Uncategorized

Maganin Hips Cikin Sauki Ga Mata

 Mata da yawa suna bukatar suga hips dinsu ya ciko tun basuyi aureba saboda yanda yake daukar hankalin da namiji to ballantana amarya Wanda ita tafi cancanta data samu hips domin daukar hankalin oga.

 kuma yana kara saka namiji yaji ya gamsu da matarsa Kafin kiyi amfani da maganin karin hips Abinda ya kamata kifara sani shine yaya yanayin jikinki yake? Ya dace ki kara hips?

 Abinda nake nufi shine akwai mace Wanda taketa kiba ita wannan batada matsakar wannan koda yake ana samu wacce kibarta tafi yawa ta sama.

Karanta: Amfanin Zogale Ga Mata Domin Ƙarin Ni’ima

 • Akwai kuma mace wacce take batada kiba amma tanada breast (nono) sosai to irin wadannan zaka samesu basuda wadataccen hips irinsu sune ya kamata surinka kokarin amfanida maganin karin hips amma mace wacce batada nono sosai tun tana budurwa ana samunta da hips itama wannan babu ruwanta da wani maganin karin hips To idan kinga ya dace ki kara hips ga hanyoyin da zaki bi in Allah ya yarda za kiyi nasara.

 (1) Ki samu dankali na hausa ko na turawa ki dafashi saiki yanyankashi sannan ki dakashi ki zuba acikin nono ko madara peak

 sannan ki zuba zuma ki gaurayashi sosai kisha zaki iyayinsa sau3 a kowanne sati tabbas wannan hadin har ni ima yana karawa mace.

 (2) ko kuma ki samu kankana ki yanyankata da gwanda itama ki fereta sai kabewa itama ki yankata kokumba (gurji) shima haka da tumatur ki yanyankashi ki wankeshi duk kiyi markadensu waje daya ki tace ruwan kinasha sau2 a rana Shima wannan yana kara hips sannan yana karawa mace ni ima.

 Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa,ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.

 Masana a wannan fannin, sun bayar da shawarwarin amfani da Abarba, Ayaba, Gwanda, Kankana, Zuma, Madarar ruwa. A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a Dan kara zuma da madara.

 Bayan wannan, mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa,ki yi kwadonsu, ki rika ci.

 Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai.

Karanta 👉: Amfanin Zogale 100 A Jikin Dan Adam

 MAGANIN ()-() KARIN KUGU (HIPS)

 ✔» man kanunfari

 ✔» man zaitun

 ✔» man hulba

 Zaki hade su guri daya ki rinka shafawa idan za’a kwanta barci za su ciko.

 KARIN KIBA

 Ki samu Zuma mai kyau ki hada da man hulba waje guda. kullum a sha cokali 2 Duk 10m kafin cin abinci.

 RAGE KIBA

☆ Habbatus-sauda 1 cokali

 ★ Zuma farar saka 1 “,”

 ☆ Dakakkiyar tafarnuwa.

 ➢ Ruwan zafi Rabin Kofi.

 Sai a zuba a gauraya sosai a sha kafin a kwanta barci a sha kafin a yi Karin kumallo, sau biyu 2 a Rana .

 ___________________________________________

RAGE TUMBI 

✯ Man habbatus-sauda

◦ Man albasa.

❀ Man jirjir

✿ man danya.

Sai a zuba Zuma a ciki a rinka sha sau uku a Rana wannan hadin yana rage tumbi sosai.

Back to top button