ne zai tashi, ina titi dan Allah Sumy ki zo””Subhanallah, gani nan zuwa amma babu wani a wurin da zai kai ki gida?””Ni ba na son damun kowa, dan Allah besty ki zo, kar na mutu a titi”Ganin ta gama abun da take yi, ya sanya a gurguje ta ɗauki jakarta, ta fita, ba ta tsaya ko ina ba, sai hanyar wurin aikin su Nabila, tana ta rarraba ido a titi tana kiran wayarta.A kan wani tudu ta hango Nabila, idanunta sun yi jawur, da alama tayi kuka sosai da sosai.Ta ce “Mai napep, bari na ɗauketa ka kaimu gadon ƙaya dan Allah, ba ta da lafiya”Ya ce “To shikenan” ta sauka ta rungumo Nabila, ta taimaka mata, ta shiga napep ɗin, sai dai babu baki, sai numfashi take sama-sama.”Arfa, meyafaru an ɓata miki rai ne?” Ta girgiza kai alamar a’a.”To menene? Haka kurum ciwon ya tashi” buɗe baki ta yi, da nufin yi wa sumayya masifar ta ƙyaleta, amma ta ji numfashin ta, zai gudu ya bar huhunta, hakan ya sakata yin shiru.Can kuma a hankali ta ce “Sumayya mu je gidanku, wurin umma”Sumayya ta jinjina mata kai, haka aka yi.umman sumayya na ganinsu hankalinta ya tashi, Nabila ta samu wuri ta kwanta.Umma ta ce “Sumayya, me aka yi mata ne?””Wallahi umma ban sani ba, kawai kirana ta yi a waya, ciwonta ya tashi”Cikin kuka Nabila ta ce “Umma dan Allah ki yi mini addu’a, ki ƙyale sumayya”Umma ta ce “To shikenan” ta din ga tofa mata addu’a, har aka samu ta yi bacci.Bayan awa ɗaya da rabi, ta farka, har ta samu ta ci abinci ta yi salla, umma ta din ga tambayarta, ko wani abun aka yi mata, amma ta ce a’a.Ganin ta ware, ya sanya umman basu wuri, Sumayya ta sake kallonta ta ce “Ke, wallahi wani abu aka yi miki, yanayinki ya nuna mini, kin ga idonki kuwa, ki gaya mini menene?”Tayi ajiyar zuciya ta ce “Sumy, ashe haka ake ji, idan aka wulaƙanta mutum mussman a gaban jama’a, a dizaga ka””Menene? Waye ya wulaƙanta ki?”Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Kin san Naja’atu Bunkure?””Ba dole na santa ba, a wurinki na santa ai””Ashe matar nan tsinanniya ce”Da sauri sumayya ta ce “A’uzubillahi, me yayi zafi, mentor ɗin taki?”Nabila ta ce “Zilwajahiani ce, abun da muke ji a kanta daban, yadda take daban. Yau muka haɗu a kotu, kin san ina cikin team ɗin barrister Bashir, tare muka je court yau.Bayan an fito, jiki na tsuma na bita, ƴan jarida sun baibayeta, na yi mata magana kin ga wulaƙantaccen kallon da tayi mini? Ba shi ne ya dame ni ba, duk da uniform ne a jikina, na cire girman kai na gabatar mata da kaina, a matsayin lawyer mai koyi da ita, amma still ban isheta kallon kirki ba. Abunka da zuciya da abun da take so, na matsa tare da miƙa mata wayata, a kan ta bani lambarta, sai ce mini ta yi ba za ta bayar ba, kar na isheta da kira. Na ce mata bakomai, a matsayina na mai koyi da ita, kuma mai ƙaunarta, dan Allah ko mintuna uku ta bani, na daɗe ina burin haɗuwa da ita. Ina son ta bani shawara a matsayina na lawyer mai tasowa, kuma ta bani tips da zan bi, na zama kamarta a rayuwa, dan ina son ta da irin ayyukan da take yi. Ta ƙare mini kallon baki isa ba, sannan ta ce ‘Ki zama kamar ni kuma? Taka matsayin da na taka? Never! Don’t even give a try, ba zaki taɓa zama ba, and leave my way please, ina da abun yi”Haka fa ta ce mini, a gaban mutane da masu yi mini dariya, da masu yi mini Allah ya ƙara wai neman suna da gidin zama ne ya janyo mini, wasu kuma su ka bani haƙuri wai haka halinta yake. Sumayya yau na tozarta, an wulaƙanta ni, duk yadda nake ganin ina da class, soyayya ta rufe mini ido, saboda ina ƙaunar matar nan fisabilillahi, wallahi da ƙyar na ƙarasa chamber, nan da nan na fara jiri, numfashina ya fara sama, kin ga dariyar da aka yi mini, wallahi na muzanta fiye da tunaninki”Sumayya ta ce “Nabila jikina yayi