Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 29 Book 2 Hausa Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)


KARANTA ZAFAFA 2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


Tsawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, after some minutes sai gashi ya fito jikinsa sanye da jeans da t-shirt, hannunsa ruƙe da wayarsa ya samu wuri ya zauna saman Sofa, cikin sauri sehrish ta gaishe shi “Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya,” a tunaninta bazai amsa ba amma sai ji tayi yace “Alhamdulillah Am well,” murmushi ta ɗan saki, kafin ta shiga haɗa masa Tea a cup mai ɗan xafi ta tura masa agabansa, hannu yasa ya ɗauka yakai bakinsa yana kur6arsa a hankali, ci gaba da saving ɗinsa sehrish tayi, kamar daga sama taji yace “Meyasa jiya ba’a kawo min fruits dana buƙata ba”!?

Murya na rawa sehrish tace “na same ka kana bacci ne lokacin dana kawo maka,” ta ƙarasa maganar tana kallon fine face ɗinsa,

Bayan wasu mintina ya kuma cewa “daga yanzu inaso a rinƙa kawo min Coffee or Tea wit fruits around 12 pm,” 

  Cikin hanzari ta amsa mashi da cewa “Insha Allah,” jinjina kansa ya ɗanyi yayin da yake ci gaba da cin pancakes ɗin data haɗa masa da Zuma,

   tsayawa sehrish tayi tana jiran ya kammala ta zuba mashi wani abun, 

  Wayarsa dake ajiye a gefensa ta soma ringing cikin sauri takai hannu zata cirar mashi tissue ya goge hannunsa adai-dai lokacin shima ya miƙa hannunsa zai cira karaf suka haɗa hannunsu cikin na juna 😌 zaro ido sehrish tayi cikin tsananin jin tsoro tana ɗan kallonsa,

  Shi kuwa bin hannun Yarinyar yayi da kallo sam ba’a yi masa irin haka amma yayi mata Uziri ne saboda da alama batasan ko shi wanene ba, gata kuma ƙaramar yarinya,

  “Am sorry,…’ sehrish ta furta aɗan tsora ce yayin da ta janye hannunta, shi kuma ya ciri tissue ɗin a natse yace “Don’t repeat that mistake again,” 

  Cikin sauri tace “Insha Allah,” goge hannunsa yayi sannan ya ɗauki wayar ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnansa, taso taji mai zai ce acikin wayar amma sai dai kash cikin wannan harshen taji yana magana wato Espanol da alama yafi jin yaren sosai ko kuma shi ya taso yana ji,

  Zuba mashi ido tayi tana kallon shi tun daga shafaffen cikinsa har zuwa saman wide Chest ɗinsa haɗaɗɗiyar ƙira, maganar haroon ta tuna dayake cewa Zaren ba Kalar yadin bane Iska ce kawai zata wahalar da mai Kayan kara, tabbas kuwa yayi gaskiya amma in ta tuna wannan karin maganar da ake Cewa *DUK KYAN TAKALMI ƘAFA CE ZATA TAKA SHI* sai taji wata irin natsuwa tazo mata, tana tunani tana ci gaba da kallon fuskarsa yadda yake Moving pink lips ɗinsa yana magana tamkar baison yi, da kuma yarda yake faman lumshe sexy blue eyes ɗinsa ba ƙaramin Yanayi yake jefa ta ba, 

“Allah yasa bada budurwarsa yake waya, koda yake aunty azmee tace baya soyayya, To Allah yasa dai bada mace yake waya ba,” ta faɗi acikin zuciyarta saboda ganin yarda yake ta faman lumshe idonsa kamar wanda ke waya da mace cikin shauƙi.

Karanta>>> Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

  tana cikin yi mashi wannan kallon ƙurullan nata ya kamata, adai dai time ɗin ya ɗan ware idonsa direct suka sauka kan na sehrish dake faman Zuba masa ido tana kallonsa abunda ya tsana arayuwarsa ba, sam bata lura  daya kamata ba saboda idonta na akan Sumar kansa, har sai da ya ɗanyi gyaran Murya cikin sauri ta wurga kwayar idonta kan tashi aikuwa har sai da ta ɗan Razana ganin ya aza idonsa acikin nata Unexcepted,

   ƴar harara ya wurga mata sannan yace “Stop looking at me, i don’t like,’ ya faɗi tare da cigaba da yin wayarsa,

   Sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunyar Kamatan da yayi tana masa kallon kurulla, amma wannan hararar daya sakar mata ba ƙaramin kashe mata zuciya yayi ba, ya jima yana wayar kafin ya kammala ya ture ta gefensa, sehrish ta cigaba da saving ɗinshi harya kammala cin breakfast ɗin nasa sannan ta tattare komai ta fuce dasu kitchen ta ajiye agefen Kitchen sink yadda in tadawo wankewa kawai zatayi, 

Daker ta iya fitowa daga kitchen ɗin saboda taga duk sun Hallara suna yin breakfast, tunkarar su tayi gabanta na faɗuwa saboda ganin hada HAROON zaune ga kuma Twins duk suna zazzaune, tunkan ta isa junaid na ganinta yasoma sakin murmushi kamar gonar Auduga, sallama tayi masu suka amsa sannan ta kalli Abbansu wanda keta faman sakar mata murmushi tace “Ina kwana Abba, fatan kun tashi lafiya,” Abban nasu yace “Alhamdulillah My Only daughter, yanzu nake tambayar azmee take cemun kin shiga kaiwa Babban yayanku Abinci,” 

“Eh hakane,” ta bashi amsa sannan ta juya ta kalli sauran ta gaishe dasu duk suka yi tsit sai kanal Yusif daya ce “Ae nayi tunanin bazaki gaishe da yayyen naki ba, yanzun nan nayi fushi dake,” 

   Murmushi sehrish tasaki tana mai mamankin hali irin na kanal Yusuf sam bakamar na sauran ba,

  “Samu wuri ki zauna mana,” Abbansu ya umarce ta kujera taja ta zauna zuciyarta na ɗar ɗar, tana a jerin inda Abbansu yake gefensa junaid daga shi sai ita, a ɗayan side ɗinta kuwa haroon ne tabbas tasan dole ya hantare ta, ga kuma AYAAN Da JAHAN da take facing ɗinsu duk ta tsargu saboda tasan halinsu suna jere tare da kanal yusif, 

  azmee da kanta tayi saving ɗinta acikin plate ta buɗe saving dish ta zuba mata Chicken pper soup

Sannan ta haɗa mata da Cofee acikin Cup☕ Sehrish ta kalli azmee tare da cewa “nagode aunty amzee”

Karanta>>> Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

 hararar ta amzee tayi alamar cewa bata son godiyar,

..a hankali take kurbar coffee ɗinta duk da kermar da hannunta ke yi, muryar haroon taji a ƙunnanta yayi ƙasa ƙasa da Voice ɗinsa don kada wani yaji yace”Su acici mala’ikun tauna, an fa samu wurin zama, to adai ci ahankali kar a shaƙe,” banza tayi dashi batace komai ba, amma sam tarasa cin chicken ɗin dake agabanta shaƙe cikin plate, 

  Sanyayyiyar muryar junaid ce ta ratsa kunnanta da cewa “Sehrish ya akai naga yanayin ki ya canza? ko breakfast ɗinki baki fara ci ba,” 

   tace “bakomai junaid kawai bana jin daɗi ne, inaji kamar na tashi na tafi ɗaki kawai,” 

  cikin sauri junaid yace “a’a reesh pls kada kiyi haka ki daure kawai ki ci, kinji My sister,” murmushi tasaki jin sunan da junaid ya kira ta dashi, ɗan ɗagowa tayi da idonta karaf suka sauka kan na Jahaan da Ayaan da suka ɗago atare, shiru tayi tana ɗan kallonsu, atare suka yatsina fuska suna yi mata wani irin kallon Tara saura kwata,

ƙasa da murya Jahan yayi tare da cewa “Ayaan kalli yarda junaid ke fira da wancan yarinyar, shi junaid kowa nasa ne, baya tsoran mutane sai sunyi masa Illah,” yayi maganar cikin nuna damuwa

   Ayaan yace “ba kai kaɗai ba jahaan, ni ma abun na damuna wlh, shiru kawai nayi amma na lura da yadda suke shiri, bazan ƙyalesa ba dole na buga masa warning Allah,

   Jahan yace “gasky kam, janyo shi yakamata muyi a ɗakin mu, muja masa kunne tunda shi shashasha ne kowacce baƙuwar fuska shige mata yake yi, sai kace ba Jinin mu ba,”