sanyi, ban taɓa zaton matar nan za ta aikata haka ba, wai meyasa mu mata, galibin mu ƴan baƙin ciki ne? Wato ba zaki zama kamarta ba, sai ka ce wayo da dabararta ne suka ba ta matsayin da take kai”.”Wallahi sumayya, ko zan rasa raina, ko da kasada, sai na tabattar da na yi suna nima, sai dai idan Allah ya ƙaddara na mutu. Amma ina roƙon Allah, in sha Allah tana raye, sai na ɗaukaka fiye da tunaninta, kuma bibiyarta zan din ga yi, da bibiyar duk wani abu da ya shafe ta, sai na rama abun da ta yi mini. I will do a background check on her””Ke fa baki iya ɗaukar abubuwa da sauƙi ba, ki ƙyaleta mana kanta ta yi wa, ni na ce me?, abun da nima ake yi mini, ni kusan kullum ake yi mini, ke yau ne kawai, kuma arfa matsayi na duniya ba na kiyama ba”Nabila ta girgiza kai ta ce “Wannan ke ki ka ga zaki iya, kuma ƙaramar alhaki ce ta wurin aikinku, wannan kuwa dizgin da ta yi mini, in sha Allah rabbi, sai na rama shi, dole na ajiye shirme, na mayar da hankali a kan aikina, ko dan fansar nan, kut wallahi matar nan ta gama cuta ta, kuma ba zan huce ba har sai na rama wallahi. Rakani titi in tafi gida” ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye.Sumayya ta danƙota ta ce “Nabila ki din ga sanyawa zuciyarki salama mana, kin fiye zafin rai, ki bi komai a hankali, kalli yadda ki ka kusa kashe kanki a banza. Idan Allah ya yi nufin ɗaukakaki fiye da ita, ita ɗin banza ta hana, dan Allah ki manta da ita, ki cigaba da rayuwarki”.Ta kalli sumayya cikin takaici ta ce “Lallai ma sumayya, dan ba ki ga abun da ta yi mini ba, a gaban mutane har da masu yi mini dariya. Ni gaba ɗaya ma ji na yi ban yarda da ita ba, abun da ake faɗa a kanta daban, abun da na gani yau a kanta daban, akwai wani abu a ƙasa, and i will run a background check on her, for the first place ma, wacece ita? Idan ta kama har bunkuren zan je mahaifarta, meyasa abun da ake faɗa a kanta daban, ita kuma halinta daban”.Sumayya ta ce “Na shiga uku, Nabila” kafin ta yi magana, Nabila ta yi waje, ta tarar da umman sumayya na salla, ta ce Umma na tafi, ta fice daga gidan.Sosai abun da ya faru ya tsayewa Nabila,da ta tuno abun sai wani irin takaici yakamata.Yau ba kowa ya san ma ta koma gida ba, dan yau babu surutu da hayaniya.Abu kamar wasa, har dare Nabila ta kasa walwala, ko fitowa daga ɗaki taƙi yi, gani take kowa yana kallonta zai gane an dizgata yau, duk iyayin na ta da jan ajin. Nabila irin mutanen nan ce masu saka abu a ran su, dan haka ko ta yi niyyar manta abun da ya faru, sai ta kasa.Ta ɗaukko wayarta, ta kunna data, ta tarar da messages ɗin sumayya, ta na ta yi mata faɗan ta yi haƙuri ta manta da abun da ya faru.Nabila ta yi mata reply da “You are not serious, ki saka ido ki yi kallo”Social media ta hau, ta shiga searching ɗin sunan barrister Naja’atu Bunkure, nan da nan sai ga hotunanta, da wasu daga cikin ayyukanta na jin ƙai, sai dai ba ta samu wani cikakken bayani da take son samu a kanta ba.Tsaki ta yi, bayan tuna yadda take mutuwar son matar nan a baya, har hotonta take sakawa a dp ɗin ta, saboda yadda take ƙaunarta, amma lokaci ɗaya a yanzu ji take yi, ba ta da wani maƙiyi idan ba ita ba.Har sha biyu da rabi na dare, ba ta samu cikakken abun da take son sani ba, sai ma zarge-zarge da suka din ga ɗarsuwa a ranta game da matar.Saukkowa ta yi daga kan gadonta, ta fice daga ɗakin, fita tayi can babban falo, ta nufi kitchen ta samu abun da za ta ci, dan yunwa take ji sosai.Fridge ta buɗe, ta samu ruwa mai sanyin gaske, da coc ta fito falo tana sha.Hasken fitila ta hango a baranda, ba a kashe ƙwan wurin ba, ga abba kullum sai yayi magana a kan rashin kashe kayan wuta, kafin a kwanta bacci.Wurin ta nufa, da niyyar ta kashe ƙwan, ta