Ayaan yace “kwarai kuwa, ae shi junaid da kake ganinsa half cast ne, ruwan Abba ne dana Mommyn mu ya ɗauko, mu kuma ruwan mommy ne kawai ajikin mu, banda na daddy,”  Wannan maganar ta Ayaan tasa kanal yusuf fashe wa da dariya ashe duk yana jin firar tasu saboda shine kusa dasu a jere, ɗagowa su kayi suna kallonsa dukansu hada Abban nasu da junaid da sehrish da azmeee,

Abban nasu yace “in ce dai ko lafiya? Kanal yusif yace “babu komai Abba, gasu nan su Ayaan da jahan ne suke fira su faɗa maka abunda suke cewa ka ji,” 

   tunkan Abbansu ya tambayesu suka haɗa baki wurin cewa “Babu komai Abba, firar wani film muke yi,’ 

  girgiza kai kawai Abbansu yayi, Haroon kuwa cewa yayi “Allah yayi wa ɗan iska uwa koda ta kara ce,” ya faɗi yana kallonsu salon jan faɗa kawai, Babu wanda ya tanka masa miƙewa Ayaan da jahan su kayi tare da yiwa Abban su sallama suka fuce.

Karanta>>> Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

💪  Fito wa marshal Omar yayi daga upstairs yana saukowa down jikinsa sanye da jallabiya ash colour sai faman ƙamshi yake yi, tunkaro su yayi Abbansu na ganinsa yafara fara’a yana cewa “Omar sai yanzu ka tashi? tun ɗazu nake ta faman waige-waige naga ta ina zaka 6ullo,

   Ɗan ƙayataccen murmushi yasaki tare da cewa “Gm Abba ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya,”

  “Alhamdulillah Son, Samu wuri ka zauna na baka abinci a baki,” cikin zolaya yayi maganar su kuwa sauran dariya su kayi, ɗagowa OMAR yayi tare da gaishe da Azmee ta amsa mashi, sannan su kuma Su kanl yusif da junaid suka shiga gaishe shi, Haroon yace “Barka da fitowa Damusa mai maganin ƙananun ƴan iska,” 

ɗan harararsa Omar yayi tare da cewa “Zaka fara wannan tsokanar taka ko? To ka shiga taitayin ka ko yanzun nan na saita maka waɗannan haƙoran naka, don naga ba’a jere suke ba,’ shima da zolaya yayi maganar ayayin da yake zama azmee kuma ta soma zuba masa breakfast ɗinsa,

   Mayar da idonsa yayi kan JUNAID dake ta faman sakar masa murmushi yace “My shagwa6a boy, irin wannan kallon haka da kake mun ko kana buƙatar wani abu ne?

  Cikin jin kunya junaid yace “Babu komai ya Omar kawai inaso inta kallon ka ne, aduk lokacin danayi kewarka,” 

  Murmushi Omar yayi kafin yace “Ae da ka sani jiya ka shigo bedroom ɗina mun kwana tare,” 

  Junaid yace “ae Abba bazai bari ba, Kishi yake yi,” gaba ɗayansu suka fashe da dariya jin abunda junaid yace, 

   Abban nasu kuwa murmushi kawai yayi tare da ɗan jinjina kai yana kallon junaid ɗin,

Haroon yace “Ae na Lura da yadda Abban mu ke ji dakai, kamar kai kaɗai ya haifa bayason komai ya same ka,’

   Junaid yace “Yaya haroon ka ta6a ganin inda mutun ke wasa da bugun zuciyarsa? to aeni zuciyar Abban tamu ce gaba ɗaya shiyasa Yafi sona,” yayi maganar wit proud,

  ta6e baki Haroon yayi yana kallonsa, MARSHAL OMAR yace “Ae bama Abban mu kaɗai ba Haroon, Junaid farin cikin kowan nan mune acikin gidan nan, bamu son wani abu ya same shi domin tamkar mu yasha fa, JUNAID BUGUN ZUCIYAR FAMILY ɗin mune gaba ɗaya,” 

  Kanal yusif ya ƙara da cewa”Maganarka gaskiya Ce Yaya OMAR, Ni kaina aduk lokacin dana aza idona akan na baby junaid wlh farin ciki ne ke ziyarta ta, kuma aduk lokacin da wani ya 6ata mun rai junaid ne ke lallashi na da kalaman sa masu kwantar da hankali, tabbas shi Yaro ne amma yana da baiwar iya sarrafa harshe wurin farantawa mutane,” 

Har cikin zuciyarsa yake wannan bayanin, junaid kuwa farin ciki ya hanasa idasa shan cornflakes ɗin dake agabansa, haka zalika Abbansu murmushi ne a fuskarsa saboda bai da Burin daya wuce yaga ana yabon Jininsa, kuma ma Junaid, 

  Haroon kuwa tuni zuciyarsa tayi baƙiƙƙirin ji yayi bazai iya ci gaba da zama ba, don haka da hanzari ya miƙe tare da fuce wa daga babban falon gaba ɗaya, sam ba wanda ya damu dashi bare su son halin dayake ciki,

  Duk fa wannan abun dake faruwa a kunnan Sehrish tana sauraron su, sam tagaza gaishe da Marshal Omar tsoran ta kada ya ƙi amincewa da ita duk da ta lura bazaiyi Tsauri ba,

  Sai da tabari duk sun natsu wuri ya ɗanyi tsit sannan ta ɗanyi gyaran Murya tare da cewa “YAYA OMAR ina kwana,” 

    Jin Muryar mace yasa shi saurin ɗagowa yaga wacece karaf fararen idanuwansa suka sauka akan na SEHRISH, ae baisan lokacin da ya fesar da Tea ɗin daya kur6a abakinsa ba, hankali atashe yake kallonta, Ajiye cup ɗin dake hannunsa  yayi tare da miƙewa tsaye idonsa akan na sehrish wadda ta gama tsorata dashi ganin yadda ya firgita da ganinta kamar yaga wata ALJANA,  tuni jikin sehrish ya soma kerma, ita kanta azmee ta tsorata da ganin reaction ɗin Omar akan Sehrish haka zalika Abbansu kanal yusif da junaid duk mama ki ya ɗaure musu kai

  Nuna ta da hannu Marshal Omar yayai tare da cewa “Keeeee !!!!!!!!!! ” gaba ɗaya ya razana da ganin yarinyar, ganin haka yasa kowannan su ya tashi tsaye suna kallonsa,

Abbansu yace “Omar meya faru ne? Na manta ban faɗa maka ba game da yarinyar nan ba, ƴa Ce Allah yabani daga sama….

.kallonsa Omar yayi a ruɗe kafin ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda tuni idonta sun cuccuko da kwalla saboda tashin hankali, 

   da hanzari OMAR ya bar dining ɗin yayi saurin haye wa upstairs part ɗinsa, zuciyarsa a cunkushe sam yagaza gane ma Idonsa dayake yi masa Gizan Fuskar Hosana da Jahad a fuskar wannan yarinyar daya gani a yanzu, 

   Bedroom ɗinsa ya shiga hannu yasa ya ɗauki wayarsa daya ajiye asaman pillow, cikin hanzari ya daddana layin aunty babba ya buga mata Call, kusan 3 times yana kira bata shiga, numbar Hafsat ya kira itama tana ringing ba’a ɗagawa,

Download>>> Jiddertul Khair Complete Document

 Wurgi yayi da wayar saman gadonsa, tsayawa yayi yana faman sauke ajiyar zuciya, hannu yasa ya dafe kansa tamkar wanda ke fama da ciwon kai, tabbas ransa na basa cewa Ba fuskarsu hosana bace a fuskar yarinyar, ya sawa ransa cewa tsananin Son da yake yi ma yaran ce da ƙaunar da yake yi musu da kuma kewarsu da yayi ya sanya Fuskarsu keyi mashi  gizau afuskar yarinyar daya gani ayanzu, tabbas Omar yayi Confusion ɗin kansa, ya rikita tunaninsa bazai ta6a yarda da abunda idonsa ke nuna masa ba akan Waccan Yarinyar…………….