na zuwa ta leƙa, ta hango nasir a kan kujera, yana ta danna system.Ta window ta je ta zura hannu, tana taɓa masa kunne. Caraf! Ya riƙe hannun ba tare da ya ɗago ba.Tayi dariya ta ce “Shi ne ba ka tsorata ba””Me ki ke tunanin zai razana ɗan sanda?”Ta ce “Ai dai ɗan sanda mutum ne, kuma na san ka ji tsoro mazewa ka yi”Yayi murmushi ya ce “Tsoro sai lauyoyi”Ta buɗe ƙofa ta fita ta zagaya in da yake ta ja kujera ta zauna sannan ta ce “Duk tsoron lauya bai kai ɗan sanda ba”Ya ɗago ya kalleta, sanye cikin kayan bacci pink, masu bargo kanta ko ɗan kwali babu, tayi parking ɗin gashinta”Murmusawa yayi ya ce “Ke kin san babu tsoro ga wanda yake riƙe makami, yayi yaƙi da ɓarna””Hmm, yi dai a hankali, dan harshe ya fi makami dafi, kar lauyoyi su baka mamaki watarana””Ina aiki kin zo zaki dame ni, ina nawa aikin, ina kallabinki?””Yana ɗaki” tayi maganar tana lashe murfin jarkar lemon hannunta.”Kalli abun da ki ke yi kamar ƴar ƙauye, sai an yi magana ki fara ke barrister ce, ke degree holder ” yayi maganar yana mayar da hankali a kan system.Ta numfasa ta ce “Wai aikin me ka ke yi ne?””Wani aiki ne mai wahala, wanda nasara a kansa, na iya sawa na samu cigaba a aikina”.Nabila ta ce “Haba dai, to Allah ya taimaka””Amin” ya amsa ba tare da ya kalleta ba.Shiri ya wanzu na wani ɗan lokaci, sannan ta ce “DSP” “Na’am barrister” “Sannu da aiki” ya ɗago ya kalleta ya ce “Kin isheni fa, za ki tashi ki bar wurin nan””Yi haƙuri, na daina magana”Ya cigaba da aikinsa, ta na shan lemonta, tana jin yadda iska ke kaɗata.Duk abun nan, Abba ta ɗakinsa ya na hango su, sai dai ba ya jin me suke cewa.Can ta sake cewa “DSP”A hasale ya ce “Ke! Meye ne? Tashi ki je ki kwanta dare yayi””Ni na kasa bacci, raina ne a ɓace”.”Ai dama kullum cikin ɓacin rai ki ke, tun da ke a rayuwarki ta duniya, baki da haƙuri tashi ki bani wuri”Ta marairaice ta ce “To ka tsaya ka ji me aka yi mini mana, dan Allah kafin na tafi, ka gaya mini me zan yi, wanda zai saka na yi suna, kowa ya sanni” tayi maganar very serious.Cikin gatse ya ce “Ki nemo in da Aminu Viper yake, ki taimaka mini na kama shi, kin ga sai ki yi suna, ni na samu cigaba a aiki”Ta fuskance shi sosai ta ce “Waye shi, a ina yake? Kamar na taɓa jin sunansa”Ya kalleta ya ce “Shi nake ta aiki a kansa, galibin aikin ta’addancin da ƴan daba suke yi, a wasu shiyyoyin da saka hannunsa, yaransa ne. An ce lallai na kamo shi, tun da yankin da ake ɓarnar ƙarƙashin kulawata yake akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison””Dan Allah idan na nemo maka shi, zan yi suna, kowa ya sanni?”Kallon baki da hankali yayi mata, ya cigaba da abun da yake yi.”Ka ga riba biyu kenan, na yi suna, kuma ka samu cigaba a wurin aiki, yes! Amma na ji ka ce akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison how? Kun tabattar da hakan ko kuwa? Ka bani hints mana, laifin me ya yi a ka kai shi prison ɗin?”.Takalminsa ya ɗauka ya miƙe tsaye ya ce “Tashi ki bar wurin nan, tashi maza”Da haka ya koreta, ta tafi ɗakinsu. Sai dai da ga koma ɗakinta, ta dinga sintiri a cikin ɗakin, sosai ta ji maganar Yaya Nasir ta shiga ranta, ina ma hakan ta tabatta.”In taimaka masa ya kama ɗan ta’adda, in nemo haƙiƙanin dalilin barinsa daga gidan yari, idan guduwa yayi me ma’aikatan suke yi, idan sakinsa aka yi laifin me yayi, aka sake shi duk da hatsarinsa, na bankaɗo ainihin identity ɗin Naja’atu Bunkure, na gyara career ta, wai ma menene dalilin da ya sa ban zama ƴar sanda ba?, na zama wata lauya yau ka kare mai gaskiya gobe mara gaskiya. Ta yi wani irin shu’umin murmushi ta ce “Accepted DSP Nasir, zan nemo maka Aminu Viper, na bibiyi laifin da ya aikata, da yadda aka yi ya bar prison.
Ayshercool.
08081012143