   Ajiyar zuciya yasaki aransa yana ƙara jin cewa bai kyauta musu ba da baije ya dubo su, amma ya shirya zuwa gobe domin ya duba su, 

  Yana gama wannan tunanin ya dawo Downstairs da sauri ya sauko a lokacin Sehrish harta gudu zuwa ɗakinta saboda ta tsorata,

  Abbansu na ganinsa yace “Omar wai lafiya meya faru ne? Naga duk ka rikice lokaci ɗaya ko don saboda wannan yarinyar ne da ka gani yanzu,” 

  Zama Omar yayi yana cewa “No ba haka bane Abba just there’s something that confused me but am ok now,” 

  Ajiyar zuciya Azmee tasaki jin yace babu komai, ci gaba da yin breakfast ɗinsa yayi anatse but still his brain was confused, 

Zuwa wani lokaci kowa ya Kammala breakfast ɗinsa sai daga bisani Sehrish ta fito suka shiga gyara gidan ita da azmee,

______________________________________________Farkawa hosana tayi da wata irin matsananciyar yunwa don hada kukan ta dama ita bata da jumurin yunwa ko kaɗan, hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hosana ke ta faman rusa kuka gashi sai faman lallashinta takeyi amma sam taƙi yin shiru sai ta runƙa cewa “baki ji yadda nake ji bane, babu komai acikina kamar zan mutu,” runtse ido jahad tayi sam tarasa abunyi, yanke shawara tayi kawai tafita waje taga ko zata samo mata abinci, tun da taga akwai visitors dake zuwa wurin marasa lafiya wata’kil ko Allah ya haɗa ta dana gari su sam mata abinci taba Hosana, tashi tayi cikin sauri tana cewa “Hosana ki jira dan Allah ki daina kukan nan, yanzun nan zan dawo,” shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,

fita jahad tayi tana faman zarya a asibitin wurin nema musu abincin da zasu ci, taimako yayi ƙaranci a arayuwar nan domin kuwa duk wanda jahad ta tunkara da niyar ya taimaka musu sai suce suma bazai ishe su ba, ga abinci nan tana gani haje-haje agaban wasu sun baje suna ci amma tarasa wanda zai taimaka musu koda da rabin plate ɗaya ne, 

   A ƙarshe da ta gaji da yawon neman taimakon abinci sai ta samu wuri abakin wata bishiya ta zuƙunna tare da kifa kanta tana faman shesshekar kuka, babban tashin hankalinta yarda zata tunkari hosana tace mata bata samo masu komai ba, 😥

Download>>> Macijine Complete Document

tana cikin wannan zuƙunnan Motar hafsat tashigo asibitin da gudu tayi parking ɗinta a harabar ajiye motocinsu, fito wa tayi fess da ita tayi wanka ta canza kayan jikinta yanzu tsadaddiyar atampha ce riga da skirt ajikinta sun bi shape ɗin jikinta very tight, ta ɗaure kanta da ɗan kwalin sannan ta yafa veil a shoulder ɗinta, ƙarasawa tayi ta buɗe back seat ɗin Motar hannu takai ciki ta ɗauko kwando mai ɗauke da kayan abincin da tazo masu dashi, bayan ta rufe motar ta wuce ciki sam bata lura da Jahad ba, haka itama jahad bata ɗago ba balle taganta,. 

   tana ƙokarin shiga cikin ɗakin da aka kwantar da hosana dr yafito suka ci karo, ganin ta yasa ya saki fara’a yana cewa” ke ce mai kula da wannan patient ɗin ko”?

  Hafsat tace “Yeah its me,”

  Dr yace “yawwa tun dazu take faman kukan yunwa gashi naga ba kowa tare da ita, amma tun da kin zo yakamata ki kula da ita, sannan idan ta kammala cin abincin akwai magungunanta dana ajiye wanda za’a bata,”

   hafsat ta amsa mashi da cewa “Shikenan dr ngde ssae,” tana faɗin hakan ta wuce ciki shi kuma ya nufi cikin asibitin,

   Samun hosana tayi tayi kukan tayi mai isarta har ta gaji, tana zaune saman gadon ta kife kanta saman guiwowinta, jin muryar hafsat yasa ta ɗagowa cikin sauri,

  Ae tana ganinta ɗauke da food stuffs a basket nan take jikinta ya soma rawa kaf-kaf kamar kura taga nama, 

   Da murmushi hafsat ta isa ta zauna gefen gadon kusa da Hosana tana cewa “Ya jikin naki”? Murya na rawa Hosana tace”da sauƙi sosai” ita burinta tafara zuba ma cikin ta abinci,

  Ajiye basket ɗin hafsat tayi ƙasa, sannan tasanya hannunta ta curo flask mai ɗauke da haɗaɗɗen ruwan tea ta ajiye sa, Cup ta curo guda biyu ne a haɗe, ɗaya ta ɗauka ta bude flask ɗin ta tsiyaya mata shi sannan ta zuzzuba mata madara da bornvita aciki har sai da yayi kauri, sannan ta miƙa ma hosana, kar6a tayi takai bakinta tana sha da hanzari har wani sauti maƙoshinta keyi kwat-kwat , kusan sau 3 tana shanye wa hafsat na ƙara mata, bayan ta kammala ta ciro kula mai ɗauke da Chips haɗi na musamman, ta zuba mata a plate, miƙa mata tayi tana cewa “ki ci a hankali saboda ciwon ki,” hosana ta amsa da “toh” Turawa kawai take yi abaki kamar zata haɗa da plate ɗin duka, bayan tagama dashi hafsat ta zuba mata fruits a plate ta bata, shima tashiga sha kamar kamar me,

   “Ina Ƴar uwarki take ne ban ganta ba”? Hafsat ta tambaya yayin da take kallon hosana,.

   Hosana tace “tun ɗazu ta fita tace na daina kukan yunwa na jira ta, har yanzu bata dawo ba,” 

  Murmushi hafsat tasaki tare da cewa “Nasan bai wuci taje nema muku abunda zaku ci bane, May be tayi tunanin na tafi nabarku ne,” 

  suna cikin magana jahad ta turo ƙopar a galabaice take tafiya saboda tsabagen yunwa, ƙafafunta har harɗewa suke yi tana tafiya kamar wadda tasha Codine,

    shigowa tayi tana faɗin”hosana sai dai kiyi haƙuri wlh bansamu komai ………’ ganin hafsat yasa ta dakatawa da maganar cikin mamaki take kallon su, hannu tasanya tana murza idonta don ta tabbatar wa kanta cewa ba mafarki take yi ba, sakin hannunta tayi tana ƙare masu kallo, Expecially  hosana data gani sai faman cusa fruits takeyi abakinta wanda hafsat ta zuba mata,

Download>>> Macijine Complete Document

Wani irin farin ciki ne ya cika jahad har batasan lokacin da ta fashe da kuka ba Don tsabar murna,

  tashi hafsat tayi ta ruƙo hannunta tana cewa “Kukan ya isa haka, tun da gani na zo ko? Halan kinyi tunanin na gudu ne nabarku shiyasa kika fita nema muku abinci”? ta tambaya tana kallon jahad dake faman shesshekar kuka tace”Nayi tunanin kin tafi kin barmu ne shiyasa na fita, ashe zaki dawo,”.

   ɗan murmushi hafsat tasaki tare da cewa “Am so sorry nayi laifi ban sanar muku ba, da asuba na tafi gida, nayi sallah bacci ya kwashe ni without my knowing bayan na tashi ne kuma na wuce kitchen na shirya muku breakfast dana kammala shine nayi wanka na fito,”

  bayani take yi jahad na kallonta tsananin mamaki ne yakamata ganin yadda lokaci guda Hafsat ta canza musu gaba ɗaya tamkar ba ita ba, tazama wata mutuniyar kirki lokaci guda ANYA?

  jan hannunta hafsat tayi ta zaunar da ita gefen hosana sannan tashiga saving ɗinta abincin tare da miƙa mata, sannan ta haɗa mata tea itama, bayan ta kammala ta samu wuri saman plastic chair ɗin dake facing gadon da suke tana kallonsu,

  A hankali Jahad ke kurbar tea ɗin tana ɗan kallonta, bakomai take jin tsoro ba fa ce kada ace Hafsat tasanya musu POISON acikin abincin da takawo su,tun da dama tasan sarai neman hanyar da zasu kawar dasu suke yi, kuma wannan ce hanya mafi sauƙi, yadda hafsat ɗin ke kallonta ido cikin Ido yasa Jahad ƙara jin wani irin Tsoro aranta nan take hannunta ya shiga yin kerma kaf!kaf!kaf! 😳😳😳

Wani shu’umin Murmushi Hafsat tasa ki tana cewa “nasan mai ki ke tunani JAHAD, tabbas abunda kike tunani gaskiya ne, POISON nasanya muku a abincin saboda wannan ce hanya mafi sauƙi da zamu kawar da ku acikin arayuwarmu, kuma zaku huta da wahalar zaman duniya,” 

   Hankali atashe Jahad ta Zazzare ido waje jikinta na kerma tace “POISON!!!!!!!!!!!!!! “

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button